na mosti ahankali wanda da alama tasbihi yakeyi, zarazaran finger dinsa na aikin bautawa mahaliccinsa wanda ya zauba masa kyak'kyawan halitta,
karan takalmin dana ji ne yasa na maida hankali na kan mai tafiyan masha'Allah hakika babu abun bautawa da gasakiya sai Allah, godiya da yabo sun tabbata ga ubangijin da yayi wannan kyak'kyawan halittan.
wani hadadden Giant handsome ne fari tass,
yanaa sanye da unifoam na Navy wanda yake white colour ajikin rigar dagaa bangaren dama akwai inda aka rubuta CAPTAIN FUDHAL,
unifoam din yayi matukar amsar sa ya kuma fidda murdadden surar sa mai firgitar da abokan adawansa,
idonshi sanye da dark space cute lips dinsa sai kyalli yakeyi,
pointed nose dinsa ya kara wa face dinsa kyau,
face nashi kewaye da bakar sumarsa mai sheki,
{wanda aka fi sani da saje}
da daukan idon mai kallonta da mai karatu,
ya karawa face din nashi kyau sosai,
haka gasahin kansa yaa sha mayuka sai sheki yakeyi gashi dayawa ga stansti ,
hannunsa dauke da hulansa, ya cigaba da tafiyaa cike da isa da takama face nashi babu annurin fara'a ko kadan sai de hakan bai sa yayi muni ba sai wani kyau da kwarjini daya kara masa ,
tafiya yake tamkar zaki mai shirin baza taro har ya iso cikin farlon agefen wannan farin halittan ya zauna yaja dogon numfashi cikin husky voice nashi yace
" how are you feeling"
ahankali ya bude snake eyes dinsa ya zuba su a fuskan Captain Fudhal wanda shima alokacin ya cire dark space din sa ya zuba mishi lion eyes nashi,
bai ce komai ba ya lumshe idonshi,
daga fannin Captain bai damu da rashin amsan nashi ba don dama yasan ba lalle ne ya samu amsa ba,
alama yayiwa house maid da hannu daya ajiye tire din abincin dake hannunsa akan wani glass centre table din dake farlon,
cikin girmama wa ya ajiye tire din ya fara kokarin serving dinsu ahankali Captain Fudhal yace
"no need you can go"
cike da girmamawa yace
"okay sir"
ya dan sadda kanshi alaman ban girma kafun ya juya ya tafi,
da kanshi ya mike ya dauki breakable plate ya zuba chips da soyayyan kwai sai pepper soup sai kuma hot choculate,
janyo centre table din yayi dai dai da inda yake kafun yace
"Tweeny sit well and eat, am very sure bakaci komai ba"
bude lumsassun idonsa yayi ya zuba su a abincin nasa nadan lokaci kafun ya kauda kansa wani sarawa yaji kansa keyi rinste idonsa yayi da karfi ahankali yake ambaton sunan Allah,
yana ji tamkar kan zai stage gida 2,
lura dayayi da halin da yake ciki ne yasa shi tasowa da sauri ya zauna agefensa ya dafa shi yace
"Fahreen are okay what is wrong with you"
bai ce mishi komai ba sai kada kanshi da yakeyi ahankali ganin haka ne yasa shi fahintar cewa kansa ke ciwo,
cikin wani yanayi ya kama kan ya fara tofa masa addu'a ya kai 30 second yana faman masa addu'a kafun can ya staya ganin ya dai na jijjiga kan nashi
"sorry Tweeny Allah baka lafiya, anya baza mu fadawa su Ammi...,"
bai gama maganan nashi ba Fahreen yace
"no no please don't tell them,"
cikin wani yanayi na storata da yanayin dan uwan nashi yace
"okay i won't but please eat"
hannu ya miko mishi idonshi akan abincin yana nufin ya bashi abincin,
bai bata lokaci ba ya dauko plate din chips din ya bashi kare mata kallo yayi bawai dan bayaso ba ko baya jin yunwa ba a'a sai dan bashida appertite ne yasa bayason abincin rabonshi da abinci tun jiya da dare,
ahankali ya kai abincin abakinshi kamar wanda aka sashi dole sai de bai fi 2 spoon yayi ba ya ajiye plate din ,
Fudhal ya mika masa bowl din pepper soup din ya dan ci kadan shima ya ajiye sai mug din hot choculate shine wanda ya shanye tas don dama yafi son abu mai ruwa da dumi,
dogon numfashi yaja yace "
"Alhamdulillah"
ya koma ya jingine kanshi jikin sofaa ya kwanta,
Captain Fudhal da kallon tausayi yake bin dan uwaan nashi, yau akalla 2 weeks kenan suke fama dashi sun rasaa abu daya dake damunshi duk ya rame ya lalace ya fita daga hayyacinsa,
gashi ya ki yadda kowa yadda iyayesu susan abinda ke damunsa,
karshe ma basusan inda yake ba su kansu ba'a san suna garin kano ba don kowa ya zaci suna gun aikinsu.
sunyi maganin asibitin babu sauyi wani abokinsu Dr nema ya basu shawaran hadawa da islamic medicine sunyi kuma Alhamdulillah don ansamu ci gaba,
sabanin da, da idan kanshi ya fara ciwo har bugawa yakeyi agini ya ringa abu kamar majnoon da kyar suke kama shi,
amma yanzu da sauki ya dena buge buge sai de ciwon kan nanan, kuma koda wasa baya so ayi maganan gidansu ko kadan muddin akayi tohh zai rikice ya fara neman inda zai sa kanshi ya buya hmmm dogon numfashi yaja yace
" ina Fareed ya staya ne nikam..,"
Daga nan waje wato balcony securities dake sanye da kakin sojoji ne suka wangale gate wani hadadden mota mai numfashi ne ta danno kanta cikin gidan tayi parking,
daya daga cikin sojojin ne yayi hanzarin zuwa ya bude cab din motan ya kai akalla 2min kafun ya zaro santalelen kafansa wanda yake sanye cikin wani arnen white designer snickers after 3sec ya zaro dayan kafan kafun ya fitoo gabaa daya,
ohhhh Allah ni Queen Mahirah sake baki 🤤 nayi har ban sanda alkalamin hanuna ya fadi ba, na sake baki ina bawa idona👀 hakkinsa.
wani mashahurin hadadden stadadden gaye ne mai zubin sammudawa ya fito daga wannan arnen car din yana sanye cikin farar dakakkiyar shadda wacce ta amsa lafiyayyiyar surar sa,
fari ne tas mai zubin larabawa, fuskarsa nada stayi tana kuma dauke da pointed nose dinsa hade da cute pink lips dinsa,
sai eyes nashi wacce ta karawa halittansa kyau da man's pride dinsa baki wuluk dashi wacce da gani ba karamin naira aka kashe mata ba sai sheki yakeyi da dukan ido 👀,
haka kanshi sanye da hula wanda ya fidda kyansa ya kuma maida shi cikakken bahaushe duk da azahiri baiyi kama dasu ba,
kana iya hango kwanceccen sumar sa baki wuluk da ita mai tarin yawa da sheki,
kallo daya zaka masa ka hango zallan nustuwa, haiba, kwarjini da annurin fara'a a fuskarsa,
kaff sojojin balcony sukayi saluting nasa kamar kullum fuskarsa dauke da fara'a da zallan girmama dan Adam ya yace
"bissimillah,"
a wani dattijo dake gefensa wanda kana ganinsa kasan malami ne,
baiyi kuskuren hada tafiya da dattijon malamin ba ya barsa ya shiga gaba shikuma yana binsa a baya har suka iso bakin farlon ya danna wani maballi kofan ta budu yace
"bissmillah malam ka shigo"
murmushi malamin yayi cike da jin dadin irin girmamawan da saurayin ke bashi ya shigo suka karaso cikin farlon, inda su Captain Fudhal suke ya nuna mishi guri ya zauna housemaid suka cika shi da kayan mosta baki,
Fudhal ne ya dubi saurayin yace
"ina ka staya Fareed tun dazu kabarmu muna jiranka"
murmushi yasake wacce take halittansa ne yace
" Malam ne yake da baki shine na jirasahi ya sallame su"
sai asannan Fudhal ya dago ya kalli dattijon ya gyada shi cike da girma mawa duk da fuskarsa amurtuke take ba ko annurin fara'a, malamin ya amsa yace
" ya mai jiki" "
" jiki Alhamdulillah gashinan de kullum ya gagara gaba ya gagara baya sai de mu godewa Allah, "
Fareed yace " kaganshi ko malam , kaga yanayin jikin nashi ko"
kai malamin ya gyada cike da jimamin abinda idonshi ya gani yace
"na gani Yarima sai de muce Alhamdulillah da abin ya staya a iya haka,"
cike da neman karin bayani suke kallonshi Fudhal yace
"ban nnn ganeee ba kana nufin rashin lafiyar tasa tafi haka kenan"
. gyada kai malamin yayi yace
" tabbas ikon Allah ne ya kubutar dashi daga ainihin abinda ke damunsa, azahiri hauka akaso yayi "
ware idaanu 😲sukayi gaba daya Fareed yace
"mun shiga uku mai kake nufi malam kar kace Biyayye haukacewa zaiyi"
girgiza kai malam yayi yace
"tabbasa haka akaso saide ba haka Allah ya stara ba"
" tohhh yanzu ya zamuyi,"
inji Fareed, malam yace
"agaskiya zan baku shawaran ku kai sa gun Imam Umar Bello,
wani babban malami ne wanda yake nan a Rugar Hardo Bello wacce take karkashin Wudil local govement.
shine kaadai zai iya muku wannan maganin,
kuma shi kanshi zai samu sauki inya yi nesa da garin nan dama Kurciya aka masa don yabar garin ya shiga duniya,"
dogon numfashi Fudhal yaja don ya yadda da maganan malamin sosai kasancewarsa malamin kakansu yasan bazai musu karyaa ba
"tohh yanzu ya zamuyi mu je can gurin mutumin,"
malam yace "babu damuwa aboki nane zan kira shi awaya in shaida masa zaku zo gobe nasan zai yi maraba daku,
ina kuma tabbar maku zaku ji dadin kasancewa dashi"
murmushi Fareed ya sake yace
"mun gode malam aini nasan Rugar ma,
ba shine wannan ruga mai ban alajabi din nan ba nasan labarin Rugar ina taso naje Allah ne bai