Matar da yanzu shigowan ta ne tayi kanta da sauri "subahanallhi Zulaihat mai ya faru "
kokarin tashi take amma ta kasa tsabar yadda heart dinta ke bugu so fast kamar zai fito waje dakyar ta mike wanda ko sakan batayi ba ta fadi rigijibbb akasa
Ware ido tayi ta karasa da gudu cikin rudu take ambatan sunan Allah ganin ko numfashi mai kyau batayi ne yasa ta kwala kara "Sawban kira Akhie dinka da gudu yana farlo ,"
KANO STATE (NIGERIA)
MASARAUTAR SUHATAJ MUHD HABIBULLAH
Court room (kotu dakin Shari'a)
"Bayan bin cike mai tsayi da akayi an kama Yarima Mubeen da laifin keta hakkin bayi ba daya ba biyu ba har goma sha biyar, sannan an kama shi da laifin cin amana da kuma bata sunan Yarima Fareed bugu da ƙari ya zubar da kima da darajar Masarautar nan mai tarin albarka.
Da duka wannan laifin yasa wannan kotu mai tarin albarka dake ƙarƙashin Masarautar Suhataj Muhd Habibullah ta yanke masa hukuncin dai dai da laifinsa kamar haka;
Na farko kotu ta yanke masa hukuncin daurin rai rai Kasancewar bai wahalar da Shari'a ba yasa ta masa sassauci batara ba kuma horo mai tsanani.
Na biyu kotu ta yanke hukuncin warware alkawarin auren dake tsakaninsa da Sarauniya Mobeena Kasancewa yaci amana sannan bada zuciya daya yake sonta ba.
Na uku zai wanke Yarima Fareed daga zargin da ake masa na lalata rayuwar bayin Masarautar nan.
Wannan shine abinda kotu ta yanke,"
Cike da girmamawa Sarkin Shela ya fuskanci Suhataj da kuma Baba sarki yadan sadda kansa Alaman girmamawa cike da isa Baba sarki ya masa alama daya mike sannan yayi gyaran murya wanda yasa kowa hankalinsa ya dawo inda yake don sauraron abinda zai fada
"Har yanzu kana da damar sanar damu dawa kake aiki a Masarautar nan?
waya saka ?
Na maka alkawarin idan ka fada zansa a maka sassauci koma a yafe maka duka laifinka naga Alaman kai yaro ne har yanzu amfani kawai ake da yarintar ka, ka fadi koma waye ne za'a masa hukunci dai dai da abinda ya aikata "
Mubeen dake durkushe akan guiwansa da dogarai a gefen hagu da damansa hannunsa ko a daure tam ya sake wani murmushin gefen baki
"For all this years kun kasa gane wanda yake hada kanku ya gwara yake wargaza maku farin ciki, shine yanzu kake tsammanin inna fada ma zaka yadda kuma zaka iya yin maganinsa"
Cike da karsashi dogarin dake tsaye akansa ya daga dori nan sa zai zuba masa
"Kai hattara karamin mutum a gaban manya kake ka kiyaye harshen ka,"
Bai kai ga zuba masa ba Baba Sarki ya daga masa hannu wato ya dakatar dashi
"Ban gane mai kake nufi ba jikana ,"
"Baza ka taba ganewa ba abinda kawai nake so kasani shine maka shinka yana tare dakai yana kuma maka tono kuskure kadan zakayi ka fada cikin wannan ramin inaso kasan yadda da wassu mutanen ba karamin illah bane ka nustu kasan mai kake ciki koda kun kawad dani inaso kusan kun kashe maciji ne baku sare kai ba, dakai nakeyi mai martaba Suhataj kar kayi tunanin dan uwanka na jini ne ke maka wannan abun don dan uwanka zai iya cin naman ka amma bazai taba tauna ƙashinka ba,"
tass!!! Kake ji Gimbiya Zunnura ta wanke fuskan Mubeen da mari
"Kaci amana ta ka tauna mun asiri Ni ba wannan tarbiyan na maka ba Mubeen kaduba kaga mutanen nan su suka maida kai mutum suka baka mukami daga jikan Waziri kazama Yarima Mubeen sun ci dakai sun shayar dakai sun tufatar da kai, ba banbanci tsakaninka da ƴaƴan da suka haifa shine zaka saka musu da Wannan danyen aikin,"
Cukumoshi tayi cikin ƙunan rai tana kuka maiƙona zuciya "ka fada mun dawa kake aiki waya ke saka Wannan ɗanyen aikin ,"
bata kai ga kammala zancen bakinta ba jiri ya kwashe ta zata fadi cikin sauri Gimbiya Fadeela dake gefenta ta tare ta inda sauran bayi suka taimaka mata cikin kankanin lokaci kotu ta hargiste hankalin kowa ya koma kan Gimbiya Zunnura tuni aka samo mata Doctor aka mika ta Clinic dake kusa na cikin Masarautar wanda yake kafin Hospital din Masarautar nan aka shiga bata agajin gaggawa.
Daga fannin Mubeen kuwa aka maida shi cikin kurkuku aka kulle shi.
Ya bar zukatan mutane da dinbin tambayoyi
Shin dawa Mubeen yake aiki ?
Waye Mubeen mai ne ne Asalinsa?
Mai Mubeen yake nufi mai kuma yakeson fadawa Suhataj Muhd Habibullah?
Domin jin amsa wannan tambayoyin ku cigaba da bina a ƙafafen sada labarai kamar haka
Arewabooks
Wattpad
Telegram
My WhatsApp group
My WhatsApp Channel
Anan zaku samu Update akai akai ko ka tun tube Ni ta wannan lambar a WhatsApp 09168962485
Story and written by
Queen Mahirah
Adapted Expert Writer 🖊️❤️
Masu comment ina godiya sosai 😁
Comment and share Please 😔
🧚THE TWO LIGHTS ✨ (RIKICIN GIDAN SARAUTA🏰)🧚
The story contains the fact sympathy,ego, Royalty, hatred, hardship, disastrous love and twin flame journey...
Masu comment 😁ina godiya Allah barmu tare.🤗
Oum Affan ina godiya da irin ƙaunar da kike nunawa littafina.❤️
Story and written by
Queen Mahirah ❤️
The adapted Expert Writer 🖊️🐊
Ga masu bukatan the two lights (rikicin gidan sarauta), zaku iya samu ta hanyar following account nawa da channel Dina kamar haka 😁
Wattpad
queenmahirah14
Arewabooks
Queen mahirah
Ko ku tuntube Ni ta wannan lambar a WhatsApp 09168962485
Don na sambada ku cikin groups da Channel nawa.
Ko kuyi searching group Dina a Facebook wato Novels by Queen Mahirah.
FREE BOOK
BOOK 1
🧚31🧚
RUGAR HARDO BELLO (KANO STATE, NIGERIA)
7:30
Zaune muke a dining kamar kullum munyi shirin tafiya school, cikin kwanciyar hankali muke cin abinci ko ince cikin nustuwa da sanyin jiki, kasancewar mun samu labarin cewa Momy ba lafiya, duk da Hamma Faruq ya tabbatar mana da cewa jikin nata da sauki sai de hakan baisa hankalin kunya kwanta ba.
"Iko sai lillahi Rabbi, kuna cin abinci kamar dole aka saku, makarantar ne baƙwa son zuwa?,
Ko abincin ne bai muku ba?"
Cewar Innani kenan da yanzu shigowan ta farlon ta taradda mu muna cin abinci shine ta hau sababi yadda ta saba.
"Ina muku magana kun zuba mun idanunku kamar na tsofin Mayu kuna kallo na"
Dogon numfashi naja na mike da niyan barin dining area don bani da ra'ayin biye mata yau.
"Ohh 😯 ni Khadijatu daga magana sai cibi ya zama ƙari, tun da baza kici abincin ba zoki kaiwa yayin baku abinci,"
Zumburo baki nayi gaba na hade gira nace yayu a ina kenan,?
Dama muna da wassu yayu ne bayan Hamma Faruq,?
Na mata tambayan ina tsare ta da lulu grey eyes Dina
"Ohh ni Khadijatu Nooriyya bana son bakin hali fah sai aka ce Miki bayan Sheik fetel ya haramta kuyi wassu yayu?
Bana son Wannan hade fuskan naki karku ƙore mana baki da bakin hali ki da ƙwayar idonkin kamar na mage,"
Cuno baki nayi gaba na kara bata face cike da zallan tabara na fara magana,
Ni Ni wallahi ba yayu na bane haka kawai, wassu masu murdadden halitta da hadadden fuska kice wani yayu na, sun wani cikawa mutane gida da ƙattin sojoji ba gyira ba dalili,
Ni wallahi bani da hadi dasu.
"Kyaji dashi ƴar tselen uwa, abinci ne de sai kin Kai musu ko zaki sheke, jiya Islam ce ta kai, toh yau ke zaki kai, kafun su saba su fara zuwa nan suna ci,"
Ware ido nayi in disbelief nace wai a ina ?
Kina nufin nan dakin ƙatti zasu na cin abinci, tab wallahi da sake, magana kike son ji ai ko zaki samu buhu buhu,
"Kede kika sani ki fito ki kai musu abinci, cin abinci anan kuwa ba abinda zai fasu, in kuma kece dani ba nine da ke ba sai ki hana mu gani ,"
Tayi magana yayin da ta bani baya wato tayi hanyar futa daga farlon, ta barni tsaye kamar statue cikinsa cike da takaici.
Cike da jin haushi na juya na fuskanci Islam nace kiji abinda matarnan take fada, kuma wallahi da gaske takeyi, Ni wallahi bana ƙaunar su ko kadan, musamman wannan mai Manyan idon,tuna shima yana sani jin wani tashin hankali i na musanman,
Cike da manyan ce Islam ta tari tissue ta goge lips dinta, dafa kafada a tayi cike da lallashi
" Cike down Noor don't bother yourself, kinsan halin tsohuwar nan sarai da kafiya, taurin kanku bazai sauya mata ra'ayi ba.
Kibarsu su zo na dan lokaci ne, su irin baƙin nan ba'a musu baƙin hali, ko baka son su kadanne zasu bar mana gidan, so kawai ayi sha'ani, amma in sun nuna ɗan yen kai then zamu nuna musu ba'a ja damu,"
Ta kammala maganan yayin da take buga kafadana with full of hope.
Turbune face nayi nace nifa wallahi reni ne da bana so, ba yadda za'a yi su mai dani baiwarsu naga su yan sarauta basu da mutunci wassu lokutan.
"Don't worry Sis, gidan mu suka zo neman magani so I don't think zasuyi gan gancin Mai damu bayinsa, inji sukayi hakan tabbas zasu taruwa kansu match da baza su iya kare kansu ba, trust me ni na fada muku haka ba'a ja damu,?"
Shike nan Allah basu ikon kama girmansu, don shine abinda zan iya fadi yanzu,
"Ameeen, so know hurry up ki kai musu abincin kinsan munyi latti, yanzu about seven fourty, let us not be let,"
Kai kawai na gyada mata na fice kamar bana so simi simi, ina fita na tarar da Innani sai surfa masifa takeyi wai ban fito da wuri ba na shanya ta, ko kula ta banyi ba don takaici na dauki abincin fuskata kamar anyi gobara tsabar bacin rai har yayi jaa, ita kanta ganin yanayi na yasa ta tsagaita da masifan nata.
Cike da gadara hadi da bacin rai nake tafiya har ji nake kamar iska Zaiyi sama dani don bacin rai, na isa bakin kofan nasu, knocking nayi da ɗayan hanuna da ba komai na kai akalla ten second Ina knocking ba wanda yace dani kala, hakan ne yasa na kara hasala ba bata lokaci na murda handle din kofan na shiga da sallama wanda nayi shi a ƙufule, shima har ilah yau ba wanda ya amsa, cikin takaici na isa tsakiyan falon nadire basket din, har na juya zan tafi nau'i kamar alamun mutum abaya na hakan yasa Ni gaggawar juya wa mai zan gani!!!
Mutum na gani zaune bisa daya daga cikin Sifa dake falon yana sanye da farar jallabiya, idonshi a lumshe da alama ba bacci yakeyi ba, ahankali soft pink lips dinshi ke mosti wanda ke nuna tasbihi yakeyi ga Ubangiji.
Kallo daya na masa na gane shine wanda mukayi karo dashi, wani dam dam!!!! zuciyata ta bayar batare da wani dalili ba, wani sabo al'amari ne ya sauko mun lokaci daya wanda na rasa dame zan fassara sa, ahankali na kumshe idonsa na kuma kara bude su tarai akansa na tuna masa Lulu grey eyes nawa wanda Ni kaina bansan dalilin yin hakan ba kasancewar Ni ba mutum bane mai yawan kallo, kamar yadda bana so a yawaita kallo na,
Ji yayi tamkar ana tsikaran naman jikinsa tsabar yadda idona ke yawo a jikinsa, tsuka yaja Wanda yasani dawowa normal sense Dina,
Cikin husky voice nashi ya fara magana cike da gadara kamar haka "Are You iut if your sense,"
Ya karkashe maganan yana kafeni da oily snake eyes dinsa masu firgitarwa,
Niko da karfin hali tsuke face dina nayi jin abinda ya fada, wanda tsabar takaici yasa na juya batare da nace mishi komai ba da niyan na falon gaba ɗaya, sai de bankai ga kara jefa kafata ba nashi yace
"If you dare turn your back on me I will scattered you into pieces,"
Tsabar taurin kai da kafiya irin nawa da kuma ƙarfin hali yasa na cigaba da tafiya majestically,
Mugun fisgan dana ji an mun ne yasa Ni ayyana cewa Mala'ikan mutuwa ne ya Kawo mun ziyara, sai de ban kai ga tantance hakan ba na jini a broad chest nashi, batare da tance tance ainihin abinda ke faruwa dani bane naji an hankada na fadi kasa nayi zaman yan bori wani razananniyar kara na sake wayyyoh!!!!!
End of page 31 follow me for more
Story and written by
Queen mahirah ❤️
Adapted Expert Writer 🖊️📖
Comment and share Please 😔
🧚THE TWO LIGHTS ✨ (RIKICIN GIDAN SARAUTA 🏰)🧚
The story contains the fact Royalty, Ego, Separation, disastrous love, Hardship, Hatred,Twin flame journey....
Story and written by
Queen Mahirah 👑🧕
Adapted Expert Writer 🖊️📖
Zaku iya tun zuba na ta wannan lambar a WhatsApp 09168962485, don na sambada ku cikin groups nawa na WhatsApp, don samun update akai akai😁
🤗Masu Comment ina godiya🙏 , wannan page din sadaukarwa ne agareki😃
FREE BOOK
BOOK 1
🧚32🧚
Cikin tsananin azaba na sake wani razananniyar ƙara wanda ya sashi toshe kunnuwan shi ba shiri, inda akwai abinda ya tsana a rayuwar shi to ƙara yana daya daga cikin su, bare wannan razananniyar ƙaran nawa mai gigita brain.
Fashewa nayi da ƙuka cike da takaicin abinda ya mun ko ƙala na gagara ce wa dan takaici,
Wata razananniyar ƙara ya sake "shut up!!! you bloody idiot,"
Mai makon nayi shiru sai ma ƙara rudewa nayi don na tsani tsawa, Ni tsoro ma nakeji shiyasa ko Innani bata mun sai de tayi ta kananan magana,
Shiko jin sautin ƙuka na ya ƙara rikita masa brain, ji yayi tamkar yayi shot dani, idonshi ko ya kaɗa yayi jaa kamar gauta.
Gadan gadan ya tunkaro ni, yamun wani wawan fincika dayasa hanjin cikina kaɗawa, hade Ni yayi da gini har muna jin numfashi juna, idona ko ras acikin nashi da suka kaɗa sukayi jaa tsabar fitina da bala'i irin nashi.
Cikin muryan shi mai razanar wa ya ce"Ni sa'anki ne ?
Am I your mate ?"
Hannunsa yasa ya bigi ginin da ƙarfi cikin bacin rai "ba magana ake Miki ba!!!,"
Cike da ƙarfin hali da taurin kai irin nawa nake karewa fuskanshi kallo , yayin da inajin tambayan da yamun naƙi kulashi, cike da miskilanci na kauda kaina gefe,
Dayan hannunshi yasa ya juyo da face Dina da ƙarfinsa, yar ƙaramar ƙarar azaba na sake, hanu nasa na buge hannunsa dake rike da haba na .
Murmushin da yafi ƙuka ciwo na sake kafin cike da gadara hadi da Izza na ce
Lemme pass Mr I have a lot to cover, naga kamar baka da abin yi, Ni ina dashi and I don't want to be let
ɗan ware 🐍 snake eyes 👀 nashi yayi, ƙarewa sparkling ✨ face Dina kallo yayi da mamaki, yana so ya tabbatar da ba mafarki yakeyi ba.
Ganin kamar bai san abinda nake nufi bane yasa ni sa both hand Dina abroad chest nashi da niyan hankaɗa shi, kasancewar yasa dayan hannunshi ya tokare ni, sai de kamar dutse aka ajiye ko girgiza baiyi ba,
Ƙarewa hannun nawa kallo yayi wanda yake kallon su kamar wani tsinke, yana da tabbacin damƙa daya yayi musu zasu yi karayar da babu mai daurin da zai iya saita su,
Cike da tsiwa da gadara na ce I told you Ina da abun yi, so kabar Ni na wuce, kai kuma da baka da abun yi sai kaje kacigaba da zaman da kasa a da kuma kin amsa sallama, naga you are good at ignoring people,
Ƙarewa small cute pink lips Dina kallo yakeyi, yanda suke juyawa da yadda salon maganan nawa ke fitowa na bashi mamaki matuka, duk da ko kana iya hango zallan shagwaba tattare da yanda nake magana, sai de hakan bai hana zallan Izza da taurin kaina bayyana ƙarara ba, uwa uba zazzakar muryana wacce tayi nasaran jefa brain dinshi a coma, wato kwakwalwar sa ta tafi hutu na wucen gadi ma'ana na yan mintina, zuciyar shi kuwa tayi sanyi kalau.
Turbu ne face nayi na cuno baki 😗gaba na ce ni ni ni wallahi ka masta na wuce,ƙato dakai ka danne yarinyar mutane a bango, wallahi ka barni ko na maka ihun gardi.
Ƙifta ido yayi na yan sakanni kafin ya bude su tarai a face Dina, wani guntun ajiyan zuciya ya sake, ya rasa ma mai zai ce kasancewar ya nemi bacin ran nashi ya rasa, zuba mun snake eyes nashi yayi yana ta kallo na, wato ya kafe ni da Mayun idonsa mai sa hantan mutum kaɗawa ,
Ganin ƙallon yayi yawa ne yasa ni tsorata da tunanin ko aljani ne ba mutum ba, ba abinda ya ƙara raza na Ni sai tuno da abinda na gani a idonsa jiya wanda a zahiri yafi karfin brain Dina, ganin abin bana ƙare bane yasa ni fashewa da kukan shagwaba harda bubbuga ƙafa, wanda ya haifar da jijjigawan komai na jikina.
Cewar Fareed da yanzu fitowar sa kenan daga dakin sa yayi wanka, yana sanye da three quatre da armless shirt,
Cike da hanzari ya hankaɗa Ni bayansa, cikin wani yanayi nason kar a ganni, musamman yadda komai na jikina ke girgiza.
Ni ko ganin na samu dama ne yasa ni fita a ɗari sanda na tabbatar da nasa ɗayan ƙafana a waje, na juyo na ce Allah ya isa na, mugu kawai azzalumi, mai danne ƴayan mutane a gini,
Ina gama fadin haka na kwasa a ɗari, aka bar Fareed da sake baki galala🤤 "I can't believe what he just heard yarinyar nan na fadi, to mai hakan yake nufi?"
Da kallo yake bin MG Fahreen wanda ya taune lips dinshi dajin abinda ta fadi,
ko kyafta ido Fareed ya gagara yi😲
"Tweeny what did she mean?"
ko kallon inda Fareed yake bai kara yiba ya ce "why don't you ask her at the first place,"
Yayi maganan yayin da yake nemawa kansa mazauni.
Baki da hanci Fareed ya sake yana bin MG Fahreen da kallo fuska da alaman tambaya😲🤔???
End of page 32 follow for more
Story and written by
Queen Mahirah
Adapted Expert Writer 🖊️📖
🧚THE TWO LIGHTS ✨ (RIKICIN GIDAN SARAUTA 🏰)🧚
The story of Royalty, Ego, Separation, disastrous love, hardship, hatred, Twin flame journey...
Story and written by
Queen Mahirah 👑🧕 (Wordsmith)
Adapted Expert Writer 🖊️📖