x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 19 - ROYALTY YAN SARAUTA

  • 54001 words
  • 57000 words
  • Out of 85109 words

Category: Love Stories

Views 1689

20 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
ta faru ba zan kira Auntyn nida kaina na fad'a mata dalilin zuwanki gurinta sai naji me zatace zata goyi bayan abinda nace ko bayan d'anta zata bi indai ta nuna abinda yace shine take kai hum'um heyyy dan'kari akwai hayaniya a gaba da tashin hankali indai akace yaron nan ya'ki na'am da auren Maryam harna hasko ya'ki da guguwar da zata faru matukar bata umarci Ahmad ya aureki ba Maryam bari dai Allah ya kaimu goben ayi wacce za'ai'' ta karasa maganar tana fitowa daga toilet ta goge gumin datai kafin ta fita ta koma part d'in Abba ta d'auka zai sake mata magana akan kiran da Maryam d'in tai mata sai kuma taga bai tanka mata ba shiyasa tana kwanciya tai saurin komawa barci saboda karma abun ya ciyo zuciyarsa ya sake mata tambaya akan haka.

•°•°•°+°•°•°•
Sanin da khaleel yayi yanzu Aiman baya 'kasar kome zaiyiwa Ayrah babu me d'aukar mataki a kansa yasa gabadaya yabi ya matsa mata iskancin yau daban na gobe dabam yakai da hatta muryarsa idan Ayrah taji gabanta ya ri'ka fad'uwa kenan tun ranar daya nuna mata cewa ga abinda yake so ta amince masa ta bashi kanta zaiyi mata komai ta'ki shikenan tun daga sannan ta sake tsanarsa take jin mugun tsoron sa batasan kad'aituwarsu guri d'aya koda yana tare dasu Hajiya Khubura ne balle kuma ace gata gashi iyasu biyu ji take kamar numfashinta zaibar jikinta tsabar firgici da take tsintar kanta a ciki kullum bata samun isasshen barci saboda shi wani lokacin kamar aljani har batasan ta inda yake shigowa bedroom d'inta ba kawai saidai ta ganshi.

Yauma kamar koda yaushe haka ya shigo mata d'aki cikin dare saiji tayi ana ta'ba mata jiki a firgice ta farka tana tashi zaune zatai ihu ya d'ora yatsarsa saman bakinsa yana cewa "shittt kiyi shiru ba wani abu bane ba wani abu zanyi miki ba kin gane nine fa Khaleel nazo taya ki kwana ne kawai big girl ba wani abu ba" ya fad'a yana shirin zama a gefen gadon zaro ido waje Ayrah tai zuciyarta na bugawa da 'karfi muryata na rawa ta matsa baya da sauri saboda saura kad'an ya zauna akan cinyarta kuma yana sane yai hakan a susuce hawaye yana zuba mata tace.

"Dan Allah ka fita min a d'aki niba 'yar iska bace kamar yadda ka d'auke ni bana son ganinka khaleel wai me kakeyi haka ne? nayi maka kama da irin 'yan iskan matan banza da zakace kazo taya ni kwana ni bana bu'kata ka fice min a d'aki domin ban kasance 'yar iska kamar yadda ka d'auke niba" tana rufe baki ya saki dariyar nuni da cewa abinda ta fad'a nishad'i kawai ya saka shi yana kallonta yace "oh me kike nufi waye d'an iskan kenan nine"? Shiru tai a razane tana kallon yadda yake binta da wani mayen kallo ganin bata bashi amsa ba ya mi'ke daga zaunen da yake yana nufar kofar bedroom d'in ya sanya mata lock kafin ya juyo yana cewa "nan da gari ya waye babu wanda zaisan tare muka kwana da asuba zan fita na koma bedroom d'ina kinji zan baki duk abinda kike so kud'i gida mota ko yawon sha'katawa kike bu'kata da kaina zan kaiki duk 'kasar da kikace kina son zuwa komai fa da kike so babu ce kawai bazan baki ba itama da ana ganinta wallahi zan baki saboda ta ko'ina kin cika mace kalli 'kirjinki a cike sai she'ki suke cikin kyakkyawar rigar barcin ki kalli fararen cinyoyinki dubi dogon wuyanki kalli le6an bakinki masu taushi da kamshi wayyo Allah Baby kin had'u fa musamman yanzu dana tsaya ina kare miki kallo babu manyan Kaya masu rufe surarki wash Baby kin tada hankalina wallahi kalleki komai a wadace dubi hips d'inki oh my God please Baby taho guna I love you" ya fad'a yana bud'e mata hannuwan sa alamar tazo gareshi qara matsawa baya Ayrah tai tana 'kan'kame jikinta tare da sakin kukan damuwa da ba'kin ciki musamman yadda taji yana lissafa tsarin halittar jikinta ji tayi kamar ta dau'ki wu'ka ta da6a masa ya mutu kota huta ganin dayai ba daina kukan zatai ba yasa ya baro bakin kofar da yake yana tahowa gurinta dur'kusawa tai tana sake fashewa da wani mayataccen kukan tace.

"Dan girman Allah khaleel karka ta'ba ni ka barni dan Allah" ko sauraron ta baiyi ba balle yace tana masa magiya bare ya ha'kura sai kanta da yazo yana saka hannu ya ri'ko nata hannnun zai mi'karta tsaye taga yana shirin ta'ba breast d'inta da qarfi da make hannunsa zata fasa 'kara ya hanata ta hanyar toshe mata baki da tafin hannunsa du'kawa yai yana d'aukarta zai nufa kan bed da ita ganin idan tai sake fa gayan nan zai cika burinsa a kanta na ganin ya lalata mata rayuwa aiko yana direta tai saurin hankad'a shi tana mi'kewa da gudu ta nufi kofar fita bin bayanta yai yana zuwa ya sake dam'karta ihu ta zunduma masa da iya 'karfin ta wanda a d'ari Khaleel ya bud'e kofa ya fita da gudu yana fita Ayrah ta karasa kofar da gudu taje ta rufe jikinta na rawa da'kyar ta iya baro gurin ta dawo tana bud'e wardrobe ta dauko Kaya kawai tasa a jikinta ta ha'kura da kayan barci hakan zaifi mata alkhairi data bari ya lalata mata rayuwa a banza koda ta koma ta kwanta bata iya barci ba sai daga baya da yake barci 6arawo ne da'kyar ya d'auke ta batare data sani ba.

Khaleel kuwa tunda ya koma bedroom d'insa kasa nutsuwa yayi ko zama bai iya yiba balle shi ya samu damar komawa barcin sai zaga cikin filin bedroom d'in yake yana goye da hannu a baya babu abinda zuciyarsa take hasko masa sai surar Ayrah tsabar jaraba da yasa a ransa har wani sid'ar baki yake kamar me shan minti can kuma ya dam'ke joystick d'insa daya mike tsaye da qarfi yana runtse ido tare da cije lips yace.

"Ohhh Baby zaki kisa a gidan nan indai baki amince min ba na rantse bazan barki ba sai nasha kalar d'and'anon za'kin da kike dashi daga ganinki zaki ni'ima dad'in ki wane zuma a baki dole nema ki amince min ko bakya so" ya karasa maganar yana bud'e ido ya kalli yadda har lokacin joystick d'in nasa yake mi'ke huci me zafi ya fitar yana cewa.

"Bazan iya barci ba bazan iya ha'kura dake ba Baby dole na koma zanyi amfani da abinda dole ki amince min batare da kin sani ba komai zai faru nayi alkawari yau bazan rabu dake ba saina cimma burina a kanki" ya karasa maganar yana bud'e drawer ya d'auko wata kwalba ya kalla tare da jingina harda sakin murmushin mugunta kafin ya bud'e bedroom ya fita yana komawa part d'inta amma kofar a rufe ruf babu yadda zaiyi ya iya shiga d'an kwankwasa mata yai a hankali saboda dare d'aukar magana yace.

"Baby please open the door" jin shiru ba'a amsa masa ba ya zagaya ya koma ta window yana zura hannunsa ya d'age labule ya ganta kwance a lullu'be ta koma barci dafe kai yayi yana sake kallonta ga 'koshi ga kwanan yunwa inama yadda tai barcin nan ace da kofar dazai shiga ko kuma d'azu ne yana zuwa shi kad'ai yasan inda zai fara ta'bawa ganin bashi da yadda zaiyi saidai kallo daga nesa yasa yaja tsaki yana barin windon ya koma bedroom haka yayita yawo yana son ya ragewa kansa zafi amma a banza har kiran sallar asuba a kunnensa tunani ne yazo masa yasan yanxu maybe ta tashi amma kuma yana tsoron kar Daddy ya fito ya ganshi bari yayi sai yaji an shiga masallaci zai lalla6a yaje kafin a fito yayi abinda zaiyi haka ya sharad'a a ransa amma yasan duk tsiya dole yaje masallaci shima idan baije ba Daddy yana dawowa zai tambayi meyasa bai ganshi ba tuna hakan yasa ya ha'kura kawai yai wanka sakamakon ya 6ata jikinsa ya tadawa kansa sha'awa a banza.

Ayrah kam da abun ta farka da daren abin bai dameta ba kamar sanda gari ya waye haka tayita kuka a bedroom ita kad'ai idonta ya zama jawur fuskarta ma haka ganin d'akinta yayi haske sosai yasa ta fahimci gari ya waye yadda zataje ta d'ora musu breakfast mi'kewa tai tana shiga toilet ta wanke fuskarta ta fito tad'au hijab tai parlor babu kowa dan haka wucewa tai ta shiga kitchen ta fara aiki sauri take ma saboda batasan haka rana ta fitoba saida ta fito yanxu ta gani gashi zataje school dole ta takaita abinda zatai musu saboda karta makara a gaggauce ta kawo musu dinning ganin babu wanda ya fito yasa ta koma part d'inta ta shirya ta dau'ki hijab da handbag d'inta ta fito gabanta ne ya fad'i lokacin da suka had'a ido da Daddy daidai sun fito shida Hajiya Khubura jiki a sanyaye ta karasa tana dur'kusawa har qasa tace.

"Daddy ina kwana"? Da'kyar ta iya karasawa muryarta na rawa shima kuma maimakon ya amsa mata sai tambaya daya jefo mata "ihun uban me kikewa mutane jiya da dare"? Jin tambayar dayai mata yasa a razane ta d'ago ba shiri tana kallon sa zuciyarta na harbawa da mugun 'karfi a tsawace yace "kallona nace kiyi ko amsa nake jira ki bani ubanme ya sakaki ihu da dare ki fad'a min tun kafin ki fusata ni na yanke miki hukuncin da baza kiji dad'insa ba" ya fad'a kamar zai kai mata duka yana zaro ido rai 6ace kuka Ayrah ta fashe dashi cikin tashin hankali ta d'ora hannunta aka tana cewa.

"Dan girman Allah Daddy kayi hakuri idan na 6ata maka rai ka yafe min bada sona nayi ihu dan na tasheku daga barci ba".

"Ok bada sonki bane to dason wa kikai ihun? Iye fad'a min dason wa kikai ihun nace ki fad'a ko saina mareki tukuna"? Ganin da Ayrah tai yana shirin kai mata marin da gaske yasa da sauri ta matsa baya tana girgiza kai zafafan hawaye suna zuba a idonta ta kasa magana ganin khaleel ya fito yasa a rud'e batasan lokacin data nuna shiba wanda a d'ari Hajiya Khubura ta zaro ido tana cewa.

"Kan bala'i lallai yarinyar nan wato sharri kike shirin 'kulla masa me kike nufi naga kin d'aga wannan mitsiyacin yatsan naki kina nuna shi nufinki shine ya saka ki ihun ko mafarkinsa kikai"? Kai Ayrah ta girgizawa tace "wallahi ba sharri zanyi masa ba kuma ba mafarki nayi ba a zahiri na ganshi da dare ya shiga d'akina wai saina bashi kain.........................

Cikin azama Hajiya Khubura ta gwa6e mata baki saboda karta 'karasa jin abinda take fad'a a masife tace "dan uwarki Khaled d'in ne zai shiga d'akin ki ubanme zaiyo miki wato saboda kin kawowa mutane 'kwarto gida kuma kinga asirinki yana Shirin tonuwa shine kike neman la'kawa khaleel 'karyar shine to wallahi bari kiji idan ma haushinsa kike ji nan gani nan bari babu yadda zaki dashi zama a gidan nan yanzu ya fara koda ace wannan mara kunyar Aiman d'in ne ya dawo bashi da bakin magana balle ke banza wacce ba'a mayar da ita mutum a gidan nan ba Kinga bangon nan ya fiki kujerar nan ta fiki takalimin 'kafatar me gadin gidan nan ma yafiki daraja a gurina wallahi kuma ki saurari gargad'i na a kanki duk ranar da tsautsayi yasa kika sake d'aukowa mutane 'kwarto cikin gida sannan kikece wai khaleel ne humm na rantse da Allah wallahi tallahi saina 'karya ki a gidan nan kuma na 6alla banza babu wani abu da wani ya isa yai min".

Allah sarki tsabar kukan da yaci 'karfin Ayrah har wata iriyar shid'ewa take numfashinta yana d'aukewa Daddy da ransa ya gama 6aci da maganar kwarton da yaji Hajiya Khubura tana ambata yace "harda kwarto kike kawo min gida Ayrah kwarto fa? Kneeldown Ayrah tai tana cewa "wallahi Daddy ka yarda dani ban kawo kowa gidan nan ba ni kad'ai nake kwana" tana rufe baki Hajiya Khubura tace "sannu sarkin musu 'karya akai miki kenan baki kawo kwarton ba tsana tasa mukai miki haka ko"? Kasa magana ayrah tai Daddy daya rasa abinda yake masa dad'i yace.

"Daga yau ta faru ta 'kare badai kin fara neman maza ba? To daki jawo min abin fad'a a gari gara nayi aurenki na huta koda me gadi ne ko kuma almajiri inyaso sai kije ki 'karata tashi kiba mutane gu kafin ki karasa kaini bango na miki duka a parlon nan" yana rufe baki Ayrah ta mi'ke jiki na 6ari ta fice daga parlon kallon Daddy Hajiya Khubura tai ganin ya shiga damuwa da yawa yasa ta saki murmushin jin dad'i a ranta tana she'ka dariya amma a fili sai tace.

"Kayi hakuri Alhaji karka saka damuwa a ranka toya za'ai 'yarka ce dai tariga ta zama kangararriya bazata ta'ba dawowa daidai ba abun da yafi sau'ki kawai shine kayi auren nata ka huta amma kasan dama na fad'a maka khaleel yace yana sonta fatan baka manta ba"?.

"Ba mantawa nayi ba amma taya zaki bar khaleel yaron karki me hankali da tarbiyya ya auri watsattsiyar yarinya irin Ayrah wacce ta riga tafi karfin mutane kawai ki 'kyale ya samu me hankali ya aura ita kuma zanyi magana da me gadi yanxu idan na fita ya bani sadaki zan d'aura musu aure satin sama" dafe 'kirji Hajiya Khubura tai tana girgiza kai da sauri tace "a'a Alhaji kar kayi haka babu komai shi khaleel d'in aiyasan halinta tunda ya zauna a gidan amma a hakan yace shi tayi masa yana sonta kuma zai aureta dan Allah Alhaji kar kayi wannan gangacin karka kar'bi kud'in me gadin nan indai sadaki kake so Khaleel zai tura maka yanzu" kaiya girgiza yana cewa "a'a tunda kince haka ki bari kawai mubu abun a sannu shikenan Allah ya shiryar da ita shi kuma dazai dau'ki 'karangiya Allah ya bashi hakuri da juriyar iya zama da ita".

Wani murmushi Hajiya Khubura ta saki tana kallonsa tace ''amin Alhaji Amin Allah ya amsa muje kayi breakfast lokaci yana 'kure maka a tafiya office" kaiya girgiza yana cewa "no barshi kawai idan naje can zanyi".

"Ok to muje na taka maka" ta fad'a tana sake gyara ri'kon kayan aikin dazai tafi dasu office takardu da wasu abubuwan suka fita saida taimai rakiya har jikin motarsa ya tada motar yabar gidan duk tana kallo sannan ta juyo da murnar kwanan nan zata zama millionaire a dinning samu khaleel da Abidah suna karyawa zama tai tare da sauke numfashi tana kallon sa cikin fad'a tace.

"Khaleel kai d'in ubanme yakai ka d'akin wannan yarinyar me kaje nema har take neman d'ora maka sharri kuma tsabar shashanci kana jinta kayi shiru da ace bana gurin yadda wannan yarinyar take da baki wallahi baka isa ka ceci kanka ba so'ko'kon banza sakalin wofi a ido kamar zakai zarra amma ina zuciyar a mace take".

Had'e rai khaleel yai yana kallon Abidah datai shiru tana sauraron zancen da sukeyi a fusace yakai mata duka yana cewa "ke dan ubanki zaman me kike zaki bar gun nan kosaina 6allaki" ya fad'a yana sake kai Mata sabon duka da gudu Abidah ta mi'ke yayin da Hajiya Khubura ta buga masa wata uwar harara tana cewa "sakalin asara yanzu ka kasa yiwa wancan figaggiyar amma da yake Abidah 'karamar dangarka ce me dad'in tsallaka shine harda dukanta dan kawai ta tsaya tana sauraron magana".

"To tsakani da Allah Umma dan uwarta ni sa'an tane a ri'ka min fad'a a gabanta kuma tayi fiki-fiki da kunne tana saurara salon ta raina ni"?.

"Ba wani ta Raina ka saidai ka raina kanka niduk ba wannan ne damuwa taba tambayar da nake meyasa ka shiga d'akin Ayrah ina ruwanka da ita so kake ka jawo min bala'i idan tai ciki ko bakai bane tunda kaita sani cewa zatai kaine kayi mata to wallahi ka shiga hankalinka ba ruwana kana jidai ko? Ka kiyayi kanka da sharrinta ka daina koda kallonta idan kuma matsuwa kayi ka aureta fad'a min naji"? Kaiya girgiza yana ta'be baki yace "ko d'aya niba aure kwana kusa a raina kawai dai yarinyar tana burge nine shiyasa na damu da ita amma ba soba".

"Aiko indai har a ranka kanaji ka damu da ita khaleel dole saidai a d'aura muku aure".

"Nifa Umma ba yanxu xan aureta ba shikenan abar maganar insha Allahu bazan sake kulata ba har sai naga lokacin dana sakawa kaina nayin auren yazo sannan zanyi miki magana" numfashi Hajiya Khubura ta sauke cikin jin d'an dama-dama tace "ok shikenan hakan yayi amma ka tabbata abinda ka fad'a min gaskiya ne karna sake ji ta kawo 'korafin ka".

"Eh na amince Umma zan kiyaye" ya fad'a yana kallonta harararsa tai zatai magana yai murmushi yana cewa "da gaske fa nake babu abinda zai sake shiga tsakanin mu dama niban ta'ba zuwa inda take ba jiyan ma kasa barci nayi kuma dana shiga bedroom d'in nata ba wani abu nayi mata ba na fito please Umma ki fahimce ni man kamar ba mahaifiyata ba kin tsaya sai tuhuma ta kikeyi alhali kinsan abinda zan aikata da wanda bazan iya aikatawa ba haba dan Allah kar kisa na fara tunanin wani abu dabam man"? Jin abinda yace da kuma sauyawa na rashin jin dad'in dayai ta gani akan fuskarsa tace "ok ok na fahimta sosai khaleel na gane shikenan ya wuce Allah ya kaimu lokacin daka d'iba na bikin naku Allah yasa ba dogon lokaci bane nidai na matsu naga dukiyar nan ta zama mallaki na ta dawo hannuna" mi'kewa yai yana cewa "saurin me kike? Zata dawo ai harsai kin gaji da ri'keta a hannnun naki kin kai ajiya banki" yana fad'in haka ya fita a parlon shiru Hajiya Khubura tai tana tunani wato khaleel ne ya shiga d'akin Ayrah da dare idan ta fahimta har ya nuna yana son wani abu a gurin ta itakuma tai masa ihu Daddy yaji yanzu yake tambayar ta itama tasan bazata ta'ba kawo kwarto gidan ba kawai ta fad'a ne saboda tasa Daddy ya fusata ya wulakanta Ayran kuma yayi shikenan burinta ya cika..........✍️Mrs Äl'ämëëñ Ähmäd çë 🌺.

Be with me at always my lover's nagode da kulawarku gareni godiya
End Ads