x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 5 - THE TWO LIGHT RIKICIN GIDAN SARAUTA

  • 12001 words
  • 15000 words
  • Out of 97531 words

Category: Love Stories

Views 523

20 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
gyara mata kwanciyar ta suka shigo da babies din harda islam aka kwantar dasu a gadonsu na yara,

Innani ta kara gyara mata kwanciyarta,

ya kai akalla minti ashirin yana zaune yana kallon face nata rayuwarshi na baya ke dawo mishi lokacin yana tare da farin cikinshi yana tare da iyayen shi da yan uwanshi,

gaba daya yanayin shi ya sauya Fatima dake kallonshi sai taji yayi mugun bata tausayi har tayi dana sanin shareshi data yi,

muryan Innani ne yayi breaking silence da cewa

"Hamma tashi kaje ka huta ka debo gajiya kayi kwanka kadan kwanta,

ga abinci ma nasan angama ka kuma kwantar da hankalinka ba abinda zai sameta sai alkairi zata ji sauki kaji,"

gyada mata kai kawai yayi ya mike badan ya so ba kallon Fatima tayi tace

"Adda Manga tashi kije ki hada masa ruwan wanka ko,"

dan sadda kanta kasa tayi tace

"tohh,"

ahankali yace

"aa tabarshi ma zan iya ba saita wahalar da kanta ba,"

"mai ne ne kuma abin wahala a aikin lada Hamma,

taje ta maka man ai taji sauki,"

" aaa tabari kawai dan jimm tayi kafun tace Adda ta maka laifi ko,"

jijjiga kai yayi alaman aa ba abinda tamun

"bari naje,"

bai jira yaji amsar da zata maido mishi dashi ba yayi ficewarsa Innani tace

"Adda Manga kin mishi wani abun ko, yadda nasan Hamma baya musu,"

dago dara daran idonta πŸ‘€tayi da sukayi narai narai dasu kamar mai son kuka tace

"Umma da gaske ban mishi rashin kunya ba kawai de na dann......,"

" kindan mai Adda,"

"kawai de.......,"

" hmmm haba Adda kiji tausayin bawan Allahn nan man yana cikin damuwa fa,

in baki kwantar masa da hankali ba wa zai kwantar masa,
yau fa akalla shekara 9 tara rabonsa da ahalinsa yau kwatsam ya hadu da daya daga cikin su ai dole yayi murna,

yana da kyau muna kyautta zaton mu akullum ban sanki da sauran fushi ba nasanki da hakuri da juriya Adda na,"

fashewa tayi da kuka 😭 tace

"Allah Umma na gagara jurewa ne,

naji storo ne kar in rasa shi ina storon faruwar hakan,"

janyota jikinta Innani tayi dan tabbas ta fahimci kishi ke dawainiya da ita,

lallashinta ta shiga yi har tasamu ta yi shiru aka kuma yi saa ta fahimce ta,

saboda Fatima mutum ne mai hakurin gaske da juriya ga zurfin ciki da kauda kai,

"ki tabbatar anjima kinje kin bashi hakuri karki bari ya kwana dake aranshi,"

" tohhh,"

shine kawai abinda tace kallon zainab data zauna adakin tana sauraron duk abinda akeyi Innani tayi tace

"ki hada mata ruwan wanka,"


dan turo bakiπŸ˜™ gaba tayi ta tashi ta shiga toilet din sai kumbure kumbure takeyi tana saka da warwara a heart nata gameda abinda ta gani azahiri da wanda ta saurara,

tasan tabbas ayanzu batada wani madogara tunda har an gane cewa yar uwarsane ita tasan shirinta ya lalace ayanzu komai zatayi abanza ne don yadda Innani ke kaunar Hamma tasan bazata taba barin wani abu marar kyau yayi tasiri azuciyanta ba akansu,

tohh ita ya zatayi yanzu haka ta gama hada ruwan wankan tana karantawasilar jaki,

Innani ta taimakawa Fatima ta shiga wankan tayi ta futo ta shirya cikin kaya marar nauyi,

aka kawo mata abinci taci ,

sai bayan azahar Zulaihat ta farka bakinta dauke da salati da Fatima da ke zaune akan gadon ta fara cin karo murmushi fatima ta sakar mata tace

" sannu kin tashi ya jikin??,"

" da sauki,"

kawai ta iya cewa ta zauna tana bin ko ina da kallo tana kokarin tuna binda ya faru

"akwai inda ke miki ciwo ne,"

murmushi tayi tace

"aa na gode da kulawarki,"

tace

" ba komai is my duty ai ke yar uwace agareni ba godiya stakaninmu,"

murmushi kawai ta mata suna cikin haka sai ga Innani ta shigo dakin ta karasa inda take tace

"aa yan biyu maman yan biyu kin tashi ne ya jikin??,"

ahankali tace

"da sauki,"

" tohh Allah kara sauki bari a hada miki ruwan wanka ko ,"

gyada mata kai kawai tayi dan ita mamaki ma suke bata,

she wonder were Akhie yasamu wayannan mutane masu kirki haka tana cikin tunanin saiga Innani ta fito daga bathroom ta iso inda take ta taimaka mata ta mike ta cire kayanta ta kaita bathroom din,

atakaice de ita tamata wanka ranan ta shiryata ta kuma bata abinci da shayi mai kauri aiko nan taji ta koshi,

sai wani son matar ya kara shiganta wani girma da daraja ta kara a idonta ata kaice sai bayan ishaa suka samu hallaruwa kamar yadda chief ya bukata,

kowa ya hallara sai de banda zainab da faruq wato little wanda bai wuni acikin gidan ba yaso yin hakan dan ya kasance da aunty shi da twins sai de an hanshi don kar ya dameta.

An bude taro da addua inda chief ya fara da cewa

"tohh de zamu so muji labarin yadda akayi kika shiga wannan hali amma kafun nan bari mu fara da gabatar miki da kanmu da asalinmu dan mu cire ki daga duhu,

nasan kina mamakin abubuwa da yawa game da mu kina kuma da tambayoyi da yawa,

tohh yanzu zan amsa miki su inshaallah.

tohh fahh readers nasan kuma kuna da naku tambayoyin kamar haka

waye Zulaihat da yayantaπŸ™„ ?
suwa suka so kasheta 🧐??

wa ya sasu wannan aikin?

Mai ne ne dalilin mahaifin little na bari familyn su???

dan wani family ne shiπŸ€”?

wacece wannan matar wa kuma take so cutar waπŸ™„πŸ™„?
wani alkawarin aure suke magana akaiπŸ‘€πŸ§ ?

mai ne ne kuma kaddaran wannan yarinyaπŸ™„πŸ§πŸ€” ?

MU HADU A NEXT PAGE DON AMSA MUKU TAMBAYOYIN KU


QUEEN MAHIRAH IDRISS

Follow this link tojoin my WhatsApp group and 🚿 me with comment and react 😁😍🀩😘
https://chat.whatsapp.com/EPeM4KtGCoJ9mrYw1Avfow
πŸ‘‡

Comment and share 😁




🧚THE TWO LIGHT ✨{RIKICIN GIDAN🏰 SARAUTA}


?Thursday, ?February ?29, ?2024





09:09:22 PM


Story and written by
Queen Mahirah
ADAPTED EXPERT WRITER πŸ“–πŸ–ŠοΈ


BOOK 1

Follow this link to join my WhatsApp group and 🚿 me with comment and react 😁😍🀩😘
πŸ‘‡
https://chat.whatsapp.com/EPeM4KtGCoJ9mrYw1Avfow

🧚7🧚

ASALINSU
Malam Umar Bello wanda aka fi sani da Chief Imam, 'da ga Hardo Bello.Hardo.

Bello ya kasance bafulatani gaba da baya wanda ke rayuwa a wata Ruga wanda ke karkashin Wudil local govement a Kano State.
Rugar Hardo Bello ta kasance ruga ce mai dauke da tarin abubuwa na al-ajabi da ban mamaki.

Ta kasance boyayyar ruga wanda ke da karancin alumma da karancin ilimin addini da ilimin zamani, kasancewarsu boyayyiyar ruga masu koyi da magabatansu,

Hardo Bello ya kasance mutum na farko daya fara ketare iyakan Rugar ya fita cikin gari, domin samun illimi na addini,

yayi yawan garuruwa karshe ya sauka a garin Kano a iskalin Malam Labaran.

Malam Labaran ya kasance mashahurin Malami wanda ya sanu a garin Kano har ma da wassu garuruwa ya karantar da Malamai da dama a wannan lokacin.

Hardo Bello ya sauka agurin Malam Labaran daniyan samun ilimin addini,

yasamu tarba mai kyau inda ya fara daukan darasi agun Mal.Labaran,

cikin shekarun da basu wuce uku ba Hardo Bello ya zama cikakken Malami kasancewaarsa mutum mai gwazo da himma, gashi yana da kaifin basira wanda shi kanshi Mal. Labaran na mamakin irin kaifin basiran da Allah yayi wa Hardo Bello, cikin shekara 3 ya haddace Al-Quar'ani mai girma da sauran litattafan musulunci.

kasancewarsa mtum mai biyayya da sanin ya kamata hakan yasa Mal. Labaran basa waassu sirri na Malunta wanda acikin daalibansa dasu ka gabata da dana lokacin ba wanda yasan dasu.

Bayan ya kammala koyon karatun ne ya fara haraman komawa Rugarsu,
Bayan komawarsa ne ya tadda mahaifinsa ya rasu yaji mutuwan mahaifin nasa sosai, basu wani bata lokaaci ba aka nada shi mastayin Hardo na rugar kuma babban malami Rugar.

Cikin kan kanin lokaci ya fara karanatar da yan Rugar nasa ilimin addini dai dai iyawarsa anko yi sa'a sun dau abin da muhimman ci,
sunyi karatu ba kama hannun yaro da Allah ya dafa musu cikin kan kanin lokaci ilimin ya bazu a Rugar kasncewar basu da yawa a Rugar.

Cikin shekaru kadan Ilimin addaini ya bazu sosai ba ilimin addini kadai ba hadda yanayin rayuwar zamani don sukan yi saye da sayarwa stakaninsu da mutanen kewayensu harma da na garin Kano,

Allah ya azirtasu da kasa na noma wanda ke daukan abubuwa da ba'a samu nan kusa,

sukan yi noma sai sukai cikin gari a musu canji da wanda zaasuyi amfani dashi,

ana haka har Hardo Bello ya fara tunanin mai yasa su baza suyi ilimin boko ba sai su fara sarrafa nasu kayayyakin da kansu, bai bata lokaci ba wajen sanar da mutanen fada sai de dayawansu basu aminta ba da hakan ba,

hakan yasa guiwansa yin sanyi har ya kai ga Uwargidanshi ta fahinci yanayin shi ta tambayi ba'asi, ba tare da shakka ba ya sanar daa ita komai,

nan ta bashi shawaran ya tura yaransa maza mana su fara yin karatun zamanin muddin yayi haka suma mutanen Rugar zasu yi,

bai rena shawaranta ba inda ya hada kan iyalinshi wato Amaryarsa Nanne sai uwargida Shatu da yayansa guda 7 wanda Allah ya azirtasa dasu,
na farko shine Modibbo sai mai bimishi Umar sun kasnce 'ya'yan Shatu wanda Allah ya bata sauran mata ne kuma yayan Nanne ne,

sai de Hadin kansu yasa baka fahintar hakan don zaka ransate Modibbo dan Nanne ne kasancewar Shatu na masa kunyan 'ya'yan fari,

haka sauaran matan ma duk suna gurin Shatu Allah ya jarrabeta da son 'ya'ya mata sai de bai bata ba shiyasa ta rike 'ya'yan kishiyarta kamar ita ta haifesu,

Hardo Bello ya sanar dasu game da karatun sai de Modibbo ya nuna rashinn amincewarsa inda Umar ya nuna amincewarsa da farin cikin jin hakan yama gagara boye farin cikin shi, Hardo Bello bai ji komai ba karshe ma godewa Allah yayi daya sa ba da daya ya basa ba,

cikin kankanin lokaci ya kammala shiri ya kai Umar Kano Gidan Mal. Labaran don dama sanda ya shaawar cesa ya kuma nuna ya aminta kafun ya kawo Umar din,

am sama masa lesson teacher waanda ya fara masa tundaga Abc, cikin kan kanin lokaci ya kware kasan cewar ya gaji mahaifinsa wajen kaifin basira, anyi sa'a yaci interview aka bashi aji 6, ya ko mai da hanakali kuma an cigaba da masa lesson ga ilimin addini ma ba'a barshi abaya ba Malam Labaran Allah ya jarrabesa da son Umar yakan kiransa da Chubado wato zababbe {choosen one} ayaren fullanci,

ya fahinci Umar har yafi mahai finsa kaifin basira ya jashi ajiki sosai inda suka tasao tare da dan Mal. Labaran kansu daya.

Wai rana bata karya sai de uwar diya taji kunya Umar ya kammala degree a BUK dake garin kano ya karanci Islamic Studies ya kuma fito da sakamako mai kyau sannan yayi suna sasai amakaranatar har ma da harin Kano baki daya kasancewar tun yana yaro yasaha jagorantar garinn Kano agasa dayawa kuma yayi nasara sosai ake ji dashi,
ko a makaranata shike jan su sallah a babban masallaci anan yasamu lakabin CHIEF IMAM, saun nemi dasu rike shi amma yaki ya nuna garin su na bukatar shi, ba yadda suka iya haka yasa suka hakura suka barshi ya koma.

komawarsa Rugar ta samar da cigaba mai tarin yawa wanda yasa mutane cizon yastan su dayin dana sani ciki harda Modibbo don har kuka sanda yayi,

cikin kan kanin lokaci Rugar ta bunkasa sosai ta shahara inda gwamnati ke neman yin kaka nika a garin suna neman kwace ta, hakan yasa mutanen garin dagewa da add'ua sosai ba dare ba ranaa har da azumi ga sadaka da sukeyi akai akai,

dayake Allah ba azzalimin bawansa bane sai ya amshi addua'arsu, gwamnati suka manta da kashin su gaba daya, duk da haka basu dena rokon Allah ba daya karesu daga sharrin makiya da magauta, ya zame musu alada ako wani karshen wata sukan yi azumi guda biyu sannan suyi addu'a don neman stari daga Allah, ga kuma saukan Al-Quar'ani mai girma da sukeyi da sadaka,

aduk lokacin da sukayi noma ko sukan cire zakka sukai a makwabtan garuruwan dake kusa dasu, sannan sukan hada kudi don taimakawa marayu da nakasassu da kuma gajiyayyu.

Ta bangare daban ko sun dage da neman ilimin boko ba kama hannun yaro sai de maza kadai keyin karatun ba mata,

cikin shakara 10 kauyen ta zama wata karamar city na Fulani ga manyan masu mukami da suke dashi don ba'a barsu abaya ba, ayanzu suna da manyan gaggaruman mashahuran yan boko wanda suka jika da ilimin boko dana addini, basu rasa komai ba suna Doctors, Engineers, police... dade sauransu, hatta makaranata sun bude mai girman gaske duk da taimakon Chief Imam,

a wannan lokacin ne aka fara bawa mata daman yin karatu wanda basuyi ba kuwa ana wayar musu da kai sosai ta hanyar bude wani class na musamman na yaki da jahilci,

akarshe de Rugar aka mata lakabi da RUGAR HARDO BELLO, kasncewar dalilinsa ne duk wannan cigaban ya samu family dinsa kuwa ana ganin girmansau sosai.

Bayan rasauwar
End Ads