x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 20 - THE TWO LIGHT RIKICIN GIDAN SARAUTA

  • 57001 words
  • 60000 words
  • Out of 97531 words

Category: Love Stories

Views 545

20 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
sani loosing control dina ni Queen Mahirah ,

har alkalamina sanda ya nemi daya fadi lallai godiya da yabo sun tabbata ga wanda yayi wannan kyakyawan halittan,

wani irin annurin haske ne ya fito daga hakorinshi dake fari tas,

gasu ajere ras kamar shi yayi abinsa hakan ya karamishi wani haiba da kwarjini na musamman,

a fannin Fudhal ya raasa ma mai zai yi kawai ya juya ya shige dakinsa,

don ayanda yaga Fahreen ma yayi murmushi yasan tabbas yaji inko ya cigaba da zama tohh fahh kashe shi zasuyi da bakin ciki,

don shima gwani ne wajen stokala amma in ya ga dama,

ga iya zaran zance inya zaro ta kamar igiyan taburma inko yayi abu sai ya starai kamar ba shi yayi ba,

ya iya stokala da neman magana amma inya stare ko kai daya stokalan baka isa kace shi yayi ba bare wanda ka kaiwa kara,

shi yasa dayawan lokaci laifin ke sauka akan Fareed tunda shi aka sani da stokala,


Ban tashi ba sai bayan sallan azahar,

sallah nayi na fito falo na samu Innani da Islam na karasowa nayi na samu guri na zauna Innani kamar ta cinye ta hau ni da tambayoyi

"ya jikin shalelena?

akwai abinda yake miki ciwo ne ?

ko akira Sheik yazo ya duba ki?,"

pls Innani slow down da wanne kike so na fara duka wannan tambayoyin kamar wadda daga ciwon hauka na tashi,

Innani bata kai ga furta maganan bakinta ba aka rafka sallama abakin farlon,

amsa sallaman tayi ta masa iso, Auwal ne ya shigo ya gaishe ta cike da ladabi kafun yace

" dama wani bako ne Malam yace ya shig ciki zakuyi magana dashi don yana da baki shi,"

"tohh Auwalu karaso dasahi ciki mana,"

da toh ya amsa mata ya fita ya iso da bakon suka shigi falon bayan sallaman da sukayi kujera Innani ta nuna mas tace

" bissmillah zauna bawan Allah,"


ba musu ya zauna akan lallausan kujeran falon bayan dannata da ya gama yi da hannu sai washe baki yakeyi,

don shi bai am taba zatan haka gidan yake ba kamar aljannan duniya,

Barira ne ta kawo masa lemo da snacks aiko ba kunya yasa hannu har bibbiyu ya hau danna wannan hadadden snacks din da lemon kwalba mai sanyi,


can da Innani taga abun bana kare ba tace " ina sauraronka bawon Allah mai ke tafe da kai,"

dakyar ya iya hadiye uban donut din daya dura a bakinsa yace

" karan jikanunki na kawo hajiya,"


jin furucin nasa yasa Innani daga kai ta dube mu inda taga kowa na yin abinda ke gabansa kamar basu ganshi bama,

dan muskutawa tayi tace " ina jinka "

sanda ya kara kai wannan donut din baka kafun yace

" wato hajiya albasa batayi halin ruwa ba a sanin Malan danayi mutumin kirki ne gaki kema kina da mutunci dubi fa irin kayan alatun da aka dankaromun,

amma wayannan jikanun naki asararru ne mayaudara kuma maha'inta sun cuce ni sun lalata mun kayan sana'ata,

kuma wallahi sun cimun mutunci a bainan nasi su kirani kazami,

abun da suka mun bazai fadu ba ni abinda na yanke wa kaina shine kawai a aura mun daya daga cikinsu,

ko kuma dukansu tunda ba uwa daya uba daya bane suka haifesu kin ga nima sai in dangwala arziki, ??

kuma shine kadai hanyan da zan yafe musu inba haka ba wallahi na barsu da Allah,

kuma wallahi na ringa musu addu'a Allah ya hadasu da bala'i da masifa ya hanasu mijin aure.....,"

batare daya karasa zancen bakinsa ba Innani ta dakatar dashi

" dakata malam wannan wani irin gidadanci ne da diban albarka,

kai harma da rashin ta fuska a shigo da kai cikin gida har cikin falo kazauna a kujera bayan abin cin da aka baka kake ta faman durawa acikin,

ka gaa sanyin ac da kamsahin turare ai ko wannan ya isa yasa ka yafe musu,

abinda suka maka amma dayake kai dan garin gaba gaba ne marar tarbiya kadubi stabar idona kace wai jikanuna maha'inta,

mayaudara kuma asararru yoh tohh in akwai babban asararre anan ai kai ne,

wai ma ba kai ne Gabdo dan ladanin garin nan ba,

ai in akwai wanda za'a kwasahewa albarka tohh kaine asarare wanda ya fito duniya da buhun asara ubanka ladani amma kai tantiri,

ahaka har kadubi santala sanatalan yan matan nan kace wai nabaka su Allah kiyaye ,

yohh tohh ba gwara ma sun mutu ba aure ba da su auri bakin kazami irinka,

harwai baza ka yafe ba toh karka yafe mana kabarsu da Allah ai dama dashi kasamesu,

kai har kasan Allah nema naga wancan shekarar aka kama ka ka dirka ciki a yar makotanku kuma ka gudu,

sai yanzu ka dawo shine ka kyalla idonka akan jikanuna zubin larabawa ko,

tohhh baka isa ba wallahi inma da maita kazo to ahir dinka wallahi,

don sun sha tabara da lahaula kaga ko sunsha maganin mayu irinka da magauta asararre,"

duk da sallaman da Chief da Fareed sukayi suka shigo bai hana Innani stagaitawa da zazzagawa mai dibino rashin mutunci ba,

shiko yayi kuriii yana kallonta yakasa cewa komai bata yi shiruu ba sanda Chief ya fara mata kirari kamar haka

" yi shiruu gimbiya sarautar mata kinga jiya kinga yau kuma zaki ga gobe insha'Allah,

sabr Khadijatul khair mar'atussaliha,"

" da ka barni Sheik na ci mutuncin wannan marar mutunci wanda bashida ta ido,"


" sabr kibarshi da halinshi," shiruuu tayi bata ce komai ba,


dago kai yayi ya fuskance ni yace" ta'al Noorul Huda ,"

ba musu na taso nazo inda yake ya zaunar dani agefensa yace

" fadamun mai ya faru mai ya hadaku dashi,"

dan sadda kaina nayi tiryan tiryan nabasu labarin abinda ya faru batare danayi kari ko na rage ba,

gyada kai Chief yayi ya dubi Islam yace " Khadijatul Islam haka ne abinda ta fada,"

gyada kai tayi cikin nuna girma tace " ehh Jaddi ,"

ya kuma cewa " Gabdo haka akayi,"

gyada kai yayi don wani kwarjini Chief ya masa na bala'i don ko ido ya gagara hadawa dashi,

" Chief yace fada mun nawa ne kudin kayan ka ,"

cikin rawar murya yace " duka dubu biyar ne,"

gyada kai Chief yayi yasa hannunshi a aljuhun riganshi ya ciro rapper na dubu daddaya ya bashi yace

" gashi ban kuma ce kaje ka lalatllalata kudin ba ahanyar banza irin yadda ka saba nasiha ya sahiga masa mai rasata jiki wanda ya sa sahi zubda hawaye

yace

" insaha'Allahu zan yi amfani dashi wajen gina rayuwata zan kuma dauki shawaran ka ya juyo ya fuskance mu yace na gode,

Allah saka da alakairi dan Allah kuyi hakuri duk laifi nane duk ni naja komai,

dama tun fari baku zo da fada ba ni na fara komai sharrin shedan ne dana zuciya,

dama tun ba yauba nakeson wani kaddara ya hadani daku na cimma burina na son zuciya akanku amma Allah bai bani dama ba,

wallahi tun baku kai haka ba nakeson yin lalata daku sai de wannan yayan naku shi ke storatar dani dan Allah ku yafe mun nine babban asararre wallahi,"

stegege Innani tayi tace " lahaula kace shirgegen azzalumi ne kai bamu sani ba,

ai ni sai yanzu na gane ka wato ma kaine wanda kaso haike mun kan shalelena tun bata fi shekara 9 ba,

bakai ne ba wanda Sheik fetel yamawa dukan mutuwa ranan,"

fashewa Innani tayi da kuka ashe ma kai kasungumin azzalumi ne bari in dauko wayata saina kira Sheik fetel yazo ya cimun ubanka dai dai gwarwado ,"

aiko jin haka yasa ya rarrafa har inda take ya kama kafanta ya fashe da kuka ??

" dan darajan annabi kimun rai na tuba na bi Allah wallahi jikan ki din nan sakago ne,

wancan karan ma daya jibge ni sanda nayi shekara ina jinya ,

bare yanxu daya zama soja kuma kato dan Allah karki hadani da basamuden jikanki wallahi zai kashe ni wancan karan ma fa shekaru shi 18 ne bare yanzu daya kai 29,"

Chief yace " yi hakuri Nana Khadijatu ki barsa yanzu na roki alfarma a maima konsa,"

tun kude shi tayi bata ce komai ba ta zauna sai huci takeyi ita kadai,

Chief yace " tashi kaje sun yafe maka,"


"tohhh na gode Allah saka muku da alkairi Insha'Allahu rayuwarku zatayi albarka,

zaku ga da kyau makiyanku kuwa sai de su ganku da ido kunfi karfinsu amma wallahi da kunyi aure don irina suna da yawa masu son lalata muku rayuwa,"

"wato bakinka bai yi laushi ba inji Innani,"

"aa hajiya na ma tafi sai anjima har tuntube yake ci yabar falon"


murmushi kawai Chief yayi ganin sai kumbura takeyi ita kadai


END OF PAGE 24

Follow this link to join my WhatsApp group and shower ?? me with comment and react ????????

https://chat.whatsapp.com/DEb6DCrj50r88WN25D5xu9

COMMENT AND SHARE ??




🧚THE TWO LIGHT✨ {RIKICIN GIDAN SARAUTA🏰}


Story and written by
Queen Mahirah
ADAPTED EXPERT WRITER 📖🖊️



BOOK 1

?Thursday, ?February ?29, ?2024
12:49:30 Am

🧚25🧚


Murmushi Chief ya sake ganin yadda Innani ta hade rai sai tattauna magani takeyi ba shi kadai ba hatta Fareed ma murmushin yake sakewa akai akai wani nishadi yakeji kallonsu ahaka sun mugun dibe mishi kewa sai yake ganinsu kamar wasu film rayuwarsu ya burgeshi,

yanayin yadda suke kaunar junansu da mutunta juna abin burgewa ne,

ga zallan kaunar dake wanzuwa a stakaninsu kallo daya zaka musu kasaan suna mugun kaunar juna ko yanayin da suke mu'amalantan juna ma ya isa ka shaida hakan,

ba abinda ya burgeshi kamar yadda aka bi komai a sassala har aka war ware case din,

yanzu da a masarautar su ne ai da an dade da yanke musu hukunci don abinda mutumin ya fada dashi za'ayi amfani,

ya dube ni yace " sannu ya jikin naki "
dago dara daran eyeballs dina nayi na zuba masa na yan seconds kafun nace da sauki na kawar da kaina ta hanyar sadda shi danayi,


murmushi yayi yace " tohh Allah kara sauki,"
akarkashin makoshi na na
End Ads