na yi magana yayin da nake sauka kasa na zauna gaban abincin daa Barira ta ajiye na bude food flaask din wanda yake dauke da hadadden dafin kaza ina da tabbacin innani ne tayi da hannunta yanda kamshi ke tashi har wani haadiyan saliva nake,
ba bata lokaci na dauaki plate da serving spoon na zuba deden wanda zai isheni da kunun kaya wanda yaci kwakwa da dabino,
batare dana bi takan Innani da zancenta baya karewa ba na hau bawa cikina hakkinsa,
Islam ma saukowa tayi ta jona ni
"tohhh iyan miskilanci abinda aka iya kenan aci akoshi ba abinda akecewa sai danne dannen munafurci,"
ba wanda ya kula ta har ta karaashi mitarta ta gama ta fice mun ci abinci ko takan shinkafa da miyan ma bamu bi ba munkoshi da nama munyi hani'an Innani ta dawo flaask din shinkafan ta bude ta ce
"dama nasan zaa rinaa ai yara kamar yayan mayu sai cin nama baza kuci abinda zai sa kuyi jiki ba sai cin nama gakunan zagalau zagalau kamar bishiyan dibino,
sai stayi ba jiki da uban kirji kamar jaka ga uban kunkumi kamar kujeran stakar gida,"
for the first time Islam ta daga kai taga Innani ta tabe baki tace
hmm hajiya innancy kenan in batayi magana ba kice miskila tayi kince zarar zance baa iya miki kamar stohuwar babur
"ku kuka sani yan stelen uwa kunga tafiya ta kuma ku tabbata yau ku zaku dafa aabinci agidan nan dan bazai yiwu ace yan mata kamar ku basa aikin komai ba wanda ko yau ko gobe in miji ya fito zaa iya musu aure,
ku zauna kasakai bakwa komai bazai yiwu ba baku iya komai ba sai danne dannen munfurci ,
kajimin stohuwar nan mune bamu iya komai din ba loakcin da kika kori Barira ai naga ke kike komai agidan ko,
anyi din ai tuna tar dake nake don naga stufar nan ta fara dagula miki lissafi
"tohh ko made mai ne ne sai kunyi abinci yau a gidan nan,"
tohhh munji zamuyi Allah raka taki gona stohuwa kawaai
"wato wannan yahh da rashin mutunci kike shegen stiwan stiya mutum ba dama amasa zance sai ya mayar,"
hmm murmushi nayi nace Innani kenan ai in kura ya manta barewa bai manta ba,
anan dake kika ce dani baki yadda wani ya fadamun zance batare da mayar masa ba,
baki yadda ba galala ๐คคInnani ta sake baki tana kallonta tace
"lalle kam kuma shine nace kici mutun cin har da ni yar costi ai nace in mutum ya fada miki bakin zance ban yadda kiyi shiruu ba,"
tohhh ke farar zance kike fada mun da zanyi shiruu in ganki ai kema kin san barewa bazai yi gudu danshi yayi rarrafe ba gado kuma ba karam bani ni bane,
bata ce komai ba ta kama hanyan futa sanda ta futa ta leko tace
"kuma wallahi ku fito kuyi abincin dare,"
murmushin Daya kusan daskarar dani Islam ta sake tace
"kuna dasawa keda mutuniyarki ,"
hajia Innancy kike ji muyi fada muyi dadi Allah kaunarta nake yi ina jinta a qalbi na ita din ne sai a sulo in baka bata wuta ba zata karka da bakin ciki,
amma irin kaunar data ke nuna mun ko Momy data haifeni bata nuna munshi,
har yau in bani da lafiya ta ringa kuka kenan kuma haka zata kwana idonta biyu tana gadina,
.adalilina fa suka raba gari da dan uwanta suka dena zumunci ta raba gari dasu dame zan saka mata a duniya,
bani dashi wallahi murmushi kawai Islam tayi ita kanta ta shaida kaunar dake stakanin Innani da Mahnoor baa shiga stakaninsu ko kadan in ma kashiga kai zakaji kunya.
ba tare da sun bi kan zancenta ba na girki ba suka cigaba da harkan gabansu bawai dan baza suyi ba aa lokacin ne da saura dan ko laasar ma baayi ba infact kaarfe 2 nema kaawai rikicin ta ne ya mosta.
CAIRO [ EGYPT]
Kamar yadda ya fada hakan kuwa akaayi sun yi shiri zasu je Egypt wato Capital na Cairo anan Sultan Muhd Habibullah ke rayuwa shida matarsa da kuma babban dansa Malik Sultan.
wannan itace daya daga cikin rules na Kingdom din sarki ne kadai ke rayuwa a Kingdom shida iyalinsa wanda ke Cairo wato City na Kasar Egypt,
.alokacin da yayi murabus kuwa zai koma Egypt da zama inda acan ma wata mashahuriyar Kingdom din ne sai de na Cairo ita keda ikon zartar da hukunci,
ta kasance daya daga cikin shahararrun Masarauta a duniya wanda ke dauke da tarihi tun kaka da kakan ni ta kuma kasance Masarauta na fari ko ince larabawa na farko wanda tarihi ta shaida su ta hanyar hada jini suka fara da FULANIN NIGERIA,
maana su ruwa biyu ne wato HALFCASS hakan ya farune da dadewa tun lokacin SULTAN ABDULMALIK DA MATARSA MALIKAT ZULAIHAT wanda ta kasance cikakiyar bafulatana na kasar Nigeria ya ga sarkin Kano.
Sultan Salahuddeen ya sanar wa iyayen sa cewa suna hanya zasu zo dan tattauna wani magana mai mahimmance,
ta bangarensu sun gama shiri ayanzu jira kawai suke ta tashi daga bacci,
suna zaune adakin sun sata gaba sai kallonta suke tayi,
dan mosti taa fara wato alaman zata tashi daga bacci ahankali ta bude lulu eyes dinta ta zuba su a fuskar Malikat Najda,
[ Queen Najda]
murmushi mai kayatarwa ta sake tace
"Momy,"
tana kokarin tashi da sauri ta tallafeta itama murmushin takeyi tace
"kintashi Binti ya kike ya jiki,"
murmushi kawai take sakewa kamar zaucecciya gyaran muryan dayayi ne yasa ta juyawa aiko tana kallonsa ta kan kame Malikat Najda tana boyewa ajikinta
"shhh dont be arfraid sweery he wont hurt you he is your Father,"
ahankali kamar Mai koyon magana tace
" Father"
gyada mata kai tayi tace
"your Dady,"
" my Dady ,"
ta fada tana murmushi tana mika masa hannunta alaman ya kama batare da tabar jikin Malikat ba sai ta zamto tamkar baby mai dafa,
.mastowa yayi kusa da ita ya kama hannunta da kyau yace
"how are you little one,"
.murmushi kawai take sakewa tace
"I love you Dady and Momy,"
murmushin da basu shirya yiba suka sake lokaci daya a kusan tare suka ce
"we love you too sweery ,"
murmushi take ta sakewa kamar mai tallen maclean
"okay now lets dress you up RINAA,"
[ Queen]
mikewa tayi da ita ta wuce dressing aroom don shiryata Sultan Salahuddeen sai binsu yakeyi da kallo tamkar zai maidasu cikinsa haka yakeji wani farin ciki ya keji marar misaltuwa
[ sai yanzu ni mahirah nake kallon kurilla a dakin ]
wani irin jibgegen daaki ne mai dauke da Royal faint da Royal furnitures wato golden colour ne da dark blue,
gadon jibgege ne inka ganshi kamar da gold aka yi wani hadadden labule ne yake kewaye da gadon,
acikin dakin harda farlo madaidai ci da jibgegen plasma tv,
akwai dressing room wanda anan closet yake sai tafkeken toilet wanda da zaran ka shiga zaka manta a wani duniya kake don sam baiyi kama da bathroom ba,
staya zayyano muku kyan wannan room din bata lokaci ne cikin kankanin lokaci ta shiryata cikin abaya Maroon colour wanda yabi laafiyar jikinta da surarta ya kwanta kyakkyawan gashinta yasha gyara sai tashin kamshi yakeyi
"Mashaallah,"
shine abinda Sultan Salahuddeen yac
" kunyi kyau you look so amazing ,"
cikin murmushin da baya daukewa a face nata tace
"thank you Dady,"
" okayy lets go nasan right know guard are waiting for us,"
veil dinta ta yafa mata suka sata a stakiya suka fito daga dakin acikin tan kamemen farlon suka bayyana kafun shima suka fito saukowa sukayi daga stairs cikin wani katon farlo wanda sai ka kure tafaiya kaafaun kasamu kujeran zama bayan wuce farlo biyu da sukayi,
suna saukowa servant suka hau basu gaisuwa sai de hannu kawai suka daga musu har suka futo balcony na gidan inda convoy na hadaddun cars ke jiransu carpet aka shifida musu wanda ya kaisu har gaban car din su da sauri guard suka bude musu kofan car din suka shiga suka dau hanya suna tafiya cikin isa da gadara,
basu staya a ko ina ba sai CAIRO INTERNATIONAL AIRPOT inda aka tana da don parking sukayi parking like always guard ne suka fito suka shinfida centre carpet mai tashin kamshi har cikin airpot din carpet din ya karasa kawanya suka musu hagu da dama suka stattaya aka bude musu cab din car din suka fito
*Mashaallah *
shine abinda na fadi ba karamin kyau sukayi ba Sultan Salahuddeen yana sanya da farar jallabiya sai wani bakin kimono irinta larabawa sai de wannan ya banbanta dana sauran wannan na maabota mulki da sarauta kadai ke sashi,
kanshi ko da hirami wacce aka nadeta yanda larabwa keyi sai de nashi abin nadin tamkar da ruwan gold akayi daga gaban akwai wani dan abu tamkar maballin riga sai de nashi dadan fadi kana gani kasan ba karamin kudi bane wannan abun,
hannunshi ko wani agogone designer wanda sai masu hanu da shuri ke sawa haka takalmin kafanshi wanda yake cover shoe mai daukan hankalin mai kallonsa da tafiya da imani,
wani ni'imanceccen kamshi ne ke tashi daga jikinshi fuskanshi sai fidda haske da annuri yakeyi,
daga gefenshi kuwa Sultana Najda ne ke sanye cikin shigan alfarma wata hadaddiyar fitted gown ne fari wanda yasha bead work sai sheki suke da daukan ido asaman wannan fitted gown din kuwa alkyabba ce wanda basu da maraba da gown din shima fari ne yasha bead work bai kasance katoba ya kasance daidai jikinta da belt nashi da aka daura sai ya zamanto kamar kimono,
kanta anyi rolling da white veil ya fito da cute face nata mai cike da annuri a stakiyansu abun kaunar su ce wato SAFEERA itama na saanye da abaya maroon colour wanda yasha arnen stones masu daukan ido da canja launi,
kanta an yane mata da veil,
sun cigaba da tafiya cikin isa da takama har cikin airpot din wanda jirgi su kawai yake jira dama private jet ne,
jagora aka musu har cikin jirgi wanda yake tamkar aljannan duniya sai baza kamshi yake basu bata lokaci ba suka dau hanyan zuwa Egypt.
CAIRO [ EGYPT]
wassu hadaddun royal cars ne wanda akalla sunkai 15 suke jiran jirgin Sultan Salahuddeen tayi landin don su kaisu masaukinsu wato SULTAN ABDUMALIK ROYAL ESTATE.
basu wani dau dogon lokaci ba jet din tayi landing cikin kankanin lokaci security suka cikaa gurin sanda aka gama cajewa tas kafun SULTAN, SULTANA DA AMIRA suka fito daga jet din,
tana makale jikin SULTANA tun dazun don astorace take ganin jamaa dayawaa agun gani take tamkar zasu cinyeta danya,
har car aka rakasu suka shiga suka dau hanya zuwa SULTAN ABDULMALIK ROYAL ESTATE.
END OF PAGE 12
Queen Mahirah
Comment and share ๐
๐งTHE TWO LIGHTโจ [RIKICIN GIDAN SARAUTA)
Story and written by
Queen Mahirah
ADAPTED EXPERT WRITER ๐๐๏ธ
?26 ?January, ?2024
9:31:16 PM
BOOK 1
FREE BOOK
๐ง14๐ง
Sun cigaba da taafiya bisa shimfidaddiyar kwaltan daya ya kaisu har hadadden estate din wato SULTAN ABDULMALIK ROYAL ESTATE.
Ya kasance estate mai dumbin tarihi da dogon zamani.
ya ginu tun lokacin Sultan Abdulmalik lokacin dayayi murabus daga karagan Mulki ya daura dansa wato SULTAN MUHD HABIBULLAH,
inda ya baro Cairo ya dawo Egypt da zama shida iyalinsa ya bar dansa acan,
sai ya ksance duk wani dan ahalin ya dawo nan da zama ya zamanto FAMILY HOUSE nasu duk wani jinin Sultan Abdulmalik anan yake rayuwa shida iyalinsa.
guri ne mai matukar girma tamkar gari kowa da sashen shi suna rayuwarsu cikin kwanciyar hankali da kaunar juna duk da na ciki na ciki baa rasa yan kustiri stome,
kamar yadda kuka san kowani Family da irin nasu mastalan bare gidan sarauta wanda shine matattaran mastaloli,
duk da haka in ka gansu sai sun baka shaawa yadda kansu yake a hade a zahiri,
a mastayinka na bako baka isa ka fahimci wani abu dake faruwa mara kyau a stakaninsu ba,
suna kokaarin hada kansu a idon duniya,
a kowani karshen wata sukan hadu donyin GET TOGHETHER hakan na kara musu hadin kai duk wani dan family yakan halatta wannan taron don ya zama dole ako ina yake a fadin duniya dole yazo,
sun sanu a fadin duniya sabida wassu baiwa da Allah ya musu Allah ya azirtasu da kudi,ilimin addini dana boko, uwa uba kyau da kwarjini Allah yamawa matansu da mazansu wannan baiwan,
kadan daga cikin abinda ya yasa suka sharah suka kuma sanu a fadin duniya kasncewarsu HALF CASS wato ruwa biyu na daya daga cikin abinda yasa su shaharah suka kuma yi suna sannan suka zama abun kwatance a fadin duniya,
iliminsu na both arabi da boko ya taimakesu wajen gudanar da mulkinsu a zamanan ce bisa tafarkin musulunci,
kyansu shi ke kara jan mutane garesu da arzikinsu daya sa musu kwarjini a idon mutane,
Allah ya musu baiwan shiga ran mutane suna da shiga rai duk yawancin su a murde suke baya ga haka suna da manya a familyn su wanda suke da manya makami a fannoni da dama,
suna da duk wani nau'in maikata kama daga land army ,navy, airforce,pilot, doctors, lawyers, prsecutors...., da sauransu yana daya daga cikin abinda ya karamusu karfi ya kuma tara musu dinbum makiya na ciki dana waje .
Basu staya ako ina ba sai bakin wani tamkamemen royal gate black and golden gate din na raga ne so kana iya hangen abinda ke ciki ita kanta gate din abun kallo ne daga hannun dama akwai wani computer wanda daga nan mutum yake neman izini ana kallon ka daga ciki wato security dake ciki na kallon ka daga nan sai sun tabbar da wayene kafun ake bude ma gate don shiga,
already sun san da zuwan Sultan shiyasa basu staya bincike ba gate din da kanta ta bude a wani slow motion hakan ya kara kayatar da abun,
danna cars din sukayi cikin wannan Estate din ko ina securitys ne gurin ya mugun staruwa staywa kwtan ta tashi ma bata lokaci ne,
sun cigaba da bin wannna shinfidaddiyar kwaltan wanda gefe da gefenta shinfidaddun flowers ne msu tashin kamshi da daukan hankali.
tako ina a shimfide yake da interlocks da flowers sun wuce gate har uku kafun suka isa wani tamkamemen Building Wanda na hango kmr castle,
wni water fall ne stakiya wanda yake kewaye da kwalta wanda dole sai kabi kafun kayi parking hakan kuwa sukayi kafun sukayi parking,
zugan securities suka musu kawanya as always sun shinfida royal centre carpet wanda yayi leading nasu zuwa main door din building din, cab din motan aka bude musu suka fito sukayi ciki,
wani tafkeken farlo ne mai kayan more rayuwa katon gaske ne mai dauke da kayan alatu da kyalekyali masu daukan sense,
.bayan wuce zafafan farlo uku da sukayi Wanda servant ke aikin bude musu kof,
ta ko Ina kwasar gaisuwan servant din keyi Wanda ko amsawa basa Yi ,
sanda suka zo bakin kofan farlon Wanda yake tamkar da zinare akayi golden colour ne kofan gashi dagirman gaske jikinshi ko anyi mishi ado da wassu duwastu Wanda Ina kyautata zaton lu'ulu'u ne da murjani harma da diamond ๐ ,
Suna bude kofan suka ja baya suka staya su Kuma suka karasa ciki kasancewar bako wani bawa ne ke da iKon shiga ba sai Wanda aka yardar masa.
basu staya a ko ina ba sai wani sashi a farlon wanda yake dauke da wassu zafafan furnitures masu shegen stada da daukan hankali da walwalin su,
zaka ranste da gold akayi yanda suke sheki da daukan eyes ๐ daga sama ko wani narkeken chandelier ne Wanda akayi shi da danyen zinare wato white gold,
Tiles din farlon kuwa dauke yake da tambarin masarautan Wanda ya Kara kayatar da komai hatta silin din falon zaka ranste da glass akayi yanda yake walwali ga wassu duwastu Wanda ke walwali da kansu suna daukan ido ๐,
hango wassu kyawawan larabawa su hudu nayi suna sanye da kayan alfarma maza biyu mata biyu bakowa bane sai sarki mai murabus da dansa wato SULTAN MUHD HABIBULLAH da dansa ko ince babban dansa wanda yayi murabus ya bawa dansa SULTAN SALAHUDDEEN mulki wato MALIK SULTAN IBN HABIBULLAH
sai matansu SULTANA MARYAM wacce take uwargidan Sultan HABIBULLAH sai MALIKAT NUBIA mata Malik Sultan IBN Muhd Habibullah.
fuskan ko wani daya daga cikinsu dauke da murmushi wanda ya juya firkici da alajabi lokaci daya sanadin tOzali da sukayi da yarinyar dake tafe dasu wanda a iya saninsu yau ta cika shekara daya da rasuwa.
atunaninsu ma wannan shine dalilin zuwan su Sultan d Sultana,
sai de sunga akasin hakan kowa bakinshi dauke da tambayoyi da alajabi wanda ya bayyana karara duk da sun kula da hakan sai de basuyi kasa a guiwa ba wajen karasawa inda suke don su gaisa su kuma samusu albarka kafin su yi abinda ya kawosu,
don anasu lissafin yau zasu koma sabida yau tuesday ba friday ba da friday ne zasu kwana sabida saturday and sunday ba zaman palace.
kamar yadda suka saba gaisuwan su ta larabawa gaisawa suka yi sannan suka yi pecking both cheeks nasu haka matan ma sukayi kafun suka zauna.
ita de sai mannewa takeyi ajikin Sultana Najda har suka zauna Malik Sultan ne yayi kaarfin guiwan tambayansu wacece atare dasu,
murmushi Sultan Salahuddeen yayi kafun yace'' atakaaice muma bamu san wacece ba mun de dauketa a mastayin wani Ilhama da Allah ya mana alokacin da muke wani hali na rashin madogara sai shi wanda ya bamu Rinaa ya kuma karbi abunsa''
"ban gane mai kake nufi ba"
inji Sultan Habibullah sadda kanshi kasa yayi cikin girmamawa yace
"wannnan itace gaaskiyar Jaddi"
ba tare da bata lokaci ba ya kwashe duk labarin abinda ya faaru wanda Sultana Najda ta fada masa ya musu da kumaa wanda yayi bincike ya tabbatar ,