ai kam bai gama rufe bakinsa ba ya jiyo Muryarta ta na fadin " me kuma na yi ? "
" kashhh ! " ya fada ya na dafe forehead din sa da hannu ya lumshe idanu
ita dai Inaya dariya ta fara yi ta shiga goga face din ta a shoulder din sa
da sauri ya mike tsaye ya na fadin " ba za ku kashe ni ba ku biyun nan " ya fada ya na fara takawa ya shiga dressing room
da kallo su ka raka shi har sai da ya shiga sannan su ka yi dariya , amma lokaci guda Inaya ta tsuke fuska ta ce mata " me ki ke yi a nan ? ba ki iya knocking ba ? "
" ba ke ce ki ka gudo da bowl din nan ba , ni kuma ina son na ga me ke ciki " ta fada ta na turo dan bakin ta , dai ita dole sai ta ga abun da ke cikin bowl din ,
( ni a nawa sanin Princess sam ba ta da hayaniya , yanzu kuma ita ce mai rigimar , tukunna ma ina Prince ni har yanzu ban gan sa ba )
hararrar ta Inaya ta yi ta na fadin " Nailah , fice min da ga daki tun ban bata miki rai ba " ta fada cikin tsare gida wai su Inaya an san minene tsare gida a na ba da umarni
daga kai sama Princess ta yi ta na fadin " Daddyyyyyy ! ! ! ! ! " ta fada da mugun karfi
ba shiri Malik ya fito da ga cikin dressing room ko button din shirt din sa bai gama sakawa ba , a tunaninsa wani abu ne ya faru da yar babyna tasa
" Princess , what happened ki na min irin wannan kiran ? " ya fada ya na karasowa wajen ta ya na kokarin saka button din rigarsa
nuna mishi bowl din da ke saman bedside drawer ta yi , ta na turo dan bakin nan nata ta ce " Daddy , ce wa Cutie na yi ta bari na ga abun da ke cikin bowl din nan , amma ta ce min na fice mata da ga nan ko ta bata min rai " ta fada cike da shagwaba ta na hura kumatu
wata yar karamar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya juya ya kalli Inaya , ya na juyowa ko ta wurga mishi wani mugun kallo ta na tsuke fuska
ba dan ya so ba ya shanye abun da ya zo fada , ya juya ya riko hannun Princess su ka fice bedroom din , gwara ya je ya rarrashe ta da ya ja fushin Cutien sa , ya san in ta yi fushi yau tasa ta kade
Inaya kuma su na fita ta ida Hayewa gadon ta konta ta lumshe idanunta
jim kadan Malik ya dawo cikin dakin ya na sallama
ba tare da ta bude idanunta ba ta amsa mishi sallamarsa
a hankali ya karaso bakin gadon ya kai hannu saman bedside drawer zai dauki bowl din da ga ajiye
ba tare da ta bude idanunta ba ta ce " ka san Allah ? ka dauki bowl din nan ka kai mata , ku da abinci sai dai na restaurant dan ba zan sake shiga kitchen din nan ba "
ba dan ya so ba ya janye hannunsa , ya zauna bakin gadon
cikin sigar rarrashi ya ke ce mata " please Cutie , ke ma kin san halin Princess in ba ta samu abun da ta ke so ba , kuma fruit salad din nan ta shiga ranta , please ki bari na kai mata "
mikewa zaune ta yi ta zuba mishi ido , cikin tsare gida ta ke fadin " shikenan ? wai me ya ka ke biye mata ne ? ba fa yarinya ba ce shekarunta 30 , a yanzu ya kamata a ce ta na da aure har da babys , amma don Allah dubi ta na nan zaune da mu bayan shagwaba ba abun da ta ke , duk ka bi ka bata ta "
" to ya ki ke so na yi in ban shagwaba ta ba ? shagwababen nawa ya gudu ya bar ni , duba tsakani da Allah tsawan three months ba mu da labarinsa , sai dai ya turo mana letter ya ce kar mu damu ya na nan lafiya , wannan shi ya koma Exiled Prince ba ni ba "
wata yar karamar dariya ta yi kafin ta daura hannunta saman face din sa ta na fadin " kar ka damu , in sha Allah zai dawo mana cikin koshin lafiya , kawai ya na son ganin ya duniya ta ke , ya na son bude ido , kar ka ga laifinsa , yanzu dai ya kamata ka yi min maganin wannan shagwababiyar dan gaskiya ba zan ci gaba da zama da ita a gida guda ba a to " ta qarashe maganar ta na janye hannunta , ta koma ta konta
wata yar karamar dariya ya yi kafin ya mike ya dauki bowl din ya juya ya fice da shi
ya na fitowa ko ya ga Princess tsaye gefen kofar dakin ta nade hanayanta a kirji , ta na faman turo baki
mika mata bowl din ya yi ya na fadin " Take it , in kuma ki bari ta kama ki ba ruwana "
da sauri ta kai hannu ta karbi bowl din ta na washe baki kafin ta dan dago ta manna mishi kiss saman kumatu ta juya da sauri ta bar wajen
da kallo ya rakata har sai da ta gama saukar stair din Sannan ya juya
๐ IN DAI KIN SAN BA KI KARANTA EXILED PRINCE BA , BOOKS 1 , 2 , 3 & 4 , TO KAR MA YI KI YI KOKARIN KARANTAWA DAN BA ZA NI GANE KOMAI BA ๐
WANNAN KARAN NA ZO MUKU DA SABON SALON SOYAYYA KAMAR KULLUM ๐โโค
BA ZAN CIKA KU DA SURUTU BA , SAI MUN SHIGA CIKIN LABARIN ZA KU GANE , WANNAN KARAN ZAI TASHI KWAKWOLWAR KU KAMAR BOMB ๐ฅ๐ฅ๐ฅ
TAP THIS LINK TO JOIN MY COMMENT SECTION
https://chat.whatsapp.com/JTfho9QngpG5Ax4LM4d4sK
_______________________________________________
[ PAGE___ 3 ๐๐โค ]
da kallo ya rakata har sai da ta gama saukar stair din sannan ya juya ya koma cikin dakin dan ya rarrashi dayan babynsa
ko da ya shigo ya tardo ta zaune ta yi zaman bokaye tsakiyar gadon , ta hura hanci
murmushi mai dan sauti ya yi kafin ya meda kofar ya rufe ya saka mata security , sannan ya juyo ya nufe ta , kai tsaye saman gadon ya haye ya sa hannu ya kontar da ita ya haye saman ta , ya yi mata runfa da fafadar kirjinsa
har ta bude baki ta na shirin ce mishi ya sauka da ga saman ta kawai ya cabko lips din ta ya fara kissing din ta cikin konciyar hankali
da farko ta fara kokarin ture shi wai ita fushi ta ke , amma sannu sannu har ta daina , jikinta ya yi sanyi ta fara biye mishi su na kissing din juna
( ๐ด๐ด i'm happy to see at least abu guda bai sauya ba , a to ni bari na tafi wani bangaran na duniya daban kafin su gama )
A takaice Masarautar Yemen ta na daya da ga cikin masarautun da ke karkashin jagorancin Daular Saudiya , amma kamar kowace masarautar ita ma wannan da nata Sarkin sai dai sunan ya banbanta dan a nan Al-Sayid a ke kiran Sarkin , Al-Sayid Abdoul-Mueed Bin Ahmed shi ne sarkin wannan masarautar , da matansa biyu Sayida Ahlame ta farko , sai Sayida Fadwah ta biyu , masarautar Yemen babbar masarautar ce dan duk cikin masarautun da ke karkashin Daular Saudiya ita ta fi habbaka , duk wani Gold da a ku samu da ga kudancin Saudiya duk da ga masarautar Yemen ya fito , bangaran economy kuwa ba a magana yadda yanayin fadar Daular Saudiya ya ke haka nata ya ke , a nan ma Sarkin shi ne president din kassar , a takaice dai dan karamin labari a kan masarautar Yemen , duk da ba za mu shiga cikin labarinta sosai ba
wata kyakyawar budurwa ce ke gudu tsakiyar kasuwar masarautar , ta na sanye da wata gown off-white , ta zallar auduga kai da ga gani sakar hannu ce , gown din ba ta da wani ado , wuya da hannu kawai a ka fidda , ko wani dan zane ba ta da , ga rigar kuma duk ta jiqe da ga kassa kamar ta shiga ruwa ga shi ko takalmi babu a kananan kafafunta , ta na yafe da wani dan karamin veil fari , amma Jelar gashinta duk ta na waje , ta bazun mata a shoulder har saman face , brown color da ita ta yi wani curly da ga kassa gwanin burgewa
yarinyar kyakyawa ce ajin farko , a shekaru ba za ta wuce 18 years ba , fara kal da ita kamar ka taba jini ya fito , ta na da sexy eyes farare kal kamar madara kwayar cikin su kuma brown ce mai mugun kyau , in ka kare mishi kallo ya so ya dan yi kama da Hazel , ta na dan karamin hanci kamar an ajiye shi tsakiyar fuskarta , da dan karamin bakinta , da wasu lalawsan lips din ta pink color , ba dan kayan da ke jikinta ba da sai na ce d'iyar wani babban dan kasuwa ne a cikin masarautar ko kuma wani na cikin fadar masarautar
ta na gudu ta na waigawa bayanta , ta na rike da wata leda a hannunta ,
ta na juyawa ta ga wasu samari biyu su na biye da ita su na fadin " ku taro ta barauniya ce ! ki tsaya na ce ! " su ke fada da karfi
sarai ta ke ji amma ta ki tsayawa haka ma mutanan wajen su na ji amma su ka share dan kowa aikin gabansa ya ke , wasu in su ka ga sun iso wajen su matsawa ma su ke su ba ta hanya
ta na a haka kawai ta ji ta bugi mutum da karfi har sai da ta saki wata yar karamar kara ta saki ledar hannunta , nan take apples din da ke ciki su ka zube a kassa
fuuuu ta yi baya za ta fadi
cikin zafin nama ya kai hannu ya riko kugunta ya taro ta dan ya san in ta yi irin wannan faduwar ba karamin ciwo za ta ji ba har kanta ya fashe
wata nanauyar ajiyar zuciya ta sauke jin ba ta kai kassa ba , a hankali ta ware idanunta
ba su sauka ko ina ba sai cikin sexy Hazel eyes din sa
nan take idanunsu su ka sarkafe cikin na juna , su ka kassa janye su
su na a haka har wadanan samarin biyu su ka iso wajen su na fadin " mun gode sir , tun dazu mu ke neman kamo ta amma yarinyar nan ta gudu "
ta na jin Muryarsa ta yi sauri ta dago da ga jikinsa ta boye a bayansa
shi dai ya na tsaye waje guda ko motsi bai yi ba
ya na sanye da trouser blue da wata Shirt white color mai dogayen hannu , da wasu tsadadun fararen sneakers a kafafunsa
gaskiya hadada ne , fari kal da shi kai ka na gani ka san balarabe ne , a shekaru zai kai 30 haka , amma ya na da murdaden jiki kamar dan dambe , ga kuma fafadan kirji kai da ga gani wannan ya yi wa mutum kyakyawan naushi sai dai wani ba shi ba
kallo daya za ka yi mishi ka san Jinin Malik Nawfel Hicham Bin Jaabar ne dan su na kama tak kamar an tsaga kara , har wadanan hazel eyes din nasa , da darck smooth hair din sa , shi ma ya daure shi a baya ya saki kanana a gaban gashi
fuskarsa a daure tamau kai ka ce an aiko masa da sakon mutuwa
a hankali ya kai hannu bayansa ya riko nata hannun ya janyo ta ya mikawa samarin nan ita
da sauri ta kwace hannunta ta na fadin " no , ku duba wlh na ajiye muku kudin apples din , ku duba saman table din "
wani dan karamin tsaki guda cikin su ya fa ya riko hannunta ya fisgota da karfi ya na fadin " mu je fadar Al-Sayid , sai ki fada mishi hakan barauniya kawai "
dan zaro idanu ta yi ta na girgiza mishi kai kamar za ta yi kuka ta ce " a'a don Allah kar ku kai ni wajen sa , zan sake biyan kudin don Allah kar ku kai ni "
ta na gama rufe bakinta ya tako a hankali ya riko hannunta , ya riko na saurayin ya raba su
cike da nitsuwa ya ce " ku kyale ta ni zan biya , nawa ne kudin ? "
ba musu saurayin ya fada mishi kudin
sai dai ku yi hakuri ni ban san minene kudin masarautar Yemen ba gaskiya
hannu ya kai cikin aljihunsa , ya fiddo bandir din Dollars sabi kal , ya na fadin " sai dai ku yi hakuri , Dollars ne kawai a hannuna " ya fada ya na raba kudin biyu ya ba su rabin ya meda rabin cikin aljihunsa
a tare samarin nan su ka saki murmushi sun ga kudi , da sauri ya kai hannu ya karba ya na yi mishi godiya , kafin su juya su bar wajen kudin da ya ba su ya yi 100 din kudin Apples din ma ba 10 ba shi ya sa su ka karba su ka bar wajen
ya na ganin sun bar wajen ya juyo da Niyyar yi mata magana kawai ya ga babu ita ba mai kama da ita har apples din duk babu komai duk ta kwashe ta bar wajen
a rude ya fara bin wajen da kallo , ace just one minute ya ba ta baya a ce har ta gudu , tukunna wacece ma yarinyar nan
ya na a haka na ga wani mutum cikin black suit ya karaso wajen , cikin girmamawa ya ce " Sir , motar ta iso "
wata boyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya juya ya fara takawa , da sauri ya bi bayansa da alamun bodyguard din sa ne
a haka su ka ci gaba da takawa har su ka iso wajen fita kasuwar
kawai sai ganin na yi ya tsaya cak waje guda , kafin ya juya a hankali ya kalli saitin damar sa
nan ya gan ta zaune cikin wani kwango , da wasu yara uku biyu maza daya Mace , su na zagaye da ita , kowane rike a apple guda sai dariya su ke yi su na ci , ita ma ta na dariya ta na kallon su har fararen hakwaren ta na fitowa
ya dan dauki lokaci ya na kallon su kafin ya juya ya ci gaba da tafiyarsa
sai da su ka fito har kasuwar wajen titi
nan na ga wasu manyan motoci guda uku a jere , duk farare kal ma su bala'in kyau , ga wasu bodyguards zagaye da motocin
su na ganin shi daya da ga cikin su ya yi saurin bude gidan bayan motar tsakiya
ko sannu bai ce musu ba ya shiga motar nan
da sauri bodyguard din ya rufe motar su ka shiga sauran motocin , da mugun gudu su ka bar wajen
SHEBA HOTEL
ููุฏู ุชุงุฌ ุณุจุฃ - ุตูุนุงุก
Kai tsaye makeken Sheba Hotel su ka nufa , a parking space su ka tsayar da motocin
da sauri Bodyguards din nan su ka sauko su ka bude mishi kofar motar
cike da kwarjini ya sauko da ga cikin motar ya na latsa wayarsa , ya nufi hall din shiga hotel din , bodyguards na biye da bayansa
duk inda ya wuce sai mutane sun juya su na kallon shi dan ba karamin burge su ya yi
shi kuwa ko ta kansu bai bi ba , ya nufi hanyar room din sa da ke bangaran VIP , musaman bangaran VIP da ke a floor na farko duk ya biya kudin yadda ba wanda zai iya shigowa wajen dan ya takura mishi
shi dama ba mutum ne da ba ya son hayaniya , shi ya sa ya ke rayuwarsa shi kadai
a haka bodyguards din sa na biye da bayansa har ya su ka karaso wajen room din sa , ya shiga su kuma su ka tsaya da ga waje
ko da ya shiga , ya ajiye wayarsa saman gadon , ya sa hannu ya fara cire button din rigarsa , har sai da ya kammala ya cire ta ya ajiye saman gadon
sannan ya zauna bakin gadon ya cire sneakers din sa ya rabe su gefe , kafin ya mike tsaye
ya sa hannu ya zame belt din trouser din shi
har ya riko trouser din sa zai yin kassa da shi ya ga an turo kofar dakin an shigo a na sallama
irin wannan matan ne ma su kula da dakuna, ni dai gaskiya ban san me a ke kiran su da shi ba wlh a to
ta na rike da wani tray da towel farare kal a sama , sai tsintsiya a hannunta za ta share wajen
ta na shigowa idanunta su ka sauka saman shi
wata irin muguwar bugawa zuciyarta ta yi ba ta san lokacin da ta saki tray din ba da kara a tare