x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 9 - ROYALTY YAN SARAUTA

  • 24001 words
  • 27000 words
  • Out of 85109 words

Category: Love Stories

Views 1693

20 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
subahanallahi innalillahi wa inna ilaihi raji'un Allah karya nuna min wannan ranar tashin hankalin bana fatan hakan ya zama gaskiya ko a mafarki haba Aunty Khairat kinji yadda kikasa zuciyata ta buga kuwa"? Dariya Khairat tai tana cewa.

"Uhmm Baby kenan nima dama na fad'a ne dan na gwada ki amma koni bazan so ki auri ya Ahmad ba saboda gaskiya auren ya Ähmäd sai mace mai mugun ha'kuri domin yana da wuyar sha'ani wallahi".

"To kin gani Aunty Khairat nikuwa me nake kallo zan yarda na amince zaman aure da ya Ahmad habawa ya Ahmad fa jama'a heyyy tabd'ijan uhmm bari kawai nayi shiru Allah ya kiyaye" murmushi Khairat tai ganin yadda ta caza Babyn yasa tace.

"Uhmm ai dazaki aure shi mukam 'yan shan biki ne da yin anko ashobi zamuyi masu kyau mu kama Hall me tsada mu gwangwaje ranar auren nan".

Kai baby ta jinjina tana cewa "wai harna haskoni a misali yau ranace ta fito na zama matar ya Ahmad kan bala'i ai wallahi Aunty Khairat dana auri ya Ahmad gara na auri almajiri wanda saiyi fita bara ya samo mana abincin da zamuci"

Dariyar daba shiri Khairat tai tana kallon Baby wacce tai maganar tsakaninta da Allah abinda ke ranta ta fad'a tace "Kai Baby lallai kin d'auko da zafi wannan da ya Ahmad zaiji tabd'ijan dakuwa zaki yabawa aya za'kinta wallahi dan banga me ceton ki a hannunsa ba kuma maybe karshen wasan ya aureki d'in yaga ya zaki"? Ta'be baki Baby tai tana cewa tace.

"Humm Aunty Khairat daina fad'a kar wasa ya zama gaskiya nikam bana fata idan iya dukana zaiyi da sau'ki d'aya kenan ai a misali yaji nace dana aureshi gara na auri almajiri kuturun ubancan wallahi inaga farfesu na zaiyi duka kuwa saiya sa wannan jikin nawa ya zama kamar gwanda tsabar nuna shin da zaiyi kawai Aunty Khairat mubar wannan wasan 'kwai'kwayon please kije kiyi wanka mu tafi kar lokaci ya qure mana".

Mi'kewa Khairat tai tana cewa "aiko dai kinyi gaskiya dan wannan maganar tawa tayi kama da tatsuniya bari nazo muje kinga ma maganar da muke naso sha'afa sweetheart yace idan munje nai kiransa zaiyi magana da Addah" ta fad'a tana wucewa da kallo Baby tabi bayanta tana murmushi wato ita kuma auren gida take so "humm ya Shadad d'an uwan ya Ahmad wajen zafin rai da iya dila mutum" ta karasa maganar tana sau'ke numfashi har taso 'kwaruwa musamman tuna cewa da Khairat tai wai ko Ahmad ya aureta kamar sake maimaita maganar akai haka ta zabura tana girgiza kai tace "ina wannan fad'a ce kawai auren gida for me never Allah ya kiyaye min wannan 'kaddarar ta sameni" saboda ta daina tunanin maganar da sukai ma yasa ta d'auko littafin da Ahmad ya bata ta bud'e tana dubawa kafin Khairat d'in ta fito su tafi..........................
MRS ÄL'ÄMËËÑ ÄHMÄD ÇË 🌹.

Manzon Allah Saw
Aminci ga muftahul jannatun naimah
Aminci ga kiblar bayi a ran qiyama
Aminci ga Mai shiryarwa cikin salama
Aminci ga duk Mai matsayi dakai ya samu
Aminci ga duk Mai girma dakai ya samu
Aminci ga duk Mai daraja dakai ya samu
Aminci ga fatuhul Akbar aya imamu Yusrah Musa ce tare dani da gaisuwa ta🙏
Ka tausayawa zuciyata naganka ko sau d'aya a rayuwata.

Thanks for ur supports 🔥 nagode masoya ana tare insha Allah.

TYPING📲YMA DUTSE NEW WORLD 🌏 YUSRAH MUSA ABUBAKAR ✨✨💯.


👑 Royalty 👑


A*W*A
ANNURI WRITER'S ASSOCIATION 💫
Home of hospitality and harmony gidan kar'bar mutane hannu biyu da zaman lafiya ÀÑÑÙRÌ haske le'ka gidan kowa koda ma'kiya na kallon ka ramin kura sai'ya'yan ta haka taken mu yake tafiyar mu babu rago babu maci amana tsantsan gaskiya muke nunawa.

STORY WRITTEN ND EDITING
✍️ YUSRAH MUSA ABUBAKAR
Mrs Äl'ämëëñ Ähmäd çë 🌺.


6~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Taibanah.

Bismilllahir Rahmanur Rahim 📿

@YUSRAHMS CE
Page 11 & 12
Tsabar yadda Baby tasa tafiyar Ahmad a ranta har mafarki tai wai ya tafi kuma harda su a rakiya saida asuba bayan sunyi sallah sunyi karatu Baby ta kalli Khairat dake shirin komawa ta kwanta duk da gari yayi haske sosai tace "Aunty Khairat kinsan wani abu? Kai Khairat ta girgiza tana kallon ta itama taji wanne irin mafarki tai harda tashi zaune tana gyara zama tace "ina jinki wanne irin mafarki kikai"? Kai Baby ta jinjina tana cewa "uhm inji me ciwon baki abun ba'a magana waifa mafarki nayi wai ya Ähmäd ya tashi tafiya mune 'yan rakiya" d'an zaro ido Khairat tai tana sakin dariya tace "tabd'ijan ahh dole kice ba'a magana wannan lamari yafi karfin mu wane mu" mi'kewa Baby tai tana cire hijab d'in jikinta ta aje tana cewa "um gane min hanya Aunty Khairat indai ba mu 'ka'kalowa kanmu dukan ban kwana ba mezai kaimu inda ya Ahmad yake randa zai tafi musamman idan ya sako kayan soldier d'in nan nasa wani irin kwarjini yake ko daga nesa na hangoshi da gudu nake 6uya kamar naga abun cutarwa haba gaskiya ya Ahmad yana lokaci muna shan kallo yau dai zamu huta please Aunty Khairat karki manta da partyn da zamuyi" Baby na rufe baki cikin tsokana Khairat tace.

"To zamuyi party amma saidai yanzu muje muyi masa sallama".

"Wa zamuyi wa sallama amma dai ba ya Ahmad ba"?.

"Shi mana ba shine zaibar masarautar ba".

"Amma da wasa kike Aunty Khairat mune zamuje yiwa ya Ahmad sallama aiko daya sallamar damu".

"No babu abinda zaiyi mana shima yau yana busy bazai bi takanmu ba tashi ma muje maybe muyi masa rakiya damu".

"Dawa za'ai rakiyar? Amma bada niba wallahi bazanje ba nida ya Ahmad saidai idan ya dawo na ganshi amma banda yau".

"Idan baki tashi munje ba baza muyi partyn ba" Khairat ta fad'a da serious face kamar gaske ta d'auka Babyn idan taji haka zatace suje sai taga ta kwanta a kusa da ita tana cewa "a fasa kawai indai sai naje gurin ya Ahmad da muyi kawai a barshi yafi" dariya Khairat tai tana cewa "humm ai baki iyaba Baby da kince ni d'in naje ni kad'ai nima fa ba iya zuwa zanyi ba kawai Ina tsokanarki ne ban fad'a miki ba tun a jiya ya Shadad ya turo min kud'in da zamuyi partyn dashi amma baisan partyn murnar tafiyar ya Ahmad bane 'karya na sharara masa ya turo min" baby dake lullu'be tace.

"Oh kice zamuyi kenan"?.

"Kwari zamuyi dan tun a jiyan na baiwa ya Hamid kud'in na fad'a masa abubuwan dazai sayo mana idan ya fita kinsan mu baza'a barmu muje ko'ina ba daga school sai gida".

Tashi zaune Baby tai tana cewa "amma gari fa ya waye haske ya fito sosai nasan maybe yanzu ai ya tafi mu tashi mu tafi part d'in Momy nifa yau da yunwa na tashi domin jiya da dare banci abinci ba iya fab-choculate d'in nan naci dan Allah Aunty Khairat tashi muje amma idan zamu shiga mu tsaya mu saurara tukuna kar muje mu fad'a muga Yaya boss" tashi Khairat tai tana dariya tace "tab kina fad'ar haka na hasko wata mugunta ace muna zuwa kofar parlon Momy kin bud'e zaki shiga ni kuma na turaki ciki da 'karfi kuma ace ya Ahmad d'in yana parlon a zaune" bud'e baki da ido Baby tai tana komawa ta bayan Khairat tace "please kar kiyi haka indai ba so kike yau nayi wunin zazza'bin wahala".

"Ai dama bayi nace zanyi ba misali nayi miki".

"Misalin jinsa nayi kamar gaske shiyasa nima nace haka" daidai sun karasa bakin kofar part d'in Momy basu shiga ba saida suka tambayi masu tsaron kofar ko Ahmad yana ciki sukai musu albishir cewa shikam tun asuba yabar masarautar nan prince Hamid ne yayi masa rakiya jin wannan daddad'an labarin yasa da gudu suka bud'e kofar suna shiga ko jira a bud'e musu basuyi ba Momy tana zaune ita kad'ai sai gani tai sun fad'a mata da gudu suna zama suka saka ta a tsakiya kowa na fitar da huci da mamaki take kallonsu da ace Ahmad yana nan sai tace ko shine ya korosu suke irin wannan gudun tashin hankalin to yanxu kuma da baya nan lafiyarsu kalau kuwa..............

Katse mata tunani Khairat tai har lokacin numfashinta bai dawo daidai ba tace "Momy ya Ahmad ya tafi ne ko yana nan"? Tun kafin Momy ta bata amsa Baby tace "Momy wai ya tafi inji securities d'in dake tsaye a bakin kofar part din nan haka ne"? Murmushi tai tana kallon su tad'an girgiza kai tana cewa "ok shine dalilin da yasa kuka shigo a haukace saboda kunsan me gyara ku baya nan ko"? Daidaita numfashi Baby tai tana cewa "da alama ya tafi kenan Momy"?.

"Eh ya tafi ko wani abu zaku bashi irin wannan nema haka nasan idan yana nan ba haka kuke ba yau kuma saboda kun tabbatar baya nan shine kuke tambayar sa"?.

Kai Khairat ta girgiza tana cewa "a'a Momy ba haka bane kawai dai mun tambaya ne amma tunda ya tafi munji dahir masha Allah da sau'ki Allah abun godiya sabuwar rayuwa ta dawo heheheee shagaliii yau zamu shana" jinjina kai Baby tai tana cewa.

"Humm wallahi yau yadda kika san sallah Aunty Khairat haka nake jin farin ciki har wata sabuwar sansanyar iska ce take ratsa ni da Yaya Ahmad ya fita daga masarautar nan shikenan kuma mun huta kafin ya sake dawowa ya sake sakamu a gaba" murmushi Momy tai tana cewa "wato a gabana kuke farin ciki da tafiyarsa ko? d'ana nefa bakusan yadda ni kuma nake jin kewarsa a raina ba amma kunzo kun sakani a gaba da maganganun ku wannan ai saiku sani kuka" tana rufe baki duk su biyun suka zaro ido da sauri Baby ta girgiza kai tana cewa.

"Please Momy kiyi ha'kuri dan Allah ya Ahmad d'in ne ba'a iya masa wallahi muma ba'a son ranmu muke masa hakan ba dole tasa saboda irin hanamu sakewar da yake".

"Ai idan ma yana nan ba hanaku sakewa yake ba kune kuke Hana kanku duk tsiya idan bakuyi laifi ba bazai dake kuba".

Ha6a Khairat ta ri'ke tana kallon Momy tace "Eh haka ne Momy amma wallahi ba mu bane muke hana kanmu ba muna son mu ri'ka wargi baya barinmu saidai yazo ya tsare gida yadda motsin kirki bazaka iya yi ba yayita muzurai yana hahhad'e rai wai shi ala dole soja haba jama'a wannan matarsa zata sha wahala indai akace itama irin takurar mu zai nuna mata".

"Kwarai Aunty Khairat idan yace d'auko min ruwa me sanyi saita d'auko tun kafin ta karaso zaice bamai sanyi ba ta mayar ta d'auko masa d'an tsakatsaki ko marar sanyi dan naga alama ya Ahmad koba nefa caji yake yanzu zaisa mutum yai shokin da tashin hankalinsa" Baby ta fad'a tana maida fuskarta kalar tausayi dariya Momy tai tana cewa.

"Lallai wato saboda kunga baya nan yayi nisan kiwo shine kuka zauna kuka kafa gulmarsa ko aiko indai mukai waya saina fad'a masa duk abinda kuka fad'a a kansa har qari sai nayi".

Yarfa hannu Baby tai tana ri'ko hannun Momy tace "Innalillahi dan Allah Momy karki fad'a so kike ya d'auki hutu saboda mu akan wannan maganar ya dawo gida yaci ubanmu ya koma kenan" kai Momy ta girgiza tana murmushi tace "a'a bazai dawo gida ba saboda daku saidai tunda ba nisa yayi ba zaisa a saka masa ku mota a kaiku inda yake yaci 'kaniyarku acan son ransa sannan yasa a d'auko ku a dawo daku gida" Momy na rufe baki Baby tace "a wuce damu asibiti dai ya Ahmad d'in ne zaisa a kaimu har inda yake kuma hukunci zai bamu harmu dawo mu samu damar iya cigaba da rayuwa batare da munga likita ba tab uhmm Allah dai ya rufa mana asiri.

"Amin Khairat tace tana cigaba da cewa "ai Baby ko zamu samu d'an hutu da sassauci a gidan nan maybe sai yayi aure kila ko muma ma huta dan ko 'ya'yan bayi bazamu fad'awa hutu ba tunda su babu wanda yake takura musu mu kuwa fa kullum kana ankare sai kace wanda kake filin ya'ki Allah yasa daya dawo gida yayi aure kawai a wuce gun".

Da sauri Baby ta d'aga hannu tana cewa "Amin ya Allah Aunty Khairat Allah yasa yayi auren nan da wuri indai hakan zaisa hankalin mu ya kwanta aidai dole zai rage matsa mana lamba yana part d'insa zai rage zirga-zirga a gurin Momy da part d'in Mami ta Nan zamuji dad'in abun" dariya Momy tai tana kallon Baby datai maganar kawai ta girgiza kai domin tasan akwai guguwa a gaba duk ranar da Baby ta fahimci Ahmad ita yake so kuma ita zai aura wai za'a kwashi 'yan kallo bata jin hakan zaizo da sau'ki sau'kin d'aya tunda Abban Baby din Sultan Ashraf ya hana yace kada a sanar mata sam a rabu da ita suje a haka iya daga ita sai Khairat sune basu sani ba amma kowa ya sani daga Momyn har Abba da Mami su Sultana Addah da Sultan Sharfaddeen mai martaba duk sun sani.................

"Momy" Baby ta fad'a ganin ta fad'a tunani dawo da kallonta Momy tai kan Babyn tana cewa "na'am" "tunanin me kike yi zamuyi breakfast"? Kaita d'aga tana cewa "ok kuje dinning man kuci tunda naga ku bakwa son masu aiki suyi serving d'inku ko meyasa oho" mi'kewa sukai Khairat na cewa "saboda tsaro Momy gara hakan kinga nan gaba a gidan mazajen mu mun riga mun saba da kanmu zamuyi nikam girki ma dan baza'a barni bane da yanzu Ina zuwa kitchen ina ganin yadda akeyi na koya amma duk da hakan alhamdulillah tunda wata rana muna fakar ido mu shiga kitchen d'in Mami mu d'an girka wani abu idan mukai searching muka gani".

Basu dad'e da zama a dinning ba prince Hamid ya shigo yana aje musu kayan da Khairat ta fad'a masa ya sayo musu baisan me zasuyi ba yana zaune suna zance da Momy yaga sun fara gyara gurin suna hura balloons suna d'aurewa ga cake da suka aje d'an karami mai kyau anyi masa kwalliya a jiki an rubuta happy valentine day da mamaki ya kalli Khairat yana cewa.

"Ummul-khairi wai wannan d'in na mene naga dai yau ba ranar valentine day bane ku kuma na me zakuyi"? Dariya Khairat tai zatai magana Momy tace "murnar tafiyar Ahmad suke shine harda had'a walima a gabana kuma na fad'a musu ni d'ana ne kewar tafiyarsa nake ji kamar nayi kuka su kuwa farin ciki suke gashi nan ka gani har party zasu had'a kuma a gabana" da sabon mamaki prince Hamid ya sake kallonsu jin abinda Momyn ta fad'a yana cewa.

"Oh duk wannan murnan tafiyar Ahmad ne lallai kun kyauta amma meyasa bakuyi jiya ba kuka bari sai yau a gabansa ya kamata kuyi ya gani amma kwazo kuna ihu bayan hari mu amfanin me zaiyi mana ko taya ku zamuyi"? Ya tambaya yana kallon dukkan su biyun Baby da take jera grapes da yankakkun Apple red and green tana yiwa cake d'in kwalliya tace.

"Yaya Abdul-Hamid murna ta zama dole yau sabuwar rana ce a garemu zamu sha shagali muyi komai muke so babu mai takura mana koda ya Ahmad ne ya dawo yau sai mun gwangwaje yasin" kai prince Hamid ya jinjina yana sakin murmushi yace "anya Baby idan Ahmad yana nan zaku iya yin wannan abun sannan yasan dashi kuke"? Cikin 'kwarin gwiwa Baby tace "kwarai ya Hamid zamuyi" ok kawai abinda yace mata bai sake magana ba Momy tana kallonsa ya zaro wayarsa ya fara daukarsu video batare da sun sani ba murmushi tai tana d'an sakin dariya wato yanxu kuma da zasu d'ago su gani maybe valentine d'in da baza ai ba kenan saidai suyita bada ha'kurin a goge videon murmushi prince Hamid yake yana ta tsokanar su suna magana duk basu san abinda yake ba har suka gama had'awa ganin zasu d'ago yai sauri yai saving yana aje wayar yace.

"Wow gaskiya cake d'in nan yayi kyau bari na dau'ki photonsa na d'ora akan DP (difi) d'ina ya fad'a yana d'auko wayarsa ya d'auka yana cewa "wannan valentine d'in ba iya ku kad'ai zakuyi ba harda ni saboda idan yana takura muku nima Ina jin babu dad'i idan kin fara Khairat ko ke ko Baby wata da kirani a waya" yana rufe baki Baby tace "ni ya Hamid bani da waya ya Ahmad ya hana na ri'ke yace sai nayi aure" ta fad'a tana zun6ura baki juyawa yai zai fita yace.

"Ok Ummul-khairi ki kirana".

"Tom" tace tana mi'kewa ta kalli Baby tana cewa "muje muyo wanka wannan abun dole saida kwalliya ina Sultan please mu kar'bo aron mp d'insa mu gwangwaje da ita".

"Mu fara yin wankan tukuna sai muje mu kar'bo maybe bazata wuce tana parlor ya sakata a caji ba dan shima yau ranarsa ce tunda ya boss baya nan muje mu fara shiryawa" wucewa sukai suka bar Momy ita kad'ai a gurin tana kallon yadda suka tsara abun nasu kamar masu yin birthday party a ranta tace "bari sai sun fara zan kira Ahmad video call batare da nayi magana ba yaga yadda ake party da murnar barinsa gida maybe idan yaga haka ya canza ya daina takura musu.

Wanka sosai su Khairat suka d'auka sun saka kaya iri d'aya an soke d'aurin kwali anyi makeup kowa da bayyanan nan farin ciki a fuskarta suka fito har lokacin Momy tana zaune wucewa sukai suna tafiya 6angaren Mami humm tun daga harabar shashin suke jiwo tashin kid'a kallon juna sukai suna dariya domin ko ba'a fad'a ba sunsan Sultan ne shima yake nasa partyn suna shiga kuwa suka ganshi zaune ga mp a gefe sai kad'a kai yake ganinsu yasa Mami tai murmushi tana qare musu kallo tace.

"Tofa 'yan matan Momy wato kuma Ashe kuna kan hanya inayiwa Sultan maganar ya rage qarar mp nan tayi yawa ku kuma wanka kuka d'auka kowa da kiwon daya kar'beshi kenan"? zama sukai Baby da har kamar tafi kowa jin farin ciki tace "Mami ba dole yau muyi tsalle mu jujjuya ba ya Ahmad ya fece ya bamu filin shan iska yau ranar gud'a ce muyi farin ciki muyi shewa yanzu ma mp Sultan muka zo mu ara zamuyi valentine a parlon Momy harda cake mukai saboda murnan ya tafi please Sultan bamu aro dan Allah" Baby ta fad'a tana mi'ka masa hannu bai
End Ads