sannan ta mike zaune ta sauko da ga saman gadon ta na fadin " zan je na shiga wanka sai na shirya mana breakfast "
gyada mata kai kawai ya yi ya na kallon ta ba tare da ya ce komai ba
murmushi kawai ta yi kafin ta juya ta fice bedroom din
ko da ta fita ya tashi jiki a sanyaye ya nufi toilet ya shiga ,
wanka ya yi ya fito sanye da bathrobe ya tsaya shafa lotion , sannan ya wuce dressing room
jim kadan ya fito sanye da wasu kananan kaya wandon Jeans da Shirt , kai tsaye bed din sa ya nufa ya Haye ya kwanta ya na kallon ceiling , ya daura hannu saman forehead ya lumshe idanunsa
kamar kullum yau ma su na aikinsu cikin nitsuwa su na hira
yanayin da ta ke tardo su kullum ya na matukar burge ta
cikin nitsuwa ta karaso wajen su ta na fadin " Ku dai kullum ku na hira , kamar kun ci hatsin kasuwa "
tsit su ka yi lokaci guda su ka ja da baya su na gaishe ta cikin girmamawa
da murmushi a face din ta ta amsa musu , ta karaso cikin kitchen din ta ta na bin wajen da kallo kamar ta na neman wani abu
fada musu abubuwan da ta ke bukata dan hada banana bread din da farko
dalilin da ya sa ta ke haka , kafin su baro Yemen sai da mahaifiyarta ta ja mata kunne a kan duk abun da zai faru ta dinga shirya wa mijinta abincinsa da kanta , hakan zai kara soyayyar da ke tsakanin su , zai ga ta damu da shi sosai tun da har za ta iya daukar lokaci ta hada mishi abinci da hannayanta , shi ya sa kullum ta ke share lokaci ta shirya mishi komai cike da so , bare ma ita kanta ba ta jin dadin cin abun da a ka shirya ba a gabanta ba
sai da ta gama hada banana bread din ta saka cikin oven
janye hannayanta Aleenah ta yi ta na fadin " ta ya ki ka san ni ce ? ko idanu gare ki bayan ido ? "
girgiza mata kai ta yi a hankali ta na fadin " No , just na ji a jikina ke ce , me ya faru ? "
" breakfast din mu ne , ni da Honey , ban saka da ke ba , dan haka koma "
" ai sai ki fada min minene ki ke hadawa na ji wani qamshi na tashi "
sai da ta kammala ta shirya musu sandwich din saman tray ta hadawa Prince coffee cikin mug ta ajiye , da fruits , sannan ta koma wajen oven dan ta fiddo banana bread din
slowly Aleenah ta juya ta kalle ta ta ga ta juya mata baya , kuma duk Maids din su na tsaye waje guda sun sunkuyar da kai
a hankali ta kai hannu cikin aljihun rigarta ta fiddo wata yar karamar bottle fara
( 🤔🤔🤔 Tak ko irin wadda Izayn ya bawa Izzat a prison , ya a ka yi ta dawo hannun Aleenah kuma ? )
da sauri ta bude bottle din , ta zube ruwan da ke ciki cikin coffeen Prince , sannan ta meda bottle din cikin aljihunta
har ta kai hannu za ta saka yatsa cikin mug din ta juya Aleesherh ta juyo
cikin nitsuwa ta ce mata " me ki ke shirin yi ? "
Dam ta ji Zuciyarta ta buga ta na zaro idanu , wasu yawu ta hadiye kafin ta janye hannunta ta na fadin " umm , dama dan na ji in bai yi sanyi ba ne "
" abun da na hada yanzu ko two minutes ba a yi ba , taya zai yi sanyi ? "
" Haka ne , na tafi garden , ki same ni a cen idan kin gama kula da babynki " ta fada ta na takawa ta fice kitchen din
Prince ya na kwance kamar dai yadda na baro shi da hannu saman forehead , ya lumshe idanunshi
abun da ya tada mata hankali shi ne Izzat da ta gani saman shi cikin iska , ta na kwance ta zuba mishi ido ta na sakin murmushi
wata razananiyar kara Aleesherh ta saki kamar makoshinta zai fado
karar da ta yi ne ya sa Izzat bacewa bat lokaci guda
Prince kuma ya ware idanunsa da sauri ya mike zaune
da sauri ya diro da ga saman gadon ya nufe ta da sauri ya na fadin " Beautie ? lafiya ki ke kara haka ? "
bai ce mata komai ba ya rungumo ta jikinsa ya na dan bubuga bayanta dan shi kansa bai san abun da zai ce , tabbas ya ji nunfashin mutum saman face din sa , kawai ya yi tunanin ko ita ce ta dawo ta na kallon shi , shi ya sa bai yi motsi ba , to in ba ita ba ce , wanene ? dan shi ya na da tabbacin ya ji nunfashin mutum , hakan na nufin da gaske aljana ce ta gani
ita dai ba ta ce komai ba ta shige jikinsa kawai ta na sauke ajiyar zuciya a jere dan ba karamar tsorata ta yi ba
" Beautie , tunaninki ne kawai , ba wata aljana , ina ta ke to ?babu komai ? ni ban ji komai ba samana " ya fada cikin son kontar mata da hankali
kuka ta sakin mishi ta na girgiza kai ta ce " Honey da gaske aljana ce na gani , ni gaskiya tsoro na ke ji "
a hankali ya sunkuyo da kansa ya sauke lips din sa saman nata ya cabko tongue din ta ya fara sha kamar ya samu sweet
ya san haka ne kawai zai sa ta yi shiru dan a tsorace ta ke ba kadan ba , abun da ta gani ya yi matukar tsorata ta
cikin sanyin murya ya ce mata " ba abun da zai faru da ke in har ina raye , yanzu mu je mu yi breakfast , na san ki na jin yunwa ko ? "
gyada mishi kai ta yi a hankali alamun Eh
a hankali ya sunkuyo ya manna mata kiss a forehead sannan ya riko hannunta su ka baro bedroom din
ya na rike da hannunta har su ka baro corridor su ka nufi dining room in da ya hango tray din da ta ajiye
wata yar karamar dariya ta yi kafin ta kontar da kanta saman shoulder din sa ta ce " ba dole na iya ba , ba na son barin dama ko da guda ce ta mallake zuciyarka "
a hankali ya zagayo da hannunsa a bayanta ya na fadin " kin riga da kin mallake ta my Beautie , sai dai in zuciya biyu gare ni ban sani ba "
dariya kawai ta yi ta lumshe idanunta
girgiza mishi kai ta yi ta na fadin " No my Honey , ci abun ka , ka sha coffee tun bai yi sanyi ba "
bai ce mata komai ba ya dauki coffeen ya fara sha
ita kuma ta dauki sandwich guda ta fara ci , ta na kwance a jikinsa
sai da ya kammala sannan ya janye hannunsa da ga saman bayanta ya ajiye mug din ya mike tsaye ya na fadin " Na gode my Beautie " ya kai karshen ya na manna mata kiss saman forehead
sannan ya juya ya nufi parlour ya zauna ya na jiran ta kammala ci
bai yi one minute da zama ba ta mike ta dauki plate din fruits da na banana bread ta ajiye saman table din , ta dauki sauran ta na fadin " Honey , zan meda dishes din Kitchen "
gyada mata kai kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba , ita kuma ta fito parlourn
ta na fita kawai na ga ya saki wayarsa , jini ya fara fitowa da ga hancinsa
a hankali ya kai hannu ya taba jinin dan ya tabbatar da gaske jini ne ya ke ji
hankalinsa bai gama tashi ba sau da ya fara tari ya na furzo jini a tare , ya ji wuyansa ya rike kamar an shake shi ya kassa nunfashi
ya na ciki wannan halin Aleesherh ta dawo parlourn ta na murmushi
ta na ganin halin da ya ke ciki ta saki wata yar siririyar kara ta nufe shi da gudu ta na fadin " Honey , me ya faru ? me ya same ka ? "
murya a disashe ya ce mata " kiro min Cutie " ya fada a rarrabe
girgiza mishi kai ta shiga yi ta na kuka ta na fadin " Honey , don Allah me ke faruwa ? duba jini ka ke zubarwa , wayo ni na shiga uku "
da karfi ya dago kai ya ce mata " je ki kira min Cutie na ce ! " ya fada da karfi har sai da ta razana ta rumtse idanunta
ba shiri ta sake shi ta tashi da gudu ta fice parlourn ta na kuka
ta na fita kawai na ga ya lumshe idanunsa ya yi baya ya fadi saman sofar ko motsi ba ya yi
ko da ta karaso bakin kofar shiga part din ta tsaya ta na tambayar Malik
daya da ga cikin su ne ya ce mata ya na floor na uku
da gudu ta shiga building din ta nufi lift kai tsaye a floor na uku ya tsaya
ya na budewa ta shigo parlourn da gudu ko sallama babu
da sauri Malik da Inaya da ke zaune a kassa saman carpet su na breakfast su ka mike tsatsaye
cikin rudu Inaya ta ce mata " Alee ? me ya faru ? lafiya ki ka yi irin wannan shigowar ? "
wasu yawu ta hadiye kafin ta ce " Momy , momy , shi ya ce na kira ku , ban san abun da ke faruwa ba "
sai da kofar lift din ta rufe sannan Aleesherh ta samu damar ce mishi " Daddy , ban san abun da ya same shi ba , mu kammala breakfast ne na tafi kai dishes kitchen kawai na tardo ya na tari ya na furza jini har ta hancinsa " ta fada ta na kuka hawaye na zubo mata bibiyu
da sauri Malik ya daga kafa ya fita har ya na hadawa da gudu
har ya iso kofar fita building din kawai ya jiyo Muryar Inaya ta na kwalla mishi kira da karfi
cak ya tsaya ya juyo , nan ya gan ta zaune a kassa cikin lift din da Aleesherh kwance a kassa kanta na sama cinyar Inaya da alamun ta sume
wani dan karamin tsaki Malik ya ja kafin ya juya ya fice da gudu dan shi hankalinsa na waje guda wajen babynsa
bayan ya fita ne ya ke ce wa dayan security ya je ya dauki Aleesherh ya kai ta Word room
ko da su ka fito kai tsaye word room su ka nufa
shi dai Faaz ya na zaune cikin garden ya na kallon duk abun da ke faruwa , ya na murmushi har da fruits a gabansa ya na sha ban san da ga ina fruits din su ke ba
bangaran Malik kuwa , kai tsaye part din Prince ya nufa , ya shigo parlourn kamar an turo shi da ga sama
idanunsa na sauka kan Prince ya ji zuciyarsa ta yi wata muguwar bugawa har sai da ya ga dishi dishi lokaci guda
da sauri ya nufe shi ya zube saman guyiwowinsa , ya kai hannayansa dukka biyu saman face d'in Prince ya fara jijiga kansa ya na fadin " Nayel ? Nayel open your eyes , please ka tashi don Allah , kar ka tafi ka bar ni , please my Nayel wake up "
lokaci guda idanunsa su ka ciko da ruwa kamar zai yi kuka
da sauri ya mike tsaye ya kai hannu ya goge ruwan tun kafin ma su zubo , ya sa hannu ya dauki Prince ya saba shi saman shoulder sannan ya fito part din da shi ya nufi word room
(😿😿abun da ya faru ya tuno min lokacin da Rouksar ta zubawa Malik poison , amma shi a lokacin kunfa ce ta fito da ga bakinsa , yanzu Prince jini ne , duk yadda a ka yi abun da Aleenah ta zuba cikin coffeensa ne ya yi wannan abun , yanzu ya za ta kare ? ga kuma Aleesherh ta sume ? 🏃♀️ bari na yi nan to , mu hadu gobe )
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng