wata yar karamar dariya Princess ta yi kafin ta saki hannunsa ta mike zaune ta na fadin " Prince , babynka ta cika kishi , yanzu ba ta ga kamar da ke tsakanin mu ba ? "
" duk dai laifinki ne , yanzu tashi ki je "
ba musu ta tashi ta na dariya ta nufi corridor ta shiga
ta na isowa bakin kofar dakin Aleesherh ta jiyo Muryarta ta na kuka
a hankali ta shiga cikin dakin ta nade hannayanta a kirji ta zuba mata ido
sai kuka ta ke baiwar Allah ta boye fuskarta cikin pillow
sai da ta kare mata kallo sannan ta tako a hankali ta na fadin " to shi kuma kukan na minene ? ko ni ma ba na da izinin zama kusa da dan uwana ? "
ko sauraron ta Aleesherh ba ta yi ta ci gaba da kukanta
a hankali ta karaso bakin gadon ta zauna ta kai hannu ta dafa shoulder din Aleesherh ta na fadin " za ki daina kukan nan ko sai raina ya baci ? "
sai a lokacin Aleesherh ta sauke wata yar karamar ajiyar zuciya ta goge face din ta cikin pillow din , ta dago kai a hankali ta kalli Princess
ta na zama Princess ta saki wani dan karamin murmushi ta ce mata " kukan kuma na minene ? ni fa sister din ki ce , ta ya za ki yi kishi da ni ? "
" sister ? " ta fada cikin rudu
" yeah , i'm Nailah or Princess , Twins din Prince , ko ba ki ga mu na kama ba ? " ta kai karshen ta na daga mata gera
ita sai yanzu ta samu damar kallon ta da kyau kuma gaskiya su na kama har hazel eyes din su , a sanyaye ta ce mata " amma ni bai fada min ba ya na da twins ba "
" shi fa Prince bai cika magana a kan rayuwarsa ba , da kin tambaye shi ya na da sister ko brother zai fada miki , amma in ba ki tambaye shi ba ba zai fada miki ba , now tell me what's your name ? "
" Aleesherh "
" Aleesherh , sunan ya yi dadi , yanzu tashi mu je ki yi breakfast ko ba ki jin yunwa ? "
mikewa tsaye ta yi ta nufi toilet ta shiga
wanke face din ta ta yi sannan ta fito , Princess na tsaye bakin kofar dakin ta na jiran ta
a hankali ta karaso wajen , riko hannunta Princess ta yi sannan su ka fito bedroom din
a tare su ka fito su ka fito parlour , nan su ka tardo shi zaune a dining table ya na shan coffeen da ta hada mishi
ba karamin dadi ba ta ji ganin ya na shan coffeen har ta saki wani dan karamin murmushin gefen fuska
dining table din su ka karaso Princess ta zauna gefen Prince , Aleesherh kuma ta zauna saman chair din da ke fuskantar tashi ta na kallon shi
su na zama ko Junior ya shigo parlourn ya na sallama ya na sanye da suit blue
da murmushi a face din sa ya karaso wajen ya na fadin " yau kuma a nan a ke breakfast ? "
" Good morning Junior " Princess ta fada ta na murmushi
chair din da ke gefenta ya janyo ya zauna ya na fadin " me ki ke yi a nan tun da safe haka ? a ka je ki ka tardo su cikin wani yanayi fa ? " ya kai karshen ya na daga mata gera
wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " to ni ina ruwana , kuma Cutie ta ce min Prince na nan shi ya sa na taho wajensa "
" shikenan tashi mu tafi " ya fada ya na mikewa tsaye
cikin rudu ta ce " mu tafi ina kuma ? ba wajen Prince ka zo ba ? ni tafiya zan yi "
girgiza mata kai ya yi ya na fadin " no , ni dama ke na zo nema , akwai wani sabon restaurant da ya bude cikin gari zan so ki raka ni "
" da gaske ? su na saida ice cream ? " ta fada cikin yar shagwaba
" to ai shagon ice cream ne baki daya , shi ya sa na ce mu je ki raka ni " ya fada dan ya san halinta da mugun son ice cream
da sauri ta mike ta sunkuyo a hankali ta manna wa Prince kiss a kumatu ta riko hannun Junior su ka bar wajen , sai murmushi ya ke ya samu abun da ya ke so
Prince kuwa ko a jikinsa sai shan coffeensa ya ke , Aleesherh kuma ta tsare su da ido ta na murmushi
sai da su ka fita sannan ta ce wa Prince " Baby , amma wannan mijinta ne ko ? "
slowly ya dago sexy eyes din sa ya kalle ta , murya cen kassan makoshi ya ce " kin ga na yi miki kama da baby ? "
" to ai ni ba wancen babyn na ke nufi ba , ina nufin masoyi haka , ko ka fi son na kira ka da Honey ? "
shiru ya yi bai ce mata komai ya dauki wayarsa ya fara latsawa
ci gaba da magana ta yi ta na fadin " Honey , ba ka ba ni amsa ba , kuma yaushe za mu tafi honey moon ? "
wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya ce " wai me na ce miki jiya ? "
marairaice mishi fuska ta yi kafin ta ce " sorry , ni just ina son mu yi hira ne "
shiru ya yi bai ce mata komai ya ci gaba da aikinsa , ya ga alamun wannan bakinta bai iya shiru ba , da ma Aleenah ya fadawa Al-Sayid ya aura mishi dan ya ga ta fi wannan sanyi
ya yi nisa duniyar tunaninsa kawai ya ji ta zauna a kujerar da Princess ta tashi , a hankali ta kai lips din ta saman kumatunsa ta manna mishi kiss
nan take ya ji wani bakon yanayi cikin zuciyarsa lokacin da Princess ta yi mishi kiss ba abun da ya ji , yanzu kuma ita da ta yi mishi har wani shock ya ji cikin jikinsa
ita kuwa ba ta ma san ya na yi ba , ta janyo tray din breakfast din da ta shirya mishi ta fara cin kayanta dan ta lura coffeen ne kadai ya ke bukata
slowly ya dago kai ya kalle ta , ta na cin abincin cike da nitsuwa nan take ya tsargu da kallon ta , har ya manta aikin da ya ke da wayarsa , haka ita ma sarai ta ke lure da shi amma ba ta tanka ba , tun da ya ce ba ya son takura yanzu kam za ta fara yi mishi fuska kamar lokacin da su ke Yemen
_______________________________________________
_ PAID BOOK
*WANNAN LITTAFIN NA BIYA NE , WANDA YA SHIRYA BIYA ZAI IYA TABO WANNAN NUMBER +22795577612 , β¦500 NE KUDIN SHIGA PAID GROUP ΖIN*
[ PAGE ___ 17 ππβ€ ]
sai da ta koshi sannan ta sha ruwa kadan , ta dauki Tray din sannan ta juyo ta kalle shi ta ce " ina son na tafi wajen Aleenah "
gyada mata kai kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba
murmushi kadan ta yi kafin ta juya ta bar wajen rike da tray din , sai da ta meda shi kitchen sannan ta baro part din
shi ma ta na fita ya mike ya baro part din
kai tsaye Garden ya nufa kassan daya da ga cikin runfuna ya zauna dan yanzu wajen ya kara girma , sun kara runfunan saboda shan iska , zama ya yi saman sofa three seaters , ya fara latsa wayarsa
ya na a haka Azmat ta fito da ga cikin part din Diya za ta tafi wajen Nesrine da ke part din MALIKAT INAS
ta na hango shi ta saki wani dan karamin murmushi ta fassa tafiya part din Malikat Inas , ta juya ta nufi garden din
da Sallama a bakinta ta shigo wajen ta na sakin murmushi
da ga in da ya ke ko dago kai bai yi ba , amma sarai ya ji ta , sallamarta ma cikin zuciya ya amsa mata ita
a hankali ta karaso saman sofar da ya ke zaune ta zauna , ta na kallon shi ta ce " Prince , shi ne ka dawo amma ko nema ta ba za ka yi ba ? ko ba ka yi kewar sister d'in ka ba ? " ta kai karshen ta na turo dan karamin bakinta
ko sannu bai ce mata ba ya ci gaba da aikinsa
" amma Prince wannan karan tare za mu koma U.S ko ? ina son na tafi U.S ko so guda ne "
wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya dago kai ya kalle ta ya ce " Azmat , please let me , aiki na ke "
shagwabe mishi fuska ta yi ta na turo dan karamin bakinta ta ce " Amma Prince , yanzu fa wajen one year rabon da ka gan ni , na kawo maka hira shi ne ka ke kora ta ? ni gaskiya babu in da zan je "
wani siririn tsaki ya ja kafin ya kauda kai ya ci gaba da aikinsa , ta na neman ta takura mishi gaskiya
ita ma ba ta ce mishi komai ba ta matso ta na lekon wayarsa duk da ba ta san abun da ya ke ba
shi kuwa ya yi shiru bai ce mata komai ba dan ya san in ya yi mata magana za ta kara takura mishi , gwara ya yi shiru ko za ta kyale shi in ta na kallon cikin wayar
βͺALEESHERH ππ
bayan ta baro part din su kai tsaye part din MALIKAT INAS ta nufa
da sallama a bakinta ta shigo parlourn , ta tardo Nesrine da Tesnim zaune su na hira , MALIKAT INAS kuma ta na cikin bedroom din ta , RIANNA ta na cen ta na fama da Faaz
da sauri Nesrine ta taro ta ta na fadin " Aleesherh ? da ga ina ki ke haka ? ko koro ki Prince ya yi ? " ta fada dan duk gashin kanta a waje ya ke babu ko Alkyaba a saman kayanta
cikin rudu ta fara bin jikinta da kallo ta na son ta ga minene su ka gani
sai da ta gama dube duben ta ba ta ga komai ba ta juya ta kalle su ta ce " Momy , ni ban ga komai ba "
" Aleesherh , ke fa yanzu matar aure ce , ko ba ki duba matsayin mijinki cikin masarautar nan bai kamata ki fito haka ba , at least sai ki saka Alkyaba da ga sama in ba ki son saka veil , dubi gashinki duk ya na waje " Fadin Tesnim
sai a lokacin ta tuno ashe babu veil a kanta , nan take kunya ta kamata ta sunkuyar da kai , murya a sanyaye ta ce " sorry momy , mantawa na yi "
wani dan karamin murmushi Tesnim ta saki kafin ta mike tsaye ta na fadin " jirani a nan " ta fada ta na takawa ta nufi corridor ta shiga
ita dai Aleesherh ta na tsaye kamar wata gunki , sai wassa ta ke da yatsun hannunta
ta na tsaye a haka Tesnim ta fito da ga cikin corridor rike da wata Alkyaba ta MALIKAT INAS , white color mai kyau da laushi da ga gani ta auduga ce , an yi mata zanen tambarin masarauta Saudiya kanana da zare pink color har wani kyali su ke
a haka ta karaso wajen Aleesherh ta saka mata Alkyabar da kanta ta janyo hular ta saka mata sannan ta ce " wannan Gift ne , ki rike ta a wajen ki , kin ga kayan da Princess ta kai miki cikin bedroom din ki ? "
gyada mata kai kawai Aleesherh ta yi kafin ta taka a hankali ta nufi corridor
sai da ta shiga sannan Tesnim ta koma ta zauna su ka ci gaba da hirarsu ita da Nesrine
Aleesherh kuma bayan ta shiga corridor kai tsaye bedroom din Aleenah ta nufa ta shiga ta na sallama
nan ta tardo ta zaune tsakiyar gadon ta na latsa wayarta cikin konciyar hankali
da gudu Aleesherh ta nufi gadon ta Haye ta rungume Aleenah
wata yar karamar kara Aleenah ta saki , a tsorace ta ke fadin " Alee , lafiya ? me ya faru ? "
wata yar karamar dariya Aleesherh ta yi kafin ta sake ta , ta koma ta zauna gefenta ta na fadin " ba komai , kawai na ji dadin ganin ki ne "
" Alee , irin wannan dirowar sau ki sa zuciyata ta buga "
" i'm sorry , ya ki ke ? "
" Fine , ina ki ka baro mijinki ? "
" ya na part din mu , please tashi mu fita , ina son na ga yanayin masarautar "
" ni ma ina so na ga yanayin masarautar , amma ina tsoron mu bace gaskiya "
saukowa da ga saman gadon Aleesherh ta yi ta na fadin " tashi mu je , kuma akwai mutane cikin masarautar ba za mu bace ba , please tashi mu tafi " ta kai karshen ta na riko hannunta
wata yar karamar dariya Aleenah ta yi kafin ta sauko da kafafunta kassa , ta dauki veil din ta saman bedside drawer ta yafa , sannan ta mike tsaye su ka fito bedroom din , Aleesherh na rike da hannunta
su na fitowa parlour Tesnim ta tare su ta na tambayar su ina za su je
Aleesherh ce ta ba ta amsa da cewa " momy , ina son mu tafi garden ne , idan ba damuwa ? " ta fada murya a sanyaye
sai da ta saki wani cool murmushi sannan ta ce mata " shikenan , amma kar ku yi nisa , akwai bangaran da bai kamata ku je ba "
" to momy " ta fada ta na murmushi sannan ta ja hannun Aleenah su ka fita
sai da su ka fita sannan Aleenah ta ce mata " wai ya a ka yi ki ke sanin amsar da za ki bawa mutum duk lokacin da ya yi miki tambaya ? ni gaskiya tsoro na ke ji "
" sai kin fara fidda wannan tsoron , in ki na nuna tsoro kowa ma taka ki zai yi .......... " ba ta karashe maganarsa ba idanunta su ka sauka saman Prince da Azmat , ta na zaune gefensa ta na kallon cikin wayarsa ta na sakin murmushi , nan take ta ji zuciyarta ta yi mata wani mugun zafi kamar ta je ta shako Azmat duk da ba ta san ta ba
ganin ba ta ida maganarta ba ya sa ta juya ta kalli wajen da ta tsare da ido , nan ta ga abun da ta ke kallo
riko hannunta ta yi ta na fadin " Alee , wacece yarinyar cen zaune kusa da prince ? kuma bai ce mata komai ? ko dai sister din sa ce ? "
girgiza mata kai Aleesherh ta yi ta na fadin " ko ma wacece za mu sani , taho mu je " ta kai karshen ta na fara takawa
da sauri Aleenah ta taro ta ta na fadin " no Alee , bar shi har ku koma part din ku , kar ya fadi wani abu da zai tozarta ki a gabanta "
murmushi mai dan sauti Aleesherh ta yi kafin ta ce " tozarci ? ni ? har yanzu ba a yi wanda zai ce zai tozarta ni a gaban wata sakara ba , duk da ina son shi , in ya ce zai bata ni a gabanta , ba zan kyale shi ba "
( πππ a yi dai a hankali Aleesherh , Prince ya wuce duk in da ki ka ajiye shi )
" please ki bari , kar ki janyo mana magana "
tsaki Aleesherh ta ja kafin ta riko hannun Aleenah ta janyo ta su ka nufi garden , sai rokon ta Aleenah ta ke amma ta ki sauraron ta , sai da su ka kusa isowa wajen runfar sannan ta daina , ta saisaita nitsuwarta
a tare su ka yi sallama su na shigowa kassan runfar
sai a lokacin Azmat ta dago ta kare musu kallo da ga sama har kassa sannan ta amsa musu sallamarsu
zama Aleesherh ta yi ta janyo Aleenah su ka zauna a tare saman sofar da ke fuskantar ta su Prince
sai da ta zauna sannan Aleesherh ta ce " ina fatan ba mu takura muku ba ? "
" sorry , but who are you da za ki zo ki zauna mana haka kamar gidanku ? "
wani kyawatacen murmushi Aleesherh ta saki kafin ta ce " I don't know too , in ki ka samo amsar sai ki zo ki fada min , ni ma zan so na sani " ta kai karshen ta na kallon Prince
hararrar ta sama da kassa Azmat ta yi kafin ta ja wani dan karamin tsaki , su na zamansu ta wani zo ta katse musu nitsuwarsu
Aleesherh kuwa ko a jikinta , a hankali ta dafa laps din Aleenah , a sanyaye ta ce mata " shikenan , komawarki , ni ma part di na zan koma yanzu "
cikin rudu Aleenah ta ke kallon ta , alamun ba ta gane abun da ta ke nufi ba
da wutsiyar ido ta mata alamun ta bar wajen
wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta ce " shikenan , but next time in kin