Members din The Two lights (rikicin gidan sarauta) update section 😁
FREE BOOK
BOOK 1
Ongoing Book
🧚33🧚
Ina fita na kwasa a ɗari, kicibus mukayi da Islam dake shirin fitowa tazo dubani ganin na bata lokaci sosai.
Cike da mamaki take ƙare mun kallo, sai haki nake kamar wacce tayi gudun fanfalaƙi, hannunta duka biyu tasa a shoulder na ta ce "what is wrong with you?
Wani ne ya biyo ki?,"
Cike da kafiya da ƙokarin seta kaina na ce a'a, mai kika gani ?,
Wani weired look ta bini dashi wato kallon tuhuma, gyada Kai kawai tayi ta miƙa mun veil Dina da 👛 purse wacce ke dauke da phone Dina, sai kuma sauran abubuwan amfani.
"Let's go we are let,"
Dan zaro ido nayi waje 👀 na ce uhhmum!!!,
Wani Dan slide view taban ta ce "uhmmm!!!",
Wani abu mai dan kauri na hadiye zut, jiki ba ƙarfi na yafa veil din nawa, na bi bayanta cike da sanyin jiki, tafiya nakeyi kamar wacce kwai ya fashe mata a ciki, yayin da Islam har ta isa inda car din yake, juyowan da zatayi taga ina tafiya kamar yar koyo gashi cike da taraddadi, ƙare mun kallo tayi na yan wassu sakanni, yayin da tsaf ta karanci halin da nake ciki na fargaba.
Na cigaba da tafiya cikin sanyi da fargaban kar ya biyoni dan Allah ya isa dana ja masa, hankali na bai kwanta ba sanda na isa gaban car din, na taradda Islam ta kafeni da sparkling ✨ eyes nata hannunta ko na cikin Pocket din palazzo jeans high waisted dake jikinta.
Ganin irin kallon da take mun ne yasa na ƙauda kaina nayi ɓangaren dama na kama handle din car din da niyan shiga, ban kai ga shiga ba aka wangale gate din, wata Hadaddiyar Rolls-Royce silver cloud ne ta Sako kai cikin gidan, bata tsaya ako ina ba sai parking space, sanda aka dau like ten second kafun na cikin motan ya bude cap din motan ya zaro one leg dinshi dake sanye cikin Black Brian Atwood brand loafers, ya dauki like tree minutes kafun ya fito gaba daya daga cikin motan, Mashaallah li annan laha Houwa ahsanul Khaaliqin, yabo da godiya sun tabbata ga Ubangijin da ya halicci wannan kyakyawan halittan, Sanye yake cikin wani Ralph Lauren black suit, fuskan shi as always a hade ba annurin fara'a, sai de hakan bai hana zallan kyansa baiyana ba, yayin da idonshi ke sanye da Black suit XL sun glasses na Company Dior.
Cike da taƙama yake taku hadi da Izza da mazan taka, yana dab da isowa inda muke tsaye kamar statue, kamshin perfume din sa Oud intense na Kamfanin Gucci ya daki hancina Wanda yasa ni jan dogon numfashi, ya kuma War ware mun jijiyoyi na da suka ɗaure yasa ni daskarewa na zama statue.
Juyowa nayi da niyan zubewa Islam abinda ke raina, sai de ga mamaki na har tayi shige warta mota, da alama ma ta dade da yin hakan, zumburo baki nayi gaba, na bude cap din motan na shiga, as always tana ta faman scrolling tana up and down a screen din wayan ta, girgiza kai na kawai nayi, nayi minding business ɗina.
Daga ɓangare Captain Fudhal bai tsaya ako ina ba sai side dinsu, Mg Fahreen da Commandore Fareed yasa mu, Fareed na koƙarin serving dinsu, kamar tsohon bujumin kurma haka yasa mu guri ya zauna bai ce da kowa komai ba, kamaar yadda ko sallama bai yi ba,
cike da takaici Fareed ya ce " waalaikas Salam, daga ina kake?,"
Dogon tsuka yaja, cikin hasala ya ce "daga inda ka aike ni ubana,"
Murmushin da yake karawa fuskanshi kyau da annurin imani ya sake, kafin ya ce" ko wani bawa yana gwagwar mayan samarwa kansa aminci amma banda kai,
baka ma nemawa kanka amincin ba, bare kuma ayi tunanin wassu su samu, dama kuma ance kaso wa ɗan uwanka abinda ka so wa kanka, to kai baka so wa kan naka Bama bare ɗan uwanka,"
cikin daure fuska ya ce "tun da ubanka ne yake bada amincin sai ka zuga shi ya hana ni,"
har ilah yanzu fuskansa na dauke da narkakkiyar murmushin sa mai tsokale idon maƙiya
"😊 ba ubana ke bayarwa ba, kuma koda shi yake bayarwa bazan taba zuga shi ya hanaka ba, sabida kai ɗan uwa na ne, amma abu daya zan ma, shine zan haɗaka da wanda zata koya maka yadda zaka nemawa kanka aminci daga gun Ubangijin ka,"
Wani mugun kallo ya bishi dashi, sai de bai ce komai ba duk da ko ran shi ya ɓaci, sai de ya zabi daya hadiye bacin ran, yasan in ma ya fito da ita baza ta haifa musu ɗa mai ido ba,
EGYPT
ABDUL MALIK ROYAL ESTATE
Shirye shirye ake ba kama hannun yaro, tun daga wajen estate din kasan ana shirin hidimar biki, kasancewar ko ina ya sha gyara na musamman in ta kaice ba Estate kadai ba gaba daya Kasar Egypt ta dauki dumin shirin auren Shahzad (ɗan sarki ) Sultan Salahuddeen kuma jikan Sarfaraz Muhd Habibullah da za'a yi, wato ɗa kwalli ɗaya kuma magajin Masarautar.
Ta wani bangaren kuma gari ya dauki sanarwar ce wa matar da Shahzad zai aura , ƴa ce ga Field Marshal MD Kahter wato Master, duk da ba'a san waye mahaifiyarta ba, kuma hakan na daya daga cikin abinda ya kara jan hankalin Mutane, sanin cewa MD Kahter mata daya gareshi, kuma ta rasu da ƴayan sa da ta haifa, sai ɗan sa namiji guda daya liutenant General muhd Baraq.
Haka na daya daga cikin abinda ya sa Egypt international airport take ta faman saukar baƙi, inda hotel dake ƙasar Egypt sai diban manyan hamshakan baƙi take yi, wanda ya haɗa da soldiers, doctors Dade sauran su, bugu da ƙari mata nata faman sauka a kasar Egypt, wanda ke zuwa daga ban garori dayawa daga fadin Africa dama duniya gaba ki daya, ba komai ya kawo su ba sai dan su san wacece matar da Field Marshal MD Kahter (Master) ya aura har ya haihu da ita, kasancewar sun Sha tun karar sa da maganan aure amma a karshe ya musu korar kare.
ABDUL MALIK ROYAL ESTATE 🏢
shiri ake don gabatar da daya daga cikin event din da yake al'ada ce a Masarautar, Shagali ne akeyi na gabatar wa daukacin ilahirin Jama'ar kasar Egypt irin siffofin da Gimbiyar su keda shi, wanda yake a ka'ida ko wacce Sultana ko Malikat ana bukatar ta kasance mai irin wannan qualities din guda shida, yana daya daga cikin abinda ke karawa Gimbiyar kwarjini da girma a idon jama'ar ta, wannan ne yasa Masarautar Egypt basa auren gan ganci, sukan yi bincike mai tsayi da Neman zabin ubangiji kafin suyi hakan.
Zawjatul Ameer har wani kumatu tayi tsabar yadda take samun kulawa da taraira ya na musamman daga daukacin jama'ar dake rayuwa a Abdul Malik Royal Estate, duk da ko kowa da abinda ke cikin sa, taraira ya take samu na musamman daga gun MD Kahter da Young master tamkar jaririya haka suka ɗauke ta, ita Ko abin nema ya samu sai Barka shagwaba takeyi iya son ranta.
EVENT CENTRE
Guri ne na alfarma wanda aka tanada don gabatar da taro na musamman wanda yake karkashin Masarautar Egypt, akan bude ta a duk lokacin da za'a gabatar da wani hamshaqin biki kamar wannan.
Cike yake Makil da jama'a wanda ke sanye cikin kayan alfarma, suna zaune bisa wassu haɗaddun kujeru da table wanda suke kamar protocol saide Royal design ne, kowa yana zaune da iyalinsa, yayin da an zube kayan alatu akan wannan table din.
Wani bangare na musamman da aka ware an mishi ado mai jan hankali, ko ba'a faɗa maka ba kasan an ware shine ga masu Mulkar kasar Egypt, yasha da royal colour kujera ce wacce ba tan tama kasan an yi barin dukiya ajikinta, sai wani shining da daukan eyes 👀 yake yi, an mishi ado da danyen gold wato white gold, sai kuma lu'ulu'u da diamond, ita kanta wutan data ke haska gurin kujeran ya ban ban ta da wanda ke haska hall din.
Sanarwa da aka soma yi na karasowar Sarfaraz da Shahana, shi yasa daukacin jama'ar hall din mikewa akan kafansu, tafiya sukeyi cikin isa da taƙama da kuma zallan izza, Sarfaraz na sanye cikin well iron jallabiya fari tas, sai kimono da ya daura akan jallabiyan, itama fara ce tas kamar net, bakin shi kuwa anyi mishi ado da golden colour, kanshi yana nade cikin white ghuthra wanda aka nade da aghal, hannunshi ko saƙale da hadaddiyar designer wrist watch dinsa, kafansa sanye cikin wani Royal loafers.
Shahana dake gefen Sarfaraz, tana sanyecikin dakakkiyar Turkian Royal satin, kanta yana rufe cikin wani hadaddiyar Royal turban white colour Wanda aka mishi ado da wassu golden duwastu masu daukan eyes, 👁️ hannunta dauke da wani cute purse dinta wanda aka kashe da hadaddun duwastu na alfarma masu shining da daukan sense, yayin da yatsun hannunta suna sanye da zobba na man,a ya masu zamu da shuni, kana gani ko ba'a faɗa ma ba kasan zallan gold ne da kuma diamond ring, kafanta shima sanye cikin Brian Atwood ankle boots, ba abinda zance sai Mashaallah iya kyau sunyi kyau ba karya abin sai wanda ya gani, duk da sun kasance masu shekaru sai de hakan bai nuna ba sam, tsabar hutun da suke samu da irin kayan da suke sawa.
Sun cigaba da tafiya bisa shinfidadden Royal centre carpet Wanda aka tana da don su har suka karasa mazaunin su, kujerar ne mai mazaunin mutum biyu,banda wal wali da daukan ido ba abinda yakeyi, zaman su keda wuya aka sanar da zuwan Malik Sultan da Malikat Nubia,
Sun shigo cikin shiga na alfarma, cikin kaya na masu ji da ƙarfin Mulki da zallan Izza, komai na Malik Sultan daban ne , kasancewar sa mutum mai wuyan sha'ani ko ince murdadden mutum.
Bayan shigowar Malik da Malikat, aka sanar da karasowar mai martaba Sultan Salahuddeen da Sultana Najda, bahaushe ya ce sawun giya ya taka na raƙumi kuma ko a gidan giya akwai babba, to hakan take, duk da kasancewar Sultan ɗa ga Malik kuma jika ga Sarfaraz bai sa tauraron sa ta dena haskawa ba, kasancewar sa karamin alhaki a tsakanin su, suna sanye cikin kayan alfarma dake nuna sudin sune ke Mulkar ɗaukacin Jama'ar kasar Egypt daya.
Sultan na sanye cikin well iron jallabiya fari tas dashi, sai white golden net kimono dake sanye saman jallabiyan, kanshi a nade cikin white guthra an nade shi da aghal, jikin aghal din akwai wani bottle Mai shegen kyau da daukan hankali, jikinshi akwai tambarin masarautar wanda aka yi da narkakkiyar gold, inda diamond 💎 ya kasance duwatsun addon ta, hannunshi saƙale da diamond wrist watch da kuma wani hadaddiyar Zobe wanda ke dauke da tambarin ko ince shaidar kasancewar sa sarki, kafansa ya na sanye cikin Black Brian Atwood loafers, fuskansa sanye da siririn eye glass Mai tsadar gaske,wacce ta fitar da kyau da kuma tsarin hancin sa, kamar yadda sumar fuskansa yake kwance lubb sai daukan ido da sheki yakeyi, da gani ba tambaya kasan ba karamin 💰 money, ake kashe mata ba, daga ɓangare daman shi Sultana Najda ne sanye cikin white fitted gown, wansa aka mishi aiki da wassu haɗaddun stones masu sparkling ✨, sai kimono ko ince alkyabba da aka daura akan sparkling fitted gown din , shima fari tas sai golden zare da akayi amfani dashi wajen ƙawata kimonon daya kasance mai tsayi har yana jan ƙasa sosai daga da kuma hannun daya kasance stagune kawai, hannunta dauke small cute purse dinta wanda aka yi amfani da golden Stones wajen yi mishi ado, sanye cikin wani designer shoe Mai tsadar gaske.
Sun cigaba ba da tafiya bisa hadadden Royal centre carpet, inda ya sada su da mazaunin su, zaman su keda wuya aka fara wani kakkauran sanarwa da kakkausar murya, wanda yasa ɗaukacin jama'ar dake cikin hall din suka mai da hankalinlin su bakin ƙofar hall din, babu karan abinda ke tashi sai karan camera, cas cas, kake ji da kuma televising da ake ta faman yi, wani wal walin haske hadi da wani azababben kanshi ke tashi, cike da rawan jiki Hadimai ke shin fida Centre carpet Wanda zai sada mamallakinta ga mazaunin sa.
End of page 33 follow for more
Story and written by
Queen Mahirah (wordsmith)
Adapted Expert Writer 🖊️📖
🧚THE TWO LIGHTS ✨ (RIKICIN GIDAN SARAUTA 🏰)🧚
The story contains the fact Royalty, Ego, Separation, disastrous love, hatred, hardship,twin flame journey...
Story and written by
Queen Mahirah 👑🧕
The wordsmith 🖊️📖
Follow my
Wattpad account
Queenmahirah14
WhatsApp Channel
Queen Mahirah's Library
Ko ka tun tube Ni ta wannan lambar a WhatsApp 09168962485, don na sambada ku cikin WhatsApp group nawa, don samun update akai akai 😁
😁Har ilah yau ban manta da ku ba masu comment 😁, inah jin dadin Irin soyayyar da kuke nunawa littafina ❤️🤗.
Wannan page din sadaukarwa ne a gare ku members din The Two lights (rikicin gidan sarauta) update section.
FREE BOOK
BOOK 1
Ongoing Book 📖
Typing 📱
🧚34🧚
Cike da rawar jiki Hadimai ke shin fida Centre carpet Wanda zai sada mamallakinta ga mazaunin sa.
Wani ni'imceccen kanshi ke tashi, ga wani haske na ban al'ajabi, ba kowa ke fidda wannan Ni'imceccen kanshi ba sai Zawjatul Ameer.
Tana sanye cikin kaya na alfarma, wani haɗadden fitted gown ne ajikinta Wanda yake launin fari, an mishi wani zukekiyar embroidery work da golden din zare, sai stones masu sparkling ✨ dake manne jikin ko wani ƙusurwa na kayan, sai wani haɗadden white net Wanda akayi alkyabba dashi, bakin sa yasha ado da stones golden colour da wassu ƙananun bells wato ringing bells, an jera shi tun daga sama har kasa, hatta bayan alkyabba sanda aka sa bell din, ba sautin da yake bayarwa sai kacal kacal !!!, wanda yake nu na da Alaman mostin rai agurin, yayin da gashin kanta ko ziri daya ba'a gani kasancewar an yane kan da veil, wato an mata rolling dashi inda aka sa mata hulan alkyabban, idan ka gangaro da kallonka zuwa face dinta nan zakayi araba da face jewelry din da akayi amfani dashi wajen rufe face dinta, anyi shine da white gold sai sheki yakeyi, shi kanshi in tayi kwakkwaran mosti da kanta wani Amon sauti mai jan hankali yake bayar wa, inka gangaro da kallonka zuwa hannunta, zaka hango su cikin white hand socks, in kayi kasa zaka hango kafanta sanye cikin white ankle straps sandals.
Daga bangaren damanta kuwa Ameer Mahbeer ne sanye cikin dakakkiyar White thoube (jallabiya), yayin da kanshi ke nade cikin white guthra wanda aka nade ta da Black aghal, fuskansa tayi fayau da ita ba abinda ke tashi sai annurin angon ci, man's pride dinshi Wanda yasha gyara na alfarma sai sheki yakeyi da daukan ido da hankalin mai karatu da kallonsa, lips nashi sai sheki sukeyi zaka ranste ya shafa lip gloss, sparkling ✨ eyeballs dinshi sai shining sukeyi, hancin shi kuwa kamar an kara mikar da shi wato an seta mishi, haka well shaped eyebrows nashi sai shining sukeyi su kadai kamar an shafa musu Vaseline, na ɓangare dama kuwa har ilah yau akwai tsagu uku wanda zaka ranste don ado akayi su, Wrist watch kirar Richard mile ne daure a tsinstiyar hannun sa, haka kafansa na sanye da wani arnen designer loafers.
Atakaice babu abinda zance sai Mashaallah li annan laha Houwa ahsanul Khaaliqin, yabo da godiya sun tabbata ga Ubangijin talikai wanda yayi wannan halittan masu daukan hankali,
Hakika yau dinbin jama'ar da suka halar ci wannan biki sun ga abin mamaki, wato sun ga ruwan kyau, masu taƙama da arziki sun rena kansu, haka mata masu taƙama da kyan sura wassu sun ji tamkar kasa ta tsage su shige, duk da basu kai ga ganin fuskanta ba, dayawa sun rena kansu, kallon ƙwayar idonta kadai yasa sun san ruwa ba Sa'an kwando bane, ko kallon idon nata ma sai mai ƙarfin hali da jarumta ke yinsa, yan mata dake burin auren Ameer Mahbeer daya wa sun sare😔, don sun rena nasu halittar, wassu daga ciki har addu'ar zaman lafiya da samun zuri'a dayyiba suka musu, ( 😅😂🤣 ba dole ba sunga halitta, jikar Sheikh an tofe ta da Suratul Yusuf).
Cikin wa'yannan yan mata har da Sabreena wanda baƙin ciki kamar ya kashe ta, Musamman ganin yadda mutane kowa ke yabon kyau irin na yarin yar da dacewar da sukayi, tsabar tsanar ta ke kara tasiri a zuciyar Sabreena, don yasan badan zuwan taba da da ita za'a yi auren ma'ana da ita ce Zawjatul Ameer.
Shazana Subaihat ji take tamkar ta shake ta ta huta domin duk lokacin da ta gabata ba abun da ke yawo mata a kwanya sai cin mutuncin da Sultan Salahuddeen ya mata, ko lokacin da ta bijirewa iyayen ta ƙi auren mutumin da suka zaba mata, bata fuskan ci irin wannan rashin mutun cin ba, har cikin ranta take jin tsabar tsanani tsanar yarinyar.
Sun ci gaba da tafiya bisa shinfidadden Royal centre carpet din wanda yayi leading har zuwa gurin zaman su, basu kai ga zama ba Sultana Najda tazo ta gyarawa Zawjatul Ameer kayanta da kyau ta samu ta zauna, yayin da shi Ameer Mahbeer ya zauna a gefen ta.
Ko ƙwaron daya halicci wannan taron ya sha ruwan jikin shi, domin kallo daya zakayi wa Sultana Najda ka hango zallan ƙauna da takeyi wa yarinyar wanda ta gagara boye hakan, a kaf tarihin masarautar ba'a taba yin Zawjatul Ameer, Zawjatul Malik ko Sultana wacce ake nu na mata irin wannan soyayyar ba.
Bayan kowa ya nutsu Rayiys alhadath (President of the event) ya mike cike da girmamawa yake tafiya har ya iso kan stage yatsaya hannunsa dauke da mike, dan sadda kai yayi Alaman girmamawa ga su Sarfaraz, san da aka umarce shi da ya dagon kafun ya dago, cikin nustuwa ya fara magana kamar haka,
"Allah ya kawo mu shekara ya kawo mu, a yau ne din bin jama'ar dake rayuwa