x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 24 - ROYALTY YAN SARAUTA

  • 69001 words
  • 72000 words
  • Out of 85109 words

Category: Love Stories

Views 1688

20 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
kirana da ba'kuwar number me yake faruwa ne"? Hawaye ne suka fara zuba mata na kwananki da yawa da take 6oyewa yau suka fito cikin kuka tace " tun ranar da Umma tasa Daddy yaje ya taho dani ta sakashi ya 'kwace wayar wai ka bani waya badan na ri'ka kiranka bane salon na kira samarin banza ne Ina kawo gidan itace ta kar'be wayar sannan ta 6alla Sim card d'in shiyasa tun daga ranar baka sake jina ba".

"Waye ya kar'be wayar a cikin su Daddy ne ko Kuma Hajiya Khubura waye".

"Umma ce amma saida ta fad'awa Daddy yasa ta kar'be".

"Toke meyasa daya saka ta kar'be bakije gurin Aunty Umma ta kirani kin fad'a min ba sai yau".

"Daddy ne yace karna 'kara zuwa gidan yai min katanga wai yawon banza nake fita haka Umma tace masa".

"Ok shikenan ki daina kukan haka yanzu zan turawa Aunty Umma dubu ashirin kije ki kar'ba ki sai wata wayar kota sha biyar ce dubu biyar d'in kuma ki barta ki ri'ka hawa napep idan zakje school ko yanxu ya baki driver da zai ri'ka kaiki ne"? Kaita girgiza tana cewa "a'a bai bani ba a kasa nake zuwa na koma" numfashi Aiman ya sauke cike da tsananin mamaki meyasa Daddy yake hakane haka kawai yadauki tsana ya d'orawa 'yar daya haifa daba haka yake ba meyasa cikin shekaru uku ya canza yana so yasan haka amma ya bari saiya dawo insha Allahu zai zurfafa bincike koda a gurin malamai ne suyi masa istahara aga abinda yake faruwa wanda su basu sani ba...........

"Yaya Aiman bansan da yadda zanje na kar'bo kud'in ba saboda idan na dawo gida bana sake fita ko harabar gidan ne saidai idan school zanje".

"To yanzu abinda za'ayi zan turowa Aunty Umma kud'in zan fad'a mata ta sai miki wayar inyaso idan kin fita zakije makarantar sai kibi tacan ki kar'ba kuma ki tabbata kin 6oyeta sosai kar wanda yasan kina da waya kinji"? Kaita d'aga tana cewa "to Yaya Aiman nagode sosai Allah ya saka da alkhairi Allah ya tsareka ya dawo dakai lafiya" "Amin Ayrah nima na gode da addu'a ki baiwa me wayar da kika ara yanzu zan tura mata kud'in zata sai miki".

"To Yaya Aiman sai anjima".
"Uhum sai anjima Ayrah" ya fad'a yana katse kiran numfashi Ayrah ta sauke tana kallon baby da murmushi akan fuskarta tace "baby nagode sosai kin taimake ni Allah ya biya ki gaskiya badan Allah yasa dake a kusa dani 'kawa tagari ba wallahi da rayuwata saita zama abar tausayawa amma koda kin ganni zan shiga damuwa kozan shiga duhu kozan kauce hanya zakiyi kokarin ki nusar dani nagode Baby" murmushi Baby tai tana girgiza kai tace "karki damu Ayrah ni dake mun zama d'aya ai babu bambanci dan kawai na amsan miki waya kinyi magana kike min godiya karki damu muna tare insha Allahu bari naje mu tafi kar lokacin sa ya 'kure" hannu Ayrah ta mi'ka mata suka gaisa kafin suka juya tare inda motar prince Hamid take saboda duk hanyar fitane daga school d'in baya cikin motar kuma a rufe take shiyasa Ayrah sukai sallama da baby ta wuce ita kuma ta jingina a jikin motar tana jiran ina ya tafi ya dawo suma subar school d'in kusan mintuna talatiin bayan tafiyar Ayrah sannan prince Hamid ya dawo kallonsa tai da alamar tambaya tace.

"Yaya Abdul-Hamid ina ka tafi ne"? Shima kallon nata yai yana saka key ya bud'e motar saida suka shiga ya tada motar suka bar cikin school d'in sannan ya bata amsa "naje masallaci nayi sallah ne saboda naga baku gama abinda zakuyi ba ni kuma bana son yin sallah ni kadai nafi sonta a jam'i tafi falala" murmushi Baby tai tana kallon fuskar wayarsa tace "Yaya Abdul-Hamid na tambaye ka"? Kaiya d'aga yana cewa "tambaye ni man niba irin Ahmad bane" jin abinda yace yasa Baby tai dariya tana rufe baki tace "laaa ni bance haka ba kawai dai tambayarka zanyi meyasa ka saka photon Yaya Ahmad akan secreen d'in wayarka"?.

"Oh tambayar da zaki min kenan"?.

"Eh".

"Saboda ra'ayi na saka sannan d'an uwana ne 'kani nane baya kusa dani yayi min nisa idan na bud'e fuskar wayata na ganshi dad'i nake ji a raina ji nake kamar na kirashi ya amsa" yana rufe baki Baby tai dariya tana cewa "to shima kenan yanzu photonka ya d'ora akan nashi fuskar wayar shima ya ri'ka ganinka kenan"? Kaiya girgiza Mata yana cewa "a'a shiba photona ya d'ora ba photon budurwarsa ne" ya fad'a yana daina kallon titi ya juyo kallon Baby yaga ya zatai zaro ido waje tai tana cewa "budurwarsa dama yana da budurwa ne"?.

"Eh yana da ita".

"Amma Aunty Maryam ce ko"? Da alamar tambaya prince Hamid yace "wacece Maryam kuma"? Dan shi ya manta ma da wata Maryam 'yar uwarsu.

"Aunty Maryam wacce tazo kwanan baya nake fada" ko itace budurwar tasa"? Kaiya girgiza mata yana cewa "a'a ba ita bace ked'in waye ya fad'a miki Maryam budurwar Ahmad ce"?.

"Ba fad'a min akai ba da idona na gani kuma kunne na yaji tace tana sonshi" zuba mata ido sosai prince Hamid yai daga baya kuma yace "ita Maryam d'ince tace tana son Ähmäd"?.

"Kwarai a gaban mu ta fad'a nida Aunty Khairat tace saita aureshi wai idan ta shigo gidan mun shiga uku".

"Kamar ya kun shiga uku Kuma ban gane ba"?.

"Humm wai akan taga yadda yaya Ahmad yake mana shine tace da laifin da mukai da wanda bamuyi ba duk zata ri'ka fad'a masa yana dukan mu yana hukunta mu kuma mu jira dawowar ta zuwanta gidan matsayin matarsa bazai mana dad'i ba sai mun raina kanmu mune zamu ri'ka yimata wankin kayanta munayi Mata girki shara da wanke-wanke" dariya prince Hamid yai yana jinjina yace "lallai ta d'auko abinda yafi 'karfinta Ahmad take so? Tab aiko wahalar da kanta zatai a banza Ahmad bazai ta'ba sauraron taba domin shi yana da wacce yake so tunda dad'ewa itace za'bin sa ita zai aura bana tunanin yana burin zama da mace biyu daga ita ya kulle kofa".

"Tofa yaya Ahmad da budurwa wai gwangwazo uhm masha Allah duk ranar dayai aure nasan shikenan matsalar mu tazama she'kak'kiya idan ya koma part d'insa ya daina zuwa gurin Momy sosai sai lokaci zuwa lokaci muma ma huta Allah yasa matar tasa ta ri'ka tsareshi a part d'insu tana hanashi fitowa ace a rana bazai fito ba saidai idan masallaci zaije ko gaida Momy" dariya prince Hamid yai harda dafe kai yana cewa "kai baby sai kace mijin tace zata tsareshi a gida Ahmad d'in ne zai yarda ayi masa haka kamar kin manta waye shi"?.

"Ai kuma Yaya Hamid ba anan take ba sai kaga duk wannan zafin nasa yazo yai sanyi idan yai auren kai kuma da baka da zafin sai kaga ka zama kaine me zafin hakan na iya faruwa".

"Ke yanxu a tunanin ki akwai macen dazatasa Ahmad yai sanyi"? Cikin 'kwarin gwiwa Baby tace "sosai ma wuya yai auren irinsu Yaya Ahmad su mata ke juyawa kamar waina wallahi kuma zakace nina fada maka muna nan sai kaga yadda ya Ahmad zai koma musamman idan matar tasa ta iya soyayya ta iya kisisina da karairaya humm ya Ahmad yana son soyayya ai na gama karantarsa" dariya ce sosai ta kama prince Hamid ya kalli Baby yana cewa.

"Ashe dama haka kika sakawa Ahmad ido bai sani ba taya kikasan yana son soyayya"? Prince Hamid yai mata wannan tambayar yana 'kureta da kallo saboda duk zatonsa ko su Momy sun fad'a mata Ahmad nasonta to amma dasun fad'a mata bazatace dama Ahmad nada budurwa ba kawai kintace tai ta fad'a.........

"Nifa ban saka masa ido ba kawai yanayin sa na gani nace zaiso soyayya ba sani nayi ba abar maganar ma haka kar naje nayi 6arin zance" ta fad'a harda kama bakinta murmushi yai yana mayar da hankalinsa kan titi daidai sun isa kofar gate d'in aka bud'e masa ya shiga direct saida ya kaita har kofar part din Momy ta sauka sannan ya wuce zaikai motar gurin aje motocin masarautar.

Babu kowa a parlor dan haka Baby bata tsaya ba ta shige part d'insu a kwance ta samu Khairat rungume da pillow ta kashe murya suna waya da Shadad tsaye tai tana kallon ta daga baya kuma tai dariya tana karasowa ta kalleta tana cewa "kaga masoyan zamani irin wannan kashe murya haka tabd'i wannan gaba zamusha kallo idan kukai aure saidai mu ri'ka rufe idonmu saboda karku makanta mu kusa mu koma yawo da sanda" ta fad'a tana kallon yadda Khairat d'in take murmushi tana sake gyara kwanciya batasan ma me Babyn take fad'a ba hankalinta yana kan wayar da suke ha6a baby ta ri'ke cike da mamaki tai dariya tana aje handbag d'inta tace "to wannan gara na bari ki gama tunda ba jina kike ba kafin nan tsaya nayi alwala nai sallah" toilet ta wuce tayo alwala tazo tai sallah harta idar tai addu'a ta tashi Khairat bata gama ba murmushi Baby tai tana kallon ta ganin itama Khairat d'in ita take kallo yasa ta girgiza mata tana nuna mata da hannu cewa ta tafi dinning taci abinci d'aga mata kai Khairat tai yayin da Baby ta fita tana sake dariyar da batai niyya ba wato saboda kartai magana su katse hirar da suke shine take mata maganar kurame da hannu da ido fita tai tana zama a dinning hankalinta kwance saboda tasan ko kwana zatai a gurin Ahmad baya nan balle taji fargabar karya shigo ya sameta ita kad'ai.

*Da dare bayan Daddy ya dawo gida yake fad'awa Hajiya Khubura cewa Aiman ya kirashi yana tambayar meyasa suka kar'be mata waya zai sai mata wata amma wallahi suka qara karbewa zasuga tashin hankali irin wanda basu ta'ba gani ba jin sa'kon da Aiman ya bayar a fad'a mata yasa ta kalli Daddy a she'ke tana cewa.

"Au nan d'in kiranka yai yake tuhumarka mun kar'be waya a gurin Ayrah saboda ya gaji sharri da rashin kunya to an kar'be d'in kuma baza'a bayar ba idan ya sake kiranka ka fad'a masa haka in jini d'an mara mutuncin yaro kawai".

"Nidai duk ba wannan ba bana son tashin hankali a gidan nan idan ya sayo mata wata karki sake karbewa ke kyale mata kayarta bana son yawan hayaniya".

"Me kake nufi na kyale ya ri'ka cimin mutunci kenan ina kallonsa kome"?.

"Ni bance yaci miki mutunci ba saboda ke uwace gareshi kawai dai nace ki daina shiga safgar wannan yarinyar yana kirana yana damuna da maganar ta bana so kin gane"? Shiru Hajiya Khubura tai cike da takaici hum wato nan Aiman 'kararta yakai gurin Daddy akan ta kar'be waya aiko wallahi ko yanzu ya sake sayowa Ayrah wata saita kar'be ta idan yana ganin bazata iya ba yasayo matan ya gani ko yana gari zatai fin hana balle baya nan har ji tayi ta matsu gari ya waye ta jawa Ayrah kunne tayi mata tas akan wannan maganar.

Washe gari tun asuba Ayrah tana gama had'a musu breakfast tabar gidan zatai school suka had'u da 'kanwar Aiman ta bata wayar daya turo kud'i a sai mata sannan ta bata dubu biyar d'in a take kuwa tahau napep sannan ta kirashi tayi masa godiya sosai a ranar ta wuni cikin walwala da jin dad'i wanda ko Baby saida taji dad'in yadda taga Ayran ta samu farin ciki shiyasa ta bata shawarar cewa duk yadda zatai karta bari su Hajiya Khubura suga wayar ta ri'ka 6oyeta.

Kamar yadda Boukar ya kira mahaifiyar Sabit ya fad'a mata sati biyu tsakani su Niseh suka kammala exam ta tattaro suka sauka da yake saukar dare sukai gidan da Boukar ya kama anan suka kwana amma tun daren sukaje ya nuna mata gidan sannan suka dawo washe gari da wuri suka tashi sukai shirin zuwa amma banda Boukar yana gida sakamakon shi abokin Sabit ne bai kamata ace Sabit ya ganshi a gurin ba duk da mahaifiyar sace ta sakashi amma abun babu dad'i sannan shi kansa Boukar din baya goyon bayan auren da Sabit yayi yafi son ya auri bayerabiya irinsu.

Nadiya tana zaune a parlor ita kad'ai sai me aikinta da take ta faman yi mata hidima daga wancan tai wancan amma duk da haka bata gwaninta sai tsawa da bala'i da zagi Nadiya take aika mata wani lokacin harda dukanta take idan tai kuskure wajen yin wani aikin yanzun ma tana zaune bayan ta gama yanka Mata kayan marmari tasa ta kunna mata TV tazo kuma ta bata 'kafofi tai mata tausa suna cikin haka sai gani sukai an bud'o kofa an shigo mace fara tar 'katuwa tana juyi da mamaki Nadiya take kallonta yayin da Seemah ta mi'ke jiki na rawa tace "barka da zuwa Hajiya bismilllah sannu karaso" (ba shishshigi taiba Nadiyan ce ta umarceta cewa idan tayi ba'ko ta ri'ka tararsa a madadinta saboda ita bakinta bazai iya wannan wahalar sannu da zuwan ba🤔) wani irin kallo Nadiya take binta dashi ganin kamar ba bahaushiya bace ga kuma yadda take 'karewa gidan kallo jin Seemah ta sake cewa.

"Karaso Hajiya shigo ciki" yasa Nadiya sakar mata harara zatai magana Seeman tace "ranki ya dad'e a kawo mata abun sha wanne kala" yatsina fuska Nadiya tai cikin wula'kanci da nuna 'kyama tad'an toshe hanci tana cewa "what wannan halittar zance ki kawowa abun sha a gidana nasan daga bolar da take yare cefa? Zaki 6ace min da gani ko saina d'auke ki da mari"? Ta fad'a cikin tsawa da gudu Seemah tabar gurin tana wucewa ta koma kitchen inda ta fito qarewa matar kallo Nadiya tai cike da mamakin me yakawota gidanta tace.

"Madam wanne irin abune wannan zaki shigowa mutane gida sakaka haka kara zube ko an fad'a miki nan gidan arna ne ba sallama wacece ke daga ina kike zo me kike nema? Wani irin ba'kin kallo matar taiwa Nadiya batare data bata amsa ba ta zauna akan kujera tana d'aga waya ta kira "hello Niseh ina Naomi din ku shigo me kukeyi a waje ku karaso man gidan nefa wallahi sai naci uban Sabit tunda ya nuna ban Isa dashi ba ashe da gaske ne abinda ake fada akansa naga yarinyar a yanzu haka tana gabana tana kallona".

Jin abinda matar tace yasa gaban Nadiya ya fad'i a ranta tace innalillahi wa inna ilaihi raji'un na shiga uku wannan ita kuma wacece a familyn su Sabit me yai mata take zaginsa da 'kwarin gwiwarta kamar wata mahaifiyarsa................

Shigowar 'yan mata biyu yasa suka katse mata tunanin da take hankalinta ta mayar kansu kamar su d'aya tsayinsu daya komai nasu iri d'aya da alama 'yan biyu ne abinda yai mugun d'aga mata d'aga hankali shine ganin yadda suke kama sosai da Sabit d'inta har dogon hancinsa da yanayin tsayawar gashin girarsa sake kallon matar tai taga itama dai kamar suke da Sabit d'in to su waye wadannan daga ina su kuma tasan dai wannan matar ba mahaifiyar Sabit bace tunda tasan tasa uwar tana rijiyar zaki to ita kuma wannan wace ita mene ala'kar su ko kanwar mahaifiyar sace da yaranta.......................

Cikin tsawa taji matar tace "ke bahausiya ina Sabit meyasa zaki aureshi kinsan yadda na tsani hausa wayasa ki aureshi"? Jin abinda take yasa a dake cike da jin haushi Nadiya tace "na aureshi d'in ki Hana tunda kece kika haifeshi tukuna ma tsaya wace ke zaki zo min gidan mijina ki tada min hankali kiyi gaggawar barin nan kafin na kira miki hukuma dan wallahi bakisan wace niba gani na kawai kikai yanzu bani da mutunci nafi bala'i zama fitina kin gane dan haka ki kama kanki".

Tunda ta fara magana matar take kallonta jin abinda tace yasa matar cire mayafin dake kanta ta d'aure shi a 'kugu tana cewa "yau zan nuna miki karshe masifar da bala'i kin tari abinda yafi karfinki yarinya daga yau zaki kiyaye tarar mace irina dama nasan bazakiyi tarbiyya ba daga ganinki rainon mace ce ke" hannu Nadiya ta d'aga mata cikin taratsi tace "karki kuskura ki zagar min mahaifiyata naji kina wani ni rainon mace ce ki fad'a min wanda namiji ya raina look madam kubar nan ku fice min daga gida kafin nai muku hauka zan gwada muku tashin hankali da d'anyan kai".

Kai madam ta jinjina tana cewa "bari mu fara gwada miki namu aike da bakine kike maganan mu kuma da dantse zamu gaya miki Niseh a shirye kuke"? Jin abinda suka ce yasa Nadiya ta fahimci Shirin nad'a mata duka suke da sauri ta d'aga waya jikinta har mazari yake tana kiran Sabit amma bai d'aga ba kusan kira hud'u wayar Sabit bata hannunsa tana bedroom ya barta jin bai daga ba yasa ta ta kira Abidah ko sallama babu tana d'agawa a hargitse Nadiya tace "hello Abidah kina jina kizo gidan nan yanzun nan" jin abinda tace yasa Abidah cewa "nazo kuma Nadiya meya faru zanzo gidanki ina school fa"

"Eh ki baro school d'in kizo yanzu ina jiranki a parlor karki tsaya sanya ki taimaka".

"A'a gaskiya indai zanzo ma saidai idan an tashi daga school wajen karfe biyu da rabi" zaro ido waje Nadiya Tai tana kallon yadda su Niseh suke harararta suna hura hanci tace "kinyi hauka ne kinsan masifar data sameni zakice wata uwa saikin tashi daga school zaki zo sannan idan farfesu nane ma anyi an shanye romon ko"?.

"Ban gane ba Nadiya wai meya sameki ne kuma bayan naji muryarki normal baki da lafiya ne ko kuma wata matakalar ce dabam"?.

"A'a lafiya lau kawai wasu karfofi ne suka zo min gidan harsu uku uwa da 'ya'yanta sai ba'ka'ken maganganu suke fad'a min dan Allah kizo yanzu akwai bala'i domin bansan daga inda wadannan masu siffar aljanun suka zo min ba".

"Ok gani nan ina zuwa gara na ha'kura da lesson d'in na taho kar suyi miki illa bari nazo muci uwar shegu mu kwana lafiya" tana fad'in haka ta kashe kai Nadiya ta jinjina tana kallonsu tace "humn 'karyar ku ta 'kare yau ku jira zuwan sister na wallahi saimun 'bab'balla ku yadda kuke d'in ba dan kun ganku d'irka-d'irka girman banza ne ba tsoron had'a damtse daku zamuji ba" Nadiya na rufe baki Sabit ya shigo kamar an jefoshi dawowar sa kenan daga anguwa
End Ads