x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 2 - NAYEL THE RETURN OF EXILED PRINCE

  • 3001 words
  • 6000 words
  • Out of 89550 words

Category: Love Stories

Views 385

14 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
Hakan na nufin Nayab bai mutu ba , Diya bai mutu ba " mama ta fada a dan razane ta na zaro idanu

shiru Diya ya yi bai ce mata komai ba , ya kassa cewa komai

yanzu me Malik zai yi in ya ji labarin Nayab bai mutu ba , zai sa a neme shi ko zai bar maganar ?
to wa ya sace Nayab ? dan wannan sace shi a ka yi in a na da Niyyar medo shi da ba za a saka doll cikin tissu din ba

🤔🤔 WATA SABUWAR KUMA , NAYAB BAI MUTU BA , KUMA DA ASWAD A JIKINSA

😱😱😱😱 KAR FA A JE HAFSAT TA ZAGAYO TA DAUKE SHI


GASKIYA SAI NA JE NA SHA MALTINA ,


Cikin rudu Diya ya ce mata " Mama , ya kamata mu koma mu fadawa Malik , ya sa a fara cigiyar Nayab , in har ya fadi hannun mugayen mutane to tabbas mu na cikin tsaka mai wuya "

gyada mishi kai kawai ta yi kafin su juya , a tare su ka bar wajen da gudu a tare
kai tsaye motarsa su ka koma , su ka shiga su ka bar wajen da gudu

kai tsaye Daular Saudiya su ka koma , ko da su ka koma part din Malik su ka wuce
a nan floor na uku su ka tardo shi zaune saman Royal chair din sa , ya na rike da hannayansa , kamar dai jiran su ya ke yi


da sallama a bakinsu su ka shigo parlourn , a hankali ya motsa lips din sa ya na amsa musu sallamar

da sauri Diya ya ce mishi " Malik , akwai matsala , Bab...... "
cikin nitsuwa Malik ya katse shi da cewa " Get out ! " ya fada a sanyaye

da sauri Mama ta ce " don Allah ka tsaya ka saurari abun da za mu fada maka , wlh Nayab bai mutu ba , kuma da Aswad a jikinsa , in a ka je wani makiyinka na kusa ya tsintse shi wlh akwai matsala "

a hankali ya mike tsaye , ya riko hannayansa a baya ya ce " shikenan , ku je neman sa , amma ba da yawuna ba , da hannuna na dauke shi kuma ban ji rai a tare da shi ba , mama kin san halin yarinyarki , na riga da na ce mata Twins ne , yanzu in ta ji labarin babu na ukun ya za ta ji ? ke ma kin san da ga ni har ku ba za ku ji da sauki ba , shi ya sa na binne wannan maganar , don Allah na roke ku ku bar maganar nan , tun wani bai jiyo ba , please "

" amma Nayab ya na raye , Ya ke ko so mu yi da hakan ? " Fadin Diya

" za ka iya tafiya neman sa in ka na so , amma ni dai na san Nayab ya koma ga mahallacinsa , kuma cikinku wani ya yi wa Cutie wannan maganar ban yahe masa ba " ya na gama fadar haka ya juya ya nufi corridor ya shige

da kallo su ka raka shi har sai da ya shiga , sannan mama ta juya ta kalli Diya ga na marairaice fuska
tun kafin ta ce wani abu ya riga ta cewa " ya ce za mu iya tafiya neman sa , dan haka ni zan je neman sa in shi ba zai iya ba , mu tafi mam " ya fada ya na juyawa zai bar wajen
ba musu mama ta bi bayansa su ka bar part din baki daya





_______________________________________________





AFTER SOME YEARS





UNITED STATE OF AMERICA ( U.S.A )




WASHINGTON DISTRICT OF COLOMBIA



a hankali ta ke sauko stair din gidan , ta na sanye da wata gown pink color mai wani belt fari da ga tsakiya , rigar mai kananan hannu ce , amma gaskiya ta hadu , babu veil a kanta , ta saki wani smooth hair baki kirin , ya zubo mata a shoulder har tsakiyar baya kai da ga gani ka san ba kananan kudi a ke kashe mishi ba

budurwar kyakyawa ce gaskiya kai ka rantse sarauniyar kyau ce , a shekaru za ta kai 30 haka , amma yanayin jikinta ka ce yar 18 ce , breast din ta ya na tsatsaye kamar an hira balan-balan , shape din ta kamar na coca cola abun dai Masha Allah , fara ce kal kamar ka taba jini ya fito , jinin larabawa , tak tak Malik a jinsin mata har shape din lips din shi kamar heart , da Hazel eyes din sa , ba dan kar ku ce na yi karya ba da sai na ce wannan har ta fi Malik kyau , bare kuma rainon Ice cream da Madara , ga kuma yanayin garin US kai ka san abun sai Masha Allah kawai


a haka ta ke sauko stair din cike da nitsuwa , kai tsaye parlourn gidan ta nufa ta zauna saman sofa , ta kai hannu saman center table ta dauki wayarta , ta fara latsawa

ta yi wajen two minutes zaune a haka kafin ta juya ta kalli kofar kitchen , ta na turo dan bakin nan nata kamar pen , cike da shagwaba ta fara fadin " Cutie ! ! , please yunwa na ke ji , tun dazu kin kyale ni a nan , sai yunwa ta kashe ni sannan ki rasa mai yi miki tausa " yanayin da ta yi maganar kai ka ce yar shekara 8 ce ta yi maganar


shiru na ji ba a amsa mata ba , kukan shagwaba ta saki ta na fadin " Cutie ! Cutie ! yunwa na ke ji pleaseeeee "

ta na gama rufe bakinta ba ga Inaya ta fito da ga kitchen , ta na rike da plate a hannu guda , da wani dan bowl a dayan
gaskiya US ta zauna mata sosai , ita da Princess ka ce yaya da kanwa ne ba diya da uwa ba ,
dama hakan na faruwa in mace ta haifu da karancin shekaru , specially in ta haifi mace dan ta fi namiji saurin girma , kuma lokacin da ta haife su ba ta wuce 15 years na dole a yi musu kallon yaya da kanwa yanayin jikinta tak irin na Princess , ita ba rama ba kuma ita ba kiba ba , dai-dai tsakiya , ta yi wani uban Haske masha Allah , in ba kare mata kallo da kyau ba ka yi ba za ka iya karance yanayin shekarunta
ta na sanye da wata Abaya white color mai kyau , sai wani dan veil da ta yafa a kanta ta na taku cike da nitsuwa


a haka har ta karaso cikin parlourn , ta ajiye wa Princess plate din hannunta , kafin ta kai hannu ta dunguri kanta ta na fadin " ki mutu da yunwa tun da ke ba za ki iya shiga ki girka wa kanki abinci ba "

" ni da na ke da Cutie na san ba za ta taba bari na mutu da yunwa ba , amma Cutie kin manta da Juice , ko shi ne cikin bowl din " ta fada ta na neman karbe bowl din dayan hannunta

da sauri Inaya ta janye Bowl din ta na fadin " ke Princess ? kin san Allah ki fita da ga idona , in shirme ki ke so na fi ki iya wa , je ki tambayi Daddynki , dan haka ki bi ni a hankali ko kuma gidan ya mana kadan "

wata yar karamar dariya Princess ta yi kafin ta ce " momy ni wassa na ke miki fa " ta fada cikin sanyin murya dan ta san halin mahaifiyarta , yanzu za su fara rigima cikin gidan sai Malik ya shiga tsakaninsu

wani dan karamin murmushi Inaya ta yi kafin ta juya ta nufi stair ta Haye
Ta na hawa Princess ta kai hannu ta dauki spoon ta fara cin abincin ,

Inaya kuma kai tsaye bedroom din su ta koma , da sallama a bakinta ta shigo bedroom din
babu kowa a ciki , kawai sai ta nufi bedside drawer ta ajiye bowl din hannunta kafin ta mike
Dai-dai lokacin da ya bude kofar toilet ya fito ya na daure da towel a kugunsa , da alamun wanka ya yi

wani cool murmushi ta saki ta na kallon shi ,
ya na nan yadda ya ke sam bai sauya ba , har wannan murdaden jiki nasa , ni ganin na yi kamar ya ma kara murdewa , wannan smooth hair din nasa ya na jike da alamun wanke sa ya yi

daga mata gera guda ya yi ya na fadin " lafiya ki ke min irin wannan kallon ? " ya fada murya cen kassan makoshi har yanzu dai na miskilancin su na nan

a hankali ta fara takowa , sai da ta zo dab da shi sannan ta ce " me ya sa za ka cire gashinka ? dama kullum Princess na cewa ta fi ka gashi , yanzu ga shi kuma ka cire shi "

murmushi mai dan sauti ya yi ba tare da ya ce mata komai ba , ya juya ta gefe ya nufi dressing mirror ya janyo chair ya zauna , ya kai hannu ya bude box , ya na shirin fiddo air dryer kawai ya ga hannunta , ta riga shi dauka

cike da so ta ce mishi " bari na yi maka "

ba musu ya janye hannunsa , ya zuba mata ido ta cikin mirror
cikin nitsuwa ta fara busar mishi gashin sa , sai da ta kammala ta sa hairbrush , ta gyara mishi shi , ta sa pin ta nade shi a baya

bayan ta kammala ta sauko ta manna mishi kiss saman shoulder ta na fadin " ka san wani abu ? a kullum ganin na ke kara kyau ka ke yi babyna "

murmushi mai dan sauti ya yi kafin ya kai hannu ya zagayo da ita gabansa ya zaunar da ita saman laps din sa
a hankali ya kai hannu ya zare veil din ta , ya ajiye saman dressing mirror

kawai ya tsaya ya zuba mata ido kamar bakuwarsa

daga mishi gera guda ta yi ta na fadin " ya ? lafiya ka na min irin wannan kallon ? sai ka ce za ka cinye ni "

girgiza mata kai ya yi ya na murmushi ya ce " ya kamata mu tafi Honey Moon my Cutie "

wata yar karamar dariya ta yi ta na fadin " kai baby , wace Honey Moon kuma , mu ai yanzu mun tsuha sai dai mu tura Prince da Princess honey moon , ba dai mu je ba "

" and so what dan mun tsufa ? kin taba ganin in da soyayya ta tsufa ne ? ko kuma son da na ke miki ki na tunanin shi ya tsufa ? ki shirya kawai mu tafi honey moon , wannan karan zan ba ki mamaki " ya qarashe maganar ya zagayo da hannunsa a kugunta ya matse ta

turo dan karamin bakin nan nata ta yi kamar ya ce zai yi mata Kiss , cike shagwaba ta ce " wai kai ba ka gajiya ne Baby ? ni gaskiya ba wata Honey Moon da zan tafi "

" ta ya ki ke so na gaji My Cutie ? kullum daÉ—inki sabo ya ke zame min , kamar ma shi ne karo na farko da na ke dandana zumarki , please ki yarda mu tafi , na shirya miki surprise "

" wacce irin surprise ? " ta fada ta na sakin wani kyawatacen murmushi

bai ce mata komai ba ya mike tsaye da ita a jikinsa
bai dire ta ko ina ba sai saman bed din su , ya haye saman ta ya yi mata runfa da fafadar kirjinsa , ya fara manna mata kiss ko ina a saman face din ta

ita dai sai dariya ta ke yi tsawan shekaru yanzu amma kullum Malik da sabon salo ya ke zo mata , har yanzu ta kassa sabawa da romance din sa , wata rana ya yi mata da dadi wata ranar kuma sai ta dinga yi mishi kuka ta na rokonsa ta kyale ta

ta na haka kawai sai jin hannunsa ta yi saman breast din ta
da sauri ta ce mishi " ya isa haka baby , ka fara yin breakfast ka ga har karfe tara ta yi "

a hankali ya dago kai ya zuba mata wadanan shanyayun idanunsa kamar na dan maye ya ce " ki fara ba ni breakfast din kafin na je na yi "

marairaice mishi fuska ta yi ta na fadin " please baby , so ka ke sai ka gama da ni na koma tsohuwa sannan za ka hakura ka bari " ta fada ta na turo dan bakin nan nata

ai kuwa bai yi wani tunani ba ya kai nasa a sama ya manna mata kiss ya na fadin " ba za ki taba tsufa ba a idona My Cutie "

murmushi mai dan sauti ta yi , har ta bude baki za ta yi magana wayarsa da ke saman bedside drawer ta fara ringing

a tare shi da ita su ka kai kallon su wajen bedside drawer
a hankali ya sauka da ga saman ta , ya zauna bakin gadon , ya kai hannu ya dauki wayar

wani dan karamin murmushin gefen fuska ya saki kafin ya dauki kiran , ya kai wayar a kunne ya na sallama kassa kassa kafin ya daura da cewa " Ammiena , ina fatan ki na lafiya ? "

Inaya na jin ya ce Ammie ta gane da MALIKAT INAS ce ya ke waya , da sauri ta mike zaune , ya haye saman bayansa ta na fadin " Ammie , na yi kewar ki sosai "

a hankali ya sauko wayar ya daura saman Hand free dai-dai lokacin da MALIKAT INAS ke fadin " ni ma na yi kewar ki sosai MALIKAT , ya ki ke da Twins di na ? "

" su na nan lafiya Ammie " ta fada ta na zagayo da hannayanta a wuyansa

cikin nitsuwa ya ce " Hope ki na lafiya Ammie , da Rianna ? "

" mu na lafiya , ya jikin naka ? "

" da sauki sosai Ammie , kamar ma ban taba ciwon ba " ya fada ya na juyawa ya mannawa Inaya kiss saman kumatu , dama ta kontar da kanta saman shoulder din sa

" Alhamdoulilah , yanzu fada min yaushe za ku zo ? tun shekaran jiya na ke jiran ku amma shiru " Fadin MALIKAT INAS cikin sanyin murya

cikin rudu ya ce mata " zuwa kuma Ammie ? ke ma kin san dai cikin watan azumi mu ke zuwa , ga shi yanzu azumi saura wata biyu ma , ba wani tsayi ai "

" ban gane ba , kenan ba za ka zo ka duba jikin Diya ba ? "

a rudu ya ce mata " Diya kuma ? wani abu ya same shi ne ? "

" Nawfel , kar dai ka ce min ba ka da labarin abun da ya same shi , tsawan sati guda yanzu "

a rude ya ke fadin " Ammie please fada min , wlh ban san abun da ke faruwa ba , duk kin sa hankalina ya tashi , ba dai wani abu ya same shi ba ko ? "

sai da MALIKAT INAS ta dauki lokaci kafin ta ce mishi " satin da ya wuce ne , na san stress ya yi mishi yawa ne har jininsa ya hau , bayan mun kai shi likita ne doctor ke cewa wai bangaran hagunsa ya yi paralyze , amma Alhamdoulilah yanzu ya samu sauki har ya na iya takawa da shi "


kalmar shahada Malik ya shiga karantawa , ya na marairaice fuska ya ce " haba Ammie , ta ya za ku yi shiru ba ku fada min ba , ai da tun ranar da ya fara ciwon ya kamata ku kira ku fada min , sai da ku ka bari har ya samu sauki sannan za ku fada min , Diya fa dan uwana ne , in wani abu ya same shi ba zan iya jurewa ba , yanzu wane hali ya ke ciki ? "

cikin sanyin murya MALIKAT INAS ta ce " na yi tunanin ka na sane da abun da ke faruwa a nan , shi ya sa kawai ban kira ka ba na fada maka ina jiran zuwanku , amma yanzu alhamdoulilah har ma ya koma part din sa "


wani dan karamin tsaki Malik ya ja kafin ya ce " shikenan , in sha Allah gobe mu na nan zuwa "

" shikenan , Allah ya kawo ku lafiya , ka gaishe min da babies di na " ta fada cikin sanyin murya da ga nan su ka yi sallama ya sauko wayar ya ajiye saman bedside drawer

a hankali ya juya ya kalli Inaya da duk ta yi sanyi a jikinsa
a sanyaye ya ce mata " tashi na je na saka kaya yanzu "

noke mishi kafada ta yi ta na turo dan karamin bakin nan nata
murmushi mai dan sauti ya yi kafin ya ce " to me ki ke so yar babyna ? "

wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce mishi " ni kai na ke so , I love you "

" i love you too , but now let me make my cloths you know how is our princess , yanzu za ta fado mana kamar da ga sama
End Ads