x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 32 - THE TWO LIGHT RIKICIN GIDAN SARAUTA

  • 93001 words
  • 96000 words
  • Out of 97531 words

Category: Love Stories

Views 548

20 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
kara lokaci har zuwa lokacin da zata dawo cikin hankalinta,

a yanzu takan hasaso abu dayawa akan auren musamman inta hasaso cewa inta dawo hankalinta akwai possibility din da zata iya cewa bata son auren ko bata son shi Mahbeer din, Wanda in Hakan ya faru tabbas babu makawa dole a raba auren ɗon baza ta lamunci ganin ta cikin wani yanayi ba musamman cikin ƙunan rai, kuma koda ita bata bukaci hakan ba tasan sarai Master zai raba auren inhar ta nuna bata son hakan , wani dogon numfashin taja a karo na biyu wanda ta yi shi a bayyane.


Cikin yanayi na yarinta wanda ya bayyana ƙarara a fuskarta ta kama hannun Sultana Najda da yake gefen fuskanta da nata soft hand din dake wani kaamshi na azo a gani mai gigitar da hankalin ma kusancin shi ta ce "Mima nayi miki laifi ne?,"

Murmushi Sultana Najda ta sake mai cike da zallan ƙauna da nustuwa kafin ta ce"waya ce Miki kin yi laifi, ai Aroosa (bride, Amarya) bata laifi,"

Murmushi ta sake kafin ta ce "really, but why do you look sad naga mood ɗinki ya canja, is there anything wrong?,"

Nodding kanta tayi kafin ta kamo duka hannun Zawjatul Ameer da nata hannun ta mikar da ita murmushi tayi ta ce,


"Mashaallah ɗiyata ta girma, ba abinda ya faru Hooriyya 😇 an so happy kin girma kin kai aure, at the other hand I pitty my self cos zan rasa ki by my side zaki zama mallakin Beer not my kin tashi daga Hooriyya kin koma Zawjatul Ameer mai cikakken iko, I don't know whether you can handle the position and the responsibility?,"

Murmushin da ya zame mata ruwan jikinta ta sake cike da shagwaba da yana yi na juyewar brain ta ce " don't worry Mima I can handle it, remember am a change person, I have already grown up."

Murmushi kawai Sultana Najda ta sake kafun ta kamo hannunta ta ce " let's go ,"


Cike da ƙasaita suke tafiya bisa wani haɗadden white center carpet Wanda aka mishi ado da wasu golden flowers Wanda suka ƙayata Centre carpet din, da zallan Izza suke taku ga wani ɗaukan ido da sukeyi na ban mamaki, wani walwali da sheki gurin keyi kasancewar an zan zara masa ado na ban mamaki,
sun cigaba da tafiya bisa shinfidadden Royal centre carpet din wanda ya sada su da hadadden stairs din da zaiyi leading dinsu zuwa hamshakin farlon da yasha ado na alfarma, duk da dama farlon ba baya bane wajen haduwa, sai de na yau din daban ne kasancewar anan za'a gudanar da taro.

komai na farlon an mishi ado da white and golden colour, ga wani kanshi na alfarma dake tashi, tafiya suka cigaba yi yayin da Sultana Najda ke rike da hannunta kallo daya zaka musu ka hango zalla ƙauna dake wanzuwa a zukatan su Wanda hakan ba karamin burge mutanen dake farlon yayi ba da daukan hankalin su kowa yana fadin albarkacin bakinsa, ga mahassada kuwa na ciki na ciki.

ko wani takun su daya yana tafiya da bugun zuciyar mahassada da makiyan su, sun cigaba da tafiya har suka sauko daga stairs din yayin da suka cigaba da tafiya bisa carpet din har suka isa inda aka tanadar musu dan zama.

Suna isowa kowa dake farlon ya mike cike da girmamawa kai a kasa, Sultana Najda bata kai ga zama ba sanda ta tabbatar ta zaunar da Zawjatul Ameer cike da tsananin soyayya da kulawa sannan itama ta zauna a mazaunin ta, cikin nustuwa da Izza daya bi ko wani ƙusurwa na jikinta 'tayi alama da hannunta alamar kowa ya zauna, ba tare da bata lokaci ko kara wani sakan ba suka zauna, yayin da kowa ke kokarin tura nasa sakon gaisuwan cike da bukatar samun matsuguni a wajen Sultana Najda da ita kanta Zawjatul Ameer, Kasancewar Sultana Najda mutum ne mai tsananin ƙwarjini da kuma kamewa hadi da rashin son reni, Bata fiye sa kanta a abinda be sata ba haka kazalika bata ɗaukan reni, bugu da ƙari mutum ce mai karancin magana wato miskila ce ta bugawa a jarida,


Ta kasance daya daga cikin shahararrun mata dake tashen kyau da iya ɗaukan wanka ta kasance cikin jerin Top five world best Queen.

Ta sharaha ta kowani fanni, kyau ilimi both Arabic da boko, a fannin kwalliya da iya ɗaukan wanka i can say she is being count out as the world best fashion model.

yanayin jikin ta baya nuna girmanta kai tsaye idan baka sani ba baza kace ita ta ajiye Young handsome billionaire PRINCE MAJOR GENERAL UMAR MAHBEER mastayin ɗa.

Kasancewar ta mace mai gyara kaanta komai nata na daban ne, takan yi order kayan amfani ta daga Company like perfume, toiletries da sauran su, ko kayan da zata sa fasalin su daban ne kasancewar a ita kadai ake producing kayan,
yana daya daga cikin abin da yasa mata dayawa keson rabarta sabida su kasance cikin shafin mujalla (magazine)ta farko wace ko wani rana sukan wallafa labarai kasancewar su shafun sada labarai da ya yi shura a fadin duniya,

Sultana Najda ta kasance mutum na farko dake bayyana a wannan shafin ta fannin ado da kwalliya da kuma sauran ɓangarorin, Kasancewar komai tayi abin burge wa ne ga jama'a.

Duk da kasancewar ta mutum mai kamewa hakan bai hana ta taimakawa marassa karfi ba sannan Bata kasance daya daga cikin masu karfin mulki dake wulakanta marassa ƙarfi ba, Wannan kenan.

Cikin nustuwa da Izza daya bi ko wani ƙusurwa na jikinta ya samu gurin zama ta dago lulu golden eyes dinta tabi ko wani daya daga cikin su dashi cikin abinda bai fi sakanni biyu ba ta ƙauda kanta batare da tace musu komai ba,

Ganin haka ne yasa daya daga cikin su wacce tafi kowa kamewa da nustuwa hadi da kyan haiba,kana ganinta kasan karatun addini yabi jikinta, cikin siririyar muryanta ta fara magana kamar haka "Assalamu alaikum warahmatullah ta'ala wabarkatuh yah Akhawaat,"

Cikin girmamawa ɗaukacin matan dake farlon wanda ko wace daya daga cikinsu ke ji da kanta ta fannin ado da kyau da kuma arziki wanda kana iya kallonsa azahiri kasancewar abubuwan da sukayi amfani dashi wajen ƙawata kansu gold, lu'ulu'u, zinare da sauran su,

sai de duk wannan ado ba wacce ta ko kamo hannun Sultana Najda bare kuma muje fannin Zawjatul Ameer da ke tashen kyau kasancewar ta mai karamin shekaru, ga hutu daya bi ko wani ƙusurwa na jikinta.

Amsa mata sallmar sukayi kafin ta cigaba da cewa "Alhamdulillah godiya da yabo sun tabbata ga Allahu subhanahu wata'ala daya kawo mu wannan rana mai tarin albárka, badan komai ba sai dan gabatar da wannan muhimmin taro da muka gada daga kaka da kakanni,
yau ta kasance daya daga cikin rana ce mafi tarin muhimmanci agare mu gaba ki daya,

Kamar yadda kuka sani yau rana ce da zamu gabatar da kawunan mu ga Zawjatul Ameer, wato kowa zai gabatar da kansa da matsayin sa a wannan ɗaular mai cike da tarin albarka, bayan an kammala gabatar da kai kowa zai bada kyautar sa ga Zawjatul Ameer,

Bari ni na fara da kaina Sunana Sayyidah Oum suleim Bint Sawban, na kasance shugaban mata ta fannin addini, sunan mijina Sheik Muhd Jabeer,"

Tana gama fadin haka tayi wa wanda ke zaune a gefen ta alama da ta gabatar da kanta, ba bata lokaci itama ta soma gabatar da kanta kamar haka" ni sunana Hidaya bint Ja'afar Ni ce matar Hisham Ibn Abdul Waheed wato Rayiys alhadath,"

tana magana cike da yanga da burin samun matsuguni a gurin Zawjatul Ameer.

Wanda ke gefen ta ne ta karbi maganan ganin cewa ita Hidaya bata da niyan tsayawa duk da ta kammala gabatar da kanta iya yi da gwallami da son cusa kanta ya hanata dakata wa, cikin dakakkiyar muryanta da babu ko digon tsoro da son cusa kai aciki ta fara magana,

" Arya bint Abanoub, ni matar Hamza ibn Abdelwahab (Qayid aljaysh) Army commander,"

Tayi maganan ne a rarrabe batare da ta damu data hade su ba kasancewar ba gurin zama take nema ba abinda ya kawo ta kawai take aiwatar wa wato gabatar da ƙanta,

Sultana Najda ne ta dago kai ta mata kallon rabin sakan kafin ta ƙauda kai cike da salo na ƙayatarwa, tana jin jina irin karfin hali na Arya halin ta na daya daga cikin abinda take jan hankalin ta gare ta, kasancewar Sultana Najda bata ƙaunar mutum mai shishshigi da cusa kai, Itako Arya cusa kai da shishshigi wannan ba sana'ar ta bane.

Sun cigaba da gabatar da kansu da nuna zaƙwadinsu na son samun gurbin zama wanda sam babu wacce tayi nasaran samun hakan.

Bayan sun kammala ne kowa ya fara kokarin nuna shi wani ne wajen bawa Zawjatul Ameer kyauta na alfarma Sayyidah Oum suleim ne ta fara bada nata kyautar wanda ke nade cikin white box da yasha nadi mai ɗaukan hankali, wata murdaddiyar giant ne dake sanye cikin farin jallabiya na mata ta karba cikin ladabi ta fara bude box ɗin don ganin mai ne ne acikin, kasancewar ta mai tsaron lafiyar Zawjatul Ameer wanda aka kawo su daga runduna na musamman na sojoji mata daga kasar Sin (China),

Ware shi tayi tas yayin da wani haɗadden Qur'ani da yasha ado da wasu duwatsu na alfarma ya bayyana, yana nan ɗan daidai wato Medium size, cover shi baki ne wuluk yayin da rubutun jikin anyi shi da golden colour sai wassu tsaddden stones ko ince lu'ulu'u da sauran abun kwalliya akayi amfani dashi wanda ya mai da shi tamkar abin ado, tana gama binciken ta ajiye shi bisa hadadden Royal stool din dake gurin,

Hidaya bint Hisham ne ta Mika nata cike da rangwada karba tayi ta bude shi wani cute small box ne dake dauke da diamond ring mai tsananin jan hankali wanda takai aka mata ko ince ta umarci ɗanta Majeed ibn Hisham bin Abdelwahab,

ya ƙera mata shi kasancewar sa mai hamshakin kamfanin da suke sarrafa abubuwan ado su sarƙa wato jeweleries, ya yinda ta umarce shi da ya ƙera zoben shi kadai bayan tsibbun data cika zoben dashi, ta Umarce shi karya yi su dayawa kuma karya ya ƙera ta a kowa, sanin cewa Sultana Najda bata amfani da abinda aka kera wa wassu sai ita kadai,

Bayan Uwar kudin data kashe wajen yin siddabaru ajikin zoben, wanda wani gagarumin bokanta dake Ƙasar Giza ya umarce ta data yi zoben shi kuma yayi wa zoben wankan tsubbu,

Hakan ne yasa ta kulla ci aniyar tako wani hali sai tasa Zawjatul Ameer tasa zoben a hannunta, da fatan cewa zai zama sanadin cikan burin da ta dade tana yi tsawon shekaru.

Hidaya na ganin za'a ajiye box ɗin a kan stool tayi saurin cewa " Please Sultana ina neman wani alfarma,"

Ko dago kai Sultana Najda batayi ba bare tasa ran samun amsa, sanin halin Sultana Najda ne yasa ta cigaba da magana,

"ina so Zawjatul Ameer tasa wannan zoben a hannunta hakan zai tabbatar mun da ta gode da kyautar dan.....,"

Kallon da Sultana Najda ta bita dashi ne ya sa ta gagara karasa zancen ya makale a makoshinta, wani irin juyi cikin ta yayi saboda kuskuren hada ido Da tayi da ita cikin kankanin lokaci ta nemi nustuwar ta ta rasa,

Da golden Lulu eyes Dinta tayi wa soldier dake tsaye alama data mai da mata da zobenta,

Ba musu soldier ta dauki zoben ta mika mata, jiki na rawa ta karba ba tare da ta san abin faɗi ba,,

Cikin tausheshshen Muryar ta mai cike da zalla izza da isa ta fara magana wanda yasa cikin hidaya kurdawa,

"A duk fadin Africa do you think akwai wanda yake da dukiyar da zai mana kyautar da zamu gode masa?

Tambayar ki nake....!!!,"

Tayi maganan cikin kau sheshshen murya wanda ya haddasa wa Hidaya saukowa daga kan kujerar ta ta zuba guiwan ta akasa jiki na rawa har kana iya jiyo yadda hakorin ta ke kara kaf!! Kaf !!,,,

Soldier dake tsaye ta daka mata tsawa "bakya ji ne Sultana na Magana kina ji....!!!,"

Cikin rawar jiki da zallan tsoro tace " ALLAH ya huci zuciyarki Sultana Amun afuwa....,"

Bata karasa zan ce ba sanadiyar kuka mai karfi daya kwace mata,

"Shut up Madam!!!,"

Cikin rawar jiki tasa hannunta ta rufe bakinta, ajiyan zuciya Sultana ta sauke na bacin ran da yake cinta kafin ta yi magana cike da karfin iko ko ince ta fara magana kamar haka,

"Sayyidah (Chief),"

Cike da girmamawa ta amsa, "take the ring and make sure kin yi bincike mai karfi a kanshi,"

"Inshaallah zanyi sanyi yadda kika ce Sultana,"

ta kammala faɗin hakan yayin da take kokarin karban zobe daga hannun Hidaya wanda ta rike shi gam taki bayarwa, wani mahaukacin tsawon da Soldier ta buga mata ne yasa ta sake box ɗin hadi da wani guntun fustari don tasan tabbas Kashin ta ya bushe.

Ƙare mata kallo Sultana tayi yayin da ta hango zallan tashin hankali da rashin gaskiya ƙarara ya bayyana, ta ce "Liya,"

"Yes your highness,"

"take her to guard room and make a strong investigate on her,"

"As you said your majesty,"

Ta gama maganar yayin da tayi Saluting nata, ta juya ta fuskanci Hidaya da tayi mutuwar zaune,

"Stand up Madam ,"
Cikin wani irin yanayi na tashin hankali ta mike tana kokarin fashewa da kuka Liya ta daka mata tsawa ta ce "shut up!!!, ko na fasa kan ki da bindiga,"

Tsum ta hadiye kukan ganin yadda ta seta bindigan akanta, sum sum suka kama hanyar barin hamshakin farlon daya ke na karshe a sashin kasancewar falko uku ne kuma kowanne kamar gari yake don girma sannan acike yake da kayan alatu da more rayuwa.

Cikin bada umarni Sultana Najda ta ce " Lesha, ki tattara kyaututtukan kitafi dasu and make sure you examine all of them ayau nake son result,"

Sojan da aka kira da Lesha ne tayi Saluting Sultana sannan ta ce "Your wish is my command your majesty,"

Tana gama fadin haka ta tattara sauran kyaututtukan tayi gaba dasu, Sultana ta cigaba da magan kamar haka" Lujain go with Sayyida Oum Suleim make sure you take good care of the ring and record all you find,"

Lujain ne ta sarawa Sultana sannan tace "inshaallah I will do as you said Your Highness,"

Ta na gama fadin haka ta juya bangaren da Sayyidah take cikin girmamawa tace "You first Sayyidah,"

Ta fadi haka yayin da take mata alama da hannu ta fara tafiya wato ta shiga gaba,

Gyada Kai tayi kafin ta mike cikin girmamawa ta ce "Ma'assalam yah Sultana,"

Gyada Kai kawai Sultanah Najda tayi, kafin ta fuskan ci sauran mutanen dake farlon ta ce "You can leave,"

Cike da rawar jiki suka Mike kowa na mika nashi sallmar suka kama hanya,

"Arya!! Tomorrow you will be appointed as my Chief advisor,"

Cewar Sultana Najda kenan wanda in ba kaga lokacin da tayi magana ba zaka ranste ba ita tayi ba, cike da wani yanayi na mamaki da farin ciki Arya ta sadda kanta kasa, cikin yanayi na girmamawa ta ce ,

"Allah kara Miki girma da daukaka yah Sultana, Ina kuma rokon Allah da ya bani ikon rike Miki amana,"

Gyada Kai Sultana Najda tayi yayin da take kara jan hankalinta ya kwanta da ita sosai, kasancewar ta dade tana bincike akanta da yanayin halayyar ta, akarshe ta tabbatar da zata rike mata amana kamar yadda Jalila bint Abdelwahab tayi wato kanwar Rayiys alhadath wanda Allah ya dauki ranta,

Murmushi Sultana Najda ta sake wanda yasa Arya daskarewa ta ce,

"You can go,"

Cikin girmamawa ta juya ta kama hanyar ta na barin farlon, tana futa Zawjatul Ameer ta rungume Sultana Najda ta fashe da kukan da tun dazu ta kunshe abun ta saboda hudubar da kullum Sultana Najda ke mata na cewa muddin tana kuka ko surutu da karban abun hannun mutane toh za'a hana ta zuwa gidan Zawjy dinta,

kuma za'a aura masa wata hakan na daya daga cikin abinda yasa take nustuwa musamman inta ga mutanen da bata sani ba, bata sake musu ko kuma rauni ya a zahiri.


"Shhhhhhh!! Hooriyya is okay,"

Kara hugging dinta tayi so tight cikin sheshshekar kuka tace "an scared Mima, na tsorata,"

Wani nannauyan ajiyan zuciya ta sauke kafin ta ce "is okay no body dares to hurt you Rania (Queen), and karki yadda da kowa, anan ba'a yadda da kowa they may easily hurt you,"

Gyada Kai tayi ta ce "bazan yadda da kowa ba Mima inshaallah, sai wanda kika ce na yadda dasu,"

Murmushi ta sake sannan ta lakaci hancin ta tace "silly, let's go and fresh up,"

"Okayy, Nima na gaji da Wannan heavy costume din da nauyi sosai,"


SHAZANA SUBAIHAT'S CHAMBER

Cikin sheshshekar kuka da yake na zallan bakin ciki da cire rai take kuka kamar zata mutu, yayin da gefe daya tana tuna irin asaran da ta tafka na rashin auran SHAZAD (Prince, dan sarki), duk da jin kukan nata take har cikin ranta saide sam bata da ƙarfin guiwan da zata iya rarrshin kanta bare ta rarrashi yar nata Sabreena, ita kanta tana bukatan wanda zai lallashi ta ya kwantar mata da hankali ya kuma tabbatar mata da cewa Shazad Muhd Kahter bazai yi kulikulin kubura da ita ba,

Suna cikin wannan yanayin ne sai ga FUAD IBN SAREE wanda ya kasance miji a gareta kuma mahaifin Sabreena ya shigo, ganin su cikin wannan yanayin ya matukar daga masa hankali har ya kaisa ga daburcewa dan a duniya in akwai abinda ya tsana bai wuce ya gansu cikin wani yanayi ba kasancewar kallon da yake musu matsayin wani dukiya ko ince hanyar samun dukiya da shahara da Allah ya bashi cikin sauki.

"Yah Allah mai ya sameki yah Najahiy,?(samu na),

Ganin mahaifin nata ne ya kara bata daman fashewa da wani kuka tana ce wa "Daddy I loose him, ba Rasa shi my dream my work is all in vein, Shazad yayi aure na tashi a tutar babu,"

Hugging dinta yayi ajikinsa cije da tausaya wa sanin yadda ƴar tasa ke ƙaunan rayuwar Mulki, dago idonshi yayi ya zubawa SHAZANA Subaihat cikin siririyar murya mai cike da kulawa ya ce,

"Ameliy
End Ads