kuka ko? Yayi kyau ku tashi ku fara kar'bar hukunci zakuga karshen azabata yau ku fara zaga min parlon nan da frog jump" yana rufe baki da sauri suka tashi kowa ta ri'ke kunne suka fara duk girman parlon da yawan kujerun sai sun zagaye su kuma babu hutu yana kallon su da yadda suka gaji amma yai banza dan yasa a ransa daga yau bazasu sake marmarin koda dariya bane idan ya tafi, suma a nasu 6angaren sun d'auka abun nasa da sau'ki amma sai sukaga baida alamar cewa su tsaya gashi Momy kamar bata part d'in har lokacin bata fito ba tsabar wahala kukan ma sun daina idonsu ya bushe.
"Ku tsaya".
Yana fad'a da sauri kowa ta tsaya a inda take tare dayin zama da6as suna mayar da numfashi tabbas sun sha wahala ko yanzu ya barsu sun azabtu mi'kewa yai batare daya kalli inda suke ba ya nufi hanyar fita yana cewa.
"Ku biyo ni".
Zaro ido waje sukai musamman Baby da taji cinyarta kamar ba'a jikinta take ba gashi harya fita mi'kewa Khairat tai da'kyar hajijiya na d'ibanta ta kalli Baby tana cewa "Baby taso mu tafi kinsan ya Ahmad yana da sauri maybe yanzu yaje part d'insu fa karmu jawowa kanmu duka bayan wannan azabar" numfashi Baby ta sau'ke hawaye na zubo mata zurr kafin itama ta rarrafa ta dafe kujera tana runtse ido da'kyar ta samu ta mi'ke kowa tana jan'kafa suka fita yadda suke jin ciwon jikinsu babu me iya sauri a cikin su dole sai a hankali suke tafiya har suka shiga part d'in nasa yana zaune sukaje da suka karasa inda yake kowa kasa dur'kusawa tai.
"Bazaku iya zama bane? Ya tambaya yana kallon su "ai bakuji komai ba kuma bakuyi nadama ba tunda har zanyi tafiya bayan kunsan waye ni dan rainin hankali har ku zauna kuna d'aura balloons da sayo cake kuyi party saboda mugu yabar gida ko? Yau kuwa zakuga mugu zanyi maganin ku" ya karasa maganar yana mi'kewa yace "ku biyo ni" kallon juna sukai a matukar razane yaufa sukam sun shiga uku ina kuma zai kaisu ina zasu sake binsa.........................
Sautin bud'e kofa ne ya dawo dasu hayyacinsu ganin ya bud'e ya fita suma suka bi bayansa garden ya shiga yana tsayawa a gurin fountain bai juyo ya kallesu ba yace "Khairat d'auko min boket guda biyu a bathroom d'ina minti d'aya na baki" jin abinda yace yasa Baby sake susucewa mezai saka su badai d'iban ruwa ba Allah yasa Khairat ta had'u da prince Hamid ya tambaye ta me zatai da boket ko Allah zai taimake su................
Ganin Khairat d'in ta dawo da botikan biyu a hannunta yasa Baby ta fahimci basu had'u dashi ba kawowa tai tun kafin ta ajiye yace "dau'ki d'aya ki baiwa Baby d'aya ku fara d'iban ruwa kuna bin flower's d'in nan kuna zuba musu ruwa yau sai kun wuni kuna watering idan tsautsayi yasa na dawo na tarar bakwa sauri ko kun tsaya hummmmnn" yana fad'in haka ya juya yabar gurin kallon juna sukai Khairat data dafe kanta daya sara tace.
"Mun shiga uku mune zamuyi watering din flowers yau innalillahi wa inna ilaihi raji'un wallahi a yanxu ma bakiji yadda nake jin jikina ba balle nazo nayita jidon ruwa ina bin flower d'aya bayan daya ina zubawa"? Numfashi Baby kawai ta sauke tana cewa "dan Allah Aunty Khairat mu fara karya dawo ya tararmu a tsaye kinsan halinsa abinda zaiyi mana bazai kyau ba" ta fad'a tana wucewa tasa boket d'in ta d'iba karasowa Khairat tai itama ta d'iba suka fara bi suna zubawa saboda tsoron kar yana kallon su yasa ko iya tsayawa basayi.
Ahmad kam kwata-kwata ma baya part d'in ya koma gurin Momy sunci gaba da maganar da suke kamar baisa su Baby komai ba itama Momyn bata tambaye shi inda suke ba duk zatonta ko lokacin data tashi amsa waya su kuma suka fita batasan suna can sun zama masu bayin fulawa ba ya 6ata lokaci sosai a gurinta kafin ya tashi ya koma part d'insu yana shiga ya bud'e kofar da zata kaishi garden ya fita tsaye yayi yana kallon su yadda duk suka bi suka ji'ke da ruwa Allah sarki bayin Allah babu wacce take iya magana a cikinsu kawai aiki suke cike da tsananin gajiya kaiya jinjina yana karasawa inda suke duk da haka basu lura dashi ba saida sukaji gyaran muryarsa a d'ari kowacce ta zabura suka juyo kallon tsaf ya sake yi musu kafin yace.
"Tunda na tafi iya abinda kukai kenan baifi guda d'ari kuka zubawa ruwa ba"? Jin abinda yace yasa kowacce mamaki ya kamata badan kar suyi 'karya ba sai suce duk flowers d'in dake garden d'in nan sun bata ruwa saidai wacce bata fito ba amma yace iya aikin da sukai kenan tunda ya tafi babu wanda tai zaman hutun minti d'aya a cikinsu saboda tsoron karya dawo ya same su...................
"Ok babu me iya bani amsa a cikinku saboda kun cika ko? Shikenan Kuci gaba da aikin dama aina fad'a muku yau wuni zakuyi kuna kar'bar punishment har dare ku d'ora inda kuka tsaya domin yanzu karfe d'aya da rabi tai" yana rufe baki Baby ta fashe da kukan tsantsan wuya da gajiya tana dur'kusawa a gabansa tare da had'e hannuwanta tace "dan girman Allah Yaya Ahmad Kayi hakuri ka yafe mana mun aikata kuskure wallahi tallahi bazamu sake ba dan Allah kayi ha'kuri" jin abinda tace maimakon ya kar'bi ban ha'kurin ta saiya sake had'e rai yana kallon Khairat wacce ke tsaye tana mayar da numfashi yace.
"Wato ke kinfi karfin ki bada ha'kurin ko? Yau kuwa bazaki bar garden d'in nan ba ke kwana zakiyi kina baiwa 'kananun tsirrai ruwa zakisan dani kike wasan............
Da gudu itama Khairat ta dur'kusa tana cewa "a'a wallahi ba haka bane Yaya Ahmad dan Allah kayi mana afuwa kayi ha'kuri wallahi mun dau'ki alkawari bazamu sake ba daga yau".
"Kuma sake man ina daidai daku nine maganin ku a gidan nan ku tashi ku 6ace min da gani" yana rufe baki suka mi'ke a susuce kowa tana neman hanyar gudu kamar zasu tashi sama fiiiiiiii haka suka fita da'kyar suka iya kai kansu part d'in Momy badon tsoron karya biyo bayansu ba dasun tsaya sun yiwa driver magana ya kawosu amma gara koda rarrafe ne suje a hakan da muguwar rawa gara 'kin tashi.
A gigice suka shiga suna huci kowacce ta zube akan kujera da mamaki Momy take kallonsu ganin babu me cikakkiyar nutsuwa a cikinsu tace ''ku kuma daga Ina kamar wanda kukai wasan ruwa duk kun ji'ke jikinku gashi kunyi wani iri kamar marasa lafiya daga ina kuke yanzun bayan zan shiga amsa waya na ganku kun shigo"?.
Kallon kofar shigowa Khairat tai zatai magana kawai saiga hawayen wahala da'kyar tace "Yaya Ahmad ne ya sakamu watering a garden tun d'azu da muka shigo bayan an kiraki a waya kin shiga part d'inki" da sabon mamaki Momy ta sake kallonsu tana cewa "ya sakaku watering kuma na tsawon wannan lokacin me kukai masa haka bayan shigowar ku part d'in kenan"?.
"Momy tsohon zance ne akan partyn da muka had'a na tafiyar dayai ne shine yace gaba ma mu sake yana daidai damu dan baki fito da wuri bane anan parlon ya fara saka mu tsallan kwad'o bayan mun gama ya kaimu garden mukai watering d'in".
"To Allah me iko akan haka ya sakaku wannan azabar kalli yadda kuka koma aini ban sani ba da yanzu naje na taho daku kuma Abdul-Hamid ma inaga baya nan shiyasa da ace yana nan bazai bari kuyi watering ba tunda kuba gardener bane gashi ya saka min ku shan wahala musamman ma ke Baby kalli yadda kike rawar d'ari ko magana kin kasa gara Khairat d'inma da d'an sauran 'karfinta ku tashi ku shiga bedroom kowa ta cire kayan kuyi wanka da ruwa me zafi sosai saiku fito ku had'a tea kusha zaku samu d'umin jiki sosai tashi kuje" mi'kewa sukai kowa najan kafa suka shiga part d'insu da'kyar sukai wankan amma a cikinsu babu wacce ta samu damar fitowa tasha tea d'in balle suci abinci duk kwanciya sukai ganin shiru basu fito ba yasa Momy tashi tabi bayansu data bud'e kofar bedroom d'insu ganinsu a kwance yasa batai magana ba ta mayar ta rufe flask ta d'auko ta dawo tana had'a musu ta baiwa kowa sannan ta koma ta sake had'o musu abinci ta kawo tasa su gaba saida sukaci Baby kam tuni zazza'bi ya rufeta sosai Khairat d'in ma jikinta yad'au zafi kamar wuta ganin haka yasa ta d'auko musu magani kowa ta 6alla tasha suka tashi sukai sallah a daddafe domin tafiya ma ko d'an kaciya bazai fad'a musu ba haka suke takawa sunayin sallar kuwa suke sake kwanciya kowa idonta biyu amma bamai magana a cikinsu saidai saukar numfashin juna kad'ai suke ji a haka har akai la'asar da magriba da isha duk saidai su tashi suyi sallah kawai su koma kwanciya babu wacce zata moru a cikin su dai a wannan ranar.
Ahmad kam bai sake shigowa part d'in Momy ba sai wajen qarfe tara da rabi yana zuwa kuwa ta balbaleshi da fad'a sosai ta nuna masa bai kyauta ba abinda yayi musu da nasan suna part d'insa lokacin daya dawo suke magana wallahi da taje ta taho dasu kashe mata 'yan matan nata yake son yi ko kuma yaya dazai ri'ka basu wahala haka Ahmad dai shuri yayi yana sauraron ta saida takai karshe ya bata hakuri ya nuna bazai sake irin hakan ba kafin ya mi'ke yana fita a part d'in ya koma nasa ya d'auko alluran zazza'bi ya dawo Momy bata parlor direct part d'in su Khairat ya shiga suna kwance kowacce tayi barci kunna fitilar wayarsa yayi yana haskasu ganin barci suke ya yaye bargon da suka lullu'ba yasa hannu ya dafa goshin Khairat yaji jikinta babu zafi site d'in da Baby take kwance ya koma itama ya dafa nata goshin kamar na Khairat d'in itama zazza'bin ya sauka mayar musu da bedsheet d'in yayi yadda yake ya rufesu yana fita a part dama so yake yaji inda me zazza'bi yayi musu allura karsu kwana da zafin jiki amma tunda duk ya sauka shikenan nan..............✍️Mrs Äl'ämëëñ Ahmad ce.
TYPING 📲Tue, Apr 1/25 10:00AM
YUSRAH MUSA ABUBAKAR 🤘💯.
👑 ROYALTY 👑
ANNURI WRITER'S ASSOCIATION 💫
Home of hospitality and harmony gidan kar'bar mutane hannu biyu da zaman lafiya ÀÑÑÙRÌ haske le'ka gidan kowa koda ma'kiya na kallon ka ramin kura sai 'ya'yan ta.
••••Dedicated to my blood••••
SALEEM MUSA ABUBAKAR
NAJA'AT MUSA ABUBAKAR
FATIMA MUSA ABUBAKAR
AISHAT MUSA ABUBAKAR
ABUBAKAR MUSA ABUBAKAR
√Wannan page din naku ne yan uwa rabin jiki Allah ya bamu ha'kurin rashin mahaifin mu ubangiji ya gafarta masa yayi masa rahma ya haskaka kabarinsa.
ANNABI SAW
Annabi farkon kasantattu wallahi ubangida ba danka ba daba abinda zai wanzu.
Da sunan Wanda ke rayuwa me tasiri darai dubba ma'kagin duj abunda baza'a kirashi da rabbi Allah ba nagode ma da sigar dazan banma ko furta uffan ba da kaban iko nake wake wanda kace kadarinsa ya wanzu.
10~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Raki'inah.
@YUSRAHMS CE
Page 19 & 20
Duk wani shiri da Hajiya Khubura zasuyi na biki sun gama Daddy yana shan kallonsu baice musu komai ba iya abinda ya kamata ace yayi matsayin sa na mijin Hajiya Khubura kuma zatai auren 'ya ya bata gudun mawa me yawa sosai da kud'i da kayayyaki a take ta saka kud'in cikin account d'inta sannan da wayo ta sake fad'a masa cewa abubuwan da zatai bata gamaba kud'in sun qare ya sake mata transfer wasu a take murna kuwa harda rawa.
A 6angaren Nadiya masai gyare gyare ake kullum ba zama ita da Abidah suyi nan suyi can khaleel kuma baya gidan kwana biyu yaje gidansu sai daren d'aurin aure zai dawo domin fushi ya d'auka da Hajiya Khubura ya fad'a mata yana son a had'a aurensa da Ayrah dana Nadiya tace a'a shi ba yanzu ba akan haka yai yaji ya tafi ko kiranta a waya bayayi idan ta kirashi baya d'auka karshe dole ta 'kyale shi tasa a ranta duk inda ya tafi ma yana gama hucewa daga fushin zai dawo ya sameta tana zaune itace ta haifeshi ko shine ya haifeta dazai ri'ka juyata kamar wata uwar wofi.
Yadda gabadaya suka d'au busy yasa yanxu Ayrah tad'an samu hutu basa bi takanta suna harkokinsu basa sakata aikin komai ko wata takura kowacce rana da inda zasu je basa samun wuni a gida ita kuwa koda yaushe tana bedroom d'inta idan kaga ta fito tofa saidai idan kitchen zataje ta d'ebo abinci ko kuma zatai wani aikin amma haka kawai dai bata fitowa gudun karma su ganta suci gaba da azabtar da ita daga inda suka tsaya addu'a take kullum ba dare ba rana tana fatan Allah ya baiwa Abidah mijin aure itama ta samu tabar gidan tasan ko iyasu ta rabu da jarabarsu zata huta saura khaleel shiko tunda namiji ne babu inda zaije saidai tai addu'ar neman tsari daga sharrinsa dan tunda dad'ewa ta gama karantarsa da halayensa d'an iska ne iya kallon da yake mata ya isheta hujja.
****Mama batasan Ahmad ya dawo gida zaiyi uziri na d'an wani lokaci ba saida sukai waya da Momy take iyota tana tambayar ina Ahmad soja marmari daga nesa Momy take fad'a mata ai ya dawo gida ma zaiyi wani abu ne amma dai ba wata dad'ewa zaiyi ba zai koma hum jin haka yasa tunda suka gama wayar Mama ta kasa nutsuwa tasa tunanin ta waje d'aya sai kaiwa take tana komowa ta kira Maryam a waya yafi sau goma bata d'aga ba kamar tai kuka sai huci take tana cizon yatsa ta yarfa hannu ta le'ka harabar gida tana cikin wannan yanayin Maryam ta dawo daga school tana shigowa ganin yadda Maman take a hargitse yasa ta dakata tana cewa.
"Mama lafiya na ganki haka wani abune ya faru"? Tsayawa guri d'aya Mama tai tana sau'ke numfashi tare da girgiza kai tace "Maryam me kike kallo ne Anya burinmu zai cika kuwa kin tsaya wannan sakarcin ace ni harna fiki damuwa da saka abun a rai inaga kullum sai nayi mafarki akan haka amma naga ke ko a jikinki haba Maryam kinyi hauka ne so kike kisa hawan jini ya kamani"? Cikin rashin fahimta maryam tace.
"Ban gane ba Mama dan Allah kiyi min bayani yadda zan fahimci inda kika dosa me nayi ne bansan akan me kike magana ba kin sakani a duhu'.
Zama Mama tai tana had'e hannunta guri d'aya ta dafe goshi tana cewa "magana nake akan Ahmad ya dawo yau kusan kwanansa shida amma ban samu labari ba sai d'azu Aunty ta kirani kamar wasa nake tambayar sa dan naji yaya sai tace min wai ya dawo zaiyi wani uziri ne ya koma".
Zaro ido Maryam tai tana cewa "ya dawo kuma Mama da gaske ne yanzu yana gari yana masarauta idan naje zan ganshi"?.
"Yana nan man tunda kikaji ta fad'a nikam indai a haka zamu tafi bana hango nasara a tare damu".
"A'a Mama ba haka bane nifa bansan ya dawo ba amma yadda nake sonshi kinsan bazanyi sanya ba yanzu ma lokaci bai 'kure min ba a raina nasa saina auri Ahmad kuma insha Allahu saina aureshi na zauna dashi na har abada koda ace mata uku yake dasu indai ya amince min zan yarda na shiga matsayin ta hud'u" Maryam na rufe baki Mama tace "ai Maryam ko mata hud'u ne dashi yace yana sonki wallahi sai kin aureshi inyaso saiki zauna matsayin 'kwar'kwara nidai damuwata kawai ki aureshi ace 'yata ta cikina dana haifa tana auren jinin sarauta an gama magana hakane burina".
"To amma Mama ya zanyi kinsan fa dole sai nad'au salo sakamakon nasan halin Ahmad tunba yauba akwai rainin wayo magana ma idan kikai masa sai yaga dama zai amsa miki balle naje a fuskar sonsa nake da aure duk ranar daya fahimci hakan nasan zansha wula'kanci ba 'karami ba" ta'be baki Mama tai tana kallon yadda Maryam d'in tai shiru tana kallon guri d'aya alamar tunani tace.
"Idan kin sone zai wulakanta ki sabida kince kina sonsa bai isa yace zai nuna miki gadara ko wani abu ba shifa namiji ne duk matsayin sa da mu'kaminsa dole ya lallashi mace ya lalla6ata kamar 'kwai koda ace itace ta fara cewa tana sonshi kin gane"? Kai Maryam ta jinjina tana cewa "eh Mama na gane to amma yaushe zanje"?.
"Yau mana Maryam dake nufin ki sai yaushe zakije saiya tafi kome haba Maryam anya kina jin yadda nake ji a raina kuwa inaga harna fiki shiga damuwa da son naga wannan abun ya zamu gaskiya bari kiji ko barci bana iya samu nayi cikakke me kyau saboda saka abun a raina danai nida nake ta dakon dawowarsa dama kamar na jawo iya adadin dad'ewar da zaiyi acan ya dawo haka nake ji tashi ki shirya yanxun nan ki tafi kawai karki d'ebi kaya masu yawa saboda kar aga haukanki ki dau'ki ko kala biyu ma" mi'kewa maryam tai tana cewa "ok bari naje na shirya" ta fad'a tana wucewa ko tsayawa wanka batai ba iya kayanta ta d'auko ta sauyo mayafi ta fito har lokacin Mama tana inda ta barta ganin ta fito yasa ta kalleta baki bud'e tana cewa.
"Na shiga uku Maryam ya haka tun daga yanxu zaki fara kuskurewa"? Kallon jikinta Maryam tai tana cewa "mena kuskure "? Fuskarta Mama ta nuna tana cewa "a haka zaki tafi gidan kamar wacce take takaba ko d'an kwalli babu balle jan baki ko powder? aiko indai haka xakije kiyi wallahi Ina me baki albishir ko kallonki Ahmad bazai ba dole sai kina d'aukar wankan kece raini wanda idan kika fito baisan lokacin dazai biki da kallo ba ki ri'ka karya harshe wajen magana idan kinga yana kallonki ko hankalinsa yana kanki ki ri'ka abunda zaki burgeshi idan kun kad'aita ku biyu kiyi iya kokarinki ki nuna masa 'yar wata alama dazai fahimci kina sonsa ko baki furta ba ya sani daga nan idan mukai sa'a saidai kiji yace yana sonki".
Murmushi Maryam tana hasko irin yadda zataji a ranta duk ranar da taji Ahmad ya furta Mata kalmar so humm ranar