x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 15 - NAYEL THE RETURN OF EXILED PRINCE

  • 42001 words
  • 45000 words
  • Out of 89550 words

Category: Love Stories

Views 397

14 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
ga ya saki spoon din , ya kankame kansa waje guda
da sauri ta mike ta nufe shi ta na fadin " are you okay ? ba dai allergy gare ka ba ? "
a rarrabe ya ce mata " no , sanyi na ke ji ? "
" sanyi kuma ? to ai nan ba wani sanyi a ke yi ba , ko dai ba ka da lafiya ? " ta kai karshen ta na kai hannu saman kumatunsa
nan ta ji jikinsa ya yi mugun zafi har sai da ta janye shi da sauri
a rude ta ce mishi " ka san ba ka da lafiya me ya sa ka taho , ai sai ka min text ka ce ba ka da lafiya zan gane "
" na san kin dauki lokaci wajen shirya wannan abun , in ban zo ba , ba za ki ji dadi ba "
maganarsa ba karamin dadi ta yi mata ba cikin zuciyarta , hakan na nufin ya damu da ita ?
dafa shoulder din sa ta yi ta na fadin " shikenan , tashi mu koma ciki ka konta "
kassa amsa mata ya yi kawai mikewa tsaye ya yi a hankali ya na dafa table , har rawar jiki ya ke riko hannunsa ta yi ta taimaka mishi su ka koma cikin
kai tsaye part din su ta meda shi , Junior na ganin su ya yi sauri ya mike ya na fadin " Prince , me ya faru ? "
Aleesherh ce ta amsa mishi da cewa " sanyi ya ce ya ke ji , kuma jikinsa ya yi zafi sosai "
" i'm sorry " ya fada ya na riko hannun Prince ya taimaka mishi ya konta saman gadon ya janyo duvet ya rufe shi har zuwa wuya
dama shi ya tafi ya kwatantawa Aleesherh ba zai iya zuwa ba , cikin sauki sanyi ke kama shi
a hankali ta karaso ta tsaya bakin gadon ta na fadin " bari na hada maka hot chocolate , za ka ji sauki da ga baya "
girgiza mata kai ya yi ya na fadin " no , kar ki damu kanki , na gode " ya na gama fadar haka ya janyo duvet din ya rufe jikinsa baki daya ya konta saman shoulder
cikin sanyin murya Junior ya ce mata " don't worry , nan da five minutes zai dawo dai'dai , za ki iya tafiya dare ya yi , sai da safe "
a sanyaye ta ce mishi " sai da safe " da ga haka ta juya ta fice
sai da ta fita sannan Prince ya fiddo kansa ya na kallon Junior ya ce " duk laifinka ne , sai ka tafi ka kawo lemon "
bushewa da dariya Junior ya yi kafin ya zagayo daya gefen ya konta ya na fadin " ya a ka yi ma ku karaso nan da sauri haka , na zata sai ka zuba mata love sannan ku dawo "
tsaki kawai Prince ya yi kafin ya meda kansa cikin duvet din har ya fara nadamar bin maganar Junior ya tilla

▪ALEESHERH 👑💞

bayan ta baro part din su Prince kai tsaye part din su ta koma ta na sakin murmushi ita kadai
ta na shigowa ta tardo Aleenah konce saman gadonsu sanye da wata yar karamar rigar barcinta pink color
karasowa Aleesherh ta yi cikin dakin ta nufi toilet ta shiga ta yi wanka, Sannan ta fito ta shirya ita ma cikin irin rigar barci irin ta Aleenah amma ita white color
ta karaso bakin gadon ta konta gefen yar uwarta ta na fadin " Aleen , barci ki ke ? "
" No " ta fada a takaice
wani dan karamin murmushi Aleesherh ta sakin mishi mata kafin ta ce " kin san wani ? yau Prince ya nuna min ya damu da ni shi ma , da ga yanzu ki ma zan nuna mishi na damu da shi ,may be da ga haka har ya fara so na "
shiru Aleenah ta yi ba ta ce mata komai ba ta zuba mata ido
kallon ta Aleesherh ta yi ta na fadin " lafiya ki ka yi shiru ? ko ke ma ba ki da lafiya ? , na lura kwana biyu duk yanayin ya yi sanyi "
" Alee , na san ki na farinciki da wannan auren za ki auri wanda zuciyarki ke so , kuma ina farinciki da hakan sosai ma , just ina tunanin abun da zai faru in a ka yi aurenku , hakan na nufin za ki tafi ki bar ni , ban san ya zan yi ba in ba ki nan " ta kai karshen kamar za ta yi kuka
nan take Aleesherh ta ji jikinta ya yi sanyi , ita duk ta manta da wannan maganar , yanzu in a ka yi auren dole ta rabu da Aleen din ta , ba ta san ma in za su sake haduwa in ta koma Saudiya
da sauri ta matso ta rungume ta dan ba ta da abun da za ta ce mata ta ji sanyi cikin zuciyata , ita kanta zafin rabuwarsu ta ke ji cikin zuciyarta
sannu sannu har barci ya yi gaba da su a haka

____________________________________________________________
WASHE GARI ⛅

Tsaye ta bakin kofar part din su Prince , ta na rike da tray din breakfast din su sai knocking ta ke amma ba su bude mata ba
har ta fidda rai kawai ta ga an bude mata kofar
sai ta ga Junior ne tsaye ya shirya cikin suit black color
wani dan karamin murmushi ya sakin mata kafin ya ce " Sorry , ina saka kaya ne , barka da safya "
" Good morning , na kawo muku breakfast ne " ta fada ta na mika musu tray din
hannu ya kai karba ya na mata godiya ya juya ya koma cikin dakin
a hankali ta biyo bayansa ta na fadin " ya jikinsa ? "
" tun da har kin zo nan , me zai hana ki duba shi da kanki ? kin ga ni yanzu fita zan yi , na bar miki amanarsa , ki kula da shi please , amma sai kin yi hakuri wlh kamar baby ya ke in ba ya jin jikinsa "
wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " zan gwada "
dariya shi ma ya yi kafin ya fice part din
sai da ya fita sannan ta tako a hankali ta tsaya bakin gadon , ta kai hannu a hankali ta janye duvet din jikinsa, har yanzu ya na sanye da jacket din sa ta jiya
wata doguwar mika ya yi ya na daga hannayansa, kafin ya juya, murya a disashe ya ce " Cutie , ki kyale ni barci na ke ji "
wani dan karamin murmushi ta saki ta na kallon shi gaskiya ba karamin tafiya da ita ya yi ba , specially ma sunan Cutien da ya ce , ga wata sanyayar Muryarsa cen kassan makoshi , yanzu kenan haka kullum za ta dinga tashi da wannan zazzakar Muryarsa ? gaskiya ya kamata ta shawo kansa kafin a yi auren
hannu ta kai a hankali ta dan bubuga shoulder din sa ta na fadin " wake up safiya ta yi "
wani dan karamin kukan kura ya yi kafin ya zabura ya mike tsaye saman gadon lokaci guda har sai da ta firgita ta na ja da baya
sai da ya dauki lokaci a tsaye kafin ya diro da ga saman gadon ya na kallon ta ya ce " coffee "
da hannu ta nuna mishi table dan ba ta da bakin magana
a hankali ya juya ya fara takawa ya nufi sofa , ya zauna ya janyo table din gabansa ya dauki mug din coffee ya fara sha
ajiyar zuciya ta sauke kafin ta fara takawa ta fice part din ta bar shi nan ya na shan coffeen
sai da ya shanye coffeen nan sannan ya tashi ya shiga toilet
jim kadan ya fito sanye da bathrobe ya wuce dressing room ya shirya cikin suit white color , ya dauki wayoyinsa da laptop din sa ya fice , kai tsaye Daular ya baro baki daya

▪MASARAUTAR SAUDIYA 👑🔥
▪INAYA 👑🕊

kamar dai kullum yau ma ta na a parlourn MALIKAT INAS , yau dai Malik ya raka Diya Fada
Faaz da RIANNA kuma su na zaune a kassa saman carpet ta na rike da book ta na koya mishi karatu dan jiya ma sai da ta kira wata prof din ta koya mishi amma ta tsere ba ta ma ce musu komai ba
MALIKAT INAS kuma ta na zaune ta na kallon su
su na a haka su ka jiyo Muryar Princess da karfi ta na kwallawa MALIKAT INAS kira
a tare duk su ka juya su na kallon kofar shigowa parlourn Inaya har sai da ta ji zuciyarta ta buga shikenan jaraba ta zo
kowa ya yi zugum ya na jiran shigowarta
da sallama a bakinta ta shigo parlourn ta na fadin " I'm here "
da sauri RIANNA ta mike ta nufe ta ta rungume ta tsam ta na dariya
mikewa ita ma MALIKAT INAS ta yi ta nufo su ta rungume su dukka biyu
dariya Princess ta yi ta na fadin " Ammie , momy , na yi kewar ku sosai "
RIANNA ce ta amsa mata da cewa " Mu haka our Princess , mun yi kewar ki over "
" to a sake ni " ta fada cikin shagwaba
ba musu su ka sake ta , MALIKAT INAS ta riko hannunta ta na fadin " gaskiya wannan karan a part di na za ki zauna "
har ta bude baki za ta yi magana ta jiyo Muryar Faaz ya na fadin " momy , ki kyale ta ki zo ki koya min ni " ya fada cike da shagwaba
kare mishi kallo da kyau Princess ta yi kafin ta kwace hannunta da ga cikin na MALIKAT INAS ta karaso gabansa ta tsugunna ta na kallon shi da kyau
sai da ta kare mishi kallo sannan ta ce wa RIANNA " momy , wanene wannan kuma ? " sai da ta yi wata yar karamar dariya sannan ta ce " kar ki damu zan fada miki da ga baya "
" okay " ta fada a takaice kafin ta kai hannu ta murde mishi kunne ta na fadin " saurare ni da kyau , a nan gidan ni ce baby , in har na kama ka ka na yi wa momyna shirme da shagwaba , sai na sa an cire maka kai , ka ji ni ko ? "
kuka ya sakin mata ya na fadin " sake min kunnena , momy ta sake min kunne "
da karfi Princess ta ce " yi min shiru ko na mare ka a wajen nan ! " ta fada ta na matse gera alamun ba wassa
ai ba shiri ya shanye kukansa ya na kallon ta
" Princess , na san halinki ba ki da kirki , please kyale shi , me kuma ya yi miki ? " RIANNA ta fada ta na karasowa wajen su , ta kwace kunnen Faaz da ga cikin hannun Princess , da sauri Faaz ya mike ya fada jikinta ya na kuka
mikewa tsaye Princess ta yi ta na fadin " ki kyale ni momy na koya mishi zama , tun da na zo yanzu , zan gyara wa kowa zaman sa a masarautar nan "
" sannu to , ke kuma a wa , za ki wuce ciki ko sai na tashi gare ki ? " Inaya ta fada ta na tsare da ta idanu
turo dan karamin bakinta ta yi ta na fadin " ni ai ba wajen ki na zo ba , ki kyale ni , kuma ina Daddyna ya ke , ina son ganin sa "
" Daddynki ya na fada , ki yi hakuri zai zo har nan ya gan ki , yanzu shiga ki yi wanka " Fadin MALIKAT INAS
gyada mata kai kawai ta yi kafin ta juya da sauri ta fice dan kar ma MALIKAT INAS ta taro ta dan ita a part din Daddynta za ta zauna
sai da ta fita sannan Inaya ta ce " Allah ya shirya ki , wlh Ammie yarinyar nan sai kun dinga saka ta a addu'a , ni ban ma san ya zan yi da ita "
dariya Malikat Inas ta yi kafin ta ce " kar ki damu , Junior zai yi maganin ta "
dariya kawai Inaya ta yi ba tare da ta ce komai ba
ita dai RIANNA sai rarrashin Faaz ta ke yi , sa va gani ta na mugun son shi tsakanin ta da Allah , da ta san wanene ainahin Faaz na san zuciyarta za ta karaya ba kadan ba
sai da ya daina kukunsa sannan ya dago da ga jikinta ya na fadin " momy zan je toilet "
da to kawai ta amsa mishi kafin ta sake shi ta koma ta zauna saman sofa shi kuma ya nufi corridor
kai tsaye bedroom din sa ya shiga , ya turo kofar ya saka mata security
wani dogon tsaki ya ja ya na fadin " kaiii wannan wace yar iska ce kuma ta shigo gidan ? , ba komai zan yi maganin ku daya bayan daya "
ya na gama fadar haka ya karaso tsakiyar dakin ya tsaya ya lumshe idanunsa ya fara motsa lips din sa ya na wani karatu mara dadin ji ni kaina ban san abun da ya je fada ba
a hankali na ga kawai ya kara tsawo yanayin jikinsa ya sauya baki daya ya koma mace
( 🤔🤔 ban gane ba ? ni fa abun ya fara ba ni tsoro, na gudu ko na tsaya ? in na gudu na za mu san ko wacece ba , in kuma na tsaya na san ba yi kwana ba yau dan ganin abun nan ya fara fin karfina 😨😨😨 amma bari na tsaya mu ga )
slowly na ga ta ware idanunta farare kal kamar madara kwayar cikinsu Blue mai kyau , ta na da dogon hanci kamar pencil da dan karamin bakinta gashinta baki kirin har tsakiyar bayanta , ta na sanye da wando da riga kamar dai wanda su je jikin Faaz da farko kafin ta komo haka , ta hadu
gaskiya ba laifi cikakiyar balarabiya, a shekaru na san za ta yi 28 to 29 years haka
wani dogon nunfashi ta ja kafin ta bude baki da wata zazzakar muryarta ta ce " Haba , har na ji dadi "
ta na gama fadar haka ta shiga fadin " Queen , ina son magana da ke ? Queen ? " ta fada cikin sanyin murya
a hankali na ga wutar dakin ta fara kunnuwa ta na mutuwa , a hankali ta tako ta nufi dressing mirror ta tsaya dai'dai lokacin duk lamps din dakin su ka mutu
Mirror din ya fara wani haske kadan kawai na ga inuwar wata kujera kamar ta Royal chair haka , na ga sahun mutum zaune a kai amma na kassa gane macece ko namiji , amma da ga jin sunan da budurwar nan ta fada na Queen tabbas mace ce
a haka na jiyo Muryarta mara dadin ji ta na fadin " ba na ce ki daina min irin wannan kiran ba ? "
wani dan karamin tsaki ta ja kafin ta ce " sorry momy , to ba ke ce ba mutum na son magana da ke sai ya shiga wani rite , ni ban da wannan lokacin "
" Izzat , ba na son shirme , kiran me ki ke min ? " ta fada da dan karfi
" Queen , yarinyar Malik ta zo yau , ya ki ke so na yi da ita ? kuma yanayin ta ya nuna sam ba ta da kirki , kar ta gana min azaba , kuma kin sani ba na bari a taka ni "
" No , ki kyale ta , ki bi tsarin mu kawai , yanzu ki tabbatar kin zubawa MALIKAT INAS poison ta mutu kafin a shiga watan azumi "
" MALIKAT INAS kuma ? why zan kashe ta ? "
wani dan karamin tsaki Queen ta ja kafin ta ce " MALIKAT AL'UMU ta riga da ta mutu MALIKAT INAS kadai ta yi wa Malik saura , in ta Mutu kin ga sai birkice , ba zai iya tantance abun da ke gabansa ba , a nan ne plan din mu na gaba zai fara ? "
janyo chair Izzat ta yi ta zauna ta na kallon mirror din ta ce " Big bro kuma fa ? har yanzu fa ban jin kin ce zai shigo plan din ba , ga kuma Izyan da ke prison , matsalar ma yanzu Prison din sun meda ta cen karshen masarautar , da ta na cikin Daular da na fito da shi "
" kar ki damu , Big bro din ku zai fito da shi idan ya zo "
da sauri ta mike ta na fadin " momy, big bro zai zo ? how ? "
wani dan karamin tsaki Queen ta ja kafin ta ce " Izzat , Izzat , ki maida hankali kan abun da ya kawo ki , in har ta dalilin ki plan di na ya baci ba abun da zai hana ni kashe ki duk da ni na haife ki "
wani dogon tsaki Izzat ta je kafin ta koma ta zauna ta na kauda kai ta ce " an gama ya shugaba "
komai Queen ba ta ce mata ba ta bace bat da ga cikin mirror din
nan take duk lamps din dakin su ka kunnu
wani dan karamin tsaki Izzat ta ja kafin ta mike tsaye ta na fadin " ni gaskia na gaji da wannan aikin , ga shi duk lokacin da na tambaye ta minene manufarta amma ba ta fada
End Ads