na bi bayan Aleesherh dan murmushin da ta yi ban yarda da shi ba
bayan ta baro Part din su kai tsaye kitchen ta nufa , ba sai na fada muku ba kun san yadda yanayin wajen zai kasance , kitchen din na da girma gaskiya ga shi ko cike da maid sai girki su ke yi , wannan kitchen din ta mutanan fada ne kadai da familyn Al-Sayid
ba ta bi ta kan Maids din ba kawai ta shiga hada mishi coffee da kanta
bayan ta gama ta shirya mishi fruits saman tray da glass cike da milk sannan ta dauki tray din ta fito kitchen din
su dai Maid su na tsaye su na kallon ikon Allah yadda ta ke gyara breakfast din cike da so , a iya sanin su cikin shekara bai wuce so guda ta ke shigowa kitchen din ya a ka yi ta iya hada irin wannan lafiyayen coffee bare ma sun san ita ba ta shan coffee
bayan ta baro kitchen kai tsaye part din su Prince ta nufa
ta na shiga ta gan shi zaune saman sofa , ya daga kai sama ya na murza shi da hannu idanunsa a lumshe da alamun kansa ya fara ciwo
har ta bude baki zai yi magana ta jiyo Muryarsa ya na fadin " wlh Junior mu ka koma Saudiya sai na yi ball da kai , yanzu ga shi kaina na min ciwo "
a hankali ta daga kai ta kalli Junior da ke ta sharar barcinsa
wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta ajiye tray din saman table
ta dauki mug din coffeen ta riko hannunsa ta saka mishi mug din a ciki
bai kawo komai a ransa ba ya fara shan coffeen dan in bai coffeen nan ba akwai matsala
ita kuma a hankali ta zagayo bayan sofar ta kai hannayanta saman kansa ta fara murza mishi shi cikin konciyar hankali
nan take ya fara sauke ajiyar zuciya a jere , sai da ya gama shan coffeen tas sannan ya jingina bayansa da sofar ya daga kai sama
sai da ya yi wajen two minutes a haka kafin ya ware idanunsa slowly
ba su sauka ko ina ba sai saman face din ta , ta daure ta tamau kamar hadari , kawai sai ji ya yi ya kassa janye idanunsa da ga saman face din ta
ganin ya tsare ta da ido ya sa ta kauda kai gefe ta na fadin " kanka ya daina maka ciwo ? ina so na tafi "
slowly ya motsa lips din sa kamar an yi mishi dole ya ce " ni na saka ki ? "
" No , amma rashin tausayina bai kai haka ba , kai ka ce min na kawo maka coffee kawai taimakon ka ne na yi " ta na gama fadar haka ta janye hannayanta da ga saman kansa ta nufi hanyar fita
bin bayanta da kallo ya yi har sai da ta kai bakin kofar sannan ya ce " Na gode "
wani dan karamin murmushi ta saki amma ba ta tsaya ba ta sa kafa ta fice
sai da ta fita sannan ya meda idanunsa ya lumshe , ya san Sarai ba ita ya yi wa magana da farko ba saboda yanayin Muryarsu ba daya ba ce , shi kansa ya rasa ta ya ya ke gane su cikin sauki haka bayan su na kama tak kamar an tsaga kara , amma kallo daya ya ke musu ya gane su
ya yi nisa duniyar tunaninsa ya ji a na yi mishi knocking
sai da ya ja tsaki sannan ya ware idanunshi ya kalli saitin kofar
wani dogari ne a tsaye
ya na ganin ya juyo ya ce " ranka shi dade mai girma Al-Sayid ya na jiran ku a parlournsa ku yi breakfast "
gyada mishi kai kawai Prince ya yi kafin ya mike tsaye ya nufi toilet ya shiga
Jim kadan ya fito daure da towel a kugunshi ya nufi dressing room dan jiya ya yi musu online shopping na kayan da za su saka kafin su koma Saudiya
jim kadan ya fito sanye da kananan kaya wandon Jeans da T-shirt duk white color, da fararen sneakers a kafafunsa
bedside drawer ya nufa ya dauki wayarsa ya saka cikin aljihunsa sannan ya nufi kofar fita ko neman Junior bai yi ba , ya na dunkule cikin bargo sai barci ya ke
bayan ya baro part din su kai tsaye parlourn Al-Sayid ya nufa dan jiya wajen zagaye zagayen shi har ya iso parlourn ba shi da labari
da sallama a bakinsa ya shigo parlourn , nan ya tardo duk Familyn Al-Sayid har da su Twins din sa , su na zaune tsakiyar parlourn a kassa saman carpet , ga abinci tsakiyar su da alamun yanzu za su breakfast
Al-Sayid na ganin shi ya saki wani cool murmushi ya na fadin " sannu da zuwa Prince , bismillah zauna , yau tare za mu yi breakfast "
cikin girmamawa Prince ya ce " ina godiya sosai da irin wannan karramawar , na san ba kowa ke samun Alfarmar cin abincin da familyn shugaban kassar nan mai Albarka , na gode amma ina sauri ne zan fita , idan har mai girma Al-Sayid ba shi da matsala da hakan "
gyada mishi kai Al-Sayid ya yi a hankali ya na murmushi gaskiya ba karamin tafiya da zuciyarsa Prince ya yi ba , tun ba yau ba , tun lokacin da ya zo masarautar neman littafi yanayin da ya ke magana ya yi mugun burge shi
godiya Prince ya mishi kafin ya juya ya yi tafiyarsa
da sauri Sayida Ahlame ta tabo Aleesherh da ke zaune gefenta ta ce " ba za ki raka shi ba ? "
tsuke fuska Aleesherh ta yi kafin ta ce " ni na kawo shi ne ? "
" Aleesherh ba na son wannan yanayin maganar taki " Al-Sayid ya fada cikin tsare gida
kauda kai gefe ta yi ta na turo dan bakinta ba tare da ta ce komai ba
" Aleenah , ina son ki taimakawa yar uwarki ta shirya mishi diner yau " fadin Al-Sayid
da to kawai ta amsa mishi kanta na sunkuye ta na shan fruits
Aleesherh kuwa sai shan tsami ta ke , kai ka ce ba saboda shi ne ta yi kuka kawai dan ya ki yi mata magana
ta na a haka ta jiyo Muryar Sayida Ahlame ta na fadin " ranka shi dade , gaskiya yaron nan ya na da nitsuwa dubi yadda ya ke magana cike da girmamawa , na so ya na da dan uwana da na ba shi Aleenah " ta fada ta na kallon Aleenah
har Al-Sayid ya bude baki zai yi magana Sayida Fadwah ta riga shi cewa " me ya sa ba za a ba shi Aleenah ba ma a kan Aleesherh "
a tare Aleesherh da Aleenah su ka dago kai su ka kalle ta
" na ga Aleesherh ita ce babba , ta ya za a ba shi auren Aleenah al'halin ita ba ta da auren , amma tun da shi kansa bai san wadda na ba shi ba kuma Aleesherh ta ce ba ta son auren , in har Aleenah ta amince sai a yi auren da ita " fadin Al-Sayid ya na kallon Aleenah alamun tambaya
dam Aleesherh ta ji zuciyarta ta buga ta na kallon Aleenah har zaro idanu ta ke
haka ita ma kallon Aleesherh ta ke zuciyarta na duka uku uku kar a je Al-Sayid ya dawo da auren kan ta , ta san Aleesherh ba za ta taba yahe mata hakan ba saboda son da ta ke wa Prince
a fusace Aleesherh ta mike ta nufi kofar fita da sauri ta fice
sai kiran sunanta Al-Sayid da Sayida Ahlame su ke amma ina ba ta jin su
sai da ta fita sannan Al-Sayid ya kalli Aleenah ya ce " Aleenah ba ki ba ni amsa ba ? tun da ita ba ta so sai na aura miki shi ? ko ya ki ka gani ? "
da sauri Sayida Fadwah ta ce " ba sai ka tambaye ta ba ta amince , na ga kai ne da iko da su ba akasin haka ba " ta fada dan burinta guda a janye maganar auren Aleesherh da Prince , ko wani za ta aura ta fi son ta auri Abdoul-Jalil wanda ke matsayin nephew din ta
da sauri Aleenah ta ce " no , Daddy wlh ba na so , ba na so " ta fada kamar za ta yi kuka
wata yar karamar dariya Al-Sayid ya yi kafin ya ce " kontar da hankalinki , ni dama wassa na ke miki , na riga da na ba shi Aleesherh ba zan sauya ba ko da ba ta son shi sai an yi auren "
wata nanauyar ajiyar zuciya ta sauke har sai da ta lumshe idanunta kafin ta mike tsaye ta na fadin " Daddy na koshi "
" shikenan " Al-Sayid ya fada a takaice , da ga haka ta sa kafa ta bar wajen ta bi bayan Aleesherh
sai da ta fita sannan Al-Sayid ya ce wa Sayida Ahlame " Za ki iya tafiya ke ma ! "
ba musu ta tashi ta yi musu sallama sannan ta tafi ya rage da ga shi sai Sayida Fadwah
cikin nitsuwa ya ce mata " Fadwah , ban san me ki ke nufi da maganarki ba , amma zan so ki sani Auren Aleesherh da prince ba abun da zai hana shi , na sani Abdoul-Jalil kamar d'a ya ke a gare ki kuma na ji dadi da har ki ka nema mishi auren Aleesherh , to Allah ya yi Aleesherh matar Prince ce , da kin yi min wannan maganar tun da farko da sai na ba shi ita , amma na riga da na bawa Prince , amma in har ya na son Aleenah ni ba ni da matsala zan ba shi auren ta "
" zan iya tafiya ? " ta fada cikin sanyin murya
gyada mata kai kawai ya yi dan ya san halinta in ba ta son abu to shikenan ba za ta so shi ba har abada
a hankali ta tashi ta fice parlourn ta bar shi nan zaune
▪ALEENAH 💕
bayan ta baro parlourn Al-Sayid kai tsaye part din su ta koma
ta na shiga ta ga Aleesherh konce tsakiyar gadon ta yi rub da ciki
karasowa ta yi ta zauna bakin gadon ta na fadin " Alee , in har da gaske ki na son shi ya kamata ki fito ki fada masa wannan shan tsami da ki ke mishi ba shi ne solution ba , yanzu ba dan Daddy wassa ya ke mana ba da yanzu ya fasa aura miki shi "
shiru Aleesherh ta yi ba ta ce mata komai ba
ganin ba ta amsa mata ba kawai sai ta daga kafadunta ta tashi ta koma saman sofa ta zauna ta na kallon ta
▪MISALIN KARFE 8 NA DARE
▪PRINCE
zaune ya ke cikin part din su ya na sanye da wasu pajama white color , da laptop saman cinyoyinshi ya na aiki
Junior na konce gefensa ya na rike da wayarsa ya na latsawa
su na a haka wani dogari ya iso wajen ya na yi musu knocking
a hankali Junior ya sauko da ga saman gadon ya nufi kofar ya na rike da wayarsa
ya na isowa ya bude kofar
cikin girmamawa dogarin ya ce mishi " ina mika sakon gaisuwata ga shugaban , Gimbiya Aleesherh ta aiko da sako zuwa ga Prince " ya fada ya na mika mishi wata paper da duka hannayansa biyu
hannu Junior ya kai ya karba ya na yi mishi godiya kafin ya juya ya dawo dakin ya na bude paper din ya fara karanto abun da ke ciki
sai da ya gama sannan ya saki wani dan karamin murmushi ya na fadin " Prince , babynka ta shirya maka diner a garden "
wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya ce " wane baby ? ni babu in da zan je kuma sanyi na ji "
da sauri Junior ya nufi dressing room ya shiga
jim kadan ya fito rike da wata jacket white color ya karaso wajen Prince ya mika mishi ya na fadin " ko wane problem ya na da solution , dan haka malam tashi ka tafi wajen madam ta shirya maka abinci "
marairaice mishi fuska Prince ya yi ya na fadin " please kyale ni , wlh sanyi na ke ji , kuma ka san cikin sauki zazzabi ke kama ni in ina jin sanyi "
" wlh ko ka tashi ka tafi ko na kira uncle na hada maka karya da gaskiya , kuma ka fi kowa sanin halinsa dan haka tashi ka tafi , it is just for ten minutes , ba ka san awa nawa ta share ta na shirya maka abincin nan ba , kuma ka ce ba ka zuwa , ka yi mata adalci ? "
tsaki Prince ya ja kafin ya sauko da ga saman gadon ya karbi jacket din ya saka , ko sannu bai ce wa Junior ba ya sa kafa ya fice
bushewa da dariya Junior ya yi kafin ya zauna wajen da ya tashi ya dauki laptop din ya ci gaba da aikinsa
Prince kuwa, kai tsaye hanyar garden ya nufa
tun da ya shigo ya fara hango ta zauna saman chair ta na rike da wayarta ta na latsawa , gabanta wata table shinfide da wani farin tissu , table din ta na cike da abinci , da fruits da juice
wajen ya na zagaye da lamps white color ma su mugun kyau , wajen dai ya yi tsab kamar so romantic
da sallama a bakinsa ya iso wajen hannayansa na cikin aljihun jacket
ba tare da ta dago kai ba ta amsa mishi sallamarsa ta ce mishi " sannu da zuwa , bismillah " ta kai karshen ta na ajiye wayarta
ba musu ya zauna ya zuba mata ido ba tare da ya ce komai ba
" what ? bari min irin wannan kallon ni ma matsa min a ka yi na shirya maka abincin nan "
" kenan ba da son kanki ki ya yi wannan abun ba ? " ya tambaye ta
sai da ta dauki lokaci kafin ta ce " Eh , why zan dauki lokaci kan wanda bai damu ba ? na fada maka ? ni wlh auren nan matsa min kawai a ka yi na yi shi ba dan haka ba ni zuciyata na da wanda ta ke so "
dan tabe baki ya yi kafin ya ce " do you know what's love ? "
sai da ta saki murmushi sannan ta ce " no , ban san minene so ba , a kansa na san minene so , ni mutunce mai karancin yarda da mutum ko a school Aleenah ce kadai friend's di ta , amma shi , tun lokacin da idanuna su ka sauka cikin nashi na ke jin kamar na mallaka mishi rayuwata baki daya , shi ne namiji na farko da zuciyata ta amince da shi , duk abun da ya ke burge ni ya ke da ga yanayin maganarsa har zuwa Tafiyarsa komai burge ni ya ke , ni kaina ban san ya a ka yi na kamu da son shi haka ba , na yi kokarin fada mishi abun da ke cikin zuciyata amma ya nuna min ya fi karfin soyayyata " ta qarashe maganar ta na daukar plate ta fara serving din sa
shi dai ya yi zaune ya zuba mata ido ya ma rasa abun da zai ce , da ga gani ta na fama da soyayya amma ko wane ? kenan shi ya sa ta ke ja da baya da shi akwai wanda ta ke so , in haka ya kamata ta yi wa Al-Sayid magana kar a aura mata wanda ba ta so
sai da ta gama serving din sa ta ajiye mishi plate din gabansa sannan ta dauki wayarta ta fara latsawa
bai fara cin abincin ba , ya ce mata " me ya sa ba za ki fada wa Al-Sayid ba akwai wanda ki ke so ? "
" na fada mishi , ya ce min na kawo shi ya gan shi , da na je fada mishi abun da ke cikin zuciyata ya koro ni , na koma na tarda ya bar garin ma , that's why ma na hakura "
https://chat.whatsapp.com/DWOwxaJuwFcGR1BPqBgf0s
_______________________________________________
[ FREE PAGE ___ 13 🕊👑❤ ]
jin abun da ta ce ya tuno mishi abun da ya faru lokacin da ta je bedroom din sa a hotel ta na ce mishi ya saurare ta amma ya ki ji , har ya kore ta a fusace , ba dai shi ta ke so ba ? ya tambayi kansa
cikin nitsuwa ya ce mata " zan iya sanin ko wanene wanda ki ke so ? "
wata yar karamar dariya ta yi ba tare da ta kalle shi ba ta ce " in na fada maka za ka sa ya so ni ne ? ko in na fada maka zai sauya gaskiyar da ba ya so na ? na fada maka ko kar na fada maka duk ba abun da zai anfanar "
bai ce mata komai ya fiddo hannu da ga cikin aljihun jacket din sa , ya dauki spoon ya fara cin abincin
ta na ganin ya fara ci ta sauke ajiyar zuciya ta ajiye wayarta gefe , amma kafin ta ajiye sai da ta saka musu music irin slow music haka sannan ta ajiye wayar , ta yi serving kanta ita ma ta fara ci cikin nitsuwa
ta yi nisa duniyar tunaninta ta dago kai a hankali ta kalle shi , nan ta ga hannunsa sai rawa ya ke da kyair ma ya ke iya rike spoon din
ta na shirin magana ta