x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 23 - THE TWO LIGHT RIKICIN GIDAN SARAUTA

  • 66001 words
  • 69000 words
  • Out of 97531 words

Category: Love Stories

Views 551

20 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
kam ai dole ki zauna amiki acan kina da mai miki kwalliya saka miki kaya gyara miki gashi inkina so har abinci ma zaa baki abakinki kuma ko cewa kikayi su kwanta ki taka su zasu kwanta,"


"wayyohh ni Mobina gasakiya larabawan nan kuna zuba mulki iya son ranku, amma ita MAHZIA ina ne bataa shiga,"

" MAHZIA bata shiga dakin Sultan sannan iyakarta farlo na biyu kinsan ako wani part akwai farlo uku tohh falon karshe Sultana ne kadai zata shiga sai daki wanna huruminta ne gyaransa.

kuma ko mahaifiyarka bata da ikon shiga wanna gurin sai matar sarki kadai,"

"shiyasa Ammi bata yadda bayi su shiga mata falonta na karshe da daki ko dakin Abbu ma bata yadda su shiga,"

" ehh ai taga anayi a gidansu ne shiyasa, yauwa zaki dawo nan da zama kuma zanayi magana da Sarkin Dogarai da kuma asamo mun guard don ba dogarai nake so sunyi kanana wannan jibga jibgan nakeso zasu fi yin aiki da kyau,"

Princes Mobina shiruuu tayi bata ce kala ba don gani take tamakar zaa takura mata rayuwarta.




QUEEN ZUNNURA'S CHAMBER {KILISA}


kishingide take a dakin huta warta bayi na zagaye da ita ta ko ina suna ta faman hidima da ita.

kallo daya zaka mata a ka hango zallan izza da isa da ke tattare da ita duk da sanyi fanka da a/c dake rest room bai hana daya daga cikin bayinta yi mata fifita ba daya ko na yayyanka mata fruit tana bata da daddaya daya kuma na bata labarai masu nishadantarwa.

sanarwan da akayi Princes Sareena na zuwa nae yasa bayin kamewaa agu daya suka saha ruwan jikinsu sanin halin Princes Sareena na rasahin mutunci da kyamar na kasa da ita ga dan banzan son girma abu kadn zaka mata tasa a maka mugun hukunci ita bata dauki bayi a komai ba bata ma sasu a jearin mutane shiyasa bayin dakea sashen ta keshan wahaala sosai .


shigowa tayi cike a da isa gadara da zallan takama da nuna ita dain wataa cea kuam daolae abata girma, bayi biyu ne ke tafe da ita daya da bangarean dama daya ta haagu tana shigowa bayin cikin rest room din suka zube tamkar zasau mata sujjada suna mata gaisuwa amma ko kallon banza basu isheta ba ta samu guri ta zauna a gefen mahaifiyarta.


alama Kilisa ta mawa bayinta dasu basau guri ganin yadda Princes Sreena ke cika tana bastewa tasan da zance abakinta ,

suna futa Gimbiyaa Zunnura ta dawao da hankalinta kan Sarauniya Sareena tayi murmushin manya tace " wa kuma ya tabo ki shalelen Kilisa da Suhataj kuma sirka agun Suhataj da yaddar Allah,"

dogon numfashi taja kafun tace " nayi wayaa da Mal. Dan kande gamea da mastalan Yarima Fahreen ya kuma tabbatar mun da cewa kurciya aka masa, ina ada tabbacin ba kowa zai yi hkan ba sai ke Momy nasan kea zakiyi haka,"


tayi maganan tana stareta da ido, murmushi Kilisa ta sake kafun tace " a kaff mutanaean masarautan nan ni kadai kike tunanin zan zame maki bangon da zai hanaki cika burinki,"


" ai ba abun mamaki bane idan hakan ta faruu tunda tun bankai haka ba nasan irin stanan da kikayi wa Fulani Nashwa da duk wani abun da ya fito a staton ta sannan kinsaha daukan alwashin cewa muddin kina da rai baza su tabaa jin dadin rayuwarsu ba,"

wani munafukin murmushi ta kara sakewa kafun tace " laa shakka fiiiii wannan haka yake ni Zunnura na fada kuma zan kara fadi in ina da rai Nashwa da 'yayanta da jikokinta baza su taba jin dadin rayuwarsu ba,"

zabura Sarauniya Sareena tayi cike da bacin rai tace " kina nufin hatta 'yata ma baza ki barta ta samu abinda take a so dan zallan sonkai irin naki, haka kawai kina kokarin hanani cika burin da ke kika taso dani akai kin samun shaawan da saon mulkan wannan masarautan shine yanzu kike so ki ruguza komai.

inaa bazan lamunci rugujewar mafarkin danayi saheakaru ina gina w a ba bazai yiwu ba muddin nawa burin bai cika ba tohhh sai de kowa ya rasa zan tauna sirrin da aka dade ana binnewa sai de ayi mutuwan kwasko kowa ma ya rasa."


gyada kai Kilisa tayi bayan gama sauraronta da tayi tace " kina ga inkinyi hakan zata shafe ni ne ke zata shafa ke zaki kwana ciki, kuma kina tunanin 'yarki da kika haifa bata hanyan aure ba zata zama Gimbiya a wannan masarautar da alama kin mnata yadda satarin yake,"

"idan bake ba wa yasan cewa Fanan bata hanyan aure na haifeta ba kuma in ma ansani laifin na waye ne???
ina kea kika daurani a wannan hanyan kika nuna mun ita ce dadin rayuwa kika turani turai nayi rayuwa irin tasu, kuma fahhh ke kika bani shawaran kashe Ishaq don kar ya tauna mun asiri bayan ya gano Fanan ba 'yarsa bace,

shine yanzu zaki zo kina mun barazana ko kina tunanin bani da prove ne inaso kisan barewa bazata tayi gudu danta yayi rarrafe baa, gado kuma ba karan bani bane.

tuggu da munafurci da biye biyen malamai duk aikin kine tun bankai ko ina ba nasan da hakan kuma na koya ya zame mun kyan saawa kuma abincin ci inaso kisa aaranki duk randa kika mun kuskure wallahi mutuwan kosko zaayi sannan kiyi gaggaawan war ware wannan sihirin kitaba kowa amma banda YARIMA FAHREEN shidin nawa ne ni kadai."

tana gama fadan haka ta yi ficewarta tabar Kilisa cikin rudu don ta rude, wani makirin miurmushi ta sake tace yaro yaro ne yaro baisan wuta ba sai ya taka mu zuba nida ke bakisan waye BLACK COBRA🐍 bane wani murmushin ta kara sakewa.





END OF PAGE 25



QUEEN MAHIRAH



🧚THE TWO LIGHTS ✨(RIKICIN GIDAN SARAUTA🏰)🧚



Story and written by
Queen Mahirah
ADAPTED EXPERT WRITER📖🖊️





BOOK 1

2️⃣6️⃣

SULTAN ABDUL MALIK ROYAL ESTATE.
Kamar kullum ma'aikata nata faman kwasan aiki kowa da aikinsa, sai de yau aikin na daban ne kasancewar za'ayi babban bako Wanda yau akalla shekara 20 rabonsa da kasar Egypt.

Wani mashahurin gyara ake wa Estate din zaka ranste SARFARAZ (King) ne zai zo.

Daga cikin kuwa wato sashin Malikat Nubia da Malik Sultan kamar su zuba ruwa akasa susha Dan murna, zuciya da gangar jikinsu na marari da muradin ganin sirkinsu Kuma da' agaresu farin cikinsu ya gagara buya duk da wani bangaren na zuciyoyinsu na shakkan ganin sa gudun kar ya tuno musu da abinda suka dau shekaru suna kokarin manta shi.

A bangaren Sultan Habibullah da Sultana Maryama ko suna shakkan zuwan jikan nasu sabida abubuwa da yawa saide Hakan ne kadai mafitan da suke dashi wato hanyar da zata warware musu kullin da suke ciki.

Daga fannin mutanen estate din kuwa kowa yasha ruwan jikinshi musamman Munafukai, zuciyoyinsu da abubuwan da suke kissimawa.

EGYPT INTERNATIONAL AIRPORT
Securities ne jibge a bakin airport din ga cars na alfarma jere akalla sunkai goma vakake wuluk, Daya ne kadai fari wanda ya kasance a stakiya yanayin yadda aka bawa gurin staro zaka tabbatar da cewa yau zaayi babban bako a kasar Egypt.


Daga cikn airport kuwa wani Dan kareren mashahurin jet ne ya sauka Mai dauke da kakin sojoji, Jet din na landing dandazon soldiers sukayi kawanya suna sanye da kakin su na Nigerian Army.

About five minutes kafun aka bude cab din jet din inda wassu kyawawan halitta suka bayya na su biyu masu stananin kama Wanda azahiri shekarunsu ya ban banta kasancewar kallo Daya zakyiwa dayan kasan matashin dattijo ne Mai ji da naira Wanda Hutu ya Rasta jikinsa ya haifarwa fatansa wani sheki da daukan hankali na musamman azahiri Babu abinda zamu ce sai de Mashaallah yabo da daukaka sun tabbata ga ubangijin talikai Wanda yayi wannan kyakyawan halittan.


Sanye yake da Ralph Lauren black suit Wanda ya amshi fatar jikinsa sosai ya Kuma haska kasancewarsa fari tas mai capturing attention, dogo ne Mai kira irin ta samudawan larabawa hannunsa ko Yana sakale da agogo na kamfamin Gucci haka kafansa sanye cikin Black cover shoe kirar Gucci.


Fuskar sa ko dauke yake da hadaddiyar man's pride dinshi Wanda yake tamkar an zuba ruwa a kan tiles sai sheki take tana walwali , dogon hancinsa ya karawa face nashi kyau haka lips nashi daidai face dinshi idonshi kuwa Yana sanye da designer dark space bakaramin kyau ya masa ba duk da fuskanshi ba annurin fara'a ko kadan sai Taron kwarjini dake shimfide.


Kallon farko baka isa ka kira shi da dattijo ba kasancewar Babu Alamar Hakan atattare dashi sabida yawan mosta jiki dayakeyi da Kuma Hutu da yake samu da naira dayabi ko Ina na jikinsa ya zauna Haka kallo Daya zaka mishi ka hango zallan IZZA da MULKI Hadi da zallan KARFIN IKO dake tattare dashi, daga gefensa ko matashin saurayi ne Wanda bazaifi 30 years ba.


Zallan kaman da sukayi ne ya tabbatar mun da cewa sun hada jini da wannan matashin dattijon Babu abinda ya bari ajikinsa yanayin stayinsu, haskensu da kamewarsu duk Daya ne sai de kun San ance Dan na gada yafi Dan koyo zan iya cewa yafi wannan matashin dattijon kyau da daukan ido duba da karancin shekarunsa, Shima Yana sanye da Hermes black suit Wanda azahiri shi ya haskata ba ita ta haskashi ba Kasancewar sa mutum Mai stananin kyau da hasken fata ya kasance mutum Wanda shi ke haska kaya ya fidda ita da kyanta ba ita ke fidda shi ba.


Batun stayi ko baa magana don har yaso yafi matashin dattijon stayi da Fadi Hadi da murdewa, haka fuskarsa zagaye yake da kwanceccen saje Mai balain daukan eyes Hannusa sakale da agogo kirar Rolex haka kafansa sanye da Black cover shoe kirar Gucci tana Kuma sanye da Black ankle socks.


Dogon hancinsa ya karawa face nashi stananin kyau haka pink lips nashi are so moist and succulent eyes nashi were so sexy suna dauke da zararan eyelashes, eyeballs dinshi kuwa grey colour ne wato (ruwan Toka), eyelashes nayi kuwa kamar shi ya zana abun shi they were well shaped, gashin kanshi kuwa MashaAllah shine abin Fadi acike yake tam gashi baki wuluk Mai sheki da stansti Babu abinda yake sai tashin kanshi atakaice perfume nasu ya gauraye gurin gaba daya.


Cike da ISA, IZZA mazantaka suke saukowa daga stairs na private jet din nasu Wanda ke shinfide da white royal centre carpet Wanda yayi leading nasu har balconyn airport din ga soldiers dake both right and left side nasu Wanda sunkai 20 koma fiyeda.


PRINCE MUHD KAHTER IBN ABDALLAH IBN MUHD KAHTER IBN ABDUL MALIK IBN ABDUL FATAH IBN ABDUL JALAL, known as FIELD MARSHAL MD KAHTER Wanda yake rike da highest rank in Nigeria 5 star general.
Da' ga SUHATAJ ABDALLAH the former King of Fulani in Nigeria and also the famous business man in whole wide world he is also known widely and called MASTER.

Sai kuma dansa wato MUHD MUBARAQ IBN MUHD KAHTER IBN ABDALLAH IBN MUHD KAHTER IBN ABDUL MALIK IBN ABDUL FATAH officially known as LIEUTENANT GENERAL MUHD BARAQ and also the 3 star general.

Da' ga FIELD MARSHAL MD KAHTER the famous business man also the prince of Fulani,
LIEUTENANT GENERAL MUHD BARAQ is known as the famous GYNECOLOGIST he is being call as YOUNG MASTER.


Sun cigaba da tafiya cike da takama har suka iso balconyn airport din wannan soldiers din sukayi gaggawan bude musu wannan galleliyar farar car din Mai sheki da daukan eyes Suna shiga aka bawa motocin wuta suka fara tafiya bisa shinfidadden kwaltan suna tafiya da zallan isa Tamkar Dan su kadai akayi kwaltan Wanda ta kasance ba kowa sanin cewa yau zaayi babban bako.


Basu staya ako Ina ba sai bakin tamkamemen gate din ABDUL MALIK ROYAL ESTATE Wanda tun da suka kaeyo kwana aka wangale musu gate suka kusta kansu ciki sun dauki wani diguwar hanya Wanda ta SADA su da wani jibgegen Building Wanda yasha ginin zamani ya mugun staruwa Wanda staya wa misaltashi ma Bata time ne ba Bata lokaci akayi parking gallagallan cars din a inda aka tana da don parking wato parking lot.


Securities ne suka zagaye motocin havu da dama inda aka bude cab din motan stakiyan cike da IZZA, mazantaka da zallan isa suka futo daga motan wayan daukan lokaci da sukayi Mai stayi,
Ba tare da Bata time ba suka cigaba da tafiya bisa shinfidadden center carpet dake gun Wansa yayi leading nasu har kofan hadadden part din nasu Mai daukan hankali Wanda yasha renovation suna zuwa suka staya a bakin kofan,

Wani dogon numfashi Field Marshal MD Kahter (Master) yaja ya lumshe idonsa dake cikin dark space abubuwa dayawa ke dawo masa cikin brain dinsa.

After 20 years gashi cikin Africa kasar Egypt kasar uwa da ubansa kuma jigon rayuwarsa wato asalin kakanninsa Masomar rayuwarsa kasar da yayi bankwana da ita sabida wassu dalilai masu karfi,
Yau da kafansa ya Tako cikinta badan an tursasa Shiba sai Dan wani dalili Mai karfi da aka masa albishir dashi Wanda yake fatan Hakan ya kasance gaskiya duk da yasani Wanda ya mutu baya dawowa Amma wani Abu na stikaransa da sasa Jin kamar akwai alamun gaskiya.


Wani dogon numfashi ya Kara ja kafun yasa hannunsa ta bangaren dama
End Ads