x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 30 - THE TWO LIGHT RIKICIN GIDAN SARAUTA

  • 87001 words
  • 90000 words
  • Out of 97531 words

Category: Love Stories

Views 538

20 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
zuciya "shi ke nan yanzu ya tafi grandpa?
Bazan ƙara kallon shi ba ?
Bazai kara kira na a waya ba?
Bazai ƙara kaini makaranta ba?
😭😭😭. Grandpa Dan Allah ku dawo mun dashi, wallahi na yadda zan aure shi a haka, na yadda koda shi baya sona, inason in saka mishi da irin kulawa da tattalin da ya yi gareni, ya nuna wa duniya babu yani, tur da irin halina duk Ni na jawo hakan daban tauna masa asiri ba da hakan bazai faru ba, duk da mugun nufinsa akaina na ƙwammace hakan ta faru da rasa kanshi da yayi yanzu , nadan Ni ce sa na di,"

ba tare da ta sani ba taji an soka mata allura, tana kokarin juyowa wani bacci mai nauyi ya dauke ta, da taimakon Dr Yusuf aka kwantar da ita bisa shinfidadden kujerar, mai taushin gaske, sauke ajiyan zuciya Fulani tayi ta ce "Allah ya kawo ka a dai dai Dr Yusuf, da naga ka shigo na zaci shine ma ,"
tayi maganan ne yayin da idonta ke cikin na
Baba sarki, "hankali na ya gagara kwanciya ne shiyasa na ce bari nazo na duba ta,"

"Hmmm tun dazu ta rikice ga jikin ta yayi zafi sosai, sai sun batu take yi shiyasa nace bari kawai na kiransa ka turo mana Dr Yusuf,"

"Hmm kinyi kyan kai, mai yake damun ta ,"

Cike da girmamawa Dr Yusuf ya ce" damuwa ne da stress, sai zazzaɓi, amma yanzu na mata alluran bacci she will be alright inshaallah, and kar ana barinta ita kadai kuma ban da yawan tunani, I mean kar barta tayi stressing brain dinta,"

Gyada Kai kawai Bana Sarki yayi, yayin da yake shafa kanta cike da tausaya wa da zallan ƙauna.



RUGAR HARDO BELLO (KANO STATE, NIGERIA)

8:00 pm

Zaune muke a falo as always kowa da abinda ya keyi muna sanye cikin light wears wato kasa marassa nauyi, Sallamar da muka ji ne yasa hankalin mu karkata in da ake sallaman, wah zamu gani ???

Commodore Fareed ne da Captain Fudhal, suna sanye cikin fararen jallabiya, dan kifta ido nayi ina juya su kafin na amsa sallamar tasu, Bismillah shine abinda nace dasu yayin a Islam tun da ta amsa sallamar bata kara cewa komai ba, cike da fara'a ya samu guri ya zauna, shine Fudhal sai cika yake yana bastewa haka har ya zauna.

Cike da fara'a ya ce "sannu ku da hutawa GENTLE ladies😁,"

Kai na dago na gansawa, sai kawai ya burge ni musamman yadda yake magana cike da fara'a, ko haka kadai ya nuna cewa mutum ne shi wanda ba shida damuwa.
Murmushin ba mayar masa nace yauwa sannu ya kuke?

"lafiyan mu kalau, ya ɗawainiya da mu?,"

Murmushi nayi na mai mai ta Kalmar ɗawainiya,

"Ehh ai ba ƙaramin kokari kuke yi ba,"

Wani murmushin na kuma sakewa don nima gwana ce a wannan fannin musamman inna samu wanda na sake dashi.

Ai ku bakin mu ne , bakon ka kuma annabin ka ne.

Gyada Kai yayi ya ce "haka ne, if I guess right ke ce Mahnoor ko?,"

Yaff Ni ce,

"Mashaallah, and this boss lady most be Khadijatul Islam,"

Murmushi nayi na ce You guess it right, she is the one.

"You know am good at guessing,"

Humm kaji Dadi ni kam am not good at guessing,
Dan karkata kai nayi na karewa Captain Fudhal kallo na yan sakanni kafin na ce, is he seek? Naga ya hade fuska kamar gumbar waina, cikin shi na ciwo ne?

Murmushi Fareed yayi ya ce "he is not, haka yake bashi da fara'a,"

Dage gira daya nayi na ce Maama luya, so haka yake kullum da face dinshi kamar anyi gobarar attarubu?

Wani mashiriritin dariya Fareed ya sake ya ce "You are so funny,"

Murmushi nayi na ce uhmm kaga ban ma san sunan ku ba?

"Ohh my name is Fareed and this one is Fudhal,"

Ohh Masha'allah I guess I know you, but where?
Ohh 😯 I remember you are Commodore Fareed, you are Air force
, and this Mr Grumpy is Captain Fudhal, I think I guess it right,

Wani murmushi Fareed ya sake ya ce"yapp haka ne, but a Ina kika san mu?,"

Ohh come on, Commodore saninku ai is not a big deal, Kuna cikin Top ten na the most famous and handsome rich guys a fadin Africa, Ni a gurin ƴan matan Class din mu ma na sanku.

"Wow ki ce min yi wuta,"
Yayi magana yayin da yake dan daga kwalan jallabiyar sa,

Dan ƙaramin dariya na sake yanda yayi ya ban dariya sosai, ina dayan kuma mai danne ƴayan mutane ajikin gini.

Dan ware ido Fareed yayi ya ce "kai kuma acikin mu yake ,"

Zumburo baƙi nayi gaba na ce 😚 ehh mana kawai daga kai mishi abinci sai ya fara wa mutum mugunta, sanda fa ya gwalmadar mun da kashin kun kumi na😞.
Zare ido 😳 Fareed yayi y ce"subahanallhi, uhmm am so sorry 😔 haka yake wallahi yana da zuciya sosai,"

Dan daga gira daya nayi nace, i guess ni bani dashi shi yasa ya mun haka, wai yana da zuciya, na fadi haka yayin da na kara turbune face nawa.

"Sorry kin san yan uwan nawa sai ahankali a musu afuwa please 🙏,"

Kara cuno baki 😗 nayi gaba nace uhmm, ohh na manta ga can abincin ku a dining table, tun dazu Innani ta ajiye, muje nayi serving naku,

Murmushi yayi yace "okay thanks 😊,,"

Yayi magana yayin da ya mike ya bi Bayan ta, shiko Fudhal sanda ya mula dan kanshi kafin ya mike, yayin da Islam tana kare mishi kallo azahiri ko zaka ranste waya take dannawa sai de idonta yana kanshi, tana karantar halayyar sa tsaff .

END Of PAGE 36, FOLLOW FOR MORE 😢😁

Story and written by
Queen Mahirah 👑🧕
The wordsmith 🖊️📖















































THE TWO LIGHTS ✨ (RIKICIN GIDAN SARAUTA 🏰)

The story contains the fact Royalty, Ego, Separation, disastrous love, hatred, hardship,Twin flame journey...

Story and written by
Queen Mahirah 👑🧕
Wordsmith 🖊️📖


FREE BOOK

BOOK 1
🧚37🧚

Fudhal ko sanda ya mula dan kanshi kafin ya mike cike da izza ya je dining area, yayin da Mahnoor da Fareed sun shagala da hira zaka ranste sunyi Shekaru tare.

Da kallo na bisa kafin na mike na fara serving dinsa, ina gamawa na mika masa abincin, komawa nayi na zauna muka ci gaba da hira ni da Commandore Fareed, sallamar Innani ne ya kaste mana hiran, cike da jin dadi ta karasa inda muke tana washe hakora kamar gonar auduga, "Mashaallah Abu yayi kyau, abinci kuke ci ashe ƴan samari,"
Fareed ne ya ce "ehh Innani Barka da dare,"

Kara washe hakora tayi ta ce "yauwa Barka, ɗan albarka, ya mai jiki?,"

"Jiki da sauki sosai, Alhamdulillah,"

"Tohh Allah ƙara sauki,"

"Amen summa Ameen"
Toh gwanar laste laste ke baza ki ci abincin bane, kizo kuci tare mana ai yafi dad'i, kuma zai ƙara muku haɗin kai,"

Ba tare da ta ce komai ba ta taso tazo dining area ta zauna tayi serving kanta ta fara ci cike da Miskilanci,

Wani murmushin jin daɗi Innani tayi taja wani dogon numfashi ta ce "Allah albarka ci rayuwar ku ya kuma ƙara hada kanku,"

Cike da zumudi Commodore Fareed ya ce "Ameen Innani, kin ga na samu ƙanne dama nawa daya ne, in zan tafi sai in kaisu gurin Ammi na ta haɗa su da Mobina sai su zama su uku, kinga mu uku suma su uku,"

wani ɗan guntun ƙwalla Innani ta goge cike da tausaya ta ce "kai yah Fareedu bawan Allah Allah de ya nuna mun wannan rana, da zan miƙa amanar dana dauka ga masu shi,"

Cike da fara'a da ƙwarewa wajen aikinsa ya ce "Ameen summa ameen, ƴar tsohuwa dama ita alƙawari kaya ne mai nauyi musamman inka rike shi a cikin ka,"

"Hmmm wassu lokutan aikewa aciki yafi ka fidda shi sarari, kasan mahassada sun yi yawa, wai kana ta kai su kuma suna ta kai,"

"So sai ma kuwa Innani ai ni zan fada Miki hakan, kinsan fa Yan zu an dena kiwon dabba sai mutum,"

Cike da jimami Innani tace "ohh duniya ina zaki kaimu, Allah de ya kare mana ku,"

"Ameen summa ameen,"

"A'a shi mara lafiyan fah, Nuriyya zo ki kai mishi abinci,"
a dan razane na dago kaina na ganta kafin na,nayi kicin kicin da fuskana na ce 😚 nifa Innani ni wallahi gaskiya ki tura Barira ta kai mishi abincin,

"Eyyeh wai samu ya fi iyawa hawa dokin maciji, in ce ki kai ki kice na aiki Barira, yar tselen uwa ke zaki kai,"

ƙukan shagwaba na fashe dashi na fara shure shure da kafa a kasa, ni ni wallahi abinci nake ci, to ke ki kai da kanki mana tunda ke kin fishi damuwa da yunwar cikin shi,

"Ehyehh kin san Allah zan zazzage Miki bakin rashin mutunci Nuriyya in baki tashi kin kai mishi ba,"

Bil hakki da gaskiya na fashe da kuka ni wallahi bazan jeba nikam, naje ya kashe ni jiya ma da kika aike ni ina sanda ya gwalmadar mun da ƙashin ƙunkumi na,

Sake baki galala Innani tayi tana kallonsa kafin ta fara tafka salati kai kace an aiko mata da saƙon mutuwa,
"Ohhh ni Khadijatu matar Sheik, Yan zu a baƙon ma sanda kika Ni na bakinku na tsiwa,"

Dan kifta ido nayi na mamaki na zaci zata fara surfa bala'i an Jimin ciwo kawai naji ta karya kwana,
"Yan zu ɗiyar nan sanda kika nuna halin naki na tiyara ,"

Zumburo baƙi nayi na ce 😚 nifa ban gane mai kike nufi ba , daga cewa ya gwalmadar mun da ƙashin ƙunkumi, sai ki fara zuba kamar ƙorama, baƙi ma ji abinda ya faru ba har kin yanke hukunci.

"Da ban san halin ki bane da sai na tsaya bin sassala, ai dama tun farko kin nuna bakya son kai abincin dama nasan za'a rina,"

Lallale Innani ya mareni kuma ke ki hanaani ƙuka,

"Ai ni Nourda bai karya ƙunkumin ki Bama ban ji dadi ba,"

Bude baki na nayi galala na yan mintina cike da kututun baƙin ciki na rike kirji na ko ince na dafa ƙirjina, na ce lalle kan Innani zaki fadi haka wai somi ta uwar wawa, lallae ai dama naga take taken ki akan wannan jibgegen basamuden, sai de ban san abin naki ya kai har haka ba amma ba komai, ai dan kinga Hamma Faruq baya nan ne shiyasa kike aikata wajen wani gardi harda maste ni a gini,

Na karasa zan cen ina maste ƙwalla, amma ba komai zan bar miki gidan, kai ƙasar ma gaba daya zan bari, sai shi ya maye miki gurbina dama naga kin fi son shi.

Na karasa maganan yayin da na mike nayi hanyan ɗakin mu.

Galala Innani tayi ta sake ɓaki ta na bina da kallo ta ma rasa mai zata ce, in akwai abinda ta tsana a rayuwar ta bai wuce taga bacin rai na ba ko ince zan bar ƙasar nan hankalinta to ranta inyayi dubu zai tashi.

Fareed ganin tuhumar bana ƙare bane yasa ya ce" ki ɓari Innani inna gama zan tafi masa dashi , shima kina ganinsa ba ƙanwan lasa bane, yana da tsokala, kuma sai wanda yasan halinsa zai gane hakan ,"

Cike da sanyin jiki Innayi ta ce "shikenan to ka kai mishi," ta karisa maganan yayin da hankalinta ke kan hanyar ɗakin mu.



KANO STATE, NIGERIA
MASARAUTAR SUHATAJ MUHD HABIBULLAH

TURAKAR GIMBIYA SAUDAT (KILISA)

Kamar kullum tana Hakim ce a sashin ta bayi na ta faman mata hidima, sai de yau shigar nata na daban ne kasancewar an yi rasuwa tana sanye da fararen kaya hannunta dauke da casbaha.
Sanarwa akayi na karasowar Sarauniya Sareena, cike da taƙama ta shigo ta samu guri ta zauna, bayin na ganin haka suka sallama kansu bayan gaisuwar da suka mata,

Cike da zallan isa ta fara magana kamar haka "bayan kin kashe shi mai ne ne kuma dalilin zamanvmakoki da kike yi anan,"

Cike da izza ta dago kai ta ƙarewa ƴar Tata kallo ta ce "ban gane mai kike nufi ba,"

Murmushi ta sake kafin tace "zaki fadi haka mana Ummi, ina so kisan wawa daban mai wayo daban,"

Murmushi Kilishi ta sake 😏 na gefen ɓaki, "yaro yaro ne wai baisan wuta ba sai ya taka, har yanzu da sauranki Sareena, na haife ki amma naga alama ban haifi halinki ba, yarinta na ɗawainiya dake, ko ince kin ɗauko halin ɗan uwan ki da ake cuta a kullum,"

Kicin kicin Sarauniya Sareena tayi da fuska tace "Ni fa ba zuwa nayi nan don ƙi mai dani yarinya ba, zuwa nayi ki fada mun mai ye dalilin da yasa kike amfani da Mubeen?
Kuma mai Mobina ta miki da kike so ki lalata rayuwar ta?"

Jijjiga Kai kawai tayi kafin ta tsuke fuska ta ce "ina so kisan ni ce mahaifiyar ki, baki da dalilin da zaki zo ki tsaya kina mun wannan tambayoyin marassa ƙan gado,"

"Hummm Ummu kenan, abin da nake so kusani anan shine duk abinda zakiyi ki tabbatar kin tauna rami dai tsayin ki kuma wallahi ki bi ahankali don duk abinda kuka shuka sai kin girbe shi tsabb,"

Cike da bacin rai tace "ya ishe ƙi haka Sareena Ni uwar ki ce ba Sa'ar wasan ki ba, ƙinyi ƙankantar da zaki zo ƙina gaya mun magana sin ranki, Ni zaƙi gani ƙice ina amfani da Mubeen mai yake da shi shudin banza ƙaramin alhaƙi, in Kuma na lalata rayuwar Mobina mai zan tsira dashi, yarinyar daki ishirin bata cika ba, ce Miki akayi ina da lokacin ɓatawa ne akan kananan ƙwari irin wa'yannan,"

Cike da rashin yadda take ƙare mata ƙallo, don in akwai abinda bata yadda dashi a duniya ba to mahaifiyar ta ne.

Mikewa tayi cike da gadara ta ce"bude na fada miki, in kina vin kasa ki ƙiyayi ta shiri,"

Tana gama fadan haka ta baza alkebban ta tayi gaba,

Wani irin ƙuna zuciyar Kilishi keyi tabbas daban dan Sabreena ƴar ta ɓace da ba tan tama yau zata baƙunci lahira, wani abu da ta tuna ne yasa ta sake wani murmushi na gefen ɓaki, ta ce "yaro yaro ne ni dake shege ka fasa, zaki gane ni ba sa'ar ki bane, ki gamaa baki shirin, kina gani zan mulki wannan masarautar babu yadda kika iya dani,"😏



Zaune take cikin wani ɗaki mai shegen duhu tana sanye da wassu kaya jajaye, ba abun da kake iya hange ajikinta hatta fuskar ta a rufe take, hannunta dauke da candle dashi take amfani wajen haska gurin, sanda na kara baza ido kafin na hango wassu samudawa zaune gaban ta yayin da take Hakim ce bisa wani kujera wanda tasha ado da ƙwaran gwal, haka wuyan ta na sanye da wani tafkeken sarka da ƙananan ƙwaran gwal, dana ƙarewa ɗakin kallo ba komai aciki sai wani table mai dauke da wani kwarya akai, da mamakina cikin shi dauke da jini a cike, sai wani ƙaton ƙwaran Gwal ciki an kunna wuta, daga gefe kuwa wasu manyan gumaka ne jibge, komai na ɗakin ja ne.
Cikin wani murya mai wuyar fassaruwa take magana "na baku daga yau zuwa gobe ku tabbatar kun gabatar da aikin dana sa ku,"

Cike da girmamawa da rawar jiki na tsoron abin da zai fito daga ɓakinsa yace" a mana afuwa INNA UWASU INNA UWA MABA DA MAMA adann ƙara mana lokaci, zamu gabatar da wani shiri yanzu yarinyar akwai tsaro mai karfi akan ta muna da buƙatar a fito da ita sai mu ƙaaddamar da aikin mu,"

Cikin razananniyar Muryar ta mai sa maza rawar ɗari ta ce " na ƙara muku ƙwana ɗaya ku tabbatar kun ƙammala cikin ƙwana uku, nake so a rufe babin wannan yarinyar."

Cike da girmamawa suka zuba sujjada a gabanta sua ce "Ran mu fansa ce gareki INNA UWASU, INNA UWA MABA DA MAMA, INNA UWASU BABU IRIN KI A DUNIYA..,"


IRAQ
HOSPITAL

Ƙawance take bisa lafiyayyiyar gadon asibiti, tana sanye cikin kaya na marassa lafiya, fuskan ta yayi fayau dashi kana ganin ta kasan taji jiki.

kallo na ƙarewa dakin zaka ranste dakin wani hamshaqin mai ƙudi ne a Nigeria, komai na dakin a tsafta ce yake, gashi komai fari tas ga sanyin ac dake tashi da wani ƙamshin haɗadden turare ko ince room freshener, daga wani ɓangare na ɗakin kuwa tamkar farlo koma ince farlo ne, yana ɗauke ɗa haɗaddun Couch da madaidai cin Chinese carpet sai Centre table dake stakiya , daga jikin gini kuwa wani ɗanƙareren plasma Tv ne.

Dawowa nayi inda gadon mara lafiyan yake anan naci karo da halittar data ɓan mamaki 😳 wai wata saɓon gani 👀 mai zan gani haka!!
Engineer Othman Ibn Abdallah (ABI), ya na zaune bisa chair dake gaban gadon, yana rike da hannunta daya, da nasa hannun, kallo daya zaka masa ka hango zallan damuwa dake shinfiɗe a face ɗinsa.
Sanda na ƙare masa kallo na hango manyan tan da yayi, sai de duk da haka bai hana zallan kyansa baiyana ba, har ilah yau yana nan yan da yake a giant balarabe, mai farin fuska da kyau wanda ke ɗauke da zallan nustuwa da Chrisma wato ƙwarjini, game da murɗadɗen jiki ko ba abinda ya sauya, yana sanye cikin Black suit wanda ya cire coat din ya bar white long sleeve ɗin.
Daga ɓangaren dama kuwa Fatima ne zaune cikin shiga na alfarma, daga nata ɓangaren itama ta manyan ta sosai, sai de gyara da kula da fata da jikin ta ke samu ya hana girman bayyana, don inka ganta zaka ranste bata fi shekara 25 ba, kasancewar ta mutum mai yiTƙaramin jiki, wani ƙyakyawan yaro ne mai kama da Abi ke ƙwance luff ajikinta, wannan ba kowa bane sai SAWBAN, wanda ya kasance ɗan auta ƙaramin ɗan Fatima mai shekara goma a duniya.

Suna cikin wannan zaman kurame da kowa ke saka abubuwa a ransa ne aka yi sallama, cikin wata siririyar murya ko ince murya mai ɗauke da zallan nustuwa, imani haɗi da zallan Izza.

Ba tare da sun ɗago kan su ba kasancewar sun san waye ne suka amsa sallamar.

Mashaallah lah ƙuwata Illah billah, wannan shine abinda na ce a lokacin da nayi tozali da wannan kyakkyawan halittan, wani farin giant ne mai kama da larabawan Fulani, yana sanye cikin kaƙin sojoji wanda yayi bala'in karbansa wato ya amshi fatar sa ko ince fatar sa ta amshi kayan, kasancewar sa mutum mai haska kaya ba kaya ta haska sa ba, fari ne
End Ads