x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 31 - THE TWO LIGHT RIKICIN GIDAN SARAUTA

  • 90001 words
  • 93000 words
  • Out of 97531 words

Category: Love Stories

Views 544

20 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
tas sai de ba irin farin nan mai kashe ido ba, i can say yana da soft and creamy white skin, kamar yadda na faɗi a farko giant ne wato ya na da tsayi da murɗadɗen jiki hadi da faɗi, fuskanshi nada fadi kaɗan da tsayi, fuskan na ɗauke da golden eyes nashi masu sheki da daukan hankalin mai kallon su, bugu da ƙari yasa maza rawar disco musamman marassa gaskiya, golden eyes nashi na ɗauke da long moist eyelashes, wanda suka ƙarawa idon wani ƙyau na musamman, sai well shaped eyebrows nashi Wanda tamkar shi ya seta abin shi, idan ka gangaro zuwa hancin shi kuwa kamar shi ya tsaida abinsa, yayin da inka gangaro lips dinsa ko they are so cute, zaka ranste red lipstick yake shafawa kasancewar su ja, fuskanshi na zagaye da kwanceccen lafiyayyiyar man's pride dinsa wanda aka narkawa Naira, baki sidik dashi ƙawance luff, yayin da kanshi yake a cike da gashi da yayi nasaran saukowa har wuyansa, baki ne sidik mai tsansti, idan ka ƙare mishi kallo zaka rasa a wani fasali zaka ajiye shi, baza ka kirashi da balarabe ba, haka ka zalika baza kace dashi bafulatani ba, sai de yanayin sa yafi kama da bahaushe wato dan Nigeria, duk da kyau da yake dashi bai hana asalin sa bayyana ƙarara ba.

Wannan ba kowa bane sai LITTLE IMAM(FARUQ) Wanda ayanzu duniya ta shaide sa da MAJOR GENERAL UMAR FARUQ IBN OTHMAN ZUNNURAIN.

Popularly known as 🐅 TIGER. Yana daya daga cikin manyan jami'an tsaron da Duniya ta shaide su , kasancewar sa Jami'i na ƙasa da ƙasa, wanda yasan aikin sa, duk da kasancewar sa mai ƙananun shekaru bai hana zallan Izza da ƙwarjinin sa baiyana ba ako ina, musamman a filin daga wato filin da zai yi fito na fito da maƙiyansa, ya kasance mutum mai tarin masoya haɗi da maƙiya, kasance warsa mutum ne da bai yadda da rashin gaskiya ba, wanda sanadin hakan ya samu cigaba da dama a ɓangare daban daban na rayuwa, a yau yake da shekara 30 da wasu watanni ya tsallaka gada da dama wadda mutane dayawa basu tsallake ba , ciki har da wayan da basu kai sa shekaru ba, idan na cigaba da baku labarin irin nasarorin da MG FARUQ ya samu tabbas zamu wuni mu hanste anan, saboda haka back to normal labari...😁



Cike da zallan isa, mazantaka da zallan Izza yake tafiya har ya iso bakin gadon mara lafiyan wanda ZULAIHAT je ƙwance luff, Abi ne ya dago tunanin idonsa ya zuba su a fuskan MG FARUQ ya ce "what did the Doctor said?,"

Digon numfashi yana kafin ya ja kujerar ya zauna ya ce " No need to worry, she is alright, Bp ta ne ya hau sai kuma zuciyar ta da tsinke but munyi magana da Dr Fauziyya ta ce mu tabbatar bata kara shiga irin wannan yanayin ba, we should make sure an mata abinda take so, so that zata rage tunani, that will help her heartbeat to settle down,"

Dogon numfashi yaja ba tare da ya ce komai ba suka ji ta fara tari tana buƙata ruwan sha, cike da rawar jiki Fatima (Ummi ) ta mika wa Abi bottle water, cikin sauri ya bude yayin da MG FARUQ ya tallafe ta ajikinsa shiko Abi ya bata ruwan, cike da ishi bukatar ruwan take sha, sanda ta kishi Dan kanta kafin ta ƙauda kai ya cire mata bottle din daga bakinta, shi kuma Mg Faruq ya gyara mata kwanciyar ta wato ya ƙishin giɗar da ita ajikin filo, cikin wani yana yi ta fashe da ƙuka mai cin rai wanda kana gani ƙasan daga ƙasan zuciyar ta ke fitowa.

Ummi ne ta ƙira Mg Faruq "Faruq zo ka ɗauki SAWBAN kuje waje,"

Ba musu a zo ya ɗauki SAWBAN da yayi wulwul da ido yana don yin kuka ganin halin da Momyn sa take ciki, be yi wata wata ba ya sa hannu ya dauke shi kamar yaro ɗan shekara uku,
ta cigaba da kuka cikin wani yanayi, jiki ba ƙarfi Abinda hau rarrashinta yana cewa "Sabr yah Ukhtie,"

Cikin sheshshekar kuka ta ce "ya zan yi hakuri Akhie a dake Ni a zamanin ƙuka , sun auren dole kuma su koreni daga gida batare da tunanin wani hali Ni Ko abin na haifa zasu shiga ba, kaduba kaga Akhie shi hankalin sa a kwance har da yin wani auren biya barni da igiyansa a kaina,"

Cike da rashin fahimta ya ce " I don't understand waye yayi auren ?,"
"Ni ma ban sani ba Akhie, yayi auren sa harda ƴarsa zama tayi aure Ita ma,"
Dan shiru yayi din sai Yan zu ya gane mai take nufi kafin ya ce "wa ya ce Miki zai aurar da ƴarsa?,"
"Ba Sawban ba ne yake fada mun and am very sure shine cos har sunan sa ya fada mun wai Shahzad ne zai aure ta,"

Dan shiruu yayi alaman tunani kai tsaye bazai ƙaryata zancen ba don shima yaji magana makaman cin wannan,

"hmmm Zulaihat I know how you are feeling right know, but I want you to know and understand Babu Wanda Ya Isa Ya hana abinda Allah ya ƙaddara faruwar sa, they abondone us Kuma sun mana iyaka da komai nasu, kin san ƙa'idar su in suka yi exiling naka to baka da wani ikon yin bincike ko Sanin abu game da Masarautar, so please come down, let it be , let the past fly away, try and brainwash them from your mind, I know is hard but try as possible as you can, mun girma mun ajiye iyali ga yaran mu sun girma ƙaramin cikin su shine mai shekara goma, pls kiyi hakuri Allah bai manta damu ba, ya rufa mana asiri ayanzu muna da duƙiyan da zamu iya ciyar da Mutanen dake Masarautar Suhataj Abdallah, gamu da yara da suka zamanto sanyin idaniyan mu, babu abinda muka rasa ku cigaba da addu'a ayanzu in muna da damuwa bai wuce na rashin Myreen ba, muyi addu'a Allah bayyana mana ita,"

Wani dogon numfashi taja don maganar tayi tasiri a zuciyar ta kafun tayi narai narai da ido ta ce "Please Akhie take me to Innani and Abba i miss them so very much,"

Tayi maganan yayin da ta ƙara narke face din ta, gyada Kai yayi ya ce "okay I will talk to Faruq zai shirya muku tafiyar,"

Dan turbune face Fatima tayi ta ce "Ni fah,"
Da wani ƙallon gefen ido na ƙasa ƙasa ya bita
dashi bai ce komai ba, ita Ko sai kara narke fuska takeyi, Zulaihat ko sai zuba murmushi takeyi don ba karamin burge ta suka yi ba, ganin in bata sa baki ba bazai barta ba yasa ta ce " shike nan sai mu tafi dasu ILHAMA da AJLAL naji sun ce gobe zasu dawo Sawban kuma jibi za'a basu hutu, shikenan sai muyi best Vocation ever, I guess we will have lot fun,"
Shiruu Ayi Bai ce komai ba, in akwai wanda ya tsana rayuwar bai wuce ace Fatima zata masta daga inda yake ba ma'ana tayi nia dashi.

Dogon numfashi yana ɗon bazai iya cewa Fatima ba zata je ba , sabida a yanzuyan son farin cikin Zulaihat ga ita ƙanta Fatima ta daɗe sosai bataje ganin gida ba,

,"hmmm okay,"

Cikin farin ciki Fatima ta bashi wani side hug batare da ta samu tayi hakan ba, sautin murmushin ZULAIHAT da ta jiyo ne ya sata ta sake shi da sauri, kawai ta rufe fuskanta, Zulaihat kuwa ta kwashe da wani dariya mai ƙyataar wa, ta fara tsokalan ta.

" Sannu Gimbiyar alkunya wai har yanzu baki dena ƙunya nan ba yau shekarar ku talatin da aure amma har yanzu baki dena ba yar fillo,"

END OF PAGE 37
Follow for more 😍😘

Story and written by
Queen Mahirah 👑
The wordsmith 🖊️📖






🧚THE TWO LIGHTS ✨ (RIKICIN GIDAN SARAUTA🏰)🧚

The story contains the fact Royalty, Ego, Separation, disastrous love, hatred, hardship, twin flame journey...


Story and written by
Queen Mahirah
The wordsmith


WHATSAPP CHANNEL
https://whatsapp.com/channel/0029VacL1MhFy723j9fdgJ20


WHATSAPP GROUP
https://chat.whatsapp.com/CztvtzKaDeqHqlqpuCyeNG


📱 Typing
FREE BOOK 📚

BOOK 1

🧚38🧚


RUGAR HARDO BELLO (KANO STATE, NIGERIA)

Cikin sanyin jiki Innani ta koma farlo ta samu guri ta mawa kanta mazauni, rafka uban tagumi tayi, yayin da take facing ɗakin su Mahnoor sai saƙa da warwara takeyi.

Cikin nustuwa Chief Imam yayi sallama wanda yayi nasaran dawo da Innani cikin normal sense ɗinta, a ƙasan maƙoshinta ta amsa sallamar tasa kasancewar bata cikin mood mai daɗi, Fareed ne ya amsa sallamar cikin fara'a da sakewar fuska, yayin da Islam ta isa har inda yake ta karbi abinda ya shigo da shi ta kuma mishi sannu da zuwa, sannan ta dauko mishi ruwan sha.

Fuskar sa ɗauke da fara'a wanda ya bawa Innani mamaki matuƙa har yasa ta fara tunanin koɗe an samu labarin Myreen ne, cikin Muryar sa mai cike da zallan dattaku da nustuwa ya ce" Barka da dare uwargidan Sheik?
Da fatan na same ku lafiya?,"

Wani dogon numfashi taja yayin da ta nemi duk wani damuwa ta rasa, ita kanta tasan tayi Sa'an miji, idan da akwai abinda ke kara sata farin ciki da son cigaba da rayuwa bai wuce Sheikh da Mahnoor ba, tasan soyayyar da ke tsakaninta da Nooriyya wannan hadi ne na ubangiji, Sheik kuwa ƙyawawan halayyar sa na daya daga cikin abinda yake ƙara mata son sa.

Authors Note
"Shin kun lura da wani abu anan kuwa🤔?

Shigowan Sheikh Innani bata ce dashi ƙala ba😞, haka bata karbi jakan hannun shi ba Wato abinda ya shigo dashi.

Amma abin mamakin anan shine, shi yana zuwa ya fara tambayar lafiyanta bayan mika mata gaisuwa da yayi.

Kuma fa karku manta cewa bata gaishe shi ba.😳

Akwai wanda zai iya fada mun mai yasa bai damu da rashin kula shi da bata yi ba?🤔

Nawa bangaren Ni Queen Mahirah nace abinda yasa Sheik bai damu da rashin karbansa da bata yi abu biyu ne✌️,

👆 Shine a lokacin da sa ya shigo ya kula da yana yinta wato ya fahimci cewa tana cikin wani hali na ƙunci, shiyasa ya mata uzuri.
mai yasa ya mata uzuri?
Shine mutum ne shi mai saurin fahimta bugu da ƙari ya karanci halayyar ta, sannan shi mutum ne mai saukar da kanshi musamman abangaren rayuwar sa da iyalinsa, wato zamanta kewar sa na aure.

✌️Ya mata uzuri sabida ba haka tasaba mishi ba, kasancewar ta mutum mai tsananin biyayya da basa kula, yana daya daga cikin abinda yasa ya mata uzuri a yau.

Darasin da zamu ɗauka anan shine, ita rayuwa musamman na aure ana da bukatar fahimtar juna, sannan ka kasan ce mai yiwa abokin zaman ka uzuri a wasu lokutan, ka kuma yawaita karantar yanayinsa a lokaci mabanbanta, ma'ana lokacin da mutum ke cikin farin ciki da akasin haƙa."


BACK TO LABARI 😁

Dogon numfashi taja kafin tace "Sannu da Zuwa Sheikh, lafiyan mu kalau, ya aiki da fama da jama'a,"

"Alhamdulillah,"

"Toh Allah kara rufa mana asiri ya Kade hau, ya raba ka da cin haram, da kuma sharrin maƙiya,"

Gyada Kai yayi cike dajin daɗin addu'ar da ta masa ya ce "Ameen summa ameen Mar'atussaliha, Allah ya yiwa rayuwar ki albarka,"

"Ameen summa ameen,"

"Ina Noorul hudah,"

in ji Sheik wanda ya tambayi Islam, cike da miskilanci ta ce "tana daki, bari na ƙirata,"

Gyada mata Kai kawai yayi, yayin da ita kuma ta Kama hanyar dakin da niyan ƙiran Mahnoor.

Innani ne ta tattara hankalinta zuwa ga Chief Imam ta ce" Mashaallah naga yau kana cikin farin ciki Allah de yasa alkairi ne ya samu?,"

Wani murmushin ya kuma sakewa kafin ya ce "yau munyi waya da Hamma,"

Washe baki Innani tayi ta ce "😁 to to mashaallah ince Zulaihatu na lafiya,?"
Bai kai ga bata amsa ba, sallamar Mahnoor ya kaste su, amsa sallamar suka yi yayin da Innani takafe ta da ido tana so tasan wani yanayi take ciki.

cike da nustuwa na karasa inda Chief Imam yake na tsugana har kasa na gaishe shi, cike da fara'a ya dafa kai na ya amsa gaisuwan nawa hadi da samun albarka.

"Mun yi waya da Abi ya ce mun nan da ƙwana uku Ummi da Momyn ku zasu zo dukansu,"

Cikin wani farin ciki wanda tun da ya ambaci sunan Abi na tsinci kai na aciki nace, Mashaallah, Allah kawo mana su lafiya, Allah sa za'a zo da Sawban dasu Ajla,

"Dukkan su zasu zo, suma gobe zasu dawo daga makaranta sun gama Exams, Muhd Sawban ma za'a basu nasu, toh zasu tafi tare da Hamma Faruq,"

Wani dan ƙaran murna na sake kafin na dan langwabe kai nace eyyah Jaddi Abi fah?

"Yana aiki shi bazai zo ba,"

Kamar zan yi kuka nace yau fah about three years rabon Abi da zuwa Nigeria,

Murmushi kawai Chief Imam ya ce "aikin ne sai ahankali,"

Turbune face nayi kafin kuma na ce shikenan Allah lah kawo mana su lafiya, i really miss Ummi so very much, Allah kawo mun ita lafiya, bari ma naje na fara shirya musu wani abun mamaki😍.

Na faɗi haka yayin da na mike da sauri nayi hanyar ɗakin mu.

Wani irin sanyi jikin Innani yayi ganin ko inda take ban gani ba balle tasa ran zan mata magana.😔



EGYPT

ABDUL MALIK ROYAL ESTATE 🏢


biki yayi biki, shirye shirye akeyi bakama hannun yaro, kasancewar yau Alhamis gobe juma'a, ma'ana gobe duniya zata shaida Zawjatul Ameer matsayin Gimbiya mai jiran gado.

SULTANA NAJDA'S CHAMBER

Zawjatul Ameer ne sanye cikin wani shiga na alfarma sai zuba shagwaba takeyi a MAHZIA (concubine, ma'ana ƙwarkwara a hausan ce, wanda anan ƙasar Nigeria masarauta na ɗaukan ta matsayin matar sarki ko ince matar da ba igiyar auren sa akanta amma sukan yi mu'amala tamkar miji da mata Sai de anan ya sha ban ban, kasancewar su Masarauta wacce take cike da ilimi na addini dana boko, anasu ɓangaren sun dauki ƙwarƙwara matsayin Jakadiya, wanda anasu ɓangaren ya zama abin gado kamar yadda kuka sani ƙa'idar masarautar SHAHARYAR ABDUL MALIK komai gada ake yi, haka itama MAHZIA ta kasance abin gado wanda har ƙarantar dasu ake yi yadda zasu gudanar da aikinsu, wanda su kuma nasu aikin shine su koyar da duk wata matar Malik ko matar Shahzad yadda rayuwar gidan Sarauta yake , ko ince yadda zata mulka jama'ar ta da kuma yadda zata zauna da mijinta).

Zawjatul Ameer sai zuba shagwaba takeyi wa Mahzia wai ita kayan ya mata nauyi ajikinta, ita Ko sai rarrashinta takeyi tana bata hakuri, sallamar da Sultana Najda tayi ne ya sa ta tsagaita wa da shagwabar nata, cikin cool voice dinta tace,

"Waya taba Hooriyya 😇?,

My sweet little darling 😘,"

Ƙara fashewa da kukan taɓara tayi har d su bubbuga ƙafa,

"Ina Mahzia ce tasa mun clothe mai nauyi,"

"Ohh sweery, you look so beautiful and fetching,"

Zumburo baƙi tayi gabaa ta ce "but Mima the cloth is too heavy,"

Ta gama maganar ne yayin da ta langwabe kanta idonta ko fill yake da ruwan hawaye wanda ya ƙara wa idon wani ƙyau da kyalli.

Hannu Sultana Najda tasa ta tallafa face din Zawjatul Ameer cike da ƙauna ta ce "ohhh Hooriyya baki ga yadda kika yi kyau bane shiyasa, You know this is how Royal blood use to dress like, and the biggest part is you are a Crown Princess."

Ta kammala maganan yayin da ta kama moist hand din Zawjatul Ameer da nata soft hand din, ta zaunar da ita akan dressing mirror chair, wani cute smile ta sake kafin ta ce "Mashaallah lah ƙuwata Illah billah, Mahbeer ya yi Sa'an kyakkyawar mata,, Allah ya baku zaman lafiya, ya azirtaku da zuri'a ɗayyiba,"

Ta ƙarashe maganar yayin da take shafa gefen fuskan Zawjatul Ameer, zuciyar ta cike da abubuwa da dama, babu abinda take fata ayanzu da wuce mafarki ta na kullum ya kasance gaskiya, idan har hakan ta faru tabbas zata fi kowa farin ciki.

Cike da nustuwa da zallan manyan ta na sarauta daya bi jikinta ta daga hannu a Mahzia ta mata alamar zata iya tafiya, cike da girmamawa ta dukar da kanta kasa sannan ta juya ta kama hanyan fita daga ɗakin.

Cikin nustuwa ta dauki cum ta shiga taje mata Kai cikin nustuwa ta shafe mata kan da mayuka masu bala'in kamshi, tufke mata gashin tayi guri guda kafin ta ciri wassu daga gaban goshi ta ɓangaren hagu da dama tayi amfani da wani machine tayi curling gashin wato ta ɗan murde su sai suka zamanto tamkar macaroni, wani box ta buɗe wanda yake ɗauke da wasu zafafan jeweleries wanda aka yi su da zallan narkekken Gold wato pure white gold,Sanya mata shi tayi a wuya ta,

* Mashaallah 😍 sai kunga yadda ya haska ya kara fidda asalin ƙyan da Allah ya mata,*

bayan ta gama ta sanya mata jeweleries din da ta dauko haɗadɗen Golden crown 👑 dake ajiye bisa wani red cushion Mai tsananin taushi da ɗaukan hankalin mai ƙallonta, dauko shi tayi ta sanya mata shi akanta wanda yasha gyara sai tashin ƙamshi yaƙe yi, cikin ƙanƙanin lokaci ta gama shirya ta cikin ƙaya na alfarma ita kanta ta burge kanta sai washe hakora takeyi,

"Mima ki ganni na zama kamar Cinderella ,"

Tayi maganan ne with full of excitement yayin da take daga rigar da ke jikinta wanda yake tamkar na Disney princess, murmushi Sultana Najda ta sake ta lakaci hancin ta ta ce "Mashaallah lah ƙuwata Illah billah, Allah ya kare mun ke daga sharrin maƙiya,"

"Amen summa ameen Mima na yaushe za'a kaini gidan Zawjy Mima 😚 ina son zama tare dashi, inaso na haifi babies kuma yace wai sai in an kaini gidan shi zai bani babies, amma yaƙi fada mun yadda zai ban wai sai in naje😗😔,"

Tayi maganan ne cike da yarinta wanda ya zame mata jinin jikin ta ayanzu, shiruu Sultana Najda tayi ta rasa mai zata ce gaba daya.


wani boyayyen ajiyan zuciya ta sauke kafin ta shafa gefen fuskanta cike da tausaya wa tana mai ayyana abubuwa dayawa a ranta tabbas ita ta kawo shawarar Mahbeer ya aure ta gudun karta subuce musu a wannan lokacin, sai de ayanzu tayi dana sani badan komai ba sai dan gani take kamar zata cutu da yawa kasancewar babu abinda ta sani na rayuwa duba da irin halin da ta shiga.

da za'a bi nata da an
End Ads