tsaye Inaya ta fito rike da hannun Aleenah , ita a tunaninta Aleesherh ce dan ta ga kaya iri daya su ke sanye da kuma da ta shiga ta tarda dayar konce , kawai sai ta yi tunanin ko Aleenah ce barci ya dauke
sai da ta karaso wajen shi sannan ta mika mishi hannunta ta ce " za ku iya tafiya "
shiru ya yi bai ce mata komai ba ya na kallon Aleenah da ga kassa har sama
sannan ya kalli Inaya ya ce " to ai wannan Twins din ta ce "
cikin rudu Inaya ta kalli Aleenah irin kallon nan na rudu
sai a lokacin Aleenah ta samu ta yi magana ta ce " shi ne na ke son na fada muku amma ba ku saurare ni ba , Aleesherh ce ke konce "
wata yar karamar dariya Inaya ta yi kafin ta saki hannunta ta ce " to ni ta ya zan sani , duk ku na kama "
" no , ba su kama , wacen ta fi wannan manyan idanu " Fadin Prince
kare mishi kallo da kyau Inaya ta yi , kenan har ma ya san manyan idanu ne da ita ?
" shikenan , Aleenah , je ki kira ta please " Inaya ta fada
ba musu Aleenah ta juya ta koma bedroom din su
saman gadon ta Haye ta na fadin " Alee , tashi mijinki ya zo neman ki "
murya a sanyaye ta ce " Aleen , cikina ke yi min ciwo wlh , ba zan iya tashi ba "
" don Allah tashi , kin ga in ku ka tafi cen shi zai kula da ke , yanzu dai tashi "
wani dan karamin tsaki ta ja kafin ta mike zaune ta sauko da kafafunta kassa sannan ta sauko da ga saman gadon ta fara takawa a hankali kanta na sunkuye
riko hannunta Aleenah ta yi su ka fito bedroom din
tun da su ka fito corridor din Prince ya tsare ta da ido , da ga ganin tafiyarta ya san ba lafiya ba
a haka har su ka karaso wajen sannan Aleenah ta saki hannunta ta na cewa Inaya " ga ta momy "
murmushi kawai Inaya ta yi kafin ta riko hannunta ta mikawa Prince
ba musu ya riko hannunta ya juya ba tare da ya ce wa kowa komai ba ya fice parlourn
sai da ya fita sannan RIANNA ta bushe da dariya ta na fadin " baby , gaskiya ba ku yi wa Prince adalci ba "
dariya kawai Inaya ta yi kafin ta ce wa Aleenah " koma ki konta , sai da safe "
gyada mata kai kawai Ta yi kafin ta juya ta koma cikin bedroom din su , Inaya kuma ta fice ta tafi wajen babynta
bangaran su Prince kuma , kai tsaye part din su su ka nufa , su na tafe ta na matse mishi hannu , ya na ji amma bai tanka mata ba
ko da su ka shiga part su ya wuce da ita bedroom din ta
su na shiga ya saki hannunta ya juyo su na fuskantar juna ya ce mata " what's wrong with you ? "
kamar za ta yi kuka ta ce mishi " Cikina ke yi min ciwo "
" wani abu ki ka ci wanda bai da kyau ? "
girgiza mishi kai ta yi a hankali
slowly ya matso dab da ita , ya kai hannu saman cikinta
dam ta ji zuciyarta ta buga har sai da ta dago kai ta kalle shi
a hankali ya fara shafa mata cikinta , a sanyaye ya ce mata " don't worry zai daina , yanzu shiga ki yi wanka sai ki konta "
ya na gama fadar haka ya janye hannunsa ya juya zai fita
da sauri ta riko hannunshi ta na fadin " please kar ka tafi , ban iya barci ni kadai ba " ta fada ta na marairaice mishi fuska
a hankali ya kwace hannunsa sannan ya tako a hankali ya zauna bakin gadonta, ya fara latsa wayarsa
ta na ganin ya zauna ta saki wani dan karamin murmushi ta taka a hankali ta shiga toilet dan ta yi wanka
โคโ ๐๐๐๐๐โโค
________________
แดสแด สแดแดแดสษด แดา แดxษชสแดแด แดสษชษดแดแด
*WANNAN LITTAFIN NA BIYA NE , WANDA YA SHIRYA BIYA ZAI IYA TABO WANNAN NUMBER +22795577612 , โฆ500 NE KUDIN SHIGA PAID GROUP ฦIN*
[ PAGE ___ 16 ๐๐โค ]
Jim kadan ta fito sanye da bathrobe , ta shiga dressing room ta shirya cikin kayan barcinta white color , sannan ta fito
har yanzu bai motsa ba da ga zaman da ya yi
a hankali ta karaso gefensa ta zauna sannan ta kontar da kanta saman shoulder din sa
wata boyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya juyo a hankali ya kalle ta ya ce " me ya faru ? cikinki har ya daina ciwo ? "
" no har yanzu ya na yi min ciwo "
" to tafi ki konta , karfe 12 fa ta yi "
" na sani , ina son na tambaye ka wani abu "
" minene ? " ya fada ya na meda kallonsa kan wayarsa ya ci gaba da latsawa
sai da ta dauki lokaci kafin ta ce mishi " ina so ka fada min yadda zan yi na mallaki zuciyarka "
" ni ma ban sani ba " ya fada a takaice
" please Baby , ka fada min mana " ta cikin yar shagwaba
shiru ya yi bai ce mata komai ba , shi kansa bai san abun da zai ce mata ba , da ya san amsar da zai ba ta da ya fada mata , asali ma shi abun da ya ke ji cikin zuciyarsa har yanzu ya kassa tantance shi , tabbas ya na jin ta cikin zuciyarsa shi ya sa ma ya iya banbanta su cikin sauki ita da Aleenah , kuma ya ke sake mata su na magana , amma shi har yanzu ba ta yi wani abu ba da zai ce son ta ne ya ke cikin zuciyarsa saboda wannan abun , shi dai kawai ya san ya damu da ita saboda amanarta a ka ba shi
ya yi nisa duniyar tunaninsa ya ji kawai ta janye kanta da ga saman shoulder din sa , a hankali ta ida Hayewa saman gadon ta konta ta juya mishi baya ta saki kuka kassa kassa
ya na jiyo sautin kukanta ya saki wani dan karamin tsaki cikin zuciyarsa ya na fadin " shikenan yanzu ni an hada ni da wani aikin "
a hankali ya juyo ya na kallon ta ya ce " kukan me ki ke kuma ? "
" to ba kai ne ba na tambaye ka ka kyale ni "
" okay , zan fada miki yanzu daina kukan nan "
da sauri ta mike zaune ta na murmushi ta ce " shikenan na daina " ta fada ta na kai hannu ta na goge hawayenta
sai da ta zauna sannan ya ce mata " okay , abu na farko da ya kamata ki sani shi ne ba na son takura , dan haka duk shirmen da za ki yi ki ka ce za ki takura min zan bar miki gidan, kuma ko Cutie da Daddy ba za su san in da zan je bare ma su ce na dawo "
nan take murmushin da ke saman face din ta ya bace jin ya kira sunan Cutie
kamar za ta yi kuka ta ce " wai wacece Cutie ? har yanzu ba ka fada min ba "
" Cutie is My momy , Cutie shi ne sunan da Daddy ke kiran ta da shi har mu ma mu ka dinga kiran ta da haka , shikenan ? kin ji dadi ? "
wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta gyada mishi kai , sai yanzu ta tuno lokacin da su ka tafi wajen Malik ta ji ya furta sunan Cutie , to hankalinta bai kawo ba
ta yi nisa duniyar tunaninta ta jiyo Muryarsa ya na fadin " yanzu konta ki yi barci "
noke mishi kafada ta yi ta na fadin " no , ka bar ni na ci gaba da kallon ka mana , wai an taba fada maka ka na da kyau ? "
" an sha fada min " ya fada ya na fara latsa wayarsa
ci gaba da magana ta yi ta na fadin " har so na ke safiya ta yi domin na ci gaba da kallon kyakyawar fuskarka mai yaye dukkan kuncin da damuwar ruhina , please ka juyo ka kalli da fararen idanunka ma su sheqi da haske kamar wani sashi na wata "
shi dai bawan Allah ya yi zaune ya na sauraron ikon Allah , har ya fara tambayar kansa anya ba wani abu ta ke sha ba ? yadda ta ke zaune ta na irin wadanan kalaman ko tsoro ba ta ji , ko shi ne ba zai iya ba kai tsaye haka , ta wani bangaran kuma ya na jin dadin kalamanta ya na ga kamar yabon sa ne ta ke yi
haka dai ta yi zaune sai zuba ta ke mishi, shi kuma ya na aikinsa da wayarsa , bai da labari har barci ya yi gaba da ita
sai da ya ji wajen ya yi tsit ya tabbatar to barci ya yi gaba da ita
a hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya juya ya kalle ta , ta na barci cikin konciyar hankali , jelar gashinta ya bazun mata saman face
a hankali ya kai hannu ya janye mata gashin ya zubawa face din ta ido , in kowa ganin ya ke su na kama ita da Aleenah shi ba ya ganin wannan kamar bai san me ya sa ba ,
sai da ya dauki lokaci ya na kallon ta kafin ya tashi a hankali ya kashe lamps din dakin ya kunna bedside lamps sannan ya fito dakin ya janyo mata kofar ya tafi tashi bedroom din
โชINAYA ๐๐
bayan ta baro part din MALIKAT INAS kai tsaye nasu part din ta koma , a nan floor na uku ta tardo Malik , ya na konce cikin bedroom din su , sanye da kayan barcinsa ya zubawa ceiling ido kamar mai tunanin wani abu
wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta tako a hankali ta nufi toilet ta shiga
wanka ta yi ta fito daure da towel a kirjinta ta na rike da wani dan karamin towel ta na goge gashin kanta
har yanzu shi dai ya na yadda ta bar shi ko motsi bai yi ba
nan take jikinta ya ba ta akwai abun da ke damun sa
ajiye towel din hannunta ta yi saman dressing mirror sannan ta tako a hankali ta zauna bakin gadon ta kai hannu saman face din sa
wata nanauyar ajiyar zuciya ya sauke ya na lumshe idanunsa a tare ya daura hannu saman nata
cikin sanyin murya ta ce mishi " baby , tunanin me ka ke yi haka ? "
wani cool murmushi ya saki kafin ya ware idanunsa ya kalle ta ya ce " nothing , just ina tunanin jarabar da Prince zai yi wa yarinyar nan kafin ya fara sake mata , na san za ta sha wuya "
wata yar karamar dariya Inaya ta yi kafin ta ce " kar ka damu ba wata azabar da za ta sha , saboda ya na son ta , ni fa da ita da Twins din ta kassa gane su na yi , shi kuma kallo daya ya yi musu ya gane wacce ce matarsa "
wata yar karamar dariya shi ma ya yi kafin ya ce " kamar ba ki san halin Prince ba , ko ya na son ta ba zai yarda da hakan ba ,
hannu ta kai ta fara shafa kansa ta na fadin " ai halinka ya dauko , kar ka damu in dai ba ta cika kunya ba cikin sauki za ta shawo kansa , kuma kai ma ka san halin Prince abu guntu ke jan hankalinsa , bare in sanyi ya kama shi ko ba ya so sai ya neme ta " ta kai karshen ta na wata yar karamar dariya
dariya shi ma ya yi kafin ya kai hannu ya janyo ta jikinsa ta fado saman chest din sa , ya na kallon cikin idanunta ya ce " wane sanyi kuma ? ki ba shi kwana biyu kadai , zai fara .. " ya kai karshen ya na dago kansa a hankali ya manna mata kiss a wuya
wata yar karamar dariya ta yi ta kai hannu a hankali ta fara balle button din rigar barcinsa , sannan ta ida Hayewa gadon ta konta a gefensa
wani dan karamin murmushi ya saki kafin ya juyo su na fuskantar juna , nan take labarin ya sauya a ka hau sabon wassa
( ๐ด๐ด ni kuma na dauki takarduna na fito dan barci na ke ji )
WASHE GARI โ
โชALEESHERH ๐๐
da addu'ar barci a bakinta ta farka da ga barcinta , slowly ta ware idanunta ta fara bin dakin da kallo , ta ga ita kadai ce cikin dakin
wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta sauko da ga saman gadon , nan ta ga wayarta ajiye saman bedside drawer
cikin rudu ta kai hannu ta dauke ta dan ita ta na tune ta bar ta a part din MALIKAT INAS
kunna wayar ta yi ta ga karfe 7 da mintina 12
wani cool murmushi ta saki kafin ta fara takawa a hankali ta nufi curtain din da ke fuska kofar shigowa dakin , ta janyo curtain na gefen dama ta rufe rabin glass din , dan wajen ya rage haske , sannan ta nufi toilet ta shiga
Jim kadan ta fito sanye da bathrobe ta tsaya gaban dressing mirror ta fara kallon Lotion din da ke sama , ta zabi guda ta shafa sannan ta shiga dressing room
after some minutes ta fito sanye da wata gown pink colour mai kyau , ta sha ruwan stone , ta saki gashin kanta har tsakiyar baya , da wasu dan kanana sun zubo mata a gaban goshi , sai tashin qamshi ta ke
kai tsaye bedroom din ta fito ta fara bin wajen da kallo , kofofi shidda ne ta gani a wajen kuma duk su na rufe , kawai sai ta nufi hanyar fita corridor din ta fito
ta na fitowa ta ga wata maid ta baro dining table ta na shirin komawa kitchen
da sauri Aleesherh ta taro ta
ba musu ta tsaya ta dawo ta zube saman guyiwowinta a gaban Aleesherh ta na gaishe ta cikin girmamawa
wani dan karamin murmushi Aleesherh ta saki kafin ta ce " mike tsaye don Allah , kar ki sake min irin wannan abun , ba kin girme ni ba "
ba musu ta mike tsaye kanta a sunkuye ta ce " haka ne ranki ya dade , na girme ki amma matsayin mu ba daya ba "
" shikenan , ya sunanki ? "
" Asmeet , ranki shi dade "
" Asmeet , don Allah akwai kitchen a wajen nan ? "
" Eh ranki ya dade "
" mu je ki gwada min please "
gyada mata kai kawai Asmeet ta yi kafin ta fara takowa ta yi gaba
kai tsaye su ka nufi hanyar fita wajen su ka fito harabar part din , su na fitowa su ka yi dama nan ta ga wata door ta zallar glass , su na isa door din ta bude
nan ta ga kitchen din cike da maids har wajen goma , kitchen din a share a goge kamar ka ci abinci a kassa , sai aiki su ke yi
duk su na ganin Aleesherh kowace ta tsaya cak su ka sunkuyar da kai su na gaishe ta kai ka ce ita ce MALIKAT INAYA
da murmushi a face din ta ta amsa musu , sannan ta fada musu abun da ta ke bukata ta shirya wa Prince breakfast , sannan ta ce musu da ga yau duk abincinsa ita za ta shirya shi
da to kawai su ka amsa mata sannan su ka fiddo mata abubuwa da ta fada
cikin nitsuwa ta fara hada mishi breakfast da coffee cike da so , bayan ta kammala ta shirya komai saman tray sannan ta dauki kayanta ta fice ta bar su su ka ci gaba da aikinsu
da sallama a bakinta ta shigo parlourn duk da ba ta san in ya na nan ko ba ya nan
ta na shigowa ta gan shi zaune saman sofa sanye da kananan kaya , wandon jeans da rigarsa duk Blue color , ya na rike da wayarsa da hannu guda ya na latsawa
Princess ta na konce gefensa ta tada kai da laps din sa , hannunta da hannunsa na sakale cikin na juna , ta lumshe idanunta da wani dan karamin murmushi a face din ta
Dam Aleesherh ta ji zuciyarta ta buga ganin su a haka , har wasu ruwa su ka ciko mata a ido , kishi ta rufe mata ido ta kassa ganin kamar da ke tsakanin prince da princess , dan kamar an tsaga kara su ke , yadda ta ke da Aleenah haka ya ke da Princess , Sai dai ita kawai mace ce
nan take jikinta ya yi sanyi , ta sunkuyar da kai , ta karaso wajen ta nufi dining table ta ajiye tray din sannan ta juya ta shiga corridor da gudu
duk wani takunta ya na sane , kawai ba ya son magana ne
sai da ta shiga bedroom din ta sannan ya ce wa Princess " kin gani ko yanzu kin saka ta kuka ? to sai ki je ki ba ta hakuri dan ni ba