x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 26 - THE TWO LIGHT RIKICIN GIDAN SARAUTA

  • 75001 words
  • 78000 words
  • Out of 97531 words

Category: Love Stories

Views 547

20 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
bamu san inda take ba kuma wani irin rayuwa take yi?

amma game hankali yana ganin diyar nan yasan tana cikin koshin lafiya tana kuma da rufin asiri ,

Hmm ba abinda zamuce sai Allah ya kare ta ya kuma rabata da sharrin makiya ya albarkacin rayuwarta sannan ya sada mu da ita ,"


Amen shine abinda kowa ya amsa masu dashi

" Yanzu wani hukunci ka yanke Muhd Kahter ,"

Dan shiru Master yayi na dan lokaci kafin ya fara magana cike da isa da zallan miskilanci

" Zan koma inda na fito da ita ,"

Shine abinda ya fada atakaice , gyada Kai Sarfaraz yayi kafin ya fuskanci Master wato Field Marshal MD Kahter

"Baza mu hana ka tafiya da ƴarka ba dan bamu da ikon hakan duk da muna da iko da kai matsayinka na ɗan da muka haifa amma zamu roki Alfarma kasancewar mune sanadin rabaka da iyalinka baza muso mu kara lalata maka rayuwa ba ,

Muna rokon Alfarma daka barta ko dan igiyar auren dake kanta na ɗanka Mahbeer duk da munyi karan banin da gaggawa zartar da hukunci na daura aure batare da neman izininka ba matsayinka na mahaifi gareta ,"

Shiru ne ya Rasta gun na yan mintina kafin Malikat Nubia tayi breaking silence din
" ibni inaso ka fada mun matsayi na agunka uwa ka ɗauke Ni ko shirka,"

A dan razame ya daga kai ya zuba mata grey eyes nashi ko sakan daya mai kyau baiyi ba ya sadda kanshi kasa don bazai iya juran ganinta ido cikin ido ba hakan na tuna masa da abubuwa da yawa a rayuwarsa wanda ya wuce

"Inka ɗauke Ni matsayin uwa inaso kabar Shazana Mehnoor (princess Mehnoor) anan kasar Egypt kabarta ta raya Sunnah na ma'aiki Annabi Muhd (s.a.w), an mata aure badan rashin gata ba ko dan akuntatawa rayuwar ta bane anyi ne don ta kasance daya daga cikin zuri'armu ta yanda koda iyayenta sun bayyana zasu bar mana ita don tana goge mana. radadin daya dade acikin zuciyar mu,

Nasan kana fushi damu shiyasa ka kuje mu na tsawon shekaru har 20,


kasan yadda ka azabtar da zukatan mu kuwa da aikata hakan da kayi?

inaso kasan shi dan adam ajizi ne tara yake bai cika goma ba sannan bawa baya wuce ƙaddaran sa haka Allah ya ƙaddara maka kai da ZULAIHAT da ƴayanku .


Ni uwace Ni na haifi Zulaihat duk son da wani zai nuna mata bayan wanda Ni zan mata ne shekara 20 nayi ina kukan zuci batare da na yi kowa yaji ba na kai wa Allah kuka na nasan shi ya jarrabeni da rashin ta, duka wannan shekarun ban taba nuna wani alama na bacin rai ba game da abinda aka yanke wa Zulaihat,
Na san ƴata takasnce bata jin magana tana da taurin kai da neman magana bayan wannan bazata taba aikata abinda ake zargin ta dashi ba na mika wa Allah komai karshe kaga abinda Allah ya saka mana dashi,

Inaso kasan abinda hakuri bai bayar ba rashin ta bazai taba bayarwa ba katafi na tsawon shekaru shin mai hakan ya kare ka dashi ?
ya rage ma ma radadin da kake ji ne ?
Nasan baiyi hakan ba sai ma kara wargaza make lissafi da yayi nasan halinka duk da kasancewar ka mutum murdadde kallo daya na maka nasan rayuwar bata maka dadi ina mai tabbatar maka daka zauna da yan uwanka ka rungume ƙaddaran ka hanu bibbiyu daka kasance daya daga cikin salihan bayi, shin kamanta cewa Allah na jarraban muminai ne cikin bayinsa inaso kayi gaggawar tuba sannan ka nemi yafiyar iyayenka, duk da irin cigaba da kasamu a rayuwarka nasan baka farin ciki dan baka da wanda zai taya ka ,

Ka koma gare su ina da tabbacin hakan zai rage ma radadin da kake ji a zuciyarka sannan rayuwar ka zatayi albarka,"

tunda ta fara magana ya sadda kansa kasa wani mugun sanyi jikinsa yayi tamkar an watsa masa ruwan kankara bai taba nadama da dana sanin barin ahalinsa da yayi ba duk tsawon shekarun nan sai yau tabbas maganan data fada gaskiya ne baya farin ciki da daukaka da kuma girma da ya samu saboda bashi da wanda zai taya shi murna a mastayin dan uwa ya kuma amfana da dukiyar daya tara masu dinbin yawa.

A hankali ya mike ya karasa gaban Malikat Nubia zuba guiwan sa yayi a gabanta hannunta ya kama yasa a saitin zuciyar sa

"Ummi zuciyata zata fashe tana cike da abubuwa dayawa ina cikin damuwa Ummi sun aura mun Zulaihat a lokacin da ban stammanta ba sannan na fara sonta batare Dana shiryawa hakan ba nayi nisa cikin kogin sonta inajin rayuwa in ba ita ba abu ne mai sauki ba,

a lokacin dana shirya bata ragamar rayuwata na bata wani bangare a zuciyata wanda ba wani mahaluƙi dana bawa, awannan lokacin aka mun bushara data haifamun ƴaya ba daya ba har biyu naji ta kara wani matsayi a zuciyata,

Naso na dawo dan nayi tozali da ƴara na amma Baba sarki ya hana hakan kamar yadda ya turani masa aiki bada son raina ba,"

Kara masta hannunta dake saitin zuciyar sa yayi ya zuba mata idonsa da yayi ja kamar attarubu

"Ummi ki fada mun idan ban guji su Baba sarki ba Mai zanyi nasan inna cigaba da kasancewa dasu zan iya aikata abinda zanyi dana sani daga baya shiyasa na zabi dana bar kasar na koma Sin (China) ba wanda yasan inda nake sai ke da Abie nayi haka ne don kuji sauki aranku nasan kuma kunajin abinda nakeji koma fiye da yadda nake ji sannan koda nayi tunanin dawowa gareku nakanji bazan iya ba yakan tuna mun da irin rayuwar da muka yi da Zulaihat abaya,

Ummi kinsan rayuwar danayi da ZULAIHAT ba abu ne da zai goge ba cikin kankanin lokaci,"

Dayan hannunta tasa a face nashi ta shafa cike da kula da zallan kauna

" komai Muƙaddari ne daga Allah idan ya ƙaddara faruwar hakan ba wanda ya isa ya hana, inaso kasan Baba sarki sun kasance sanadi ne kawai na faruwar hakan kasan komai da sanadin faruwar sa Kadaina ganin laifinsu suma bada son ransu hakan ta faru ba ka yafe musu ka kuma nemi yafiyar su hakan zai sanyaya ranka,"

"Zanyi hakan Ummi amma ba yanzu ba yanzu ina da bukatar kasancewa da ƴata ina kuma bukatar ta samu lafiya kamar yadda kika bukata zan barta tayi rayuwar aurenta amma bana naso mutanen duniya su san da ita kamar yadda ban bukatar Masarautar Kano su san da ita bawai dan ban yadda da ita mastayin ƴata bane inaso nayi bincike akan abubuwan da suke faruwa a Masarautar Kano daga rashin Othman da mukayi har zuwa na ita Zulaihat din tabbas akwai lauje cikin nadi akwai wanda ke shirya faruwar hakan don yana so ya cimma wani buri nashi ta hanyar mana ƙare dangi.

Yanzu ina da labarin cewa an rasa yarima mai jiran gado sannan kafin hakan Baba sarki yayi kokarin korar Fareed daga Masarautar bayan kananan abubuwa da suke faruwa,"

"Tabbas maganan ka gaskiya ne Kahter akwai abinda ke faruwa musamman ta bangaren shi ABDALLAH akwai wanda ke amfani da hankalinsa sai de ban san taya hakan ke faruwa ba amma akwai matsala gagarumi,"

Dogon ajiyan zuciya Malik Sultan yaja kafun ya fara magana cikin nustuwa
"Haka ne abinda kuka fada gaskiya ne amma yanzu abinda ya kamata mu maida hankali wajen samarwa Mehnoor lafiya sannan Musa staro mai karfi akan ta duk da bamu sanar da duniya asalin wacece ita ba, sai de mutanen dake family nan sun san da haka kuma kunsan a wassu lokutan shi munafikinka taburman ka ne,"

Cike da yadda sukayi na'am da abinda Malik Sultan yace.

END Of PAGE 29

Comment and share Please









THE TWO LIGHTS (RIKICIN GIDAN SARAUTA)




Story and written by
Queen Mahirah
Adapted Expert Writer



Ina godiya sosai 😁 OUM AFFAN da irin kaunar ❤️ da kike nunawa littafina wannan page din sadaukarwa ce agareki🤣😊

FREE BOOK

BOOK 1



PAGE 30



IRAQ



Wani katafaren Mansion ne mai dauke da kayan alatu da more rayuwa, tun daga waje kasan ba karamin kudi mamallakinta ya kashe mata ba, ita kanta gate din abun kallo ne daga ɓangaren dama akwai wani ƙaramin sign board da aka manna ajikin gini wanda yasha ado da kwalliya na musamman zaka ranste da glass akayi don yadda yake ɗaukan eyes 👀 ita kanta yadda akayi rubutun abun kallo ne tamkar da ruwan gold haka yake ɗaukan ido gashi anyi shi in a stylish form an rubuta ENGINEER. OTHMAN IBN ABDALLAH MANSION.

Daga ciki kuwa wassu fusatattun Body guard ne masu sanye da baƙin suit idonsu garkame da baƙin eye glass ba alamun ko fara'a a fuskansu.

Wata dalleliyar Car na hango mai ɗaukan ido da hankalin Me kallonta ta shigo cikin Estate din, Bata tsaya ako ina ba sai bakin tamkamemen Mansion din wanda aka rubuta Engineer. Othman Ibn Abdallah ,
cikin kankanin lokaci aka wangale musu gate din suka shiga cikin Mansion din Mashaallah shine abin na Fadi tabbas anyi barin Ƙudi ko ta ina anyi masa kawanya da kayan more rayuwa ba abunda ke tashi sai sanyi da kanshi hadaddun Flowers ga wani designer interlocks da aka zuba a harabar Mansion din.

cike da takama wannan dalleliyar Car din ta cigaba da tafiya bisa wani shinfidadden kwaltan dake shimfide inda ya sada su da wani gate din na daban inda wassu murdaddun sojoji ke kula da shiga da futa ba tare da bata lokaci ba suka wangale gate din Kasancewa sun san waye aciki, Car din ta cigaba da Rasta shinfidadden kwaltan har ta isa parking lot wato inda aka tanadar don parking cikin jerin wassu hadaddun cars wanda yasa na fara tunanin 🤔 ko Company mota nazo ina cikin wannan tunanin ne karan bude cap din motan ya dawo dani normal sense Dina,


Cike da mamaki na sake baki🤤 ganin wanda ya fito daga cikin wannan lafiyayyiyar Car din.

Sanye yake da School uniform fari ne tas tamkar balarabe mai tsananin kyau da ɗaukan hankali Fuskansa ɗauke da fara'a wanda ya kusan zautar dani 🤯 sabida wani annurin kyau daya bayyana a face dinsa Kasancewarsa mutum mai dogon hanci madaidaici wato dai dai face dinsa na yara ga small cute lips din sa wanda yake pink colour ga dara daran lulu eyes 👀 dinsa da well shaped eye brow dinsa gashin kansa zaka ranste na mata ne kasancewar sa baki wuluk mai tsantsi.

Murmushi ya sake yaron cikin muryansa me zaƙi da dadin sauraro "thanks Masroor " ya faɗi haka yayin da yake mika mishi hanu alaman ya bashi school bag dinshi,

Cike da girmamawa wanda aka ƙira da Masroor ya dan duka dai dai tsayin yaron da bazai wuce ten years ba ya bashi school bag din, karba yayi ya fara tafiya cike da nustuwa yana dumfaran wani Duplex wanda yasha white paint gefen hagu da dama kuwa flowers ne wanda suke from different varieties,

ya cigaba da tafiya yana dumfaran tafkeken ginin mai hawa biyu wato Duplex daya daga cikin soldiers din dake tsaye agun ne yayi saurin mara masa baya ya bude masa well designd kofan dayake tamkar glass sai de koda wasa baka kallon wanda yake ciki sai de shi ya ganka.

Tabbas Allah ba azzalumin bawansa bane duba da irin arzikin da aka kashe awannan farlon sai ka ranste ba'a duniya kake ba zamu iya cewa aljannar duniya ce wannan farlon komai na cikinsa unique ne white and black dashi akayi anfani wajen ƙawata farlon da kayan ado kana shigowa sanyin ac da kamshin air freshener ne zai fara maka welcome .

Da shigansa house maid din dake faman jera abinci a dining area ne ta fara welcoming nashi tana sanye da wani kaya wanda ko ba'a fada ba kasan uniform ne Black and white sai half sunna dake kanta wanda yake fari tas dashi da fara'a a fuskanta take tarbansa hakan kaɗai ya isa ka fahimci akwai shakuwa mai ƙarfi a stakaninsu,

"'Ahlan wa sahlan you are highly welcome Mr SAWBAN, Good afternoon,"

Cike da fara'a wanda da alama halittansa ne yace da ita "Afternoon Nanny Maya,"

"Where is my Mom?,"

Da index finger dinta tayi pointing wani kofa dake saman beni "she is inside her room,"

"Okay 😊 but I hope she is fine?,"

"Yes Mr Sawban she is fine,"

Kanshi kawai ya gyada kafun cike da zumudi yayi hanyar stairs wato matakala ya hau directly dakin da yake facing yayi knocking ko jira baiyi an mishi iso ba ya shiga dakin Kasancewa abude yake sannan ita kanta kofan da Tom print take aiki.

Cikin hadadden farlon ya Rasta da gudunsa ya wuce daya daga cikin kofofin dake farlon ya bude ya shiga cikin narkeken dakin da yasha ado na alfarma wata mata na hango zaune ko ince kishingide bisa royal king size bed ta lumshe idonta tana sanye da white abaya mara nauyi da ado kanata sanye cikin white turban tayi kyau matuka hannunta da chasbahanta tana ja da alama dhikr take yi kana kallonta kasan balarabiya ce mai ji da kyau da zallan ISA da Takama kana kallonta kasan Hutu ya Rasta ko ina ajikinta ga wani haske da Annauri dake fitowa daga fuskanta.
Cike da murnan ganinta ya shiga da gudu "Oyo momcy,"

Ware large eyes dinta tayi ta zuba masa su na yan wassu sakanni kafin ta sake wani kayaceccen smile daya sa na kusa zaucewa mikewa tayi daga kishingiden da take ta ware masa hannunta ya fado ƙirjinta cikin melodious voice dinta ta fara magana wanda kana ji kasan ta haɗa da jinin sarauta

"Ooyo yo my dear I miss you so much 😍 my boy ,"

"Nima nayi missing dinkin Momcy how was your body?
I hope you are fine ?"

cike da ƙauna ta fara shafa yalwacecen sumar kanshi " am fine little pumpkin I have recovered,
How was your day at school ?"

"It was superb but inna tuna baki da lafiya sai naji wani iri "

Folding face dinshi tayi ta lakaci hancin shi "uhmm You don't have to worry that much am fine I already recovered,"

"Okayy but kinci abinci ,"

Murmushi tayi kafun ta gyara masa zamansa mai kyau ajikinta

"You don't have to worry about me,
Ahaaa that remind me how was the Mathematics Class Mai aka muku yau?,"

Tabe baki yayi "The class is so boring Mom Maths teacher din mu yayi tafiya wai zaije wajen aure a can Egypt there Crown Prince will marry ,"

Wani rass taji a ranta dajin abinda ya fada haka kawai ta tsinci kanta cikin wani yanayi na waswasi wanda ita kanta bata san na maiye ba duk da bayau ta saba shiga wani yanayi ba in an ambaci kasar Egypt hakan na tuna mata da wasu abubuwa da suka faru a baya wanda yanzu bata fatan tuna su kasancewar ta fara sabon rayuwa mai cike da kwanciyar hankali kafin wannan ƙaddara ta sako kai wanda ya dawo mata da komai sabo har ya haifar mata da Bp dinta ya hau sosai.

"Momy kinyi shiru baki ce komai ba ,"

Firgita tayi ta dawo normal since dinta "ohhh sorry pumpkin muje ka cire uniform dinka ko kayi wanka ko in maka ,"

Murmushi ya sake cike da jin kunya " Ni Mom zan yi da kaina ai na iya ,"

"Okayy as you wish your majesty,"

Murmushi ya sake cikin jin dadin sunan data kirasa dashi wanda ta saba kiransa dasu ko ince ire-iren sunan.

Tare suka fito daga dakin nata Suka nufi dakin dake kusa da nata shiga sukayi ko ba'a fada ma ba kasan wannan dakin mamallakinta yaro ne kasancewar komai na yara ne a dakin Sannan anyi amfani da white and blue colour wajen ƙawata Dakin, dressing room suka wuce directly ta taimaka masa ya cire uniform dinsa sannan ya shiga bathroom cikin mintinan da baifi uku ba sai gashi ya fito daga bathroom din yana sanye da bathroom towel , Dan ware ido tayi da ganinshi don batayi tsammanin ganinshi yanzu ba,
"Ohh my God of mercy Sawban don't tell me cewa har kayi wanka,"

Gyada Kai yayi yace ehh Momy na fita sosai ko

Sake baki tayi tana kallon shi "as how Sawban ?
gaba Daya fa baka fi 3 min a bathroom din Nan ba and wai ka gama wanka wannan jika jika kayi ba wanka ba ,"

dan zumburo baki 😙 yayi gaba "Mom nayi wanka mai kyau fa da bath foam ma nayi amfani ba soap ba har sponge sanda nayi wanka dashi yau ,"

galala tayi tana kallonsa "yah Allah sawban don't tell me baka amfani da sponge dama in zakayi wanka ,"

Willi Willi ya fara yi da ido 👀kamar barawon ƙaya

"That shows magana ta gaskiya ne kenan ,"

dan sadda kanshi yayi kasa ya fara zagaya gurin da yake tsaye da kafansa ko ince babban ya tsantsa,

Ajiye kayan data dauko mishi tayi bisa hadaddiyar gadon dake dakin wanda aka lailaye da bedsheet blue color jikinsa da zananen avengers inda yake ta karasa tasa hannunta a kunci sa ta tallafo

"These shows baka wanka da sponge sawban so kake ka zama dirty boy "

da sauri ya girgiza mata Kai alaman a'a murmushi ta sake ta Kano hannunshi akan chair dake gaban dressing mirror dinshi ta ajiye shi tagoge mishi jikinsa tsaff ta shirya sa cikin kayansa marar nauyi sky blue armless t-shirt da white 3 quarter.

Cikin kankanin lokaci ta gama shirya sa suka fito farlo already an jera masu abinci a dining area can suka wuce suka samu gurin zama after serving nashi da tayi ta shiga bashi abincin a baki.

"Momy mai yasa mu baza muje Egypt ba tunda muma yan can ne "

Wani rasa taji a ranta wanda yasa take ta ajiye spoon din hannunta ta dago ta ganshi

"Mai yasa za muje Egypt?""

"Muje auren ɗan Sarkin Egypt Ameer Mahbeer naji ance za'a yi taro sosai wai an dade ba'a yi aure ba kuma wai ƴar Ameer Muhd Kahter Ibn Abdallahh zai aura,"

Fas fass!!! Kake ji ƙaran breakable cup din dake hannunta ya fadi wani ras zuciyanta ya bayar cikin kankanin lokaci
End Ads