Farlo na fito anan na samu Islam na jirana itam cikin nata shigar mai daukan hankali mikewa tayi tace
" muje kar muyi latti"
kai kawai na gyada mata don sam yau ban tashi da son yin magana ba,
tare muka fito harabar gidan muka wuce side din Jaddi don musu sallama shi da Innani.
da sallama muka shiga farlon muka yi sa'a mun samesu a farlo,
Innani tace a'a shalelena har kun fito" ban iya cewa komai ba sai Islam ne ta gyada mata kai,
Jaddi yace " Allah kare ya kuma dawo daku lafiya"
da Amin Islam ta amsa niko a kasan makoshina na amsa,
bayan dogon addu'a da Innani ta surfo mana kamr yadda ta saba muka kama hanya.
mun fito muka samu Auwal har ya fito da mota,
ta bangare daban kuwa sai gyara guest room akeyi duk da dama agyare yake,
haka kawai na stinci kaina da stinkewan zuciya da bansan name ba.
school ya kaimu kamar yadda ya saba muka shiga tun daga gate din school din muke kwasan gaisuwa ta dalibai da wassu malamai da ma'aikata har muka isa staff room,
bance kala ko gaisuwan ma sama sama nake amsawa,
koda muka je staff din ma ban kula kowa ba,
haka ko da na shiga class yau ba walwala su kansu daliban sun sha jinin jikinsu da ganin yanayi na duk sai suka subure.
Innani ne ta zubawa Chief ido na yan sakanni kafun tace "Sheik,"
yace na'am "Nana,"
wani dogon numfashin ta kara saukewa kafun tace " niko ka kula da yanayin Noor yau gaba daya ta subure,
ni wallahi gaba daya a storace nake da wannan lamarin kana ganin baza a samu mastala ba,
anya baza mu kware ta da yawa ba, ni inaga kamar mu mai da can Iraq din ta cigaba da zama zaifi,"
murmushi Jaddi ya sake yace " ba yadda muka iya da abinda Allah ya kaddara,
ko bangon duniya zamu kai Noorul Huda bazai hana ta shiga wannan yanayin ba sabida kaddaran tace,
ba'a ja da ikon Allah namu addu'a da fatan alakairi,
sannan kasancewar da zasuyi a tare shine kadai hanyar war ware wannan mastalan,
in ba haka ba daga shi har ita ba wanda rayauwar zata mawa dadi."
dogon numfashi Innani taja tace to "Allah zaba mana abinda yafi alkairi,"
Amin shine abinda Jaddi yace.
Wasu hadaddin mota ne na bugawa jarida sukayi parking akofar gidan Chief Imam,
motoci ne na alfarma wanda sai wane da wane ke hawanta mota biyar,
hudu daga cikinsu bakake ne daya ne kadai fari wanda yake a stakiya,
ajikin ko wani plate na motan an rubuta COMMANDORE AJ sannan ko wanne da tambarin masarauta ajiki,
ban gama ankarewa ba saida naga dan dazon soldiers sun fito sun yi kawanya a motan stakiyan,
suna cikin haka aka bude musu gate din gidan tare da basu izinin su shiga nan kuwa wannnan farar motan ta danna kanta cikin gidan bata staya a ko ina ba sai a parking space,
nan yayi parking sojojin ne suka dawo cikin gidan suka kara yiwa wannan motan rumfa suka bude cab din motan na both hannun hagu da dama cike da takama da mazan taka suka fito su biyu daga motan,
suna sanye cikin half jamfa daya fari daya kuma sky blue,
ya matukar amsar su ya fidda zallan mazantakarsu da kwarjininsu hadi da haiba,
Captain Fudhal ne ya taimakawa Major General Fahreen ya fito daga motan,
Masha'allah yana sanye cikin dakakkiyar yadi black colour wanda ya fidda zallan kyansa da kamalansa,
fuskarsa tayi fayau da ita sai lumlumshe ido yakeyi kamar mai jin bacci,
Fudhal ne ya kama hannunsa suka fara tafiya kafun Commandore Fareed ya jera musu,
suna tafiya cike da izza da mazantaka hakika Allah yayi halitta anan domin inka gansu sai ka kara ganinsu haka baza kaso ka dauke idonka daga kansu ba ko ba'a fada ba mahaifiyarsu ba karamin kokari tayi ba,
haka ka zalika ba karamin baiwa Allah ya mata ba na haifan wayannan zaratan samarin masu murdadden halinta,
haittansu kadai abin birkitar wa ga makiyinsu,
dakatawa sukayi da tafiyan don hango Chief da suka yi dama Auwal ke musu jagora zuwa maasaukinsu,
kallo daya ya musu ya jijjiga kai ya hango tarin mastaloli da suke dauke dashi wanda a zaahiri ba kowa ke iya gani ba sai wanda Allah ya kaddara,
wato wanda Allah ya masa baiwaa, ko su kansu basu san dashi ba .
fuska dauke da fara'a ya karasa inda suke,
yace"sannun ku daa zuwa bissmillah,"
jagora ya musu har part din da aka tana da musu ya kuma bude suka shigo wani dogon numfasahi suka ja gaba dayansu,
wani ni'imanceccen kamhi suka shaka mai kwantar da hankali dasa nustuwa ga waani sanyi mai rasta jiki,
"bismillah"
shine abinda chief ya fada ganin su staya daga bakin falon basu iso ba,
shigowa sukayi suka samu guri a kasa suka zauna ganin ya zauna akan kujera,
ba komai ne ya su yin haka ba sai dan ganinn kwarjininsa da kamalan sa ga wani hasken imani da yakeyi,
murmushi yayi yace "ya kuka zauna daga kasa,
ku tashi ku hau sama kasan da sanyi inkuma ni na sauka tohh,"
sunso yimasa gardama amma kimarsa da girman zatinsa da suke hangowa ya hanasu yin hakan hadi da last statement nasa yasa su hawa kan lumstatan kujerun na alfarma,
suka zauna sannan suka mika masa gaisuwa cike da kamala ya amsa musu cikin yaren fullanci yana murmushi yace
"ko baku iya ba"
murmushi dukkansu suka sake kafun ya kuma cewa
"nan ne masaukin ku ga dakuna wanda kwa zai iya amfani dashi,
zaku iya shiga ku duba in bai yi muku ba sai acanja muku,
Fareed sarkin saukin kai da fara'a ne yace
" nan ma yayi ba sai ancanja ba mun gode da kulawarka gare mu"
murmshi Chief yayi yace "gyada kai yace Masha'Allah yanzu sai ku shiga ku huta ko kafun anjima sai muyi magana"
ya kammala maganan yayin da yake mikewa staye da niyan basu guri don su sha iska.
kowa dakin da ya masa ya shiga cike da kwanciyar hankali suka wasta ruwa sannan suka shirya cikin kaya mara nauyi,
kamar sun hada baki duka suka jallabiya farare tas,
suka fito falo suna fitowa suka samu an jera musu abinci reras akan centre table dake falon ba musu suka karasa inda abincin yake don dama ko breakfast basuyi ba,
suna zuwa Fareed ya fara bude flasks din wani kamshi ne ya daki hancinshi har san d ya lumshe idonsa,
bakomai ne acikin flask din ba sai hadaddiyar kaza data sha dafin stofi,
dan Innani da kanta ta dafa musu dayan ya bude doya ne da kwai sai tashin kayan kamshin yake da tafarnuwa,
daya kuma wani dan bowl ne fruit salat ne aciki da kuma hadaddiyar tea a tea flask ga kuma dibino shima acikin nasa ma'ajiyar,
gyada kai Fareed yayi yana jin jina musu jikinshi har rawa yakeyi wajen daukan plate yayi serving kanshi,
Fudhal da shi kanshi tun dazu hadiyar yawu yakeyi ya buga stuka abinka da mai hancini
"mistchhhww dube shi sai wani rawar jiki yakeyi kamar bai taba cin abinci ba"
ko kula shi baiyi ba ya zuba abincinsa yadda zai isheshe shi ya kuma dauka plate ya zuba wa Fahreen ma ya mika masa bai masa musu ba ya karba,
Fudhal ne ya sauka gaban abincin don zuba nashi,
" awwww wai dama zaka ci "
ko kula shi baiyi ba sai kara hade fuska da yakara yi,
murmushin da take halittan sa ne ya sake yace
aikin kawai mutum sai dan banzan burga,
ai na zaci kai da kataba cin abincin baza kaci wannan dinba dan renin sense,,"
ko kula shi baiyi ba ya fara bawa cikinsa hakkinsa.
"kai Allah de yayi albarka a matar gidan nan ni dole ma na shiga na mata godiya kamar tasan dama yunwa nakeji wallahi,
kuka ne kaawai banyi ba da zamu zo kuka wani daga wa mutane hankali wai muyi sauri kamar zamu bar duniyan,"
yana maganan yana turo baki yana bata fuska,
idan ka kare masa kallo zaka hango zallan shagwaba dake tattare dashi,
"Fudhal yace tun da gidan na kanin ubanka ne sai ka shiga kamata godiyaa,
dan shishsigin stiya sai shegen son cusa kai a inda ba'a gayyace ka ba da son asan da kai"
" murmushi ya sake yace to Alhamdulillah dalilin shishigin da cusa kan nawa aka sanni a gurare da dama wanda wani katon gardi baije ba,
kuma ba'a san dashi ba yayi karasa maganan nashi yana auna mishi harara"
" nuna kanshi yayi yace nine katon"
" dubawa zakayi dan renin wayo kawai "
sallaman da Chief yayi ne ya kastar dashi daga abinda yake niyan fada,
amsawa suka yi ya shigo ya zauna fuskansa dauke da murmushi,
yace "saannunku da bakunta da fatan ban takura muku ba,"