x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 19 - THE TWO LIGHT RIKICIN GIDAN SARAUTA

  • 54001 words
  • 57000 words
  • Out of 97531 words

Category: Love Stories

Views 540

20 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
mai da ta marar amfani ta hanyar mai da shi majnoon,

amma kunsan Allah ba azzalimin bawan sa bane,

yana kaunar bawansa fiye da yadda uwa ke kaunar danta,

sannan bawai rashin son sa da yakeyi bane yasa ya bar wassu miyagu daga cikin bayinsa na cutar dashi,

kamar yadda kuka sani Allah ya kaddara abin da zai faru da mutum tun kafin zuwanshi duniya,

sai de abu 2 na iya canja kaddaran mutum na 1 shine karfin addu'a,

na 2 kuma shine sihiri,

wayanan na canja kaddaran mutum bawai dan Allah ya gaza ba a'a sai de dan ya barka da halinka yaga yanda zaka kaya,

yakan baka sa'a na wassu lokuta kafun komai ya kubuce maka,

tohh anan abinda nake so ku gane bakomai bane illa game da sha'anin rayuwar dan uwanku,

wanda tun tashin shi rayuwarsa yake adagule badan komai ba sai dan sharrin miyagu,

wanda sukayi kokarin canja masa kaddaransa sabida son zuciyarsu batare da sanin halitta na daban suka mai dashi ba,

akarshe wassu daga cikinsu sunyi kokarin sabauta shi batare da sanin cewa hakan da sukayi sun kara hadashi da kaddaranshi ne ba,

abun da zamu fahimta anan shine su sunyi nasu yanxu kuma lokacin na Allah ne,

abinda nakeso ku gane anan shine arayuwa kowa da nashi kaddaran da fadi tashi,

ako wani family suna da nasu salon rikicin sai de RIKICIN GIDAN SARAUTA ya ban banta dana ko ina ,

anan akwai mutanen da ba Allah azuciyarsu wanda basu dauki sabonn Allah ako mai ba muddin zaasu samu biyan bukatansu,

sun manta cewa duka wayanan abubuwan aaduniyan zamu barsu kamar yadda muka samo su,

sun dauki shirka sana'ar yinsu sunyi amfani dashi wajen raba kan wannan ahalin don samun cikan burinsu,

sai de Allah baya bacci akaikai ce ya hada ku tahanyar da ku kanku baku sani ba,

ya hada kawu nan ku ya kuma dauke idon makiyanku da kanku yasa sunyi tunanin burinsu yacika na son ganin bayan yan uwanku,

tohhh Alhamdulillah komai yayi farko zaiyi karshe anjima za'a kawo muku ruwan magani wanda zaku na amfani dashi kaba gayan ku,

na karya sihiri ne da kuma kariya sanan zan baku addu'ar da zaku nayi wanda zai sa makiyanku manta wa da kashin ku,

zaku zamo shafaffu a allon stafinsu ma'ana zaku zama invisible ga makiyanku,

fatan shine Allah karbi ibadun mu,"


cikin sanyin jiki suka amsa masa da ameen,


murmushi yayi ganin yadda jikinsu ya mutu gaba daya ga wani yanayi daya bayyana a face nasu, ya dubi Captain Fudhal yace

" Yarima ko nace Captain Fudhal,

shi rayuwa ahankali ake binta musamman inka na so kaci moriyarta da zancen cikinta,

sanin wassu abubuwa lokaci guda bayana nufin warwarewar mastalan data yi shekara 20 da ginuwa ba,

sannan awassu lokutan yana da kyau mu fawwala Allah komai awananan duniyar da kake ciki yanxu musamman ma kasaar mu Nigeria,

babu gaskiya acikinta wannan na nufin koda ka tauno abinda yake abinne tofa sai de kabar hukunci a hannun Allah ubangijin talikai,

shi yafi kowa iya hukunci,

kuma ita gajen hakuri yana daya daga cikin abinda ke iya sauya kaddaran mutum anan Allah zai barka da halinka yaga iya gudun ruwanka,


sannan inasao ku cire duk wani tan tama akanmu ku kuma fahin ce mu ku jami'ai ne,

tohh inaso ku ganmu da idon basira ku kuma fahimce mu da kunnen basira,

ku dauki yaran nan tamkar yan uwa a gareku na tabbata baza kuyi dana sani akan hakan ba,

abinci da kuma gyara muku sashin ku zasu na yi sai wanki akwai mai yinshi in da injin wanki kuke so yayi muku zai yi inkuma da hanune duk wanda ya muku,

ku dauka mu daku abu daya ne shine fatana yana gama fadan haka,"

ya mike ya da niyan tafiya Fareed ne yace " mun gode Jaddi insha'Allahu zaka same mu ayadda kake so kuma basai an wahalar dasu ba na kawo mana abinci,

zama mu shiga muna ci tare dasu in ba damuwa,"

cikin fara'a Chief yace " ba komai ai duk abu daya ne,"

har bakin kofa Fareed ya raka shi ya dawo yana shigowa Fudhal ya jefa mishi wani harara yace

"sannu uban yan shishhigi kana wani kokarin cusa mu jikinsu, dakai da su din duk daya kuke sai wani cusa yaran yake jikin mu kamar wani ...,"

bai gama zaancen ba sana din wani wawan stuka da Fareed yaja

" mtschwwwww kaide har abada kan ka bazai taba dauka ba kan mutum kamar an dura dusa baya fahimtar komai,

ba abinda ke shiga ya zauna kamar ba yanzu ya gama maka nasiha ba,

ohhhh na ma gane kai storonka kar zance na ya tabbata na saaka wanke wanke,

tohh wallahi ka ajiye ya zama jazaman kayi wanke wanke agidan nan tunda naga shine abinda kake gudun,"

yana gama fadin haka ya fuskanci Fahreen yace

"Tweeny ina fatan ka saurari abinda mutumin nan ya fada,"

gyada mishi kai kawai yayi murmushi ya sake yace " inka kula kamar akwai lauje cikin nadi,

in mun maida hankali zamu iya samun abunda muka dade muke nema in ka fusakanci zancen shi nacewa yann uwan mu da muka rasa ,

kasan ba mutum daya muka rasa ba mun rasa mutane na farko yayan Abba mun da aka rasa shi duk da cewa ance ya mutu amma ai babu wani kwakwaran shaida akan mutuwarsa,

kuma fahhh kasan bamu san komai game dashi ba ko a photo bamu taba kallonsa ba,

labarin ma albarkacin Fulani ne muka ji muka san sa ,

sai kuma Amni da twins dinta kaga shima ance tayi accident after all babu koda ashes dinsu ne da kuma car din,

sai kuma Pops da Mubaraq kasan about 20 years bamu san inda suke ba and am very sure Mubaraq ne yayi hiding information dinsu,

you know he is wizkid on computer ko charles barbage dayake father of computer bazai nuna mishi kanta ba,

so the point here is akwai possibilities din da wannan old man din yasan wani abu very important things game da family din mu,

and the biggest part is who are these ladies mai yasa suke kama da larabawa tunda su Fulani ne?,"

shiruu dakin ya dauka kowa da aabinda yake sakawa ta fannin Fahreen wannan yarinyar ne ta fado masa arai da incidence din da yayi occuying a staka ninsu,

wani irin sarawa kanshi yayi ga wani bugu da heart din shi yayi acikin abinda bai fi 2 sec ba ya nemi nustuwarsa ya rasa, sai de ba wanda ya fahimci hakan,

fannin Fudhal kuwa shiruuu yayi bai ce kala ba yana ta nazari game da wannan yarinyar lamarinta ya daure mishi kai sosai,

" nide inaga kamar yadda ya bukata muzauna dasu mu kuma dube su da idanun basira,

tohh muyi hakan am very sure baza muyi regreting ba ,

after all ni na yadda da stohon kallo daya zaka masa kasan he is man of God,

koda kalaman bakinsa ya isa kasan shi ba mai maula bane ko neman guri,

wassu fa kamar abun bauta hka suke ganin mu stabar son duniya,

kamar su mana sujjada sufa in just one glance you will understand they are not intrested in all such things,

kudin mu da sarautar mu bai damesu ba sun dauke mu kamar jikanun su ne kawai,

sannan da alama badan ya tara abin duniya yake malunta ba don ya riga da ya tara ko daga yanayin garin ma after all ni nasaan labarin Rugar nan,

sai de banyi tunanin yakai harr haka ba this malam is very famous,

shi ya kawo cigaba a Rugar naji ance sun riki Allah daya,

kuma in mutum yazo da niyan cutar dasu baya ma ganin Rugar,

bace wa takeyi shiyasa gomnati bata san dasu ba ga kuma yan bindiga da sukayi yawa amma bana tunanin sun taba kawo musu hari,"

Fudahal yace " tohh aku sarkin magana kai kuma daga ina kasamo duka wannan jawabin,

kai fa kace baka taba zuwa Rugar ba amma sai wani bayani kake bawa mutane na bogi,"

Fareed yayi murmushi yace " Captain kenan ance ma ni mace ne irinka mai zama guri daya,

nifa pilot ne ba navy ba a sama nake yawo ba cikin ruwa ba,

ni ba kifin rafi irinka bane ni mikiya ne mai hangen nesa,"

hade face Fudhal ya karayi yace " ni sa'anka ne Fareed da kake wa reni,"

tunstirewa da dariya Fareed yayi harda rike ciki yanaa ta babbaka dariya,

shiko kamar ya fashe dan haushi har wani jaa fusakar shi tayi yace

" wallahi zanci ubanka,"


dakyar ya stagaita da yin dariyan yace "basai kaci ba tunda uban nawa sa'anka ne marar kunya kawai,

wanke wanke ne de sai kayi wallahi ko kaki Allah,"

ya kuma tunstirewa da daria shiko ba karamin kula yayi ba,

Fareed bai ankara ba yaji ya jefo mishi throw pillow,

ya jefo mishi aiko ya mike da gudu yayi hanyan dakinshi sanda ya tabbatar ya isa sai ya juyo cikin wani siririn murya wanda idan ba ka ganshi ba bazaka yadda shi yayi magana ba

yace " mai wanke wanke,"

da gudu yayi kanshi shiko ya shige dakin ya rufe, buga kofan yake da iya karfinshi,

Fareed dake ciki yace " wallahi inka fasa musu kofa zaka ci ubanka dan sai ka biya,

ko in hada ka da wannan yarinyar dan naga alama storonta kakeyi,"

ai ko cakk ya tsaya dajin furucin,


"kai Fareed muna fiki ne har ya akayi yasan tana bani storo,"

yayi maganan ne ba tare da sanin ya fito fili ba don duk azanton shi aranshi yayi bai barga ba sanda yaji Fareed ya tuntsirewa da wani mugun dariya ,

ba Fareed ba har Fahreen sanda ya sake lallausan murmushi daya
End Ads