x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 21 - NAYEL THE RETURN OF EXILED PRINCE

  • 60001 words
  • 63000 words
  • Out of 89550 words

Category: Love Stories

Views 408

14 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
su
wata doguwar ajiyar zuciya Malik ya sauke kafin ya kalle shi ya ce " lafiya za ka watsa min ruwa ? "
" nothing " ya fada a takaice ya na tsare shi da ido
ya na gama fadar haka ko Inaya ta iso wajen ta na sallama , duk ba su ji lokacin da ta fito building din ba , ta na rike da tray din Fruits , ta zauna bakin ruwan ta na kallon su
dariya Malik ya yi kafin ya matso bakin ruwan ya dauki fruits guda ya kai baki ya na dariya
ta kai hannu saman face din sa ta na fadin " Ka na girma ka na abu kamar baby "
dariya kawai ya yi sannan ya yi baya ya sa hannu cikin ruwan ya watsa mata a fuska
wata yar karamar kara ta yi ta na kauda kai ta ce " please kar ka bata ni "
" shigo mu yi wassan da ke " ya fada ya yawo cikin ruwa , har ya wuce Prince
girgiza mishi kai ta yi ta na fadin " no , Zan dai zauna ina kallon ku , Prince ba za ka sha fruits ba ? "
girgiza mata kai ya yi kafin ya ce " thanks "
ba ta ce mishi komai ba ta zuba musu ido ta na murmushi , Malik sai wassa ya ke cikin ruwan kamar wani karamin yaro
ta na a haka kawai ta ji kamar a na kallon su irin last time , da sauri ta mike tsaye ta na kallon dutsen
ba ita kadai ba har Prince sai da ya ji kamar a na kallon su , su ka zubawa Dutsen a tare shi da ita
sun yi wajen one minute haka zugum kafin Prince ya ce wa Malik " Daddy fito da ga cikin ruwan nan " ya fada ya na nufar bakin ruwan ya fice
cikin rudu Malik ya ce " Lafiya ? me ya faru ? "
Inaya ta amsa mishi da cewa " Baby yi sauri ka fito ! " ta fada da karfi cike da tsoro da alamun wani abu aljanunsu su ka jiyo , in ba ku manta ba Prince shi ma ya gado aljanunta , may be shi ya sa Malik bai ji abun da su ke ji ba
kafin ma Malik ya iso bakin ruwan wasu ruwa su ka sauko da ga saman dutsen da muguwar karfi , lokaci guda su ka tafi da shi
wata razananiyar kara Inaya ta saki , Prince kuma ya na fadin " Daddy ! " da mugun karfi
duk yadda Malik ya so fita da ga cikin ruwan ya kassa sai tafiya da shi ruwan su ke yi ga shi ko wajen duk duwatsu ne sai buguwa ya ke ciki
da sauri Prince ya fara gudu bakin ruwan ya bi Malik , ya na a haka kawai ya ga Malik ya bugu da wani dutsen , nan take kansa ya fara zubar da jini , jikinsa ya yi sanyi ya sume
" Daddy ! " Prince ya fada da mugun karfi ganin abun da ya faru da Daddynsa
hankalinsa bai gama tashi ba sai da ya hango wata waterfall , yadda ya san kassar saudiya , ya San akwai wani teku bayan masarautar kuma tabbas ruwan nan cikin tekun za su Zube , in har Malik ya fada cikin tekun nan to tabbas mutuwa zai yi
kamar kiftawar ido na ga idanunsa sun koma farare kal , gashin kansa shi ma ya koma fari kal , pin din da ya daure shi ta fadi nan take ya fara tashi cikin iska
Inaya na ganin gashin kansa ya koma Fari ta tsaya da ga gudun da ta ke ta na sauke ajiyar zuciya
lokaci guda na ga Prince ya tsunduma cikin ruwan nan , amma sam ba na iya ganinsa cikin ruwan kamar ya bace
haka dai na tsaye ina bin ruwan da kallo ina jiran fitowarsa
ina a haka kawai na ga ya fito da ga cikin ruwan dauke da Malik , ya yi sama da shi cikin iska ya na kallon Dutsen da ruwan su ka zubo , nan ya ga wani bakin abu kamar inuwar mutum tsaye su na kallon juna kafin ta bace bat
sai da ya bace sannan ya sauko kassa bakin ruwan , ya kontar da Malik , dai'dai lokacin da Inaya ta karaso wajen su ta na bin Prince da kallo
a hankali na ga kwayar idonsa ta fara fitowa , har idanunsa su ka dawo dai'dai gashin kansa amma har yanzu white ne
da sauri ta daura hannayanta biyu saman cikin Malik ta fara dannawa da karfi , duk lokacin da ta danna sai ruwa sun fito da ga cikin bakinsa , a haka har su ka daina fitowa
amma Malik ko motsi ba ya yi
da sauri Prince ya mike ya dauki Malik ya saba saman shoulder ya nufi hanyar komawa cikin building din , Inaya na biye da bayansa
bayan sun koma bedroom din , kai tsaye saman gado ya kontar da Malik ya bude bedside drawer ya fiddo A box ,
cikin nitsuwa ya yi wa Malik dress a wajen da ya ji ciwo
sai da ya yi mishi dress sannan ya kontar da kansa saman kirjinsa ya na sauraron bugun zuciyarsa
ajiyar zuciya ya sauke kafin ya dago ya kalli Inaya da ke tsaye bayansa ta ce " momy kar ki damu , suma ce kawai ya yi "
wata nanauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta zauna bakin gadon , ta riko hannun Malik ta manna mishi kiss
a hankali Prince ya mike ya nufi kofar fita
da sauri Inaya ta ce mishi " Prince , ta ya za ka fita a haka , ka tsaya na kawo maka ko jallabiya ce ka saka "
gyada mata kai kawai ya yi kafin ya juyo , ita kuma ta mike ta shiga dressing room
jim kadan ta fito rike da Jallabiyar Malik brown color ta na mika mishi
a hankali ya fara takowa ya karbi jallabiyar ya saka ,
ya na sakawa Idanunsa su ka sauka saman dressing mirror , nan ya ga gashin kansa har yanzu white color ne
zaro idanu ya yi da karfi ya na kallon kansa , a rude ya kai hannu ya fara shafa gashin kansa ya na janyo sa gaban face din sa
kamar wani zarrare ya ke fadin " momy , my hair , what happened ? ya a ka yi ya koma white haka ? "
cikin sanyin murya ta ce " Prince , calm down ba abun da ya faru "
" kamar ya na kontar da hankalina ? momy gashina ya koma white ki na ce min na kontar da hankalina , i'm sick ? ko dai ruwan nan ne ? tsaya ya ma a ka yi Daddy ya fito da ga cikin ruwan ? ni ban ga lokacin da ya fito ba ? "
wata yar karamar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta lumshe idanunta a hankali , ta ware su , sun koma farare kal dama kayan jikinta white color ne , ta bude baki a hankali ta ce " Abyad , fito ina son magana da ke "
ta na rufe bakinta ko Idanun Prince su ma su ka koma white color , nashi na komawa white nata kuma su ka sauya su ka dawo dai'dai
cikin nitsuwa ta ce " Abyad , me ya sa har yanzu gashinsa ya tsaya fari ? "
wannan karan ba Muryar Prince na jiyo ba , muryar Abyad na jiyo ta na fadin " momy , ni ma ban sani ba , momy sai kun yi hankali , na ga wani abu da ya tayar min da hankali "
" ni ma ina ji a jikina kamar a na bibiyar mu " ta fada ta na takowa a hankali ta zauna bakin gadon
a hankali shi ma ya tako ya zauna , sannan ya ce " momy ba bibiyar ku a ke yi ba , abun da ke son cutar da ku ya na tare da ku , ina ga saboda tsoron da na ji ne gashinsa bai dawo dai'dai ba , momy wlh ba karamin abu ba ne na gani "
wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta riko hannunsa ta ce " kar ki damu ba abun da zai faru in sha Allah "
gyada mata kai ya yi a hankali kafin ya lumshe idanunsa ya sauke ajiyar zuciya a hankali , kafin ya ware su a hankali , idanunsa sun dawo dai'dai amma har yanzu gashinsa har yanzu white ne
tun kafin ya ce wani abu Inaya ta ce mishi " kar ka damu , gashinka zai dawo dai'dai "
" when momy ? ta ya ya zama white haka lokaci guda , ni dai na san ba na shafa color "
" may be da ga ruwan ne "
" ruwa kuma ? " ya fada a dan rude
gyada mishi kai ta yi kawai sannan ta ce " tashi ka tafi ka yi wanka , may be in ka zuba mishi hot water zai dawo dai'dai "
wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya mike ya fice bedroom din , ya rasa abun da ke faruwa , ya San dai shi ba yadda za a yi ruwa su sauya color din gashin mutum lokaci guda haka , sai dai in wani abu ne a cikin su , ya kuma a ka yi Malik ya fito da ga cikin ruwan , shi dai ya san ba shi ya fiddo shi ba , ba kuma Inaya ce ba , ya a ka yi to ya fito ? da wadanan tambayoyin a kansa har ya baro part din
bangaran Inaya kuma , ya na fita ko ta ida Hayewa saman gadon ta zauna gefen Malik , ta daura hannun saman kansa
cikin sanyin murya ta ce " ban san abun ke shirin faruwa da mu ba , amma na san Allah ba zai bari wani abu ya samu ahalina ba , da a ce yanzu Abyad ba ta fito a jikin Prince ba ta ceco ta ka da ban san ya zan yi da rayuwata ba , na san in har ka fada tekun nan ba za mu taba samo ka a raye ba , ya Allah , ko ma minene ke shirin faruwa ka yi mana tsari da shi , ko wasu makiyan gare mu bayan idon mu ya Allah kar ka ba su damar cutar da mu "
ta kai karshen ta na sauke wata nanauyar ajiyar zuciya , a lokacin ko jiyo Muryar Malik ya na kiran sunanta a hankali
wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta ce " ga ni nan Baby , ba abun da ya faru da kai "
slowly ya ware idanunsa , ya na kai hannu ya dafe kansa dan ba karamin zafi ya ke mishi ba , a sanyaye ya ce " my Cutie , me ya faru ? kaina mugun zafi ya ke min "
" ba komai Baby , kawai ka bugu ne cikin dutse , amma ba abun da ya faru "
ajiyar zuciya ta sauke kafin ya yi kokarin mikewa zaune a hankali ya jingina bayansa a forehead din gadon ya na kallon ta
sai da ya dauki lokaci kafin ya ce " Cutie , fada min gaskiya , na ga sarai lokacin da ruwa su ka tafi da ni , na ga kuma lokacin da gashin Prince ya fara komawa White kafin na suma "
shiru ta yi ba ta ce mishi komai ba dan gaskiya ba ta da amsar da za ta ba shi , ita kanta ba ta san abun da ke faruwa ba
ta na a haka ta ji ya rungume ta a jikinsa , nan take kuka ya kubce mata ta juya da sauri ta boye face din ta a kirjinsa ta na fadin " da yanzu wani abu ya same ka ban san ya zan yi da rayuwata , ba zan iya rayuwa babu kai ba "
wani dan karamin murmushi ya saki kafin ya ce " ki kontar da hankalinki , ba abun da ya faru da ni , kuma in sha Allah ba abun da zai raba mu , ko mutuwa ta zo a tare za ta dauke mu "
dariya kadan ta yi cikin kukan nata
sai da su ka dauki lokaci manne da juna sannan ya sake ta
kokarin sauka da ga saman gadon ta yi ta na fadin " bari na je tara maka ruwan wanka "
da sauri ya riko hannunta
tsaya wa ta yi ta juyo ta na kallon shi ta na tambayar shi me ya faru
marairaice mata fuska ya yi ya na fadin " yunwa na ke ji " ya fada a sanyaye
hararrar shi ta yi ta na shirin rufe shi da fada ya riga ta cewa " ba fa irin wanda ki ke tunani , da gaske yunwa na ke ji "
" shikenan , shiga ka yi wanka zan je na shirya maka abinci "
ba musu ya saki hannunta , su ka sauko gadon tare
ita ta fita , shi kuma ya shiga toilet cikin nitsuwa ya yi wanka ya fito ya shirya cikin wasu pajama blue , sannan ya dawo ya zauna bakin gadon , dai'dai lokacin ta dawo bedroom din rike da tray din abinci da fruits , ta karaso ta zauna gefensa ta ba shi abincin da hannunta kamar wani baby

_ PAID BOOK

*WANNAN LITTAFIN NA BIYA NE , WANDA YA SHIRYA BIYA ZAI IYA TABO WANNAN NUMBER +22795577612 , โ‚ฆ500 NE KUDIN SHIGA PAID GROUP ฦŠIN*



โคโš˜ ๐๐€๐˜๐„๐‹โš˜โค
________________
แด›สœแด‡ ส€แด‡แด›แดœส€ษด แดา“ แด‡xษชสŸแด‡แด… แด˜ส€ษชษดแด„แด‡

THE BIGINING ๐Ÿ•Š๐Ÿ‘‘โค


โค๐Ÿ‘‘ ๐‘ด๐‘จ๐‘ณ๐‘ณ๐‘จ๐‘ฒ๐‘ฐ๐‘ต ๐‘ด๐‘ฌ๐‘ฌ๐‘น๐‘จ๐‘ฏ โค๐Ÿ•Š



https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i



_______________________________________________

_ PAID BOOK

*WANNAN LITTAFIN NA BIYA NE , WANDA YA SHIRYA BIYA ZAI IYA TABO WANNAN NUMBER +22795577612 , โ‚ฆ500 NE KUDIN SHIGA PAID GROUP ฦŠIN*



[ FREE PAGE ___ 19 ๐Ÿ•Š๐Ÿ‘‘โค ]





โ–ชPRINCE ๐Ÿ‘‘


bayan ya baro part din Malik da Inaya , nashi part din ya nufa , saman hanyarsa sai da ya tsaya ya daure gashin kansa a baya sannan , duk in da ya wuce sai dogarai sun dinga bin sa da ido kamar ba su san shi ba , ya na ganin su amma bai kula ba ya ci gaba da tafiyarsa a haka har ya iso part din sa
da Sallama a bakinsa ya shigo parlourn , duk da ma sallamar ba ta fito fili sosai ba , kassa kassa ya yi ta
a hankali ta dago kai ta na amsa mishi sallamarsa
ta na ganin shi ta mike tsaye ta na fadin " Baby , me ya samu gashinka , kuma kayan jikinka ? " ta fada dan ta ga lokacin da ya bar part din , ba jallabiya ba ce a jikinsa
ko sannu bai ce mata kawai ya nufi corridor ya shiga
a hankali ta mike ta bi bayansa , har sai da ta ga bedroom din da ya shiga
shiga bedroom din ta yi , ta na shirin yi mishi magana kawai ta ga ya cire jallabiyar jikinsa ya tilla saman gadon , dama short ne kadai a jikinsa , cak ta tsaya ta zuba mishi idanu ta na zaro su
ta na tsaye a haka har ya juyo su ka yi ido hudu
wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya ce " lafiya ki ka biyo ni ? ko sai na fidda short din shi ma kin gani sannan za ki tafi ? "
wani dan karamin tsaki ta ja ta na kauda kai gefe ta ce " to sai me in ka fidda , a ka ce maka ban san abun da ke ciki ba ne , ni kawai na zo na ga in ka na lafiya ne " ta na gama fadar haka ta juya za ta fita
taku biyu kawai ya yi ya damko hannunta , ya janyo ta ya gama bayanta da bango , ya dafe bangon da hannayansa biyu ya saka ta tsakiya
cikin wata siririyar murya ta ce mishi " yi a hankali mana , haka sai ka ji min ciwo "

cikin tsare gida ya ce " me ki ka ce ? maimaita na ji "

hararrar shi ta yi sama da kassa kafin ta ce " ni ba abun da na ce , sake ni na tafi "

" babu in da za ki je , wai ke bakinki bai iya shiru ba ? a ka ce miki komai za ki iya fada kai tsaye ? "

" to me na fada da ba dai'dai ba ? na ga a gaban mijina na ke " ta kai karshen ta na daga mishi gera ta dago hannu a hankali ta fara yi mishi tafiyar tsutsa da yatsarta saman kirjinsa har zuwa saman mararsa

slowly ya lumshe idanunsa ya sake bude su saman face din ta , nan take duk sigar jikinsa ta mike tsaye

wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya janye hannayansa ya nufi toilet ya shiga ya medo kofar ya rufe

da kallo ta raka shi har sai da ya shiga sannan ta bushe da dariya , ta yi tunanin dukan tsiya zai yi mata dan har wata bugawa zuciyarta ta ke , amma ta ga ba abun da ya yi mata

har ta juya za ta fita wani abu ya ce mata kar ta tafi
ai ko ta bi maganar zuciyarta ta koma ta Haye saman gadonsa ta zauna ta zubawa kofar toilet ido ta na jiran fitowarsa

sai da ta yi wajen good 45 minutes zaune a haka sannan ya fito daure da towel a kugunshi , da wani dan karamin ya na goge gashinsa , sam bai lura da ita ba sai da ya karaso wajen dressing mirror sannan ya gan ta zaune ta zuba mishi
End Ads