x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 26 - NAYEL THE RETURN OF EXILED PRINCE

  • 75001 words
  • 78000 words
  • Out of 89550 words

Category: Love Stories

Views 396

14 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
karaso ta na gaishe da Rianna

da murmushi a face din ta ta amsa mata
sannan Aleenah ta ce mata " Aunty , please ina son ganin Princess , akwai maganar da zan yi mata "

da sauri Faaz ya dago da ga jikin Rianna ya na fadin " wace magana ? "

kare mishi kallo da kyau ta yi ta kauda kai
wata yar karamar dariya RIANNA ta yi kafin ta kai hannu saman kansa ta na fadin " my baby , ba a katse manya idan su na magana "

cikin yar shagwaba ya ce " sorry momy "

murmushi kawai ta yi kafin ta kalli Aleenah ta ce mata " za ki iya tafiya , part din ta na cikin building din Malik , floor na biyu "

da to kawai Aleenah ta amsa mata kafin ta juya ta fice amma sai ta kalli Faaz da kyau su ka yi ido hudu sannan ta fice

da kallo ya raka ta har sai da ta fita
cikin zuciyarsa ya na fadin " dole na ji maganar nan , an ya yarinyar nan ba ta san wani abu a kai na ba ? "

bangaran Aleenah kuma bayan ta baro part din kai tsaye part din Malik ta shiga , a tunanina za ta shiga amma sai na ga ta tsaya a bakin kofar ta bawa daya da ga cikin guards sako da ta na son magana da Princess

ba musu ya juya ya shiga cikin building din
ita kuma ta juya ta fara takawa a hankali ta na kai kawo

ta yi wajen five minutes a haka kafin ta ga guard din nan ya fito , Princess na biye da bayansa ta nufo ta

ta na isowa gabanta ta ce " Hi ! me ya faru ? "

" please mu tafi waje calm haka " Aleenah ta fada

ba musu Princess ta ja ta su ka tafi garden
sai da su ka zauna sannan Aleenah ta shiga maida mata abun da ta jiyo Faaz na fada bayan tafiyarta

mikewa tsaye Princess ta yi ta na fadin " dama na sani , tabbas wannan yaron aiko shi a ka yi dan ya cutar da mu "

ita ma Aleenah mikewa tsaye ta yi ta na fadin " amma momynku ta na bala'in son shi "

" na sani , sai na fara nuna mata wanene Faaz kafin na samo wanda ya turo shi "

karasowa gefenta Aleenah ta yi ta tsaya ta na fadin " ta ya ? idonta fa ya rufe a kansa , ta na son shi da gaske , kuma duk wani makircinsa ba ya yi a gabanta , zai yi wuya ta yarda da abun da za ku ce "

shiru Princess ta yi kamar mai tunanin wani abu
cen sai ta saki wani murmushi ta ce " ke za ki taimaka min "

dan zaro idanu Aleenah ta yi ta na fadin " ni kuma ? "

" Yes , abu na farko da za ki yi , ki samo min sunan gidan marayun da ya gudo , ta haka ne za mu sanin ko shi wanene "

" ni gaskia ba zan iya ba , kuma ta ina zan samo sunan ? kin san dai ba shi zan tunkara kai tsaye ba , in na tambaye shi zai gane wani abu "

" na sani , amma ba shi ba za ki tambaya , momy za ki tambaya , na ji Daddy na ce wa ta na san adopting din sa , kin ga dole sai ta san gidan marayun da ya ke , ki tambaye ta kawai , ita ba za ta yi tunanin wani abu ba "

" da ga nan kuma fa ? "

" da ga nan mu fara investigation a kansa , dan ma wanda zai taimaka min ne ya yi tafiya yau , sai gobe mu fara "

ta na rufe bakinta su ka jiyo Muryar Aleesherh da ga bayan su ta na fadin " me za ku fara ? "

a tare su ka juya su na kallon ta tsaye a bayan su ta tsare su da ido

Princess ta amsa mata da cewa " me ki ke yi a nan ke kuma ? "

wani dogon nunfashi ta ja kafin ta zauna saman sofa ta buga uban tagumi ta ce " fitowa na yi shan iska , Babyna ya tafi ya bar ni , ji na ke kamar na tashi na bi bayansa "

bushewa da dariya Aleenah ta yi kafin ta karaso gefenta ta zauna ta na fadin " sannun ma su baby , irin wannan kewa haka ? dukka fa bai yi two hours da tafiya ba , da ya ce one week zai yi da ya ke nan ? "

" da sai dai mu tafi tare gaskiya , ni ko yanzu ji na ke kamar na yi kuka "

murmushi mai dan sauti Princess ta yi kafin ta tako a hankali ta tsaya gabanta , ta sunkuyo , ta kai hannu saman face din Aleesherh ta na ware idanunta kamar wani abu ta ke nema

cikin rudu Aleesherh ta janye face din ta ta na fadin " lafiya ? me ya faru ? "

" yaushe ne First time din da ku ka yi sex ke da Prince ? " Princess ta tambaye ta

dan zaro idanu su ka yi a tare su na kallon Princess ko kunyar tambayarta ba ta ji ba

Princess kuwa ko a jikinta ta ci gaba da fadin " kar ki yi tunanin wani abu , just zan so na sani if your are Pregnant or not , amma ba abun da na gani , may be nan da two weeks na fara ganin alamun , tashi mu tafi wajen Cutie , za ta rage miki kewar Babynki ' ta kai karshen cikin zolaya

ba musu Aleesherh da Aleenah su ka mike su ka bi bayanta su ka nufi part din Malik


*WANNAN LITTAFIN NA BIYA NE , WANDA YA SHIRYA BIYA ZAI IYA TABO WANNAN NUMBER +22795577612 , ₦500 NE KUDIN SHIGA PAID GROUP ƊIN*
*HAR ZUWA RANAR FRIDAY ZAI KASANCE ₦ 300*


β€πŸ‘‘ 𝑴𝑨𝑳𝑳𝑨𝑲𝑰𝑡 𝑴𝑬𝑬𝑹𝑨𝑯 β€πŸ•Š

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i


_______________________________________________



[ FREE PAGE ___ 26 πŸ•ŠπŸ‘‘β€ ]


β˜† SAUDIYA CENTRAL PRISON β˜†

β–ͺIZZAT

zaune ta ke a waiting room saman chair ta zubawa kofar shigowa ido
ta yi wajen five minutes zaune a haka kafin Izayn ya shigo dakin babu ko sallama

ta na ganin shi ta mike tsaye ta na fadin " haba don Allah , tun dazu na ke jiran ka "

bai ce mata komai ba ya fiddo wata yar karamar bottle da ga cikin aljihunsa da wasu ruwa farare a ciki
ya mika mata ya na fadin " sai kin yi hankali wajen aiki da shi "

hannu ta kai ta karba ta na fadin " Ba ku fada min abun da zan yi ba "

a hankali ya tako dab da ita ya kai bakinsa saitin kunnenta ya fara yi mata rada

( πŸ€”πŸ€” ko me ya ke fada mata , da ga ji ba alkhairi ba ne )


da sauri ta ja da baya ta na girgiza mishi kai ta na fadin " gaskiya ba zan iya ba , a ka je a ka kama ni fa ? " ta fada a dan razane

" ba za a kama ki ba , kawai ki san yadda za a yi laifin ya koma kan wani cikin fadar , wanda za a iya kama shi cikin sauki "

shiru ta yi ba ta ce mishi komai ba da alamun tunanin wani abu ta ke yi

" ni zan tafi , ki san yadda za ki yi , da ga yanzu kar ki sake dawowa wajena " ya fada ya na juyawa zai fita

da sauri ta ce mishi " why ? ba ka son na dinga zuwa ? "

a hankali ya tsaya , ba tare da ya juyo ba ya ce " no , Ina son Mai girma Malik ya san da zamana cikin kassar Saudiya , da ga nan kuma ki jira ni a Daular , ba zan jima ba zan fito "
ya na gama fadar haka ya fice

sai da ta dauki lokaci zaune cikin prison din ta na tunaninta kafin ta baro , ta bi hanyar da ta ke bi kullum ta koma Daular




β˜† DAULAR SAUDIYA β˜†



β˜† MISALIN KARFE 8 NA DARE β˜†



Yau dai duk ahalin Malik sun hadu a part din sa , a floor na uku , yau tare duk za su yi diner , da Diya , Nesrine , Tesnim , Abdoul , Rianna , Princess , Azmat , Aleesherh , Aleenah , har da Faaz , sannan uwa uba Malik da Inaya

sai abinci su ke ci su na hirar su gwanin burgewa , musaman Malik ya jima bai tara ahalinsa haka ba su ka yi diner

Ita dai Aleesherh ta yi shiru kanta na sunkuye ta na wassa da spoon din ta cikin plate din ta

ta yi nisa duniyar tunaninta ta jiyo Muryar Inaya ta na fadin " Alee , lafiya tun dazu ba abun da ki ka ci sai wassa ki ke da spoon din ? ko ba ki jin jikinki ne ? "

girgiza mata kai ta yi a hankali , ta na shirin magana Princess da ke zaune gefen Inaya ta riga ta cewa " Cutie , ba wani ciwo da ta ke , kawai ta na kewar Babynta ne " ta kai karshen ta na wata yar karamar dariya

wani dan karamin murmushi Malik ya saki kafin ya ce " to sannu ke kuma , ina laifi dan ta na kewar mijinta , na ga ke ma naki tun da ya tafi bai kira ki ba "

da sauri Abdoul ya ce " Malik , Yaushe Princess ta yi miji ba na da labari ? " ya tambaye shi dan shi yanzu duk yawancin abun da ke Faruwa cikin masarautar ba shi da labari saboda yanzu shi office din President ya koma da aiki , Diya kuma ya na a Fada

murmushi mai dan sauti Malik ya yi kafin ya ce " ka tambaye ta ga ta nan zaune gefenka "

da sauri ta ce " Alee , ba ki fadi abun da ke damun ki ba ? ko ciwo ki ke mu ke na duba ki ? " ta fada dan ta na san kawar da zancen


sai da Inaya ta yi wata yar karamar dariya sannan ta ce " Alee , rabu da wannan , fada min me ke damun ki ? "

murya a sanyaye ta ce " ni ma ban sani ba momy , tun da yamma nana ke jin gabana na faduwa , kamar wani mugun abu na shirin faruwa "

a hankali Malik ya dafa shoulder din ta dan dama a gefen hangunsa ta ke zaune , cikin sanyin murya ya ce mata " ki kontar da hankalinki , ba abun da zai faru "

ya na gama rufe bakinsa su ka jiyo wayar Diya ta na ringing

a hankali ya mike tsaye ya na fadin " ku ci gaba bari na amsa "
da to kawai su ka amsa mishi sh ka ci gaba da cin abincinsu ba wanda ya ce ufan dan Aleesherh ta kashe musu jiki

Diya kuma Parlourn ya koma ya zauna , sannan ya dauki kiran ya kai wayar a kunne ya na sallama cikin nitsuwa

a daya bangaran Muryar wani Matashi na jiyo ya amsa mishi sallamarsa kafin ya ci gaba da fadin " Please ina son magana da mai Girma Malik "

" Da shi ka ke magana " Diya ya fada

sai da ya dauki lokaci kafin ya ce " Ranka shi dade , na kira ne da ga kassar London a UK , dan sanar da kai Jet din Yarima ya tashi da Bomb , a cikin airport din kassar "

" What ? " Diya ya fada da mugun karfi ya na mikewa tsaye har ya saki wayarsa ta fadi kassa

nan take hankalin kowa ya dawo kansa , sai innallillahi wa'ina illaihi raji'un ya ke furtawa kassa kassa

da sauri Malik ya mike ya nufe shi ya na fadin " Diya ? what happened ? "

a rude Diya ya shiga ce mishi " Malik , Jet din su ne Prince ne , ya tashi da Bomb a cikin airport "

wata razananiyar kara Aleesherh ta saki ba tare da ta sani ba ta na toshe bakinta da dukka hannayanta biyu

da sauri Aleenah ta rungume ta
kamar za ta yi kuka ta ce " sai da na ce muku ina ji a jikina wani abu zai faru "

" please ku kontar da hankalinku , ba abun da ya faru da Prince , ba su cikin Jet din " fadin Malik

a tare duk su ka ce mishi " ba ya cikin Jet din ? ta a ka yi ka sani ? "

" sun ce a cikin airport ne , may be ba su kai ga shiga bomb ya tashi da Jet din " ya fada ya na son kontar musu da hankali

su na a haka su ka jiyo wayar Aleesherh ta na ringing
hannu Aleesherh ta kai saman table ta dauki wayar ta na kallon screen din
lambar ta kassar UK ce , kawai sai ta kashe kiran dan a tunaninta dan su ce mata Jet din Prince ya tashi da Bomb ne su ka kira ta ko kuma su ce su na Hospital

ta na kashe shi ko wani kiran ya sake shigowa
wannan karan ba ta kashe ba , ta dauki kiran ta kai wayar a kunne ta na jiran ta ji abun da za a ce mata

kawai sai ta jiyo Muryarsa ya na fadin " Yaushe ki ka fara jin tsoro haka ? ba sace ki za a yi ba "

da sauri ta mike tsaye ta na fadin " Baby ? ba abun da ya same ka ? "

" please kontar da hankalinki , ba abun da ya same ni , please ki kai wa Daddy wayar ina son na yi mishi magana "

a hankali ta fara kuka ta na fadin " don Allah ka dawo , kar wani abu ya same ka "

" ki fara ba ni Daddy please " ya fada a sanyaye

ba musu ta sauko wayar ta nufi Malik ta mika mishi ita , ta na zubar da hawaye

hannu ya kai ya karbi wayar sannan ya kai ta a kunne ya na fadin " Prince , ba abun da ya same ka ? ina Junior ? "

" ba abun da ya same ni Daddy , just Junior ya samu dan rauni a kansa , bayan haka ba abun da ya same mu "

" shikenan Allah ya kara kiyaye gaba , yanzu yaushe za ku dawo "

" kun san dai Jet Ι—ina ya tashi da Bomb ko ? sai kun turo mana wani jirgin za mu iya baro kassar "

wata yar karamar dariya Malik ya yi kafin ya ce " shikenan , gobe ina sa Helicopter ya je ya dauko ku "

" okay Daddy , sannan please ku kula min da ita ba na son ta saka damuwa a ranta , sai na zo " ya na gama fadar haka ya katse kiran

sauko wayarsa Malik ya yi a hankali sannan ya mikawa Aleesherh kayanta ya na fadin " kar ki damu , ba abun da ya same shi , gobe za su dawo , Princess ! please zo ki kai ta bedroom Ι—inki ta kwana a nan gobe sai ta koma part Ι—inta "

da to kawai Princess ta amsa mata kafin ta karaso ta riko hannun Aleesherh su ka shiga corridor ta wuce bedroom din ta da ita

sai da su ka bar wajen sannan Malik ya kalli sauran mutanan wajen ya da ce " please ku kontar da hankalinku , ba abun da ya same su "

da to kawai su ka amsa mishi sannan su ka yi mishi sallama kowane ya tafi part din sa
sai da Malik ya kwantar wa Diya hankali ya tabbatar mishi ba abun da ya faru da su , sannan ya raka shi har part din sa su na tattaunawa a kan abun da ya shafi masarautar , akwai wata shawara ta musaman da su ka yanke amma ba za su fadawa kowa ita ba sai an yi arba-in na rasuwar MALIKAT INAS

( ko ma minene mu na jira mu ji 😌😌 )

bayan ya raka shi kai tsaye part din su ya koma , ya wuce bedroom din sa
ya na shiga ko ya tardo Inaya zaune bakin gadon ta zubawa kofar shigowar ido da alamun tunanin wani abu ya ke

a hankali ya juya ya rufe kofar ya saka mata security , sannan ya tako a hankali ya zauna gefenta

sai da ya dauki lokaci kafin ya ce " ina tunanin mutum guda ne ya yi wannan aikin , wanda ya ke son ganin bayan Prince shi ne ya yi sanadiyar Ammie "

wata doguwar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce " ni ban ma san abun da zan ce a kai ba , duk yadda a ka yi wanda ke mana wannan aikin ya na a tare da mu , in ba haka ba ta ya ya san Prince ya tafi UK , har ma ya na shirin dawowa "

" haka ne , yanzu me ki ke so mu yi ? "

a hankali ta juyo ta kalle shi , ta saki wani dan karamin murmushi ta ce " me fa za mu yi ? mu zuba ido mu ga abun da su ke shirin yi mana "

wata yar karamar dariya ya yi kafin ya janyo ta jikinsa , sannan ya kwanta ya yi mata runfa da kirjinsa
ya na kallon cikin idanunta ya ce
End Ads