"Eh man tunda ku manyan yayu kun'ki yi mu saimu rigaku ai kuma tambayi Mama kaji aure zanyi ni".
"Wai haka ne abinda ya fad'a Mama"? Prince Hamid ya tambaya cikin kokwanto kai Mama ta girgiza tana cewa "a'a bansan zancen ba idan ma yana da ita ko auren zaiyi ban sani ba saidai da wasu yayi shawara" kallon Amaan dake 6oye dariyarsa yayi yana cewa "wato son auren kake kenan"?..
"To wa yake 'kinsa baka fad'a min kai yaushe zakai ba"? Kai prince Hamid ya girgiza yana cewa "nikam da sauran lokaci saidai Ahmad yanzu shine a online bani ba domin ni ko budurwa bani da ita".
"Au Ahmad d'in aure zaiyi amma ban sani ba"? Mama ta tambaya tana kallon sa kaiya girgiza mata yanaiwa prince Hamid kallon kana shiga safgata fa kafin yace "ni ba aure zanyi ba kawai dan yaji dad'in bakinsa ya fad'a niban tashi yin aure ba sai gaba sosai" yana rufe baki prince Hamid yace "ji 'karya ba wani nan malam ka daina wani wayancewa ka fad'a musu gaskiya".
"Ai gaskiyar na fad'a musu" a she'ke prince Hamid yace "a hakan"?.
"Kwarai a haka d'in".
Tashi Mama tai tana kawo musu abun sha sannan tace "Ahmad Abdul-Hamid yace aure zakai dama kana da budurwar ne bamu sani ba"? Kaiya girgiza yana cewa "nifa Mama ba aure zanyi ba kawai ya fad'a ne" sauke ajiyar zuciya Mama tai tana hamdala a ranta harda sakin murmushi tana jinjina kai tace "yauwa fa Ashe wasa yake aina d'auka da gaske ne Allah ya kaimu Allah ya kawo mace ta gari musha biki tunda mune iyaye" ta fad'a tana hasko wani abu a ranta dan tunda dad'ewa take fata da son a cikin yaranta Maryam ko Humairah wani ya samu ya auri d'aya a cikin Ahmad ko prince Hamid yanzu kuma take jin batun Ahmad zaiyi aure shine taji hankalinta ya tashi saida yace bayi zaiyi ba taji dad'i har mantawa tai da suna hira tsabar tunanin data tafi iya su uku ne suke zancen su sun dad'e a gidan daga baya suka mi'ke zasu tafi tare da aje mata kud'i da atampha kamar yadda suka saba duk lokacin da suka xo mata cikin jin dad'i tayi musu godiya tare da Amaan suka mi'ke shima zai fita daga gidan sukai harabar gida acan ma saida suka sake tsayawa sukai hira sosai sannan sukai mai sallama suna shiga motar da suka zo da ita shima da yake fita zaiyi tasa motar ya nufa daidai an bud'e gate d'in motar Maryam ta shigo su kuma sun fita da mamaki ta bisu da kallo domin kafin Ahmad ya d'aga glass d'in ya rufe ta ganshi da sauri ta Parker ta fito amma sunyi nisan da ko hannu ta d'aga bazasu ganota ba ha'kura tai ta shiga gidan ganin Mama zaune a parlor ga kud'i a gabanta da atampha zama tai tana kallon kayan tace.
"Mama wa nake gani kamar Ahmad ne yazo gidan nan ko yanxu suka fita dama ya dawo ban sani ba"? Kai Mama ta d'aga tana cewa "eh shine tare suke da Abdul-Hamid yanzu suka fita baki had'u dasu ba a harabar gidan saboda na le'ka naga suna tsaye da Amaan"? Kai Maryam ta girgiza tana cewa "Bamu had'u ba na shigo sun fita kuma da yake Ahmad yana da gudu a mota kafin na fito na d'aga musu hannu sunyi nisa amma naso mu had'u wallahi nifa Mama haka kawai nake jin ina son Ahmad d'in nan amma shi babu ruwansa dani ko gaisuwar arziki bata shiga tsakanin mu taya zan samu harya karkato da hankalinsa kaina mu saba ya kamu da sona nidai ina sonsa wallahi" kallonta sosai Mama tai tana cewa "kina son Ahmad kikace Maryam"? Kai Maryam ta d'aga tana cewa "eh gaskiya ina sonsa Mama da ace zai amince ya aureni zanyi farin cikin da ban ta'ba yiba" Maryam na rufe baki Mama tai murmushi tana jinjina kai ta kalleta tana cewa.
"Maryam ni kaina ina so d'aya daga cikinku ya auri Ahmad ko Abdul-Hamid ina so nima naga hakan ta faru haka kawai nake jin ina son hakan shiyasa yanzu da Abdul-Hamid yake cewa wai Ahmad d'in aure zaiyi bakiji yadda naji gabana ya fad'i b.........................
Bata bari Mama ta karasa ba a zabure ta zaro ido tana cewa "aure zaiyi kuma na shiga uku"? Kai Mama ta girgiza tana kallon yadda lokaci guda Maryam d'in ta burkice tace "a'a ba aure zaiyi ba ashe wasa Abdul-Hamid d'in yake dan yaji me Ahmad zaice ne gashi gobe zai tafi da kamar ace bai dad'e da dawowa ba wallahi kayanki zaki tattara kije musu ko sati biyu kiyi ki samu ki ja hankalinsa ki ri'ka shishshige masa ta yadda ko baya sonki ko bai fahimci kina sonsa ba daga baya ya gane kema ya soki" gyara zama Maryam tai tana cewa.
"Allah Mama".
"Allah kuwa da gaske Maryam zan tayaki indai kina sonsa zan samu Aunty nayi mata maganar in yaso ta sameshi ta fad'a masa Allah yasa ya amince zai aureki" da sauri Maryam ta d'aga hannu tana cewa "Amin ya Allah Mama wallahi nima haka nake fata wani lokacin har mafarki nake ya aureni muna tare" murmushi Mama tai tana cewa "humm kamar yaune insha Allahu zai aureki ya zauna dake idan akai masa tayi bazaice a'a ba zai yarda nasan muddin Aunty ce ta fad'a masa bazai musa taba kawai kisa a ranki kamar kin aure shine kin zauna dashi ina so kawai naga na had'a jini da 'yan sarauta a rayuwa kamar yadda Aunty Allah ya d'agata ta lokaci guda Aliyuddeen ya ganta nima naso ace Ashraf 'kaninsa ya yarda ya aureni amma ya'ki aurena har jinya saida nayi na dad'e a asibiti banyi tunanin zan warke har nayi doguwar rayuwa haka ba kwatsam muka had'u da Abban ku shikenan na ha'kura da Ashraf hankali na ya dawo kansa kema inai miki fatan ki taki sa'a irinta Aunty Ahmad ya soki ya aureki tunda dai kinji baida budurwa dagewa zaki idan ya sake zuwa gida kije duk wata hanyar da kikasan zaki burgeshi ita zaki bi kinji"? Kai Maryam ta jinjina tana sakin murmushi tace "Allah ya Allah ubangiji kana gani kana ji ya mahaliccin samai da 'kassai ina ro'konka ka cika min burina akan bawanka Allah ka lamince min ka 'kaddara Ahmad shine mijina wanda zanyi rayuwa mai cike da inganci dashi" tana rufe baki harda Mama wajen tayata cewa "Allah Amin Amin in Allah yaso Maryam ke matar Ahmad ce sai kin aureshi ki kwantar da hankalinki tunda muna da ala'ka dashi hakan bazai zama abu mai wuya a gurin muba" fuskar Maryam cike da annuri tace "shikenan Mama Allah ya tabbatar da abinda kika fad'a bari naje nayi wanka dan na d'ebo rana wannan anguwar da naje kawai saboda naga Ahmad hankalina ya fita daga jikina yasa banji zafin ba sai yanzu" ta fad'a tana mi'kewa da niyyar idan tayi wanka saita fito taci abinci domin 'karfe d'aya da rabi tayi tana barin parlon Mama data bita da kallo ta sauke daddad'an numfashi tana cewa "ubangijin rahma ya amsa mana addu'ar mu Allah yasa Maryam ta dalilin ki mafarki na ya zama gaskiya ki auri Ahmad da ranar nayi rawa na qara nayi farin ciki nai gud'a nai shewa a gaban kowa Allah ya kaimu da alkhairi" ta karasa maganar tana tashi itama ta shiga bedroom.
Ahmad kam suna komawa gida part d'in Momy suka shiga babu kowa daga Baby sai Khairat domin yau basu je school da safe ba sai karfe hud'u zasuje lecture shima ba dad'ewa zasuyi ba suna zaune a dinning ya shigo bayansa prince Hamid Baby ce ta fara ganinsa ta d'ebo abinci a spoon zata kai baki suka had'a ido da sauri ta janye nata tana fad'in "innalillahi wayyo Allah dama Yaya Ahmad ba nisa yayi ba.....................
Bata gama tunanin da take ba taji saukar muryasa yace "ku sauka a dinning d'in nan" da sauri ta dawo nutsuwarta zuciyarta ta harbawa ganin har lokacin ita yake kallo da sauri ta mi'ke zata bar gurin kujerar data tashi ya zauna yana cewa "ke dawo nan ina zakije wannan sauran jagwalgwalon da kika bari waye zai cinye miki shi" tsayawa tai tare da juyowa ta dawo zata dauka yace.
"Serve me" d'auke numfashi tai na wani lokaci kafin da'kyar muryarta na kokarin fara rawa tace "me zan saka maka"? Bai d'ago ba baiyi magana ba ta d'auka ko baiji bane saboda akwai Bluetooth a kunnensa saida ta sake maimaitawa sannan ya d'ago yayi mata kallon minti biyu kafin ya sake cewa.
"Serve me" tun batai motsi ba prince Hamid dake zaune a d'aya daga cikin kujerun dinning shima har Khairat tayi serving d'insa tabar gurin ganin yana neman wahalar da ita gashi bai bari ta gama cin abincin yadda zaibi jikinta ba yace "kaga malam ba'a ciki da mugunta tai serving d'inka me? Ta tambayeka me kake so ka sake cewa wata uwa tai serving d'inka" mayar da kallonsa kan Baby yayi yana cewa "kinga Baby rabu dashi saka masa duk abinda kikaga dama ki tafiyarki kije ki karasa cin abincin ki yabi jikinki" jin abinda prince Hamid yace yasa Baby tad'an saci kallon Ahmad taga sam ba inda take yake kallo ba hankalinsa nakan waya shawarar prince Hamid tabi kawai ta bud'e dishes tai serving d'insa abinda itama ta za'ba taci ta d'auka zaice a'a ta sauya masa sai taji baiyi magana ba hamdala tai a ranta cikin azama kuwa tabar gurin ta koma tayi bedroom domin can taga Khairat ta nufa bayan sun tashi.
Prince Hamid saida ya bari Babyn ta wuce ya kalli Ahmad yana cewa "amma kai kam bansan ranar da zaka canza ba Ähmäd ba yanzu ne lokacin da zakaji takaici ba sai gaba irin wannan had'e ran da kake mata ya kamata ka daina kullum ina tunatar maka ita ka za'ba matsayin abokiyar rayuwarka wacce kake sa ran da ita zakai rayuwar aure amma baka da wacce zaka ri'ka yiwa muzurai sai ita kasan cewa kuskure kake aikatawa kuwa"? Kai Ahmad ya kad'a yana cewa "yanzu bani da lokacinka ka bari zuwa dare zan nemeka domin bana gane abinda kake fad'a yanzun" kai prince Hamid ya jinjina yana cewa "ok kada Allah yasa a gane akwai ranar ganewar tana nan zuwa indai baka canza ba" yana rufe baki Momy ta fito ganin basu Baby ba alamarsu ta kalli su Ähmäd da suke zaune tace.
"Abdul-Hamid kun dawo kenan ya kuka barosu fatan duk kowa yana lafiya"?..
"Ok ina Khairat da Baby suke kohar sun gama cin abincin ne"? Kai prince Hamid ya girgiza yana cewa "a'a ga mugun daya kore su nan suna bedroom d'insu" "tofa bedroom kuma haba Ähmäd daka 'kyale su kujeru nawa ne a dinning basai kace su koma gefe ba amma saika kora min yaran cikin bedroom" d'agowa Ahmad yai yana kallon ta yace "haba Momy ina kan dinning suma suna kai saboda kafad'a ta d'aya take da tasu tab aiko da sunci duka".
Kai Momy ta girgiza tana cewa "tsiya ta dakai Ahmad mugunta meye abun cin dukan dan kawai kana kan dinning suma suna kai ba 'kannin ka bane"?.
"Kannai nane Momy amma bana so su rika ganin damata kamar yadda suke ganin sau'kin halin Abdul-Hamid shiyasa suka raina shi nikam basu isa ba ko kallo nayi musu sun sani" murmushi Momy tai tana kallon sa da abinda yake fad'a kafin ta jinjina kai tana komawa ainishin parlon ta zauna tunda tasan me hali baya fasa halinsa a haka ya taso tun suna yara ma ba sau'ki 'ya'yan bayi ma sunci duka sosai kusan kullum sai ya daki yara sama da biyar hud'u uku har gajiya Momy tai tun tana fad'an ta ha'kura saida yayi hankali kuma ya daina kowa ya huta su Khairat kuma suka hau layi su kuwa idan ba aure sukai ba babu ta yadda za'ai ya daina horasu.
Khairat tana zaune taga Baby ta shiga da sauri da plate a hannunta zama tai tana sau'ke numfashi tace "kai jama'a gaskiya ya Ahmad yana da wuyar sha'ani wannan matarsa ta banu da tsiri" dariya Khairat tai tana gyara zama ta kalli Baby data bud'e plate d'in data shigo dashi taci gaba dacin abincin tace "humm ai naso na tsaya naga yadda diramar zata kasance saidai da yake na gama hadawa ya Hamid nasa kuma idan na tsaya boss zai iya cewa na tsaya gulma yasa na taho naso ace naga yaya kuka 'kare" baby data kai lomar abinci tace "ya muka 'kare kuwa tambayar sa nayi abinda zanyi serving d'insa bazai fad'a ba saidai ya sake cewa serve me kiji dan Allah" sabuwar dariya Khairat ta kumayi tana cewa.
"Ai ya Ahmad humm nifa harna matsu gobe tayi ya tattara ya koma mu huta".
"Duk matsuwarki Aunty Khairat baki kaini ba kawai dan babu yadda zanyi ne ai inaga gobe sai mun had'a party wallahi bayan ya tafi" murmushi Khairat tai cikin tsokana tace "wai inama ace wannan maganar da muke yana jinmu tabd'i da azabar da zamu sha kafirin dake qabari ma saiya fimu samu nutsuwa" daina cin abincin Baby tai tana ture plate d'in tace.
"Wallahi Aunty Khairat har kinsa abincin nan ya fita a kaina da kikace inama ace yana jinmu haba yanxu ace ya Ahmad yana jin wadannan maganganun da muke akansa ai yau kam saidai muyi kwanan asibiti dan bana tunanin zamuje gobe a hayyacin mu".
"Garama ki karasa cin abincin ki ba jinmu yake ba balle yad'au matakin daya saba hum gaskiya gayen nan yana garamu" mi'kewa Baby tai tana cewa "nikam abincin nan ya gama fita a kaina barima kiga na tashi wanka zanyi kawai na shirya kamata yayi ace kafin mu tafi lecture d'in nan mu le'ka Sultana Addah" ta fad'a tana shiga toilet Khairat tana zaune wayarta tahau ringtone ganin me Kiran yasa ta gyara zamanta tana d'auka ta kashe muryar suka fara waya Baby na jinta saida ta gama ta fito ta kalli Khairat tana jinjina kai kafin ta saki murmushi tana cewa "kaga masoyan asali" hararar ta Khairat tai tana cewa "kajita ko wai Baby ce maicewa kaga masoyan asali" zaro ido Baby tai tana cewa "a'a Aunty Khairat yada haka kinsan ya Shadad bashi da mantuwa so kike a ranar daya dawo ya kar'be ni da kamun kunne ko"? Khairat bata kula taba sai wayar data mi'ko mata tana murmushi tace.
"Yace ki kar'ba ai banice na had'a ku ba dama yana jinki".
Kar'ba Baby tai tana karawa a kunne tace "hello Yaya ina yini"? daga 6angaren Shadad yace "wato Baby kin raina Khairat ko ashe dama bayan tahowata haka kike mata"? Zaro ido Baby tai tana girgiza kai kamar tana gabansa tace "wallahi Yaya ina bata girmanta yanzun ma tsokanar ta kawai nake yi bada wani abu nace hakan ba".
"Ok yayi ya kike ya karatu fatan kina dagewa"?.
"Eh sosai Yaya ina kokari kuma ka tambayi Abban mu kaji".
"No basai na tambaye shiba ai ina tambayar Ahmad duk wani abinda kuke yi kuma yana fad'a min idan yabar gida saina dawo tambayar Abdul-Hamid" had'a ido Khairat da Baby sukai suna jinjina kai oh wato dama ashe baya nan ma yana tambayar ya suke suna karatu ko a'a da yake Baby tana d'an sakewa dashi ba kamar Ahmad ba tace "ya Shadad me ya Ahmad yace maka daka tambayi muna karatu ko bamayi"?.
"Ina ruwanki da amsar daya bani baiwa sweetheart wayar nagama dake" dariya tai tana mi'kawa Khairat wayar ta wuce gaban mirror Khairat na kar'ba tace "nimafa ta Babyn me ya Ahmad d'in yace maka dan naji hankali na bai kwanta ba".
"Wani abu yace min aida ya fad'i cewa bakwa mayar da hankali zaki sani saboda da yanzu na kira wayarki na muku fad'a amma hakan ma tunda gobe zai tafi zansa Abdul-Hamid ya d'ora inda Ahmad d'in ya tsaya kafin na dawo" murmushi Khairat tai tana cewa "ai kuma ya Hamid bashi da fad'a irin naku koka wakilta shi babu abinda zaiyi mana".
"Dama badan yayi muku wani abu zan wakilta shiba a'a kawai ni damuwata ya kula da karatun ku shine kawai"
"Ok nagane aikuma muna karatun sosai kuma ko Abban mu ka tambaya".
"Basai na tambaye shiba komai ina sani zan kiraki zuwa jimawa yanzu ina da uzuri".
"To muma dama gurin Sultana Addah zamuje".
"Yayi idan kunje ki kirana ina son zanyi magana da ita ta wayarki".
"Ok zan kiraka ba dad'ewa zamuyi acan ba muna lecture karfe hud'u da rabi nida Baby".
"Ok karki manta ki kira"?.
"Tom zan kiraka bye" ta fad'a tana katse kiran kai Baby dake zaune ta girgiza kai tana juyowa ta kalli Khairat sai kawai taji dariya tazo mata murmushi ta saki tana mi'kewa tace "lallai Aunty Khairat me masoyi wato ke auren had'i kike so"? Kai Khairat ta jinjina tana cewa "kwarai auren gida nake so tunda ina son wanda zan aura ai ba wata damuwa ko kema shi kike so kiyi"? Khairat ta tambaye ta cike da tsokana ba arziki kuwa tasa Baby da sauri ta girgiza kai harda zaro ido kamar wanda Khairat d'in ta fad'a mata abun firgici tace "wayyo Allah Aunty Khairat dan Allah ki rufa min asiri kar wani ya jiki" hhhhh dariya Khairat tai tana cewa "ba wanda yai mana la6e iya mune anan part d'in kawai kedai tsoron kine na gado da kika saba amma Baby meyasa ke bakya son auren gida yana da dad'i fa kuma ki gwada kema zaki gani" Khairat ta karasa maganar tana she'kewa da dariya ganin yadda tasa Babyn ta sake 'kwalalo ido waje tana cewa "tabd'ijan nikam saidai nace Allah ya tsari gatari da saran shuka wallahi ko kad'an bana son auren gida".
"Kuma idan wani a cikin su ya Ahmad d'in yace yana sonki fa tsakanin shi da ya Hamid nan kuma ya zakiyi"? Dafe 'kirji Baby tai tana cewa "a'uzubillahi