An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
GODIYA
Godiya da yabo sun tabbata ga Allahu { s a w}, wanda yabani baiwa da basiran rubuta wannan littafi, ya kuma bani daman rubuta shi, da haka nake rokon Allah ya bani ikon kammala rubuta wannan labari da rai da lafiya na.
SANARWA
banyi wannan littafi dan cin zarafin wani ko wani ko wata ba, wannan labarin kirkirarren labari ne, aguji sarrafashi ta ko wani hanya, wannan labarin mallakin marubuciya ce.
AUTHORS NOTE
Zan fara da mika godiya ta ga Allahu {s a w}, da ya bani baiwa da basiran rubuta wannan littafi, daya kasance shine littafi na farko da na fara wallafawa, wanda ya kasance kageggen labari, ina fata Allah ya bani ikon kammala rubuta wannan littafi cikin koshin lafiya, wannan littafi ya samu kyakyawan rubutuwa da staruwa daga ni Queen Mahira Idriss ina rokan ALLAH daya yafe mun kurakuren dana yi aciki, wanda nayi dai dai Allah bani ladan tare da masoyana.
THE TWO LIGHT [RIKICIN GIDAN SARAUTA]
The story contains the fact Royalty,Ego ,Separation , disastrous love, Hatred, Hardship, Twin flame journey...
Story and written by
Queen Mahirah
ADAPTED EXPERT WRITER πποΈ
FREE BOOK
BOOK 1
π§ 1π§
Wata hadaddiyar mota ce bugun bature mai numfashi da daukan ido da hankalin mai kallon ta, motace wanda sai wane da wane ke hawanta,
gudu motar take tamkar zata bar duniyan, daga bayan motan kuwa wata mota ce ke binta cike da zarra da son cin mata, tamkar zasu bi takan wannan bakin mota mai numfashi da daukar hankalin,
acikin motan kuwa wata kyakkywar farar mata ne tamkar balarabiya ke zabga gudu cikin tashin hankali,
kallo daya zaka mata kasan ba'a cikin hankalinta take ba, gefenta ko wassu kyawawan twins ne wanda ke ta faman zabga kuka da alama yunwa sukeji sai de itakanta mahaifiyar tasu bata da ishesshen nutsuwar da zata iya shayar dasu ayanzu burinta su kubuta daga hannun wayannan azzaluman,
cikin muryar kuka da stananin tashin hankali da firkici tace "yah Allah save us from those evil monsters, yah Allah Protect me
and my children,
ta cigaba da cewa Allah ka stare mu da dukkan starinka ka kare mu....,"
batare da tagama zancen dake bakinta taba motan monsters din data ambata tabigi motarta da karfin gaske cikin zallan rashin iman hakan yasa tayi loosing control nata suka gangara wani jeji parking nasu motan sukayi,
wassu garada guda biyu ne suka fito daga cikin motan kana ganinsu kaga cikakkun yan daba ba ko digon imani a goshinsu,
dayan ne ya leka yace "oga sun sheka fa ita da yayan nata," batare da wanda aka kira da ogan yace komai ba phone nashi ta hau ringing ya dauka, yasa a kunnen shi cikin muryanshi na rikakkun yan daba yace "Allah ja zamanin gimbiya komai ya kammala mun sheka su zuwa barza'u, yau zasu yi kwanan lahira"
daga cikin wayan akayi maganan da baifi na 30 sec ba,
shiko ya amsa da cewa" komi yana kan stari gimbiya,"
kitttt ya ajiye wayan yace "Labaa??,"
yes oga
"muci star mubar nan kar asamu mastala, wannan yar jagaliyan ba mutunci ne da ita ba, ana samun mastala kadan aradu wannan rocket din baza ta bamu salalan mu ba,"
wanda aka kira da laba yace" ta isa oga mu sace mata iska kai,"
"wai awa din,"
"a ita gimbiyar mana,"
" laaba baka san waye bakar maciji bane, duk rashin imaninka ta dama ka ta shanye ka, to wannan da kake gani kaho ne kawai bai fito mata akai ba, shima dan taurin da kaan yayi ne, ko balai ya ganta canja hanya yakeyi,"
"kai ogaa ita wace irin halitta ne aljana ce ita,"
" Laaba"
"naam oga,"
"to ko a aljanu sai anyi bincike mai zurfi kafin asamu irinta, muci star kar muyi biyu babu"
wuffff suka shige motarsu suka bata wuta suka bar gurin, wannan bakar motar kuwa ta cigaba da gangarawa tana kutsawa cikin bishiyoyi
bata staya ako ina ba sai wani tafkeken gona mai girma, mai dauke da mutane suna ta faman aiki ko ince kowa da aikinshi,
wannan motan gadan gadan tayi kan wani bawan Allah dattijo daa akalla zai kai shekara 50 da yan dauri,
yana sanye da fararen kaya kanshi sanye da fula da tasha rawani irin na manyan malamai, fari ne tas kallo daya zaka mishi kasan bafulatani ne gaba da baya
goshin shi dauke da tabon sallah wanda ya karawa kyakkyawar face nashi annuri da hasken imani,
hannunshi ko sarkafe dana wani yaro da akalla zai kai 9 years yaron yana sanye da farar jallabiyarsa da hirami shima fari hannunsa dauke da wayan wasansa yana nan kamar dan larabawa.
ba ji ba gani wannan motar tayo kansu kamar zata take su,
cikin ikon Allah ta hadu da wani duste daya sa ta staya chak, ta fara hayaki daya ke nuna motan na iya tarwatsewa in any second
cikin tashin hankali mutanen da ke ta faman aikace akikace a gonan sukayo inda wannan dattijon yake shida yaron da hannunsu ke sarkafe dana juna har yanzun kowa da abinda ke fadi,
shiko wannan dattijo hankalinsa na kan wannan motan dayake stammanin hadari yayi kuma ran wanda ke cikin motan yana hadari,
cikin muryansa mai cike da nutsuwa imani da zallan tausayi da sanin darajan dan Adam, yace wa daya daga cikin samarin dake gurin,
"ku fito da wanda ke cikin motan kar ya illata,"
cikin girmamawa saurayin ya dukar da kanshi yace
" tohhh malam,"
shi da sauran samarin suka karasa jikin motan don bada agajin gaggawa a wanda ke cikinta,
ko wani daya dagaa cikinsu bakinsa dauke da addu'an neman stari da kariya,
basu sha wiya ba suka bude motan inda suka yi tozali da wannan matar da kanta ke kife jikin sterin motan da alama ta dade da suma, yaran ko har yanzu basu dena wannan kukan nasu ba,
cikin sauri daya daga cikin samarin ya kawo mota akasa matar, wannan bawan Allahn da aka kira da malam ya amshi yaran ya shiga front seat na mai zaman banza shida wannan yaron, matar ko tana back seat,
nan suka dauki hanya suka fara kusta hanya basu jima ba suka iso wani kayaceccen gari,
dan dai dai abinshi mai karancin mutane da yalwar shukoki tako ina,
baza ka kira wannan kauyen da ruga ba dan da alama sun fisu wayewa sai de yanayin kan kantar mutanen garin yatabbatar da cewa ruga ce,
amma na zamani dauke yake da gine gine na zamani dai dai karfin talaka,
hanya suka dauka direct basu tsaya ako ina ba sai wani madaidaicin hospital, abin shaawa dan dai dai kamar mutanen garin,
parking sukayi a kofar hospital din ko ince aka bude musu gate din hospital din suka shiga ciki,
inda aka tanadar dan parking sukayi parking motar tasu driver ne ya fita ya kira maikatan hospital din suka zo da gado biyu na yara da manya aka sa wayannan bayin Allah aciki,
direct emergency room aka wuce da su aka fara basu agajin gaggawa,
wani Dr ne yazo cikin girmamawa suka gaisa da wannan dattijon yakuma masu iso zuwa office din babban likitan hospital din ya basu mazauni da abinsha,
baa wani dauki lokaci ba saiga babban Dr ya bude office din ya shigo da alama aiki ya kammala,
fuska dauke da faraa ya karaso inda dattijon yake yace
"Alhamdulilah zamu ce mun samu nasaran dawo da numfashinta da izinin Allah, yanzu de mun mata alluran bacci dan tana da bukatan hutu, jininta ya hau ta firkita sosai, ni nayi mamaki ma da abin ya staya ahaka ko rauni daya babu ajikinta kuma nayi bincike babu abinda yasameta sai jinin da ya hau kawai,"
" Alhamdulillah "
shine abinda chief Imam yace fuskanshi dauke da murmushin daya bayyana zallar kyanshi sanan yace
"yaran fa,"
zama Dr ya gyara kafin yace
"suma suna lafiya, sai de suna bukatar mahaifiyarsu ta shayar dasu suna kuma bukatan wanka"
shiruuu Chief Imam yadanyi tukunna kafin ya sa hanunshi a aljuhun riganshi ya ciro wayarshi yayi dialing wani number baa jima ba akayi picking sallama yayi aka amsa mashi kafin yace
"Binti ya jikin naki,"
ta amsa ma shi da "Alhamdulilla
Abba da sauki "
kafin yace" Allah kara sauki,"
ta amsa da "amin,"
yace "kun koma gida ne,"
tace" aa yanzu muke shiri ,"
yace "ku jirani ina zuwa yanzu,"
"tohh Allah kawoka lafiya,"
kittt ya kashe wayan,
Dr ne yace" little Imam yau ba magana ne yana maganan ne cikin zolaya,"
yaron da aka kira da little imam yace "good morning uncle"
morning Faruq, how are you ?,"
yace "am fine,"
" and how is your sister,"
cikin muryansa na yara yacigaba da amsa masa tambayarsa
yace "she is pretty fine,"
"uncle can i ask you something"
"why not my dear am listening,"
"uncle mai yasa babies din nan ke crying sun ji ciwo ne,"
"aa babban mutum basu ji ciwo ba yunwa sukeji, and they need fresh air,"
"toh mom nasu tayi feeding nasu mana akaisu gunta haka Khadijtul Islam ma take intana jin yunwa, sai tayi ta kuka ko Jaddi"
yayi maganan ne inda oily eyes π nashi acikin na Jaddin nasa, da alama karin bayani yake nema gyada masa kai yayi alaman ehh,
"toh uncle kaji Jaddi nama yace ehh hurry up and take them to there mom,"
murmushi Dr yayi yace "there mom is unconcious she is sick,"
ido little Imam ya waare,π yace "ohh i pitty them, toh yanzu mai zaa musu,"
"sai de abasu milk,"
inji Dr hannun Jaddin shi ya kama yace
"pls Jaddi help them, they are in need of help,"
murmushi Chief Imam yayi ganin yadda Faruq ya marairaice face nashi, idonshi harda guntun kwalla ahankali cikin nutsuwar sa da yake halittansa ne ya mike staye ya kama hannun Faruq kafin yacewa
"Dr akwai milk din ne,"
da sauri dr yace
"ehh akwai,"
jijjiga kai Chief Imam yayi yace
"akawo yaran dakin da Fadima take zata kula da yaran, ita da ummanta,"
murmushi dr yayi, aranshi yana jinjina karfin imani da tausayi irin na Chief Imam yana da tabbacin tsintar wayannan bayin Allahn yayi kuma ba sune na fari ba mutum ne shi mai son taaimako,
"okayy"
shine abinda Dr yace wa Chief Imam jagora Dr yamasa zuwa dakin da yake bukatan zuwa, ya kuma bude masa kofa.
bai shiga ba sanda yayi sallama ya tabbatar an amsa masa sallaman da yayi,
wata siririyar murya ce ta amsa sallaman tana mai masa maraba da zuwa,
little Imam ne yayi saurin riga chief imam shiga fuskarsa dauke da fara'a, ya shiga da sauri yayi gurin matar da ta amsa sallaman, wacce baza tafi shekaraa 25 ba a duniy,
fara ce kyakkyawa son kowa kin wanda yarasa, kallo daya zaka mata ka tabbatar da cewa ita din jinin chief imam ne, mahaifiyar little Imam{Faruq},
da gudu ya karasa gurinta ya rungume ta,yace
"oyoyo Ummi na"
murmushi tayi ta shafa kanshi daya ke dauke da yalwaceccen bakin gashi mai stansti da yawa tamkar na yayan larabawa,
breaking hug din nasu yayi yace
"Ummi ina innani da khadijatul islama, ina suka je"
murmushi tayi ta shafa gefen face nashi cike da kaunar gudan jinin nata kuma mai sunan mahaifinta abin kaunar ta, tace
"suna bathroom, innani namawa Islam wanka,"
"okay,"
inji little imam kafin ya kara cewa
"ahaaa that remind me, Ummi kinsan mai ya faru kuwa yau da muka je farm da Jaddi,"
muryan chief imam sukaji abayansu yana cewa
" tohhh sarkin hira kabar Ummin naka ta huta mana"
da sauri little imam ya taso yazo inda Jaddin nasa yake ya kama hannunsa yace
"Jaddi ina babies din Ummi tayi feeding,"nasu sai granny tayi musu wanka,"
Ummin little imam ne ta sauko daga kan gadon marassa lafiyan da take ta stuguna har kasa ta gaisar da chief imam,
wanda yake mahaifi awajanta fuskarsa dauke da murmushi ya amsa gaisuwar yar tasa yana mata ya jiki, tace
"da sauki Abba jiki Alhamdulillah,"
"haka ake so Allah kara sauki,"
karan bude toilet din da suka ji yasa suka mai da hankalinsu, wata kyakkyawar dattijuwa ce ta fito daga bathroom hannunta dauke da baby, wanda ke nade acikin towel na yara pink colour fuskarta dauke da murnushi, ta iso cikin dakin tasamu guri ta zauna tace
"sannu da zuwa Sheik kun iso lafiya,?"
murmushi chief imam yayi, cike da kaunar matar nashi yace
"mun same ku lafiya ya mai jikin,"
murmushi tayi tace
"jiki alhamdulillah,"
" to ALLAH kara sauki,"
little faruq dake gefe ne ya turo bakinsa gaba yayi kicin kicin da fuska, kamar zaiyi kuka yace
"ni ni ba ruwa na da ke bazan kara kula ki ba, kuma ki bamu Islam din mu, tunda abin naki haka ne, "
dattijuwar da Faruq ya kira da innani
tace "kaji dan kesan uwa ani zakawa badala da iya shege,"
fashewa da kuka Faruq yayi ya rike hannun Jaddinsa yace
"Jaddi kaganta ko tana zagi na,"
murmushi Chief Imam yayi yace
"mai ya faru ne haka, kai da innanin ka mai ya hada ku haka,"
Faruq ne yayi magana cikin childish voice nashi yace
"ba ita bane bata mun sannu da zuwa ba ko gishe ni bata yiba, ta fara gaisheka bayan kuma nine babba, kuma fa ni da zuwa na ita na fara tambaya,"
"kai kai gaskiya innani bata kyauta ba, ya zata ki gaida mai gidanta to yanzu barta kayi hakuri ka yafe mata baza ta kara ba kabarta da halinta,"
murmushin jin dadi Faru yayi π yace
"tohh Jaddi na barta, kuma baza mu bata yan biyun mu bako,"
gyada masa kai yayi abinka da salihin bawan da bai fiye magana ba, sai ambaton Allah innani ne ta daga kai ta kalla Chief Imam fuska da alaman tambaya da neman karin bayani game da abinda little yace,
kallo daya ya mata ya fahimci abinda ke ranta dama ance labarin zuciya atambayi fuska
{ nikoπ Queen mahirahπΈ nace ada kenan yanzu labarin zuciya atambayi whatsapp status din mutum}
batare da wani bata lokaci ba Chief Imam ya zayyana masu komai cikin nutsuwa datake halitta ce agareshi,
Innani da mahaifiyar Faruq sun girgiza matuka da jin wannan labarin sun kuma tausaya wa wayannan bayin Allah wato matar da yayanta, batare da sun gama jajanta abun ba suka ji sallaman Dr, wanda basu amsa ba sanda suka suturta jikinsu maana suka sa mayafi sannan suka amsa masa sallaman , da yayi garesu,
suka kuma bashi izinin shigowa shida wassu nurses guda biyu, hannunsu dauke da babies din shi kuma Dr hannunsa dauke da milk din da zaa basu,
wayannan nurses din suka nufi gun Innani wanda ta kwantar da Islam datayi bacci batare da an sa mataa kaya ba, karban dayan tayi itama Ummin Faruq ta karbi daya kusan atare suka furta masha' allah ganin irin kyawun da Allah ya azirta wayannan yaran dashi, tamkar larabawan EGYPHT,
Innani tace "ayyah bayin Allah dube su yanda suka yi ja, dagani sun sha wahala da'alama kuma basu saba da ita ba, da gani ma wannan basu yi arba'in ba, kaman sa'anun Islam nema,"