shiru daina kukan zanyi wa Daddy magana idan ya dawo jeki part d'inki bari na sayo miki magani ina zuwa" juyawa yayi ya fita itama da sauri ta shige part d'inta tana zuwa ta wuce toilet ta cire kayan jikinta daya ji'ke sannan ta fito tasa wasu ta kwanta saboda jikinta ya zama kamar wuta tsabar zafin ciwon zazza'bin dake cin jikinta.
Hajiya Khubura tana zaune a bedroom tana waya da d'anta Khaleel sai ganin su Abidah tai sun shigo aguje harda ihunsu a firgice ta cire wayar daga kunnenta tana kallon yadda suka hargitse tace "lafiya meya faru ihun me kuke"? Nuna kofa Nadiya keyi da hannu tana cewa "Aiman ne".
"Aiman me kukai masa ya biyo ku har part d'ina dan raini"? Abidah na huci tace "dan kawai nasa wannan shegiyar yarinyar ta wanke mana hijab d'in zuwa islamiyya akan haka ya biyo mu zai dake mu".
"Ya dake ku saboda bashi da hankali? Aiko wallahi dana d'ebo masa hukuma yau saiya gane ruwa ba sa'an kwando bane yanzun yana ina"? Ta tambaya tana kallon kofa gani take kamar zai shigo.
"Yana parlor nasan bai fita a gidan ba jiran mu yake mu fita".
"Ku fita yayi muku ubansa wannan akwai tambad'addan yaro gabadaya yabi ya hanamu zaman lafiya a gidan nan humm bari Alhaji ya dawo na rantse da Allah sai yayi mana iyaka dashi idan ba haka ba ko kad'an bazai ri'ka bari kuna iya zaman parlon ba saboda ba gidan ubanku bane shima ba gidan ubansa bane duk ranar da yayi muku gori kar kuji tsoron sa ku rama sawa tace kuyi masa tas zagi na tozarci sannan ya dakeku ya daki kud'insa muje parlon" ta fad'a tana wucewa gaba suka bi bayanta cikin d'ari-d'ari ganin baya nan yasa Nadiya jan tsaki tana cewa.
"Gaskiya wannan gayen anyi mugu haba dan tsaraba ace ganinsa yasa mutum ya rud'e" ta'be baki Abidah tai tana jijjiga kai tace "hummm ina jiran fitarsa ai na shiga part nata naci uwar uwarta dan wallahi bazanyi wannan gudun a banza ba" Abidah na rufe baki Nadiya tace "to kema kenan balle kuma ni yau tsabar dukan da zanyi mata saita kasa tash................
Bata karasa ba taja bakinta tai shiru tana rarraba ido ganin Aiman ya shigo da leda a hannunsa tsayawa yayi yana kallon su fuskarsa a had'e yace "ban baku ha'kuri ba duk wacce a cikin ku take jin ta isa ita 'yar iskan kanta ce idan na fita ta ta'ba lafiyar Ayrah zan nuna muku karshen rashin kunya" yana fad'in haka ya wuce da harara Hajiya Khubura tabi bayansa ganin ya bud'e kofa ya shiga tace "mitsiyaci mara mutunci ai wallahi duk ranar daka sake dakar min 'ya'ya nima zakaga yadda ake wasan tsutsa a rana saina had'aka da hukuma" mayar da hankalinta kansu tai tana cewa "kuje kitchen ku d'ora mana wani abu da zamu ci tunda yana gidan ba bari zaiyi tayi mana aikin komai ba saidai aikin da zakuyi bashi taci domin saita biya ko daga baya" ta fad'a tana zama domin tunda suka fito a tsaye take wucewa su Abidah sukai suka fara aiki suna sake shirya plan d'in abinda zasuyi mata kawai sai ganin Aiman sukai ya shiga kitchen d'in rawa jikinsu ya farayi yana tsaye a kofar kitchen d'in ba damar da zasu fita ransa a mugun 'bace yake kallonsu yace.
"Daga yau zan kashe muku warning na 'karshe akan takurawa Ayrah wallahi tallahi na rantse da Allah duk ranar da tsautsayi yasa na sake shigowa gidan nan na tarar kun sakata aiki ko kuna yi mata wani abu da bai gamshe niba humm abinda zan aikata muku bazai fad'u ba saboda munin matakin dazan d'auka a kanku domin gidan nan gidan mahaifin tane ba gidan ubanku ba baku Isa ku hanata sakewa da jin dad'i ba kaddara ce zata gitta na sake zuwa naga kunyi abu sa6anin fahimta ta zakuga abinda zai biyo baya" ya karasa maganar yana shiga kitchen d'in da sauri suka antayo waje da gudu suka baro kitchen d'in tea Aiman ya dafawa Ayrah saboda tace iya shi zata sha ya zuba a cup baisa mata komai a ciki ba ya d'auka ya koma d'akin nata tana kwance har lokacin aje kofin yayi yana kallon ta yace.
"Ayrah tashi ki kar'ba kisha magani" ya fad'a yana d'an yaye rufin datai juyi tai da'kyar ta tashi zaune tana jingina bayanta a jikin fuskar gadon tea d'in ya mi'ka mata yana 6allo maganin ya bata kar'ba tai tana sakawa a bakinta tasa ruwan tea d'in ta had'iye mi'ka masa sauran tai zata koma ta kwanta yace "karki kwanta ci wannan ko guda biyu ne" kaita girgiza tana cewa "a'a bazan iya ciba saidai anjima" tana fad'in haka ta kwanta tare da lullu'ba shiru yayi yana kallon ta zuciyarsa na zafi ganin yadda suke neman kasheta da azabarsu Daddy yana sane ya'ki d'aukar mataki shi zai d'auka da kansa zaiyi maganin abun huuuuuuhh ya sauke ajiyar zuciya yana du'kawa ya rufeta kafin ya d'ago yana cewa "shikenan zan tafi idan an jima zan dawo" kaita d'aga a hankali tana cewa "nagode Yaya Aiman Allah ya saka da alkhairi" "Amin" yace yana juyawa ya fita babu kowa a parlon jinjina kai yayi yana wucewa yace "ina daidai daku zan kamaku zakuyi bayani nine maganin ku" saida suka ji fitarsa daga gidan sannan suka samu damar fitowa sukai abinda zasuyi"..................................
✍️Mrs Äl'ämëëñ Ähmäd çë 🌺.
We will meet again.
Yusrah Musa Abubakar YUSEEN AL-AMEEN CE.
TYPING 📲Wed Mar12/25 10:42AM
YUSRAH MUSA ABUBAKAR ✨✨.
👑 ROYALTY 👑
ANNURI WRITER'S ASSOCIATION 💫
Home of hospitality and harmony gidan kar'bar mutane hannu biyu da zaman lafiya ÀÑÑÙRÌ haske le'ka gidan kowa koda ma'kiya na kallon ka ramin kura sai'ya'yan ta haka taken mu yake tafiyar mu babu rago babu maci amana tsantsan gaskiya muke nunawa.
STORY WRITTEN ND EDITING
Yusrah Musa Abubakar Maman little Zarahn Aunty.
3~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Shahidina.
@YUSRAHMS CE
Page 05 & 06
Washe da yake weekend ne Baby tana bedroom har kusan qarfe goma da rabi Khairat tayi iya kokari taga ta tasheta amma ta'ki tashi da tayi magana saidai ta sake gyara kwanciya taja bargo ha'kura tai ta rabu da ita zuwa sha biyu sultan ya shigo yana cewa "Aunty Baby ki tashi" bud'e ido Baby tai tana kallon sa cikin muryar barci tace "meya faru kake tashi na"? Da serious face yace "Yaya Ahmad ne yake nemanki" zaro ido tai tana tashi zaune tace "Yaya Ahmad kuma me zanyi masa nidai nasan ko jiya bamu had'u dashi ba harna kwanta tunda yasa na buge kafata lokacin da zan canzo hijab yanzu kuma yake nemana" juyawa Sultan yayi yana cewa "Nima bansan me zaki masa ba yace dai mu taho tare karna rigaki zuwa" jin abinda yace gashi harya kusa fita daga d'akin yasa Baby mi'kewa da sauri tana cewa "Sultan ka jirani man so kake yaga kamar banji maganarsa ba"? Kai Sultan ya girgiza yana cewa "a'a cewa yayi idan na bari kika rigani zuwa gunsa tunda yau weekend ne wuni zanyi ina hawan bango da tsallen kwad'o" dirowa Baby tai tana cewa.
"Kuma nifa so kake ya kashe ni kenan gara kai zai iya 'kyale ka amma ni yau me cetona saidai Abba dan Allah Sultan ka jirani" tsayawa yayi yana cewa "to kiyi sauri man gaskiya zaki jawo min aiki fa" tun bai rufe baki ba ta d'auko hijab tasa tana cewa "muje to kar lokacin daya d'iba ya fita yana ina"? Fita sukai Sultan na cewa "yana part d'insa fa" a firgice Baby tace "part d'insa kuma innalillahi na shiga uku" ta fad'a daidai sun fito parlor Mami tana zaune amma tsabar rufewa da idon Baby yayi bata lura da ita ba har suka fita suna shiga part d'in su Ahmad da prince Hamid suka fara cin karo zai fita da sauri Baby tace.
"Yaya Hamid dan Allah ka taimaka min" kallonta yayi da alamar tambaya yace "meya faru"? Kaita girgiza tana kallon ko'ina kar tayi magana Ahmad yana kusa ya jita ganin baya nan tace "Yaya Ahmad ne yake nema na".
"Yake nemanki me kikai masa"?.
"Wallahi ban sani ba Yaya Hamid ina kwance Sultan yaje ya tashe ni wai nazo".
"Ok kinga karki d'aga hankalinki ba wani abu bane tunda ba laifi kikai masa ba jeki kar lokaci ya 'kure" ya fad'a yana wucewa ya fita yana fita sukaga Ahmad ya bud'o kofa daga shi sai farar singlet da three quarter d'in wando gabanta ne ya fad'i da sauri ta karasa daidai ya zauna yace "Baby meyasa tun d'azu na tura kiranki sai yanzu kikaga damar zuwa"? Dur'kusawa tai tana cewa "Yaya ina kwana"?.
"Ban kwana ba aiba wannan na tambaye kiba ki bani amsar da nake son ji meyasa baki zo akan lokaci ba raini ko"?.
"A'a wallahi Yaya ban tsaya a ko'ina ba".
"Ok 'karya nake kenan kinzo daidai lokacin da nace ko"? Ya tambaya yana d'agowa ya kalleta da sauri ta girgiza kai tana cewa "a'a dan Allah kayi hakuri" bai tanka mata ba sai Sultan daya kalla yana cewa "kai kuma meka tsaya kallo kana bukatar wani abu ne"? Kai Sultan ya girgiza yana cewa "a'a".
"Fita a nan".
Tun Ahmad ya rufe baki Sultan ya nufi kofar fita da sauri dakatar dashi Ähmäd yayi yana cewa "kai dawo min nan" cak Sultan ya tsaya a yadda ya d'aga kafarsa baiyi gaba ya ajeta ba bai dawo baya ya ajeta ba cike da tsoro ya had'iye yawu.
"Bakaji abinda nace maka ba saina tashi? zomin nan" cikin azama Sultan ya dawo yana zama kusa da inda Baby take yace "kayi ha'kuri Yaya" rufe ido Ahmad yai yana cewa "6ace min da gani" da gudu ya mi'ke yana fita yabar iya Baby wacce ta gama rud'ewa bata son ta ganta daga ita sai Ahmad a guri hakan razanata yake shiru tai tana sauraron taji me zaice amma dai baiyi magana har kafafunta suka gaji sakamakon a dur'kushe take jin suna mata ciwo kuma bata so tayi motsi yace wani abu yasa ta d'aure shi kuwa tun lokacin da yace Sultan ya fita idonsa yake rufe baisan ma a wanne yanayi take ba tayi matukar gajiya amma bata da damar ce masa meyasa ya tsayar da ita haka taci gaba da ha'kuri har yai ra'ayin kansa taji yace.
"Baby".
Da sauri ta amsa dan tasan duk hakan wani tarkon yake son had'a mata tace.
"Na'am"
"Shiga ki wanke min toilet zanyi wanka".
Da mamaki ta d'ago tana kallonsa ganin idonsa a rufe yasa ta samu damar iya kallonsa a ranta tana cewa "ikon Allah salon da kuma ya d'auko kenan yanzu nice zan dawo mai wanke masa toile...............
Bata karasa ba taji yace "Baby mene kike kallo na ko banida matsayin dazan saka ki aiki naga kin shiga jin mamaki ko"? Mi'kewa tai tana cewa "a'a Yaya kayi hakuri bari na wanke maka" ta fad'a tana shiga "ki had'a min ruwan wanka no hot no cool" ya fad'a har lokacin bai bud'e idonsa ba shiga Baby tai tana 'karewa bedroom d'in kallo ya tsaru sosai tabd'i kamar d'akin mace irin wannan kayan 'kyale-'kyale haka abun ban sha'awa har batasan lokacin data karasa gaban wani tsuntsun roba me kama da tantabara ya baza fuka fukansa anyi masa kwalliya da blue da white d'in kala yayi kyau sosai ta kasan kafofinsa an rubuta ZUHRA da manyan ba'ki da sabon mamaki take kallon sunan amma dai ba ita Zuhran yake nufi ba watace dabam dama Yaya Ahmad yana da budurwa a hakan gashi sunan su iri d'aya da alama itama halinsu d'aya dashi dan tasan a yadda Ahmad yake bazai auri mace wacce ba irin ra'ayin sane da ita ba to amma a ina take? Ta tambayi zuciyarta shiru tai can ta tuna abinda ya kawota bedroom d'in ta manta a inda take tsabar shagala da 'kawar d'akin datai afujajan ta wuce toilet ta had'a masa ruwan bayan ta wanke ta fito kenan ya shigo had'a ido sukai da sauri tayi kasa dakai tana cewa.
"Yaya na had'a maka" bai kulata ba saida ya wuce ya kusa shiga bathroom d'in sannan ya dakata batare daya juyo ba yace "ki jirani a parlor kada kije ko'ina" had'iye wani yawun tashin hankali tai da'kyar tace "to" sannan ta samu a hankali ta d'aga kafarta ta fita parlon ta samu guri ta zauna kamar yadda ya umarceta saidai tambayar dake ranta shine akan me zai tsayar da ita me kuma zatai masa to idan tajira shi ya fito me zaiyi mata kodan batai laifin dazai daketa ba shiyasa yake 'ka'kale 'ka'kale dan ya samu mafaka shigowar prince Hamid daya dawo saboda shima ya kasa nutsuwa sakamakon ganin Babyn a part d'in Ahmad kar yaci zalinta yasa ya dawo aiko yana shigowa ya ganta zaune dakatawa yayi yana cewa ''Baby zaman me kike kuma ina Ahmad d'in"?.
"Yana wanka cewa yayi na jirashi kar naje ko'ina" jin abinda tace yasa ya jinjina kai bai sake magana ba ya wuce yana bud'e bedroom d'in Ahmad ya shiga bai fito ba tsayawa yayi har ya gama wankan ya fito ganinsa yasa prince Hamid had'e rai yana cewa "Ahmad meyasa ka tsayar da Baby a parlor bayan ba wata tsiyar zatai maka ba"? Kallonsa Ahmad yayi batare da ya bashi amsa ba ya wuce gaba mirror yana ri'ke da karamin towel a hannunsa yana goge jikinsa karasawa prince Hamid yai yana cewa "Ahmad na sani kana son yarinyar nan tun tasowarta amma meyasa kake koyar da ita jin tsoron ka bazaka ji dad'i ba a gaba fa saboda idan ka aurenta kafin ta saba dakai za'a dau'ki lokaci mai tsawo kai baka tunanin hakan ne"? Kai Ahmad ya jinjina yana had'e yatsun hannunsa guda biyu ya muza suka bada wani kalar sauti kafin yace.
"Bana yi saboda bana son wargi maganar na koyar da ita tsorona wannan ba haka bane ina kula da rayuwarsu ne ta hanyar nuna musu bazasu sake ba idan Ina nan hakan ma tarbiyya ce ba ina takura musu saboda zalunci bane kamar yadda kai kake zatona ina kokarin ganin cewa sun zama na kirki masu ladabi wanda za'ai alfahari dasu fatan yanxu ka fahimce ni Abdul-Hamid Aliyuddeen Sharfaddeen"? Numfashi prince Hamid ya sauke yana cewa.
"Ok na fahimta amma Ahmad abunne yana yawa wallahi musamman akan ita Babyn bakai mata da sau'ki gara Khairat da Sultan ma meyasa kafi matsa mata".
"saboda so".
Kawai shine abinda Ahmad yace yana baro gaban mirror ya dawo ya bud'e wardrobe zai dau'ki kaya prince Hamid dake binsa da kallon mamaki yace "ban gane saboda so kafi matsa mata ba? ba wannan ce amsar daya kamata kaban ba".
"Wacce kake son ji"?.
"So nake ka fad'a min meyasa kafi matsa mata a cikinsu kace wani saboda so niban yarda ba wanda kake so baka son ganinsa a damuwa ko kaganshi yana kuka amma kaifa kaine zaka daketa da kanka sannan kace sone wanne irin son ne wannan da mutum zai ri'ka cutarka kuma yace sone"? Ahmad yana sauraron sa amma bai bashi amsa ba saida yasa kaya ya gama abinda yake sannan ya juyo 6angaren da prince Hamid d'in yake tsaye ganin irin kallon da yake masa yasa ya saki murmushi yana cije lips yace.
"Abdul-Hamid bansan yaushe ka koyi saka ido ba ada babu ruwanka amma yanzu abu ko babu kai saika d'auka meyasa kake shiga rayuwar wani kaima kaji da kanka man"? Qara had'e rai prince Hamid yayi yana cewa "ni ba wannan na tambaye kaba ka fad'a dalilin ka na takura mata shine kawai amsar da zaka ban kuma ka tabbata ka fad'a min abinda zan yarda dakai meyasa wacce kake sonta kafi matsa mata"?.
"Ok kaima kana son koya ne kake so na fad'a maka"? Ahmad ya tambaya yana d'auke masa gira da sauri prince Hamid ya girgiza kai yana cewa "wa nii? Allah ya sauwake na zama mugu dai kamarka bana fata damuwa ta ka fad'a min ta yadda akai mugunta ta zama so"? Murmushi Ahmad yai yana cewa "ta yadda ake yi man saboda ina sonta yasa nake takura mata nake bata horo a koda yashe domin nine zan zauna da abata sannan son da nake mata bana yi mata ko kaina bana yiwa na damu da ita fiye da yadda kake tunani bana jin dad'i idan har ban ganta ba domin itace mahad'in rayuwata mother of my kids bani da kamarta fatan yanzun ka gane abinda nake nufi"?.
Wani kallon uku saura kwata prince Hamid yayi masa a she'ke yace "au haba a hakan ta zama duk wadannan abubuwan daka lissafo"? Kaiya jinjina yana cewa "kwarai kuwa ko kana tantama ne"?.
"Eh taya kake tunanin zan yarda dakai da abinda ka fad'a"?.
"Ta yadda ake yarda man".
"Toni bazan yarda dakai ba Ahmad domin ba gaskiya bane abinda ka fad'a kawai dai kayi hakan ne dan ka kare kanka kuma baka isa ba".
"Ok zaka hana kenan a bani ita tunda kaine ka haifeta ko"?.
"Ban haifeta ba amma idan nacewa Abba ya hanaka aurenta ko kuma naje gurin Sultan Sharfaddeen nakai 'kararka akan abinda kake mata shikenan na kashe case d'in taka tazo karshe zaka gane kurenka kaima ka koma hannun 'yan sari".
"Da gaske? Humm idan kai haka zaka matukar burgeni saidai ka sani ko ramin gyare zaka kai qara ta bazan fasa auren Baby ba idan kuma kaga ban aureta ba to d'ayan biyu kodai ita koni wani ya mutu ko kuma dama can ita ba matata bace domin wannan yarinyar da kake gani rayuwata ce ita bani da kamarta kaima kasani saidai ka'ki fad'ar gaskiya sonta a raina yake duk wani motsi da zanyi da sonta nake motsawa I hope yanzun ka yarda"? Kai prince Hamid ya girgiza yana cewa.
"Da sau'ki dai".
"Ok baka yarda ba kenan"?.
"Eh kusa da gun idan kana so na yarda dakai da abinda ka fad'a to daga yau karka qara dukan Baby ko kuma ka daina mata tsawa sannan ka dawo lalla6ata ta yadda zata saki jiki dakai har itama ta daina tsoronka ta kamu da sonka domin yanxu itakam a cikin zucuyarta tsoron kane fal ya cikata da ace tasan kana sonta to wallahi da tsoronka da zataji sai yafi haka maybe kasa zuciyarta ta buga ko ta kamu da ciwon firgita shiyasa nake sake fad'a maka abinda