ajikin kofan da Babu handle sai wani scanning machine cikin kankanin time yayi scanning hannunsa wani Dan Kara yayi kafun kofan ya bude da kansa, kamshin da sanyin farlon ne ya bigi hancinsa Wanda ya sashin saurin jefa kafarsa cikin hadadden Royal farlon Wanda ya kawatu da kayan alfarma kayan kudi sai walwali yake ta ko Ina da gani ba tambaya kasan Naira ta koka anan,
Da Bismillah abakinsa ya shiga ciki wani sanyi yaji ya mamaye ko wani sashin na jikinsa Wanda ya tursasa cewa "hmmm no place like home,"
Yayi magana ne cikin voice nashi Mai taushi da amon sauti wacce da zaran anyi magana da ita dole ka saurareta wata iriyar LION VOICE ne dashi mai wargaza taro yasa mara gaskiya ya koka.
Ahankali ya juyar da kanshi bangaren da lieutenant MUHD Baraq yake ya kamo hannunsa yace " Baraq,"
Ahankali ya dago oily eyes nashi ya zubawa mahaifin nashi kafun yace "POPS,"
Batare da ya Kara cewa komai ba ya buga kafadan shi kawai don maganan ta masa nauyi bazai iya furta komai ba sake shi yayi ya bi hanyan wani stairs ya hau wani dakin ya shiga ya rufe kofan,
Anasa bangaren wato MUHD MUBARAQ wucewa yayi wani dakin da yake akasa ya shiga dukda Tarin damuwan da yake ciki da bugawan da zuciyanshi keyi Bai sa ya zauna ba shirin wanka kawai yayi, ya Kai akalla 6 minutes a bathroom kafun ya futo Yana daure da towel a waist nashi hannunshi ko dauke da wani towel din yana stane gashin kanshi dake digan ruwa Bai staya wasting time ba ya shiga dressing room ya shirya cikin farin jallabiya ya futo ba ko hirami akansa, sai baza kanshi yakeyi Babu abinda yake buri da son gani ayanzu da ya wuce yarinyar da aka kira da sunan Yar uwarsa ta jini wato kanwar sa Daya rasa tun Yana da shekara 9 aduniya jiyake tamkar duk wani mastalolinsa sunzo karshe gani yake tamkar ance mahaifiyar sa zai gani wacce yau kimanin shekara 20 da Yan watanni rabonsa da Jin dumin jikinta.
Cike da sauri ya futo daga dakin a iya tunaninsa zai samu Pops ya shirya Yana jiransa Amma da mamakinsa bako alamunsa Dan furzar da iska yayi yayi hanyan stairs din cike da mazantaka yake hawa da sauri sauri cikin kankanin lokaci ya karasa hawa ba Bata lokaci ya shiga dakin bakinsa dauke da sallama ba wani hasken kirki adakin sai wassu dimmm light, hangoshi yayi zaune akan King size bed din dakin hannunshi dauke da wani Abu Wanda Yana da tabbacin pic din Mom dinshi ne wato matar field Marshal MD Kahter
Ya zubawa frame din photo ido yana Kallo ahankali ya karasa ya zauna kusa da shi hannunsa yasa ya Karbi pic din ya zuba mata oily eyes nashi wani dogon numfashi yaja kafun ya yace " Mom where are you??
Why do you choose to leave us??
Pls come back we are in need of you, we really miss you
We miss you so much mom look at how Pops change he badly miss you more than I did,"
Dogon numfashi yaja ya cigaba da magana ya Kara kurrawa pic ido kamar Mai son gani wani Abu aciki kafun ya Maida duban sa ga mahaifinsa yace " Pops kashirya muje muji Mai zasu ce I badly wanna see her I feel like mom zan gani pls pops let's go,"
Dogon numfashi yaja badan yaso ba sai Dan kaunar da yakewa gudan jinin nasa Wanda ayanzu kallo yake tamkar shine kadai abinda ya rage masa aduniya, mikewaa yayi akan kafansa ya shiga cikin jibgegen bathroom din don yin wanka Bai wani Bata lokaci ba ya futo ya wuce dressing room ya shirya cikin well iron jallabiya Wanda yake fari tas Mai tashin kanshi ko hirami baisa ba ya futo suka kama hanyar futa, balcony part din suka futo jikin securities har rawan yakeyi wajen tambayan su inda zaa kaisu kamar bazaiyi magana ba sanda ya mula dan kansa kafun yace
"Sultan Malik chamber,"
Ba Bata lokaci driver ya dauko wata hadadden Royal car ya faka a gabansu aka bude musu cab din motan suka shiga cike da kulawa driver ke tuki har suka iso Sultan Malik Chamber Wanda tunkafun su iso aka sanar da zuwansu suna isa aka baza musu hadadden center carpet ga securities Tako Ina har ila yau cike da IZZA suka Rasta kan wannan royal center carpet din har ya sada su da tafkeken kofan hadadden farlon Wanda securities suka wangale musu shiga sukayi yayin da securities suka stattaya abakin hanyar suka karasa cikin farlon inda suka hango Su Sultan da Malik da Kuma matan su stayawa yayi cakk Yana kare musu kallo Daya bayan Daya kamar maison gano wani Abu acikinsu Wanda shine maka sudin zuwansa ganin baiga komai bane yasa ya juya zai futa batare dayace komai ba sai de muryan Daya ji yahana shi yin Hakan,
Cikcikin muryanta Mai cike da tausayi rauni da Kuma zallan hakuri tace "ibnii,"
Cakk ya staya yaja dogon numfashi kafun ya juyo baice kala ba sai kare mata kallo da yayi abinda ya hango a idonta ne yasa jikinsa yin sanyi Babu komai cikin idonta sai zallan kauna , tausayi , rauni bege da Kuma zallan storo.
Jikinsa ne yayi sanyi yasa ya kama hannun Mubaraq suka karasa har inda suke wato stakiyan farlon suna staye curko curko Bai staya ako ina ba sai agaban Malikat Nubia sadda kanshi yayi kasa Bai ce mata komai ba sai janyo Mubaraq da yayi ya Mika mata shi kamar jariri dauke idonta tayi daga kanshi ta Mai da shi kan Mubaraq wanda take hawayen dake makale a idonta ya zubo hannunta har rawan yakei wajen folding face dinshi rasa abinda zatayi ne yasa ta fashewa da kuka Mai ban tausayi shiko Mubaraq hannu yasa ya goge mata hawayen Yana jijjiga mata Kai alaman tadena rungumota yayi ya shiga rarrashinta cikin nustuwa har tadena kukan.
Sauran mutanen farlon ko sunyi shiru kamar ruwa ya cinye su sai de duka sun zauna ganin shi Mai gayya Mai aikin ya bawa kansa mazauni batare da ya kula kowa ba.
SARFARAZ (king) wato Sultan Habibullah ne yayi gyaran murya yace "Alhamdulillah Babu Abun da zamu ce ga Allah sai godiya mun Dade Muna jiran wannan ranan da zamu gyara kuskuren mu duk da mun San ba Mai gyaruwa bane,..
Sai de Muna Neman afuwarka bisa yanke hukuncin da mukayi ba tare da mun sanar dakai ba haka kazalika bamuyi dogon bincike VA munyi amfani da karfin iKon mu mun zartar da hukuncin da har ilah yau Muna kuka dashi,
hmmm tohhh Alhamdulillah wai kana naka Allah na nashi bamu zata ba bamu stammanta ba muka samu wannan diyar duk da bamu da tabbacin abinda muke hasashe sai de Muna sa ran gaskiya ne kasancewar lokacin da aka sameta mun yanke hukuncin hadata aure da Ameer Mahbeer duba da yadda starin family yake nayin bincike kafun aure da Neman zabin ubangiji yasa muka dage da addu'a akan wannan lamarin,
Tohhhh Alhamdulillah abinda muka ganii ya bamu mamaki munga abinda bamu Yi zato ba domin anawa bangaren mafarkinnayi da Zulaihat tana bani wannan yarinyar amastayin amana na bukaci data fada mun inda take Amma batayi Hakan ba sai de tace dani wannan yarinyar itace makulli Kuma hanyar dazai sadamu da ita domin ita din jininta ne sannan zata warware mana wassu kulli da muka Dade Muna Kokarin warwarewa Sannan tasanar dani sunan yarinyar wato MEHNOOR.
Bayan na tashi daga baccin da bana raba dayan biyu na iKon Allah ne don da kwanciya na da tashi duk nayi su cikin minti Daya,
batare Dana Bata lokaci ba na Tara sauran iyalin na tambayesu Mai suka gani Suma abinda suka sanar dani kenan da wannan na samu karfin guiwan daura musu aure ita da Ameer Mahbeer Wanda ayanzu ta tashi daga SHAZANA MEHNOOR (princes mehnoor) ta zama ZAWJATUL AMEER,"
Shiruu ne ya mamaye gurin ba Wanda yace kala suna jiran Master yace wani Abu sai de kamar yadda sukayi zato baice kala ba kamar yadda baiko nuna alamun yaji Mai suka ce ba,
Mubaraq ne yace" Jaaddii pls let us see her first,"
Dan gyada Kai Sarfaraz yayi yace wa Shahana (Queen) " kira Najda ta kawota ,"
Gyada masa Kai tayi kafun ta Yi abinda ya umarceta, ba Bata lokaci aka bude kofar farlo na biyu,
ba kowa bane face Sultana Najda da Zawjatul Ameer Wanda take sanye cikin kayan alfarma yau fuskanta Babu burka an bar mata shi abude gefen hagun ta ko Ameer Mahbeer ne shima yayi kyau cikin normal outfit nasu na larabawa wato jallabiya da hirami.
Tafiya suka fara Yi cike da nustuwa batare da sanin illar da suke haifar wa Master ba wato ko wani taku Daya nasu Yana tafiya da bugun ❤️ heart nashi Wanda ke barazanar fasowa sai de samm ya gagara dago kansa bare yaga Mai ke faruwa.
Mubaraq dake zaune ne yayi gaggawan mikewa yace " mommmmcyyy,"
Jin wannan furucin ne yasa field Marshal MD Kahter dago oily grey eyes nashi ya zubawa fuskan Zawjatul Ameer...........
Queen Mahirah
Comment and share pls
Kuna mun sharhi Hakan zai sa na fahinci labarin na shiga
Zaku iya mun comment ta group dina HV BY QUEEN MAHIRAH
Ga Wanda baya group din ko yayi gaggawan shiga don samun update akai akai zaku iya tin tuba na akan wannan lambar 09168962485 a WhatsApp
Ko kadannan wanna link din zai Kai ka har group din
https://chat.whatsapp.com/DEb6DCrj50r88WN25D5xu9
🧚THE TWO LIGHT✨ (RIKICIN GIDAN SARAUTA🏰)🧚
Story and written
BY QUEEN MAHIRAH❤
ADAPTED EXPERT WRITER📖🖊️
️
BOOK 1
PAGE 2️⃣7⃣
Wani irin bugu ❤️ heart nashi yayi Jin abinda Mubaraq yace Wanda yasa shi dago da oily grey eyes nashi ya zubawa Zawjatul Ameer su ko mostin kirki ya gagarayi wani irin shock ne ya dirar masa lokaci Daya Wanda dazaa staga jikinsa da baza a samu jini ko digo daya ba amma dayake soja ne mai karfin Hali da jarumta yasa baka isa kafahimci halin da ya shiga ba ko tantance wani yanayi yake ciki.
Sun cigaba da tafiya har suka iso cikin farlon idonta Yana kan Mubaraq Daya kafe ta da oily eyes nashi tana mishi kallon kamar na sanka kokarin tunowa take amma ta kasa Hakan ne yasa ta cuno baki gaba ta Kalli Sultana Najda tace "Mima who is that guy??,"
And why is he starring at me like this??"
Saurin kama hannunta tayi ahankali tace "keep quiet Hooriyya??,"
Cuno bakinta ta karayi ta kwabe face zaunar da ita Sultana Najda tayi kafun itama ta samu guri ta zauna a gefenta sai suka sata a stakiya ita da Ameer Mahbeer Dan gyaran murya Sarfaraz yayi yace
" Kahter ga diyarka Mehnoor duk da har yanzu bamu da tabbacin Hakan Amma Muna fatan zaka bamu Hadin Kai wajen tabbatar da Hakan ta hanyar bincike har mukai ga gyara kuskuren mu,"
Sai a sannan ya Mai hanakalinsa wajen Sarfaraz yace "where did you find her,"
Sarfaraz ya kira sunan Sultana Najda sannan ya gyada mata Kai alamun tamasa bayani tunda ance Waka abakin Mai shi yafi dadin sauraro.
Dan gyaran murya tayi cike da nustuwa tace " ranar wata Jumaa a kasar Cairo na fita don ziyartar kabarin Safeera kamar yadda nasaba, a hanyata ta dawowa ne Daya daga cikin car din dake convoy nawa ya bige yarinya Hakan ya tilasta mana stayawa kasancewar Muna gabb da shiga Estate yasa na umarci driver Daya dauketa asa ta a car mu kaita hospital dake Kingdom din kafun daga baya a nemo iyayenta,
Hakan kuwa akayi har an wuce dani ciki sai naji bazan iya tafiya ba batare Dana ga wa aka bige ba, nayi saa baa shiga da ita theater room ba Hakan yasa aka bani daman ganinta Wanda ya haifar mun da stayawan numfashi na na wucen gadi ganin fuskan da bazan taba manatawa ba wato Safeera ƴata data rasu,"
Dan jinkirtawa tayi tana dogon numfashi kafun ta cigaba da cewa
"Bayan na farfado ne Dr ya sanar dani an shiga da ita theater room tana da bukatar amata aiki a Kanta sabida buguwan da tayi,
Cike da tashin hankali nacewa wa Dr ya tabbatar anyi aiki yadda ya dace sannan a maidata Royal Apartment ya amsa mun da tohh kafun ya futa don ya aikata abinda na bashi umarnin yi.
After four hours suka futo daga theater room Kuma Alhamdulillah an samu nasara Nan aka Mai data R.B.A sai de Bata farfado ba.
Nan na bada umarnin a nemomin iyayenta sai de da mamakina an gama binciken duniyan baa same suba infact she is not our citizen,
airport aka koma don yin bincike ko yawon bude ido tazo sai de to my own surprise Trafficking nata akayi sai tayi kokarin escaping anan ne car ya bigeta,
An dauki kwanaki ana bincike Amma babu wani improvement cos mutanen dasukayi trafficking nata sun gudu and the worse part shine jirgin nasu yayi hastari karshe sun mutu batare da ansamu kwakkwaran shaida akansu ba kasancewar Komen su na bogi ne passport nasu da indigin duk na karya ne.
An cigaba da Bata kulawa sanda takai good 2 weeks Bata farfado ba har na soma cire Rai ranar Dr Salman ya sanar dani cewa ta farfado ba Bata lokaci na tafi hospital din Nan na sameta ta tashi a firkice Dr yace tayi loosing memory dinta and she is suffering from Agoraphobia shine abinda ya haifar mata da storon mutane she hate seeing crowds of people but da yake God is wonderful and blood is thicker than water Bata kini ba. Infact she called me Momy ta yadda dani mastayin uwa na dauketa muka koma Chamber na da ita aranar na sanar da Sultan abunda ake ciki kasancewar ban sanar dashi ba na Kuma nemi alfarma Daya yadda nayi adopting dinta, anan yace dani sai mun zo Egypt duk abinda su Sarfaraz suka yanke shi zamuyi.
Alhamdulillah sun yadda an Kuma yanke hukuncin hada aure stakanin ta da Ameer Mahbeer anan akayi bincike da Neman zabin ubangiji tohh akarshe mun samu wani muhimmin bayani game da ita Wanda muke fatan ya kasance gaskiya ,"
Furzar da iska yayi kafun yace
" how about the health issue,"
"Dr yace widing two to three weeks brain dinta zai fara functioning Mai kyau she may be able to remember wasu fact a rayuwarta muddin Taga abinda ta sani and ta fara Hakan yanzu cos jiya taji ana HAUSA itama tayi ta Kuma ce ta iya dn yanzu tana Yi but of to know da sauranta,"
Dago da kanshi yayi ya zuba mata oily eyes nashi kafun ya kauda kanshi yace " I need to investigate by my self I need to blood tested her first ,"
Ahankali tace " UKHTIE, TWEENY,"
Hankalinsa ne ya dawo Kanta Jin abinda take Fadi Wanda azahiri Mubaraq take Kallo,
Da hannu ta fara pointing nashi tana cewa " I know him Mima he is my TWEENY my UKHTIE,"
Dan juya ido Sultana Najda tayi tace " Ukhtie Kuma Hooriyya he is not a girl he is a guy NAMIJI ne shi,"
Zumburo baki tayi tace " but he is my TWEENY,"
Shahana ( Queen) tace "dama ke Yan biyu ne ,"
Dan jimmm tayi ta juya eyes dinta kafun tayo folding face dinta da both hand dinta "hmmm I don't know, all I know here is he is my TWEENY,"
tana fadin haka ta koma inda Mubaraq yake ta zauna ta kama hannunshi tace" tweeny tell them kace ka sanni Kaga basu yadda dani ba Kuma gaskiya nake fada kagani Kaine ga grey eyes naka ma ga pointed nose,"
tana magana yayin da take Jan hanacin nashi murmushi ya sake Mai kayatar wa daya sata yin karamin ihu in such a way da kana ganin kasan na jubilation ne
"Is you, you are the one pls don't leave me again kaga Zawjy ma shine Hamma na Amma yace wai shi sunan shi Mahbeer Umar ba Hamma Faruq ba Amma Kai ka yadda Kai Ukhtie na ne ko ,"
Gyada mata Kai yayi itako ganin haka ta rungumeshi tace " I love you Tweeny karka Kara barina ,"
"Gyada Kai yayi yace I love you too sister bazan barki ba daga Nan har gaban abada Muna tare ba Mai Kara rabamu but promise kema baza ki manta dani ba and zaki kaini wajen momy da Mahnoor,"
Cike da rashin fahimta tace "ai Kaine Mahnoor momy kuma ban San inda take ba ko taje Ina ma ma ohhh Hospital can taje ,"
" Pops she is the one kaji ta kirani da Mahnoor Kuma tace Momy na Hospital that means she is still working as a gyne doctor,"
"I need Her blood group and genotype the biggest part I need both of you to under go DNA test,"
Dan daga gira daya Mubaraq yayi in disbelief yace "ni din ne baka yadda ce wa ni danka bane ko ita da ko makaho ya laluma yasan wannan jininka ne kaga yadda take kama da Momy Kuma Kafi kowa sanin cewa Mahnoor na kama da Kai Mehnoor Kuma da momy ke kama,"
Master ido ya zubawa Dan nashi Wanda tamkar an staga Kara a stakaninsu hatta halayyar su ta miskilanci , taurinkai , kafiya , da zuciya suke iri Daya kauda kanshi yayi Bai ce mishi kala ba abunda yasani Babu Wanda ya isa ya canja mishi kudirinsa nayin DNA test,
Malik Sultan yace "Baraq ya isa he is your father you are not supposed to talk to him like this you should show some respect ,"
"But grandpa kanajin abinda ya fada ko for all this years Yana nufin kallon shege yake mun kenan ,"
" Mubaraq ka fahimci mahaifinka ba abinda yake nufi ba kenan I know right now he is confused kasan fa yau good 20 years kenan da muka samu labarin rasuwar momynka da twins Amma kwatsam a samu daya daga cikinsu kaga akwai sarkakiya let him investigate,"
Shiru Mubaraq yayi Bai Kara cewa komai ba , Sarfaraz ya dauki waya ya kira Dr Salman yace yazo yanzu suna bukatan shi,
Cikin kan ka nin lokaci sai gashi ya iso aka masa iso ya shigo bayan gaisar dasu da yayi Sarfaraz ya sanar dashi abinda zaiyi cikin kankanin lokaci ya fara