x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 18 - ROYALTY YAN SARAUTA

  • 51001 words
  • 54000 words
  • Out of 85109 words

Category: Love Stories

Views 1679

20 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
amma ita kad'ai sai murmusawa take saboda wani lokacin idan ta tuna cewa Ahmad ko bakai masa lefi ba zai nemi d'an wani abun damuwa ya d'ora maka dan kawai ya dake ka ko ya saka punishment dariya ta saki tana aje littafin itama ta kwanta a kusa da Khairat................✍️Mrs Äl'ämëëñ Ähmäd çë 🌺.

See you tomorrow morning.
Tnks for ur supports 🔥.
Be with me at always my lover's.

TYPING 📲 Mon April/2025 8:56am
YUSRAH 🤞 MUSA 🤞 ABUBAKAR

👑 ROYALTY 👑

💫A*W*A💫
Home of hospitality and harmony
ANNURI haske daga Allah marubuta masu hazaka hikima da sanin ya kamata masu cike da baiwa da basira mahankalta ma'abota iya magana da sarrafa harshe.
____________________
_____________________________
_____________________________________

In the name of Allah the must benefits and the must merciful ALLAH THE MOST HIGH DOESN'T SLEEP ALLAH THE MOST HIGH IS PURE HE ACCEPT ONLY WHAT IS PURE.
Manzon Allah SAW
May the blessings and the peace of Allah be upon you ya rasulullah muna sonka fiye darai da iyaye da dukiya no success with you, you the light of every darkness you have no limits.

12~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Qaiminah.

Bismilllahir Rahmanur Rahim 📿

@YUSRAHMS CE
Page 23 & 24
Maryam tana ta dakon dawowarsu part d'in ta shirya bala'i iri-iri amma shiru har dare taga basu sake le'kowa ta ciji yatsa ta qara kamar zata fasa ihu haka take jin takaici ji take a ranta inama zata iya dawo da d'azu da babu abinda zai hana taiwa Baby mugun dukan halaka wanda koda a gaba akace tai mata kallon banza bazatai ba amma hakan ma ba ha'kura tai ba tana nan da ita ta kasa ta tsare jira take ta shigo part d'in kawai ta dam'ki wuyanta ta matseta sai taga ta kusa mutuwa numfashinta yana shirin fita kodama ace zata barta ganin ba dawowa zasuyi ba gashi kusan qarfe tara da rabi tayi harta kwanta ta mi'ke tana d'auko hijab d'inta ta fito tayi sa'a kuwa Ahmad yana gurin Momy wani irin daddad'an numfashi ta sauke da sauri ta karasa tana zama ta sauya fuska ba walwala muryarta da yanayin damuwa kamar zatai kuka tace.

"Momy ina yini"? Kallonta Momy tai sosai ganin yanayin ta da yadda take sunkuyar dakai yasa ta fahimci akwai abinda take so amsa mata tai tana cewa "Maryam lafiya kuwa naganki a haka kamar bakya jin dad'i ina su Khairat d'in ko har sunyi barci ne saike kad'ai suka bari"? Kaita girgiza kuma ta'ki ta d'ago ta kalli Momyn dan karta gane cewa abinda zata fad'a mata 'karya ne.............

"Ina jinki Maryam meya faru"?.

Kukan 'karya ta fashe dashi tana goge ido kamar gaske tace "Momy me nayiwa Khairat ina matsayin 'yar uwarta amma dan nazo gidan nan kamar wacce a kanta nake xaune tun ranar da nazo ta sauya min fuska babu maganar arzikin da zata shiga tsakanin mu sannan ta daina kwana a part d'in nan bansan inda suka koma da kwana ba ni kad'ai nake kwanciya kamar wata mayya ban Isa nayi wargi a cikin su ba sun had'e min kai ita da wannan yarinyar Baby gaskiyar ban ta'ba tunanin hakan daga Khairat ba da wani ne yace idan nazo zata wula'kanta ni bazan yarda ba saida na gani da idona wai d'an uwanka ya ri'ka ma kallon banza sabida kazo gurin sa" ta karasa maganar tana sake fashewa da sabon kukan 'karyar da take yi Momy data zuba mata ido tana kallon ta kuma tana sauraron abinda take cewa har takai aya daga ji tasan wannan ba gaskiya bace had'i ne kawai irin na Maryam Khairat bazata ta'ba yi mata wani abun rashin dad'i ba amma saboda kar tace ta baiwa 'yarta gaskiya ita kuma ta bata rashin gaskiya tunda d'an Adam ba'a iya masa sai tace.

"Subahanallahi Khairat d'in ce meyin duk wadannan abubuwan batare dana sani ba meye ya had'aku da farko ai naga lokacin da kika zo tana ta murna sai hira kuke kuna dariya cikin nishad'i amma ko sati baki ba har kunyi fad'a yanzu ina ita Khairat d'in take"?.

"Ni bansan inda tai ba tunda suka fita ban sake ganin ta dawo ba wai sunbar min part d'in na dafa na cinye tunda na gaji maita".

"A'a subahanallahi baki gaji maita ba sannan bazaki dafa ki cinye ba sunyi hauka ai ba'ko mutum ne me girma da karamci wanda zaka karrama shi kake nan nan dashi amma su sai suke miki irin haka? Kiyi hakuri zanyi musu fad'a gobe idan Allah ya tashe mu lafiya zan sa6a musu indai sun tabbatar min cewa hakane abinda kika fad'a".

Ko kunya babu Maryam tace "wallahi hakane gaskiya na fad'a miki Momy kamar ni ace wannan yarinyar Zuhra take kowa sunan nata bai dameni ba? Humm wai akan Ahmad yace na tambaye su waye shi d'azu bayan ya tafi na tambaye su ta hau yimin rashin kunya tana zagina tsinuwa iri iri da ashar kamar wacce nayi wani abun muniya daga tambaya wai kuma a hakan har fad'a take waisu 'ya'yan sarakuna ne jikanun sarki da sarauniya ba'a ta'ba su a wanye tafiya izza da girman kai a jininsu take".

Baki bud'e Momy kebin Maryam da kallo yanzu kam tasan 'karya take Baby bazata ta'ba yin wannan abinda ta lissafa ba domin ba irin tarbiyyar da aka koya musu ba kenan "Babyn ce ta zageki sannan ta fad'a miki dukkan wadannan maganganun marasa dad'in ji"?.

"Kwarai itace Momy ai zagin datai min bazan iya maimaitawa ba saboda muninsa taci mutuncina sosai d'azun nan ta wulakanta ni fiye da kima gaskiya Momy kiyi mata fad'a haba yarinyar nan kamar mara nutsuwa haka take abinda taga dama bayan ta qare min zagi harda cewa tasan karshe dawa zan had'ata bazai wuce Ahmad ba kuma shima ba tsoronsa take ba kawai dai tana d'aga min qafa ne da taga ni ba'kuwa ce kiji fa Momy idan ba rashin kunya ba Ahmad ba yayanta bane? Amma cewa tai shima yayi kad'an yace zaiyi mata wani abu ko yad'au mataki a kanta zagin datai min kuma ta zagi banza ba wanda ya isa tararta da wata jakar magana akan abinda tai min".

Kai Momy ta girgiza tana sakin murmushin da bata shirya ba domin wannan wasan 'kwai'kwayon da Maryam ta shirya batai nasara ba ko Ahmad baya duniya qarewarta kenan ta tabbata Baby bazata ce bata tsoronsa ba ko tace babu wanda ya isa ya hukunta ta balle tasan yana cikin gidan hum ta fahimci ba zaman lafiya ya kawo Maryam gidan ba babu wata ziyara da tazo musu kawai tazo d'aga musu hankali ne dole zata dakatar da ita dan bazai yuwu ta ri'ka shiryo 'karya tana zuwa tana karanta musu ba dan ta zama gizo.................................

Katse mata tunani Maryam tai ta hanyar cewa "kuma abun ba'kin cikin ma harda Khairat itace me taya ta tana zugata ta wulakanta ni wai nazo musu gida zanyi kwad'ayi ina gidan ubana da bazan zauna ba ko baza'a iya ri'ke ba shiyasa ta tattaro na dawo musu nazo ina addabarsu to suna daidai dani idan ban had'a tsunmokara na nabar gidan nan ba wata rana sai sun yimin dukan dazan kasa tash..................

Bata karasa ba Momy tace "kinga Maryam kiyi shiru haka ya isa dan Allah bana son sake jin komai indai su Khairat ne kiyi hakuri zanyi magana dasu tashi ki tafi ki kwanta Allah ya tashe mu lafiya" shiru Maryam tai zuciyarta babu dad'i wanda tazo tana yin maganar danya tanka harta gama ko kallon inda take baiyi ba balle tasa ran zaice wani abu zazzafan huci ta fitar tana mi'kewa kamar zata rufe Momy da duka akan tafiya ta kwanta d'in da tace tayi da'kyar ta mi'ke tana turo baki tace "saida safe" ko jiran amsar da Momyn zata bata batai ba fuuuu ta wuce tana bud'e kofa ta shiga tana rufowa da qarfi kai Momy ta jinjina tana bin kofar da kallo zatai magana Ahmad da yaja tsaki yace.

"Momy zaman me take banga amfanin zuwanta ba tunda tazo gidan nan take had'a fitina da damuwa a tsakanin yaran nan suna zaune lafiya haka kawai ta baro gidansu taxo ta d'aga musu hankali to wallahi bata isa ba ki fad'a mata sa'ko daga ni ta had'a kayanta ta koma gidansu idan ta'ki zataga sakamakon taurin kai zan nuna mata niba sa'an wasan ta bane tsabar ta rainawa mutane hankali Babyn ce zata iya fad'ar duk wadannan stupid d'in maganganun data lissafa ai daga nan zaki fahimci zama tai ta shirya kayanta nasan halin 'kannai na nasan abinda zasu iya da wanda bazasu iya ba dan haka ki fad'a mata tayi taka tsantsan karta kuskura na sake jin bakinta ya shirya wasu banzayen kalamai sannan ta jigina su tace Wai Khairat da Baby ne suka fad'a idan ta sake ranar zata ga 6acin raina dan zan nuna mata tayi kuskure".

Sauke ajiyar zuciya Momy tai tana cewa "gaskiya ne Ahmad dukkan zancen nan da Maryam ta fad'a babu 'kamshin gaskiya a ciki kawai dai na biye mata ne kartaga kamar ina goyon bayan su wulakanta tane nikuma duk d'aya suke a gurina bana bambanta su itace take kokarin saita fahimci a wanne irin muhalli na ajeta".

"Ok abinda take son sani kenan? Ta samu zan sanar da ita Allah yasa na sake jin ta maimaita hauka irin wanda tai yanzu na rantse da Allah ranar saita kwana da tsattsaman jiki babu ruwana da girmanta indai tai abinda ba daidai ba saina hukunta ta kamar yadda nake hukunta su Khairat" yana fad'in haka ya mi'ke yana shirin fita yace "goodnight Mom ki huta lafiya"? "Ok Ahmad Allah ya kaimu saida safe" yana fita Momy ta mi'ke taje ta saka lock a kofar kafin ta dawo ta wuce part d'inta Maryam dake la6e tana jin komai hawayen ba'kin ciki ne ya zubo mata ba maganar da Ahmad yayi ne ta 6ata mata rai ba a'a ganin datai har lokacin bata fara samun lambar yabo wacce xata samu shiga a gurinsa ba shine ya sakata kuka ashe dama duk wankan da take d'auka da kwalliyar da take yi baya gani a banza takeyi ko kallo bata ishesa ba balle ta fara kokarin jawo hankalin sa sakin kofar tai tana kuka taje ta d'au wayarta a daren karfe sha d'aya tayi amma bata lura da wani lokaci ba saboda tashin hankalin da yake gabanta Mama take kira burinta kawai ta d'aga suyi magana Kota samu salama.

Mama tana kwance a bedroom Abban su Maryam shi kuma yana gaban laptop yana rage aiki yaji wayarta na ringtone da mamaki ya kalli Mama da ke sharar barci kamar ya tashi ya duba waye me kira a wannan daren sai kuma ya fasa ya mayar da hankalinsa kan aikinsa jin an sake kira yasa yai tsaki yana tashi yaje har inda take kwance ya tasheta cikin magagi Mama ta bud'e ido tana cewa "Alhaji lafiya kake tashi na" batare daya bata amsa ba ya juya yana komawa inda yake da mamaki ta tashi zaune tana kallonsa zatai kira na uku ya shigo zaro ido waje tai cike da fargabar waye yake kiranta a wannan daren kodai akan haka Abba yai fushi da sauri ta dau'ki wayar tana kallon number Maryam jikinta na 6ari ta kasa d'agawa har kiran ya katse kallonta sosai Abba yai yana cewa "Waye yake kiran wayarki a wannan daren"? Kai Mama ta girgiza cike da tsoro muryarta nadan rawa tace "Maryam ce" jin abinda tace yasa baida niyyar d'agowa amma saida ya daina abinda yake yi ya kalleta kamar bazai tanka ba sai kuma.

"Maryam dai me zatai miki a wannan daren nifa irin haka ne bana so hankalina bai kwana da yarona yaje wani guri har yayi kwanaki ba kawai dai na barta ne saboda naga gurin yayarki zataje amma badan haka ba wallahi babu inda ta isa taje a wannan yanayin da ake ciki tana mace bana so ta ri'ka nisa da gida" shiru Mama tai tana rarraba ido ta kasa magana sai numfashi da take saukewa kamar wacce tai gudu ganin duk tabi tayi tsuru-tsuru yasa yad'an girgiza kai yana mayar da hankalinsa kan aikinsa bai sake ce mata komai ba Mama da jikinta ya gama sanyi so take tayi masa bayanin abinda zaiji ya gamsu kuma ta kasa sannan tabi bayan kiran Maryam d'in nan ta kasa kusan rabin awa tana zaune ta kasa kiranta domin batasan me zatace mata ba saboda Abban kar yaji abinda suke shiryawa ya hana ita kuwa tasa a ranta cewa koda ace aurenta zai mutu indai burinta na Maryam ta auri Ahmad zai cika bata da matsala zama bazawara ba damuwarta bace tunda ba'a kanta farau ba kafinta an saki wasu bayanta ma za'a sake wasu tunda tasan idan Maryam d'in ta aureshi akwai jin dad'i gani take hatta gidan da zata zauna Ähmäd ne zai gina mata.....................

Sabon kiran da Maryam tai mata neya dawo da ita daga duniyar tunanin data fad'a da sauri ta mi'ke tana dirowa daga kan gadon ba arziki ta nufi kofa ta bud'e ta fice Abba daya bita da kallo ya jinjina kai kawai yaci gaba da uzirinsa ita kuwa Mama part d'inta ta shige har bedroom ta shiga toilet tai qasa da murya tana d'aga kiran tace.

"Hello maryam kina jina? Ina jinki meya faru kike kirana a daren nan kinsa Alhaji zai zarge ni"? Mama na rufe baki Maryam ta fashe mata da kuka tana cewa "Mama gaskiya bazan iya ba wallahi na gaji kaina bazai d'auka ba tun daga yanxu na fara kwasar ba'kin ciki a gunsa taya kuma zan shawo kansa wallahi nikam bazan iya wannan masifar ba da kinji irin maganganun daya fad'a min d'azu Wai saiyai min dukan hallaka sabida wata shegiyar cousin d'insa ta zageni nakai qararta gurin Momy yayi min tas yace qarya nake yi nikam na gaji Mama gida zan taho bazan iya ba ha'kurina yaje karshe".

Jin abinda take cewa yasa cikin kad'uwa Mama tace ''ban gane bazaki iya ba kenan ha'kura zakiyi dashi ki dawo gida ki zauna tare damu kome naji kina wata magana wacce bata gamshe niba"?.

"Eh Mama gida zan taho domin zamana anan bashi da wani amfani kawai 6ata lokaci nazanyi Ahmad bazai ta'ba kallona ba balle ya soni da kinji abinda yake cewa d'azun wallahi kema abun saiyai miki ciwo a ranki baza kiso na sake koda sakan d'aya ne a gidan nan ba dan haka nikam gobe tun asubar fari zaki ganni bazan qara zuwa gidan nan ba na ha'kura da Ähmäd" ta karasa maganar tana sake rushewa da kukan ba'kin ciki.

Hankali tashe Mama tai saurin girgiza kai kamar Maryam d'in tana ganinta tace "a'a kul na haneki karki kuskura kiyi wannan gangacin karna ga kafarki kin dawo gidan nan saidai idan Ahmad shima yabar gari kin gane ki qara ha'kuri yaushe ma kikaje gidan da zaki fara 'korafi ai dole saikin dad'e dama koda ma ace zai saurareki".

"Wallahi mama nikam na gaji bazan iya ba haka kawai zan zauna yana yimin kallon banza shegiyar cousin d'insa tana zagina da fad'a min ba'ka'ken maganganu na cewa gidansu naje na sameta ba itace tazo ta sameni ba abun ba'kin cikin harda Khairat a ciki" takaicin maganar da Maryam ke fad'a ya gama rufe Mama ji take inama zataga Maryam a yanzu da take mata wannan sakaryar maganar da saitayi mata dukan tsiya meyasa bazata kamasu tai musu duka ba tana zaune suna zaginta idan Maryam d'in bazata iya dasu ba ita zataje har gidan taci ubansu a gaban Momyn tunda tana sane ta bari suke mata abinda suka ga dama.........

Kukan da Maryam take harda shid'ewa yasa Mama ta sake harzu'kowa a masife tace "ke dan uwarki ki rufa min baki shashashar banza kawai kenan tunda kikaje uwar me kika tsaya kallo baki abinda ya kaiki ba sai yanzu zaki kirani da daren nan ki dameni da kuka dan kisa na kasa komawa barci na kwana ina tunani"?.

"Nayi iya yina Mama na ko'karta kamar nayi hauka amma Ahmad ko mutum bai mayar dani ba kamar package ka cire abinda yake ciki ko wani abu mara amfani haka ya mayar dani ko saurarata bayayi gashi ya kusa tafiya inaga bazai sake kwana biyu ko uku ba gaba zai koma" dafe 'kirji Mama tai tana cewa "ya kusa tafiya kuma na shiga uku Maryam zaki d'ora min masifa da bala'i me kike son cewa ya kusa komawa bakiyi 'ko'kari kinyi wani abu dazai amfane muba"?.

"Nayi wallahi nayi Mama kawai Ahmad ya fita dabam ne a cikin maza yana da wuyar sha'ani baya yin abinda bai dameshi ba baya shiga safgar daba tasa ba bayayin abinda yasan bame amfani bane a gunsa da ace Abdul-Hamid ne matsayinsa da duk haka bai faru ba wallahi ko kaffara bazanyi ba da ace shid'in ne da yanzu an wuce gurin na tareshi na fad'a masa abinda ke raina kuma nasan zai amince min amma shifa na tabbata idan yasan ina sonsa maybe karshen ala'ka ta dashi kenan kona jawo ya koroni daga gidan".

"Ya koroki saboda kinje gidansu humm aiko wallahi bai isa ba zanyi magana da Auntyn nizan kirata na fad'a mata dalilin zuwanki da zamanki a gidan inyaso ita saita fad'a masa na tabbata indai yaji haka shikenan ai ko baya sonki yasan kina sonsa sannan batu ya biyo ta gurin mahaifiyar sa idan tace masa ya aureki dolensa ya amince ko baya so shiyasa nake fad'a miki ki qara ha'kuri nasara tana gaba idan gari ya waye ki saki ranki karki nuna wani abu ma ya faru ki nuna musu bariki har ita wancan yarinyar da kike magana akai ki sharesu kawai kiyi abinda ya kaiki ki manta dasu kinji"? Kai Maryam ta d'aga tana goge fuskarta tace "ok shikenan Mama na fahimta zanyu yadda kikace" "yauwa Maryam har kinsa naji dad'i ki tsaya ki nutsu kiyi abinda ya kaiki ni bari na koma kar Alhaji yaga na fito na dad'e" "ok Mama saida safe"? "Tom mu kwana lafiya" ta fad'a tana cire wayar a kunnenta tare da tsayawa tana jinjina kai ta ciji yatsa tana cewa "tabd'ijan amma lallai Maryam tsabar d'anyan kai kice zaki dawo gida batare data kin jawo hankalin Ahmad kanki ba humm wallahi bazan amince hakan
End Ads