Faruq da tayi zurfi cikin kogin tunani ne tayi firgitt ta dawo normal sense dinta, jin abinda Innani tace
"bari na hada masu ruwan wanka inna wanke su sai abasu madaran nasu su sha, "
cewar Innani Ummin Faruq tace
"to umma,"
mikewa tayi ta kwantar da baby dake hannunta ta shiga toilet ta hado ruwan dumi ta fito dashi, tazo ta dauki wanda ta jiye ta cire mata kayanta tas, ta nufi gurin ruwan da ita ta sata aciki ba shiri ta bude bakinta ta fara kuka enyehh enyehh,
abinka da jariri kowa yasan al'adansu ne kukan wanka, haka ta wanketa tass, tasa ta cikin wani towel ta nade ta, mika wa Ummin Faruq ita, ta karbi na hannun nata itama tamata wankan,
ita ko Ummin Faruq ta fara bata milk ๐ผdin ba musu ta karba ta fara sha, har abin tausayi, kamar wanda akamawa horon yunwa, ita kanta sanda idon ta ya cika da kwalla dan tausayin babyn, Faruq dake gefen Ummin nashi yace
" kai Ummi ganta kaman zata cinye feeder, ๐ผga yanda take sha gaskiya she is so starving,"
daga bangaren Innani kuwa ta gama mata wankan tass itama ta fara bata milk din, hka itama ma kamar zatayi swallowing feeder,๐ผ kana gani kasan ba karamin yunwa suke ji ba,
na hannun mahaifiyar Faruq ne ta fara koshii, inda ta daura ta a shoulder dinta tayi ga'sta sannan ta saukar da ita,
daga cikin kayan Islam aka duba musu kayan sawa over roll tasa mata wanda ya amshe ta, bayan lotion data shafa mata tasa mata diaper da perfume, ta taje mata yalwaceccen gashin kanta mai dan karen yawa da stansi hadi da laushe baki wuluk dashi,
fula tasa mata gudun kar mura ya kamata dan sai hattishawa take ta yi, ba karamin kyau tayi ba haka itama na hannun Innani ta shiryata, sun yi kyau ba kadan ba,
dukansu uku aka kwantar dasu aguri daya, sai suka zama abin shaawa tamkar yan uku,
Faruq yace "woww ummi look at them kamar wassu triplet,"
Innani ta amshi zancen da cewa
"mashaallah gansu kamar yayan larabawa, sai Islam din ma ta saje dasu kamar wata balarabiya ta zama itama, har wanin kama suke kamar uba daya ya haifesu,"
wanii dummmmm kirjin ummi ya bayar dajin maganan Innani daya zo mata tamkar saukar aradu ta ka,
tabbas shine abinda take hange tun kallon farko data mawa babies din, yanayin kaman jinin da suke da mahaifin su Islam ya fito karara,
dan baza kace suna kama na fuska b saide na jini da yana yin halitta irin su haskensu da gashi sai kuma wani tabo data gani wanda mahaifin su Islam na da shi haka Islam da Faruq din ma nada shi,
ta taba tambayarsa tabon ta mai ne ne ya amsa mata da cewa gadon gidansu ne
to mai hakan yake nufii shin wayannan yaran suwa ye ne???,
daga ina suke???
mai ne ne hadinsu da mijinta???,
karde abinda take gudu ne zai faru, dako haka ne tana gabb da rasa ranta
Chief Imam dake gefe ne wanda yake kula d yananyinta tun dazu da irin kallon da takewa yaran,
ya fahimci irin halin da ta shiga wanda shima anasa bangaren haka ne yace Bintiii.............!!!!!!!!!!
Story & written by
Queen Mahirah
ADAPTED EXPERT WRITER ๐๐๏ธ
BOOK 1
๐ง 2๐ง
Chief Imam daya gama fahimtarta ne ya kira ta cikin muryanshi ta nutsuwa kamar haka
"Binti,"
firgitt ta dawo normal sense dinta tace
"naam Abba,"
da wuri ta saukar da kanta kasa, ganin irin kallon daya ke binta dashi yace "
"mai ya sameki,ko jikin naki ne,"
kai ta jijjiga mishi tace
" aa Abba lafiya na kalau"
"kin tabbata, "
tace" ehh Abba,"
kai ya gyada yace
" yayi kyau, munyi waya da mahaifin su Faruq yace gobe zai zo ya duba ku,"
kara saukar da kanta kasa tayi cike da kunya tace
"to Abba,"
sai wani bangare na zuciyarta na cigaba da stinkewa akai akai, Innani tace
"to yanzu Sheik ya za'ayi da yaran kaga mu yau zamu koma gida, kuma bai dace a rabasu da mahaifiyarsu ba, duk da ba shayar dasu zatayi ba, amma de suna bukatan dumin jikinta,"
gyada kai yayi yace
"to ya kike ganin zaayi yanzu",
"tohh nace ko zamu bari sai gobe sai kawai mu tafi gaba daya, tunda likitan yace zuwa gobe zata farfado,"
murmushi yayi yace
"duk yanda kika ce haka za'ayi uwargidan sheik,"
murmushin itama ta masa, shiko yana daya daga cikin abinda yasa yake kara sonta, sabida yanda take darajashi wanda yakai duk abinda ya fito daga hannunshi shi, shima nashi darajan na daban ne, ga tausayi shi kam yasan yayi saan mata,
Faruq ne ya kaste musu hanzari da cewa nikam
"yau anan zan kwana nida triplet dinaaa," ya fada in his childish voice Innani tace
"cununu da baki, ba inda zaka kwana gida zaka koma, gun Umaima ku kwana tare,"
{wato mama karama} make kafada yayi, yace
" nikam aa anan zan kwana ba gurin Umaima ba, ni agurin Ummi na zan kwana,"
" eyyehh,!!"
abinda Innani tace
"sai mu gani, tunda kaine dani bani ne da kai ba,"
"nikam aaa anan zan kwana, ai ni mijinki ne dole kiyi abinda nace"
Ummin shi ne ta fisgo shi, cikin jin haushin yanda yake musayar zance da mahaifiyarta tace
"baka da hankali ne, saar ka ce ita dazatayi magana kaki ji wakafi eyyeh,"
Innani ne ta mike da sauri ta karbi Faruq daga hannun Umminsa, tace "
Fatima kashe shi zakiyi ne, ina ruwankin dashi,"
cikin kuluwa tace
"haba umma kiji yanda yaron nan yake miki rashin kuny,"
dakuwa ta mata tace
"hungo naki Fatima nace hungo naki, ina ruwanki ake yayi wa rashin kunyan, kuma mai abun rashin kunya ni ba kakarsa bace, "
shiru tayi bata ce komai ba sai tafasa da zuciyanta keyi tana jin haushin yanda Faruq ke wasta magana a Innani duk yanda yaso, bata son hakan amma innani ta gagara gane wa, ba dama ta kwabe sa sai ta nuna bacin ranta,
ba abinda yakara bata haushi sai ganin yadda innani keta faman rarrashin sa da take yi,
itako har wani hawayen bakin ciki take yi, Abban tane ya kira ta ya nuna mata gefensa, wato tazo ta zauna ba musu taje ta zauna,
murmushi yayi yace "sabr ya Binti, dena zubar da kwalla akan danki, hakan ba kyau, ko bakya so yayi albarka ne,"
da wuri da jijjiga kanta ta goge hawayenta, murmushi ya kara yi yace
"Imam yaro ne,amma yana da fahimta, innani mahaifiyar ki ne kuma tana da fada, sannan tana kaunar Imam kuma bata son laifinsa ko kadan, ke kuma bakyason yanda yake yi mata wani abun ko,"
gyada mishi kai tayi yayi murmushi yace,
"tohh yanzu kinsan Imam nada fahimta, cikin nutsuwa zaki na daura shi akan hanya, ki nuna masa abinda yake ba dai bane, ba dole sai agaban innani zaki stawatar mishi ba aa daga baya sai ki kirashi ki mishi fada, akan abinda yake mata, sannan ki dena yin fushi dashi haka, dan zai iya jawo masa mastala arayuwar sa, in ya bata miki rai ki daure ki samasa albarka, ki kuma masa fatan shiriya, sannan kiyi kokarin daura sa akan hanya, ki kuma dena bata ran mahifiyarki akan Imam, in suna abu karki kula su ko ma kibar inda suke, inta bukaci kimasa fada to sai kiyi,"
"tohhh Abba inshallahu zan kiyaye",
" Allah miki Albarka, "
"amiiin Abba"
sallaman da akayi ne yasa hankalinsu ya koma kan wanda yayi sallaman tare da amsa masa,
wata yar matashiyar yarinya ne tashigo, hannunta dauke da basket wanda da alama na abinci ne sai wani jaka,
kallo daya zaka mata ka hango stananin kaman da suke da innani,
Faruq ne yaje da gudu ya mata oyoyo itama oyoyon tamishi kafin ya karbi jakan hannunta suka karaso har kasa ta stuguna,
cikin yaren fulatanci ta gaisar da Chief Imam ya amsa fuska dauke da faraa, ta juya bangaren innani ma ta gaishe ta, itama ta amsa sannan ta gyada ummin Imam, ta mata ya jiki, ta amasa mata gaisuwar duk cikin yaren fullanci,
Faruq yace" Umaima zo kiga triplet din mu"
murmushi tayi tace
"kaide little baa rabaka da shirme, triplet kuma a ina, ina muka samu yan uku,"
hannunta yaja yace
" zo kigani,"
haka yakaita har gaban gadon yaran dake kwance abin shaawa,
ware ido ๐tayi ta dafe kirji tace
" kai mai zan gani,"
ta juyo ta fuskanci su ummi tana neman karin bayani little yayi wufff yace
"mata stintar su muka yi nida jaddi na harda mamansu,"
waro ido tayi tace "
mun shiga uku stintarsu kuma, umma wai haka,"
tabe baki tayi tace
"bakiji abinda ya fada bane ko karya zai miki,"
"shine kuma aka wani hada su da islam kalen su shafa mata wani cutan waya sani ma ko aljanu, ne gaskiya bai dace ahadasu da islam ba,"
hannu tasa da niyan dauke islam innani ta daka mata wani stawa
"keeee karki kuskura baki da hankali ne waye sa'an ki anan, ke zaki nuna mana abinda ya dace muyi, wa kika fi,"
zumburo baki tayi gaba tace
"haba umma ni mai kuma nayi ai gaskiya na fada, kawai daga stinto yara sai ahada su da namu dube su fa kamar wassu yayan aljanu",
innani ne ta hau banbami da sababi shiko,
Chief Imam bai ce kala ba sai hasaso abubuwa da dama da yakeyi game da yartashi Zainab, wanda halinta ya ban ban ta dana yar uwarta,
kai kaf gidan ma ita halinta daban ne ita tana da bakin hali, bata son mutane bawai hayaniya ne bata so ba bare ace miskila ce aa ita nata bakin hali ne ayanda ya auna, tana kuma da hassada wanda har yar uwarta ma takanyiwa, tana kuma da girman kai da son ace tafi kowa, yana da labarin irin tabaran datakeyi arugarsu ko abota bada kowa takeyi ba sai mai kudi,
kuma yanzu ma yasan kyan yaran data gani ne yasa ta ce wa kamar aljanu,
haka koda aka haifi islam sanda tayi furucin daya girgiza shi, wai ita ma sai ta auri balarabe wanda yafi mijiin yayarta kyau ta haifi yayan da suka fi na yayarta kyau,
firgitt ya dawo normal sense nashi jin kukan jariran da alama sun tashi daga bacci,
kuka suke ba kakkautawa wanda suka ki yin shiru innani tace
"wannan bazaa akai su gun mahaifiyarsu ba kuwa, ko in sukaji dumin jikinta zasuyi shiru,"
ballawa Zainab harara tayi tace
"muna fuka mai bakin halin stiya sai ki dauki dayan muje ai,"
,Chief bai ce kala ba ya mike ya musu jagora har dakin da mtar ke kwance abun tausayi suka shiga,
tabbas duk inda zaa kwatanta kyau matar nan takai har tafi dan ko kyau da kanshi ya ganta sai ya bata guri,
stawan da innani ta mata ne ya dawo da ita hankalinta
"zaki bani yarinyar ne ko saina gaggaura miki mari,"
sum sum tamika mata dan duk rashin kunyar ta tana storon innani ta dake ta,
dan sai tayi kwanaki bata ware ba karban yar tayi ta kwantar da ita akirjin mahaifiyarta yanda tayi wa dayan,
kamar kibtawa da bismillah kuwa sukayi shiru basu kara cewa komai ba, suka yi shiru sai sauke ajiyan zuciya da sukeyi akai akai, cikin mintina kadan suka koma bacci balla mata harara innani tayi tace
"kije ki dauko mun jakan kayana da kayan sawan yaran, ki kuma kawo mun abinci,"
zumbura baki tayi tace nifa ban san inda kayansu yake ba, tana magan tana aunawa matar dake kwance harara wanda bata ma san tanayi ba,
innani ne tayi kanta tamkar zata gaggaura mata mari ko ince da niyan gaggaura mata mari ganin hakan yasa ta fita da gudu
tana fita ta hadu da Abban su wato Chief kallon daya bita dashi ne yasa ta hadiyan yawu tasan tabbas ransa ya baci matuka akan abinda tayi,
ita ta manta cewa yana dakin ma tayi wannan diban albarkan wani miyau mai zafi ta hadiya, dan tasan zataci stelen uwata dan Abba yamafi umman zafi sosai,
ai da sauri ta wuce kanta har wani hardewa yakeyi ta isa bakin kofan dakin saide abinda taji yar uwarta ta na fada ne yasa ta ja burki,
,wani murmushi tayi na nasara dan tabbas ta samu makamin da zata fatattki matarnan da yayanta daga gidansu, dan tasan muddin matar nan zata cigaba da zama agidansu tofa kashinta ya bushe,
yanzu ma tasan sai Abba yaci ubanta dole tasan yadda zatayi ta ingizasu wani murmushin ta karayi ta murda kofan dakin
QUEEN ๐ MAHIRAH ๐ธIDRISS
๐งTHE TWO LIGHT โจ[RIKICIN GIDAN SARAUTA๐ฐ]๐ง
Story & written by
Queen Mahirah
ADAPTED EXPERT WRITER ๐๐๏ธ
BOOK 1
Follow this link to join my WhatsApp group shower ๐ฟ with comment and react ๐๐๐คฉ
https://chat.whatsapp.com/DEb6DCrj50r88WN25D5xu9
๐ง3๐ง
Murda handle din kofan tayi ta shiga cikin dakin inda ta hango ta tana zaune bisa sofa dake dakin da alama tayi zurfi cikin tunanin da take yi,
cike da kissa tayi wani murmushin munafurci ๐sannan ta karasa inda take tasa hannunta a shoulder dinta wanda yasa ta dawo daga duniyar tunanin data lula,
kara marairaice face nata tayi tace
"Adda Fati kema kina tunanin abinda nakeyi ko ?,"
cikin rashin fahimtan abinda take nufi tace
"mai kenan",
dan cuno๐ baki tayi gaba
"come on Adda don't pretend kidena acting as if like bakisan abinda nake nufi ba,
after all kin san komai",
dan hade fuska tayi
"nifa bana son shirme kiyi magana yadda zan gane kidena mun shiga da futa",
marairaice face nata tayi sai tazama abin tausayi,
"game da twins din nan nake magana nasan kema bawai kin yadda dasu bane musamman yadda inkika kula suke kama da little da ita kanta Islam din ma kamar yayi yawa ni dana gansu har na fara jin shakku,"
cike da zakuwa da son kin gasgata abinda yar uwar nata ke kokarin fada
" shakku akan mai,"
itako ganin yadda Addan nata ta dan rude ne ta kuma kafeta da ido, yasa tayi saurin sadda kanta kasa tana wani culprit din smile๐ a heart nata,
"yi hakuri Adda (yaya or anty) naga kaman ranki ya baci ni bari ma naje nayi abinda aka aiko ni,
dama Innani ne tace nazo na diba mata kayanta ita da sabin jikokin nata data samu daga gurin sirkinta,
ban san ma mai tagani ajikinsu ba wanda yasa sukafi Islam mutunci agunta ko dan ma ba abin mamaki bane yadda naga wannan mahaifiiyar tasu ba abin mamaki bane in hakan ta faru,"
tana maganan ne cike dason tunzura yar uwar tata bata yi kuskuren data bari suka hada ido ba,
sai de tana satan kallonta da kuma fahimtar irin yanayin data shiga wanda da alama hakan ta ya cinma ruwa,
ta cigaba dayin aikin daya kawo ta yayin da take cusa mata zancen da tasan tabbas zasuyi tasiri a zuciyar duk macen data cika mace mai kishin mijinta da aurenta,
wanda sai ka kai zuciyar ka nesa kafin ka kubutar da kanka daga halaka cikin stawa tace
"ya isa wai mai kike nufi ne",
murmushin nasara tayi a heart nata kafin ta karaso inda take hannunta dauke da basket da jakan kaya ta dire su agaban yar uwarta tace
"abu biyu nake nufi anan, na farko mahaifiyarki ta fifita wassu bare akanki wanda bata san asalinsu ba,
ta tafi ta barki alokacin da kike bukatanta,
haka danki ya kaurace miki ya tafi gun 'ya'yan da baa san daga ina suke ba,
abin dubawa anan shine mai zaisa little yin hakan??
aganina ba komai bane ke jansa sai jini, ina nufin jinin dasuka hada da yaran,"
ba shiri ta dago manyan idonta ta zubasu akan Zainab, da ta cigaba da zuba zance
"ehh abinda nake nufi kenan yaran jinin Faruq ne shiyasa jikinsa ke rawa akansu,
sanin kanki ne Faruq baya shiga harkan yayan mutane amma yaran nan ko ina aka kaisu yana bayansu sabida mahaifi daya garesu kuma shine mahifin Faruq k.......,"
hannu ta daga mata " ya isa Zainab bana son maganan banza, ni ba sa'ar ki bane da zakina fada mun duk zancen da kika ga dama hak mijina ba abokin wasan ki bane,
da umma ta tafi gunsu ai ba kina tayi ba su sun fini bukatar taimakon ayanzu shiyasa,
in Faruq yaso yaran to wannan ra'ayinsa ne", .
murmushi Zainab tayi tace" Adda kenan shiyasa kullum ake cutarki sabida kin fiye tausayi da yawa,
asibitin nan acike yake da masu aiki mai yasa ba'a umarcesu dasu kula dasu ba,
ita umman Dr ne,??
kuma shi mijin naki mai ya hanashi zuwa ya duba ki in yana da gaskiya,
ina tun kafin ayi suna dayazo bai kara zuwa ba,
kuma ai yasan baki da lafiya naga tun cikin ki yana wata 5 ya dawo dake nan rugar,
to shi waliyyi ne da zai zauna ba mace har na stawon wata hudu,
shi yasan abinda yakeyi kuma ba komai bane sai barikanci anan yasa mu yaran nan,"
tasssssssss kakeji Fatima ta wanke Zainab da marin da sanda taga taurari, sannan ta nuna ta da manuniyar ta
"this should be the last time da zaki kara fadin maganan banza akan mijina,
if not i will make sure i break every single bone from your body",
Zainab dataji marin tamkar saukar aradu ta ka ta gagara ko mastawa daga inda take,
.she is suprise cos Addan ta bata taba ko da zungurin taba arayuwarta duk dako irin azaban rashin kunyan datake mata, ko wani bata so taga yana tabata amma yau ita ta mareta da hannunta,
"Adda ni kika mara akan wassu kazaman bare da bakisan asalinsu ba,
stintattun mage ni Zainab Adda akan na fada miki gaskiya shine kika mun haka akan mutumin da bakisan asalinsa