x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 25 - THE TWO LIGHT RIKICIN GIDAN SARAUTA

  • 72001 words
  • 75000 words
  • Out of 97531 words

Category: Love Stories

Views 533

20 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
gudanar da abinda ya kawosa sanda aka sha Daru kafun aka Diba jinin Mehnoor kamar zata mutu kallo Daya zakayiwa Master ka hango zallan kauna ganin yadda take ta kuka ne yasa ya cewa Dr "ka mata ahankali,"

Kowa na farlon sanda ya daga Kai ya gansa Jin yadda ya sassauta muryansa Wanda Hakan ya kasance sabon Abu a garesu sanin halinsa na nuna halin ko in kula ga kowa.

Cikin kankanin lokaci aka Kai blood din lap aka fara test .



RUGAR HARDO BELLO (KANO, NIGERIA)


zaune nake ni Mahnoor a falo ni kadai nayi zurfi cikin kogin tunanin abinda ya faru dazu wanda nake gani tamkar mafarki nayi saide da alama ba hakan bane kasancewar mun gaisa da daya daga cikin bakin da mukayi hakan ne ya tabbatar mun da cewa ba mafarki nakeyi ba hmm!!! dogon numfashi naja na lumshe narkakkun eyes dina masu kama da ruwan madara.

na dau akalla minti shabiyar ahaka batare da na mosta ba sai de zuciyata yana cike da tambayoyi da dama wanda ni kaina ban san wa zai ban amsa ba .

sallaman da Islam tayi ne yasa na ware manyan lulu eyes nawa akasan makoshina na amsa mata sallaman da tayi gefena tazo ta zauna ta dafa sholder na "how are you feeling know ?,"

murmushin yake na sake mata kafin na bata amsa da am feeling fine


"okay yanzu mai kike so kici sai na dafa miki ,"

dan turbune face nayi nace don't stress your self am okay


"you most be joking tun breakfast fa da mukayi baki kara cin komai ba kuma ina lura dake ko breakfast din ma baki ci sosai ba and now you are telling me wai you are okay as how?
yanzu fah karfe hudu yayi ,"


Cuno baki na nayi gaba nace nifa na koshi bana Jin zan iya cin komai a yanzu infact bani dama appetite


" Okay naji but tell me Mai yake damunki yanzu naga kamar akwai abinda ke scattering brain dinki ,"

Dogon numfashi naja kafun nace I don't know sis ban sani ba kawai inaji kamar an kulle ni inaji kamar an daura Abu Mai nauyi a heart nawa, Ina da tambayoyi da dama na rasa wa zai amsa mun su, na karasa zancen nawa cikin kunan rai


"In baki manta ba kafun zuwan wannan lokacin Jaddi y sanar dake cewa duk abinda zai faru dake cikin kwanakin Nan ki dauke shi a mastayin jarabawar ki kinsan ko wani bawa da nashi jarbawan ,"

ban mantaba Islam Amma Ina da tambayoyi da dama Wanda nakeson abani amsar su ko naji saukin abinda ke damuna

"Ina so kisan ayanzu ba Wanda zai amsa miki wannan tambayan naki infact ko an amsa miki ba lalle ki fahimci abinda ke wakana ba kede kawai ki bar komai ki mika komai ga ubangijin ki shi zai magance miki komai ,"


dogon numfashi naja kafun nace Islam da gaske ne munyi ɓaki ko mafarki nakeyi abinda ya faru dazu gaskiya ne, na Kai karshen zance nane yayin da na zuba mata oily grey eyes nawa

gyada mun Kai tayi "ehh munyi baki ƴaƴan Suhataj ne suka zo sun kawo Dan uwansu bashi da lafiya,"


kina nufin Wanda mukayi karo dashi dazu

gyada Kanta tayi wato alaman ehh

dogon numfashi naja yah Allah how could this be possible

"what happened Noor?,"

girgiza kaina nayi I don't know?

But definitely akwai abinda ke shirin faruwa dani Islam bazan boye Miki ba all my life inajin kamar akwai wani bangare Wanda Babu ajikina and heart nawa Bai taba bugawa haka ba dayawan lokaci Ina tunanin bani da zuciya ne at all duk da nasan is impossible mutum ya rayu Babu zuciya but for me Ina rayuwa ne batare da zuciyata tana bugawa ba,
but today for the first time naji heart nawa yayi bugu Mai karfi Wanda yasa nayi loosing control dina I feel like yau na shiga wani Sabin rayuwa Mai cike da kalubale da dama Wanda kunnuwa baza su ya sauraronta ba yau naji inason sanin wace ce ni ?
Waye mahaifina ?
Ina Yan uwan mahaifiyata suke?
Kuma Mai Nene sanadin barinta gida?

Innani dake bakin kofan ne zuciyanta yayi wani wawan bugu Wanda yasa tayi saurin dafe setin zuciyanta Jin yanda yake barazanan fitowa waje,

wannan shine abinda take storo ranar data ke barazanan zuwanta lokacin da baza ta iya juran gani da sauraro ba wato lokacin da gaskiya zatayi halinta lokacin da Mahnoor zata so komawa gun ahalinta Wanda Hakan bakaramin hastari bane da barazanan ga rayuwarta domin bakin da ya furta Kalmar ƙi afari ko ya dawo ya furta so to ba abun yadda bane .



END OF PAGE 2️⃣6️⃣


STORY AND WRITTEN BY
QUEEN MAHIRAH ❤️
ADAPTED EXPERT WRITER📖









THE TWO LIGHTS ✨ ( RIKICIN GIDAN SARAUTA 🏰)




Story and written by
Queen Mahirah
ADAPTED EXPERT WRITER 📖🖊️



Free book


BOOK 1


2⃣8⃣.


RUGAR HARDO BELLO (KANO , NIGERIA)

Dogon numfashi Islam taja "do you think sanin hakan zai gyara abunda ya dade da afkuwa ne ?

babu abinda Hakan zai amfane mu dashi ayanzu Daya wuce bacin rai da tashin hankali, ni kaina a wassu lokutan nakan ji Ina bukatan sanin asalin mahaifin mu badan komai ba sai Dan wassu irin kalamai da ake jifan mu dashi musamman in muka je gidan Hardo,

nakanji Ina bukatan sanin wacece ni ?"

folding both hand dina tayi da nata soft hand din ta cigaba da cewa "aduk lokacin dana daga Kai naganku inajin wani kwanciyar hankali Ko ba komai Ina daku mastayin Yan uwa Kuma ta bangaren mahaifina,

Noor ayanzu bani da wassu Yan uwan Daya wuce ku, duk da Ina bukatan sanin asalin mahaifina da dalilin barin ahalinsa sai de idan nayi la'akari da wassu abubuwa nakanji komai ya futa daga raina,

duk da cewa acikin mu ba Wanda yasan dalilin da yasa iyayen mu barin ahalinsu kasancewar basu sanar damu ba har ilah yau Kinga Hakan na nufin bamu Kai sani ba ko lokaci bai yi ba ko Kuma sanin hakan bashi da wani amfani agaremu."

Huhmm Islam I understand what you are saying but don't you think is high time for Mom and Abie su sanar damu suwaye su ?

We spend about 18 years without knowing our identity , look Islam idan mun nemi da musan asalin iyayen mu doesn't mean that munyi betraying su Innani sanin su baya na nufin zamu koma gurin su da zama ko mu manta halaccin dasu Innani suka mana ba sun riga da sun nuna bamu da mutunci a idon su basu Kuma Kaunar mu.

"Hakane gaskiya kika fada Noor Nima bawai ina nufin zamu Yi betraying su Innani bane kawai banason mu fara abinda zamuyi Dana sani ne kuma kinsan mu mata ne baza mu dauwama agida ba watarana dole muyi aure shiko kinsan dole sai da asali akeyinsa in basu fada mana yanzu ba gaba zasu fada,"

Hakane maganan ki gaskiya ne amma de duk da haka munci kwakwa mun Sha wiya duk da ma mudin ba kanwan lasa bane,

"Ahh toh ba dole mu zama mafadata ba irin stangwaman da mutane ke nuna mana bamu fa isa mu shiga cikin Yara Yan uwan mu muyi wasa ba sai an ci zalin mu wassu ma gudun mu sukeyi wai bil Jinnu ne mu ba bil Adama ba,"

har kin tuno mun yanda na gurda Bodado Kai Amma taji jiki,

"ai ni naso da Surrayya kika gurda ita data yi Hadin munafukar yarinya ni haushi take ban wallahi da ita da uwarta ,"

Murmushi na sake mai cike da ma'anoni masu yawa ,

Hmmm ni yarinyar ma tausayi take bani yadda sam uwarta ta sangarta ta sam Bata da tarbiyya haka wai take son Hamma Faruq,

"Mtchww hmm Aiko iska Yana wahalar da Mai kayan Kara wahalar da Kanta da zuciyanta takeyi a banza don ruwa ba sa'an kwando bane toh ma Banda abinta Mai Hamma Faruq zaiyi da marar tarbiyya irin ta ita fa Bata ganin darajan kowa Bata kallon kan kowa da gashi ko kadan Umaima bata yi tarbiyya Mai kyau agareta ba ,"


ni na rasa wassu iyayen Mai yasa suke haka wallahi sai subi su sangarta yaransu Dan su kadai Allah ya basu suki basu tarbiyya Mai kyau sai de suyi ta nuna musu hanyar Jin Dadi ko waya ce musu Hakan tarbiyya ne oho,

basa tuna tar dasu game da tashin kiyama da hadarin rayuwa dadin duniyan kawai suke sanar dasu sun manta cewa ita duniyan ba matabbata bace ,

sun manta cewa rayuwar duniya aro ce komai na cikinta aro ne Kuma haka zaka mutu ka barsa akai ka kabarinka ko Dan kanfai Babu sai likkafani akuma binne ka acikin kasa karkashin kasa.

"Su Ina suke tuna haka su dadin duniyan kawai suka sani ,"

Tohh Allah kyauta ya kare mu da kariyarsa ya Kuma sa mufinkarfin zukatan mu,

"Amin,"

Innani da zuciyanta ke lugude ne ta sauke wani nauyayyen ajiAn zuciya tayi hamdala ga ubangiji kafun ta juya ta bar gurin tama fasa shiga farlon.

Bayan sallahn magarib Innani ta umarci Islam data zo ta Kaiwa bakin abinci ba musu tazo ta dauki abincin da aka jera akan wani hadadden basket ko ince cikin basket cike da nustuwa da Kamala ta kama hanyar data San zata sada ta da guest room abakin kofan ta dire basket din tayi knocking kofan ba'a wani dauki dogon lokaci ba aka bude mata tare da Bata izinin shigowa.

Cikin siririya voice dinta tayi sallama Daya sa su Mai da hankalinsu ga Wanda yayi sallaman, cikin su biyu da suke zaune a farlon Fareed ne kawai yayi karfin halin amsa mata as always face nashi shinfide da fara'ar dake Kara masa kwarjini da kyan haiba,


"Sannu da aiki uhm I guess Islam ko ,"

gyada masa Kai tayi alaman ehh cikin yanayi na rashin son magana Mai stayi musamman da wayanda Bata saba dasu ba ,

Murmushi ya Kara sakewa "Masha'Allah mun gode Allah yayi Albarka ya saka da alkairi,"

Kai ta Kara gyada masa kamar kullum da face nata da Babu fara'a , har ta juya da niyan futa sai ta dawo cike da miskilanci tace "you guys should check out the food ko akwai Wanda bakwa so sai a canja ,"

tayi maganan ne a miskilanci sannan hannunta na cikin Pocket din track suit nata Wanda yake da kalan sojoji ajiki ma'ana Yana Nan kamar kakin sojoji

"Okay"

shine abinda Fareed yace kafun ya sauko ya bude hadaddun warmers din da suke dauke da abinci na farkon ya bude tuwo ne aciki na semo wanda ke sanye acikin fararen leda,
na biyun ya bude miyan egusi ne aciki Wanda yasha stock fish da nama zubu zubu ga kamshin cray fish dake tashi da alayyaho Daya karawa miyan kyau , har wani lumshe idonshi yayi Jin wani daddadan kamshin dake tashi Mai sanyaya rai da zuciya,

Rufewa yayi ya bude dayan warmer shiko yana dauke da dabjen kaza wanda yasha hadi na musamman sai tashin kanshi yakeyi na tafarnuwa da correander hadaddiyar Jug din ya bude wanda ke dauke da damu na fura sai kuma wani glass bowl Mai murfi shima dauke yake da fruit salad, wani kayaceccen murmushi Fareed ya sake

"Masha'allah komai yayi bamu da abin fadi sai de muce Allah saka da alkairi ,"

kai ta kuma gyada wa ta juya da niyan tafiya sai kuma ta juyo dara daran eyes nata ta zuba a fuskar Captain Fudhal ta gyara stayuwanta mai kyau ta fuskance shi da kyau,

" hey Mr grumpy idan mutum yayi sallama amsawa ake yi ba a hade rai ba, inka amsa sallama ba yana nufin girma ka bawa mutum ba sannan ba zubar da girma bane,

ita sallama wajibi ne ga Musulmi in kuma yayi ta yakan samu lada kaga kenan inka amsa sallama ba faduwa bane ko zubar da girma you should take extra careful of this your behavior cos bazai kaika ko ina ba ,"

tana gama fadan haka ta juya tayi tafiyar ta cike da isa da takama taku take daya bayan daya har ta fita daga farlon inda tabar Captain Fudhal cikin zullumi da tunanin wani irin gida Allah ya kawo su daga zuwan su zuwa yanzu yaga abubuwan da suka charger masa brain har ya fara zargin anya ba aljanu bane.

Gyaran murya Fareed yayi "uhhumm Bismillah Captain sauko ga abinci ,"

yayi magana ne cike da neman magana da zallan stokala , shiko Fudhal hade face yayi kamar anyi masa bushara da an bashi sarautar iblisai ,

"Mtchww,"

dogon stuka yaja yayin da ya mike ya wuce bedroom dinshi , shiko Fareed tunstirewa yayi da dariya sanda yayi mai isan sa kafin ya zuba abinci a plate da komai ya kai bedroom din Fahreen ya iske sa zaune akan lallausan bed ya mikar da santala santalan kafansa idinsa alunumshe yana ta daman tasbihi ga Allah.

Da sallama a bakinsa ya shiga dakin amsa masa sallaman yayi akasan makoshinsa shiga karasawa yayi ya ajiye abincin akan bed side drawer dake dakin shiko ya zauna bakin gadon

"Akhie tashi Kaci abinci kar yayi sanyi ,"

ware lulu eyes nashi yayi ya zuba su a face din Commandore Fareed bai ce dashi kala ba sai gyara zaman sa da yayi yanda zai ji dadin cin abincin , shiko Fareed ganin haka yasan mai yake nufi ɗaukan plate din yayi wanda yake dauke da tuwo da miyan egusi ya mika masa kamar baya so ya karba ya zubawa abincin na mujiya kamar wadda aka bawa stusta yaci ko yaron da aka mawa dole yaci .

"Ko in baka abakin ka ,"

Harara ya watsa masa ya dauki spoon din ya fara kai abincin a bakinsa wanda bai san sanda ya lumshe idonsa ba har kwanyarsa sanda ya amsa dadin abincin
shiko Fareed zuba masa eyes yayi yana kallon sa ya manta when last ya gansa yana cin abinci haka , lura yayi da kallon da Fareed ke masa cikin husky voice nashi yace " stop starring at me like this so kake na kware ne ?,"

murmushi Fareed ya sake"a'a kawai ina farin ciki ne da yadda kake cin abinci yau ba tare da an ma dole ba ,"

Tabe bakinsa yayi cikin halin ko in kula"Kai Kaci abincin ne ,"

girgiza kai yayi "a'a so nake sai ka koshi tukunna na,"

Hade girmansa yayi "ni yaro ne ,"

"a'a kai marar lafiya ne wanda yake bukatan a kula dashi ,"

tabe baki yayi yana mai daga kai kadan "uhmn naji tashi kaje ka debo abinci kazo Kaci , Fudhal yaci ne ,"

"Nopp Bai ci ba ,"

Daga kai yayi a takaice yace Why

"Zuciya yayi dan Islam ta mishi wa'azi akan amsa sallama ,"

girgiza kai yayi cikin wani yanayi "fudhal har yanzu bai canja ba da wannan saurin fushin nashi ba dama a fada maka gaskiya sai kafara fushi ,"

"I guess anan zai samu mai seta sa cos that girl ba storo a idonta ko kadan baka ga yadda ta stare shiba Mr grumpy mafa take ce masa ,"

gyada Kai MG Fareed yayi "je ka debo abincin kazo Kaci ,"

Murmushi yayi yace okay




EGYPT
ABDUL MALIK ROYAL ESTATE

Zaune suke cikin kayaceccen farlo mai girman gaske mai kuma dauke da abubuwan ban al'ajabi na ado da ɗaukan hankali kayan marmari ne zube cikin wani hadadden tire wacce kamar da gold akayi shi yana ajiye bisa wani Centre table na stakiyan farlon wanda royal chairs sukayi kawanya a farlon .

Sarfaraz ne akan 2 Seater shida Shahana sai Master dake Hakim ce akan one Seater yayi Crossing leg din sa gefensa ko Young Master ne shima akan one Seater yake zaune sai 3 Seater wanda Malik Sultan da Malikat Nubia ke zaune.

Shiru ne ya Rasta farlon na yan mintina shigowa daya daga cikin hadiman da aka bawa ikon shigowa ne yayi breaking silence din cike da girmamawa ya dukar da kanshi kasa ya nemawa Dr Salman izinin shigowa wanda dama tun da tun shi suke jira, ba'a dauki wani lokaci ba sai ga Dr Salman ya shigo cikin girmamawa wa ya gaishe su kafin ya sallamar da yar paper dake hannun shi wanda dama ita ce maƙa sudin zuwan
shi Master ne ya karbi paper a gadarance yana bin paper da kallo wanda akayi stepling da steppler ,

Sallaman Dr Salman akayi ya tafi don aikinshi ya kare .

Sanda ya dauki akalla two to three minutes Yana karewa paper kallo kafin ya War ware ta bayan cire karfen da yayi, ba komai bane acikin paper sai result na test din da akayi zubawa rubutun dake cikin paper ido yayi yana bin ko wani harafi yana karantawa cike da nustuwa dan ware idon shi yayi wanda yasa mutanen dake farlon cikin zullumi dason sanin mai ke cikin paper.

END OF PAGE 28


Story and written by
Queen Mahirah
Adapted Expert Writer


Comment and share










THE TWO LIGHTS ✨ (RIKICIN GIDAN SARAUTA







story and written by
Queen Mahirah
Adapted Expert Writer

free book

BOOK 1

2⃣9⃣


EGYPT

ABDULMALIK ROYAL ESTATE
Cike da nustuwa yake bin ko wani harafi na cikin paper yana karantawa dan ware eyes yayi hakan yasa mutanen dake farlon don sanin mai ke cikin paper.

Ya dauki akalla minti biyar Yana karewa paper kallo da nazarin abin da yake ciki kafin ya lumshe grey eyes nashi yana furta Alhamdulillah bai ce komai ba ya mikawa Sarfaraz paper Shima ya karanta wani kayaceccen murmushi a sake cike d murna na tabbatuwa e abinda suke hasashe

"Alhamdulillah yabo da godiya sun tabbata ga Allah subhanahu wata'ala, Masha'allah, Allah mun gode maka daka nuna man wannan rana "

Hannunshi ya daga sama yayi kirari ga Allah subhanahu wata'ala ya cigaba da cewa ko a mafarki ban taba yin makamancin wannan ba hakika Allah baya bacci sannan ba azzalumin bayansa bane, tabbas mun tafka babban kuskure mun kuma zalunci Shazana Zulaihat (princess Zulaihat) Ashe tana da gaskiyar ta mun yanke mata hukunci mai tsanani,

idon mu ya rufe mun zabi kare mutuncin Masarautar mu fiye dana ƴayan da muka haifa amma Alhamdulillah da ita bata kasance irin mu ba ta zabi data rasa ƙima da darajanta don ta ceci rayuwan ƴayan ta sai Allah ya dafa mata duk da
End Ads