x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 28 - ROYALTY YAN SARAUTA

  • 81001 words
  • 84000 words
  • Out of 85109 words

Category: Love Stories

Views 1681

20 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
mi'kewa yana sake kallon jikinsa yana kuma tunanin taya zai fita ya tafi gida idan ya cire rigar daga Nan Kuma ya fita da ita a hannu karya had'u da Mama ko Amaan su tambaye shi wani abu tuna hakan yasa ya zaro towl karami daga aljihun shi ya goge duk inda miyan ta 6ata masa duk da ba fita yai ba kawai dai ya ragene bud'e kofa yayi ya fita yana fatan Allah yasa karya had'u da kowa yayi sa'a kuwa domin Amaan baya gidan Mama ma bata parlor da sauri ya wuce harabar gida ya shiga motarsa ya nufi hanyar gate yana yiwa me gadi horn yazo ya bud'e masa ya fita ya sani idan yaje gidansu a haka zaisha fad'a a gurin Ummansa dan haka bai nufi hanyar gidan nasu ba ya tafi nasa gidan kawai gara yaje can yayi wanka ya canza wasu kayan inyaso saiya koma hakan zaifi.

Humm Maryam kam tana gama fad'a masa wadannan maganganu da watsa masa miya ta fita direct part d'in Mama ta shiga ai kuwa ta sameta sai zaga bedroom d'in take tana goye da hannunta a baya ganin Maryam d'in ta shigo yasa da sauri ta tsaya tana cewa "yaya ya kukai dashi me kikace masa fatan kinyi abinda bazai dawo mana gida ba ko"? Kai Maryam ta jinjina tana cewa "kwarai nasan har abada bazai manta da hakan ba shiyasa na Kona masa rai zuwa nayi na tarar da ya Amaan acan ya sakani na d'ebo drinks da snacks nakai masa Wai hakan bai isaba saina dad'o Niko na d'ebo masa shinkafa na d'ebi Miya da yawa a kwano ina ganin ya Amaan ya barmu mu biyu na d'auke kofin dayasa na xuba masa juice a ciki na kware masa shi a kansa sannan hakan ma da naga bai gamsu ba na dau'ki miyar itama na watsa masa ita a jikin farar shaddar sa sannan na fad'a masa munanan kalamai marasa dad'in ji nasan yanzu kam shikenan dole xai barni bazai sake waiwayata ba" kai Mama ta jinjina tana sakin murmushin jin dad'i da farin ciki tace "yauwa 'yar albarka naso ace kin had'a masa harda mari dan yasan da gaske ba sonshi kike ba amma hakan ma ya fahimta komai ya wuce".

"Komai bai wuce ba Mama kinsan zai iya idan yaji gida uwarsa ta gani yace nice ita kuma ta fad'awa mahaifinsa daga Nan magana ta dawo gurin Abba na shiga uku nasan ya Amaan ma saiya kusa kasheni dan duka shiyasa gara naje gidansu har gaban gyatumar tasa na sake masa masa warning dan tasan d'an nata bai samu kar6uwa ba yaje can ya nemi daidai dashi ya aura".

"yauwa shikenan ma hakan zakiyi karshen abun kenan maza jeki kar lokaci ya 'kure mana idan kin dawo mayi maganar a nutse itama uwar tasa idan ta kawo miki rainin wayo ki mata tsiyal zagi irin na tsamar nama zakiyi mata indai ta shiga safgarki ki nuna mata ita tsohuwar banza ce bata iya haihuwa ba 🙊".

"Ok Mama bari na dawo" ta fad'a tana juyawa ta fita motarta ta d'auka kanta tsaye babu wata fargaba kojin tsoro taje gidansu har lokacin Ashraf bai koma ba yana can gidansa Ummansa na zaune a parlor taga Maryam ta shiga ti'kas ti'kas babu ko sallama taje har gabanta kamar zata rufeta da duka ta ri'ke 'kugu tana cewa "kece mahaifiyar Ashraf ko? Kodan basai na tambaya ba da gani babu tambaya ai ga kamanni nan na gani to bari kiji ba zama ko tambaya ya kawoni ba zuwa nayi na fad'a miki idan d'anki ya dawo ki fad'a masa ya fita daga gonata niba sa'ar aurensa bace nafi karfin auren banza irinsa karya kuskura na sake ganinsa a gidan mu idan tsautsayi ya sake kaishi zanyi masa abinda har abada bazai manta dashi ba ki fad'a masa sa'ko daga Maryam kiyi masa albishir cewa abinda nayi masa yau wanda zanyi masa a gaba sai yafi wannan muni" tana fad'in haka ta juya fuuu ta fice da kallo Hajiya Rabi'atu ta bita cike da tsananin mamakin wace wannan yarinyar meya had'a su da Ashraf itafa kamar naso ta gane wacece ita kamar Maryam d'in Hajiya Halima kodai itace? (Abinda yasa bata santa ba saboda iya mahaifin Maryam da mahaifin Ashraf ne suke abota amma su a junansu ba ruwan kowa da kowa shiyasa Hajiya Rabi'atu batasan Maryam bace kawai kama tagani ta gane) kaita jinjina a ranta tana cewa "Kai babu wata tantama itace amma meya had'a su me Ashraf yaje yi gurinta tazo min har gida tai min fitsara bari ya dawo naji aiko indai yace min sonta yake kafin ya rufe baki saina daukeshi da mari yadda tazo ta tsiyata ni d'in nan wannan yarinyar bata da tarbiyya bata gaji arziki ba" mi'kewa tai ranta a 'bace ganin bazata iya jiran dawowar saba gara ta kirashi yazo taji meye ya had'asu dan bazata sake d'aukar raini irin haka ba yanzun ma jira take ta kirashi taji indai bashi da laifi tayi mata haka har gida zataje taci uban Maryam d'in domin ita mace ce me zafi ba'a kawo mata raini...............Mrs Äl'ämëëñ Ähmäd çë.

See you tomorrow morning
Be with me at always my lover's.

TYPING 📲Wed, Apr/9/25 7:56AM
YUSRAH MUSA ABUBAKAR 🤘💯.

👑 ROYALTY 👑
(Girman sarauta _ 'yan sarauta)

WhatsApp no:+234 816 098 3083
Mrs Äl'ämëëñ Ähmäd çë.

ANNURI WRITER'S ASSOCIATION 💫
Home of hospitality and harmony gidan kar'bar mutane hannu biyu da zaman lafiya ÀÑÑÙRÌ haske le'ka gidan kowa koda ma'kiya na kallon ka ramin kura sai'ya'yan ta.

S*W*E
✍️Yusrah Musa Abubakar Maman Fatima Zarah Elham little Zarahn Aunty Momyn Ashraf.

18~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil hafizinah.

Bismilllahir Rahmanur Rahim 📿.

@YUSRAHMS CE
Page 35 & 36.
Lokaci ya wuce da yawa kwana da tashi asarar me rai tafiyar Ahmad yau shekarar biyu cis baizo gida ba ko kad'an su baby har sunyi graduate sun d'ora sabuwar makaranta Shadad shima yazo gida sau d'aya yaga su Mami yana komawa kuma dama saura shekara d'aya ya kammala degree d'insa shikenan ya dawo gida ya bud'e babban company wanda yake juya gwala gwalai da sarrafa su amma a wannan karon ma yazo zaiyi azumi saboda sun samu hutu sai bayan sallah shima Ahmad da sukai waya da Momy yace mata wannan shekarar a gida zaizo yayi azumi su Baby tunda sukaji haka suke shirye shiryen zuwansa da taka tsantsan tun kafin ya dawo kowa ta shiga taitayinta ranar da aka fara azumi na farko sunyi tunanin zasu ganshi sai sukaga shiru haka washe gari ma har dare babu labarin sa kullum zuba ido suke su ganshi har akai goma baizo ba kasa ha'kuri Baby tai suna zaune tare a parlon Momy take cewa.

"Nikam Momy na tambaye ki man Yaya Ahmad koya fasa zuwa azumin ne"?.

"Nima ban sani ba Baby saidai ki tambayi Abdul-Hamid ko sunyi waya dashi ya fad'a masa ya fasa amma meyasa kika tambaya"? Gyara zama Baby tai saboda tasan baya nan tace "Momy naga har anyi goma bai zo bane shiyasa nayi tunanin ko fasa zuwan yayi"? Kallonta Khairat tai cikin tsokana tace.

"Au marmarin zuwansa kikeyi kenan kamar wanda zai kawo miki abun dad'i kodai kewarsa kike"? Gwalo ido waje Baby tai tana cewa "naji kewar wa tabd'i na rasa wanda zanji kewarsa sai ya Ahmad uhm amma dai fad'a kike dan dad'in baki ko"?.

"A'a ba fad'a nake ba da gaske nake miki maganar ba wasa nasan meye a ranki tunda zuciya ba ganinta ake ba"..

"Uhmm babu abinda yake raina sai alkhairi".

"Ai dama alkhairin ake so kuma nima alkhairin na fad'a ni dama nafi son idan zuwan ma zaiyi yazo baki a bud'e lokacin mun koma school aidai mun rage zaman gida ba kamar yanxu da kullum muna nan idan ba'a same mu a gurin Momy ba za'a ganmu a gurin Mami ko 6angaren su Sultan kinga kuwa ai bamu huta ba ka sayar da akuya tazo tana goga maka danga idan kuwa muna school saifa lokacin da muka dawo".

"Haka ne to Allah yasa ma sai bayan sallar zai daw.......................
Jin 'karar tafiyar takalmi yasa Baby bata karasa ba tai saurin juyawa tare da Khairat lokaci guda suka zaro ido ganin Ahmad ya shigo sanye da kayan soldier fuskarsa a rufe da facemask duk 'kamewa sukai musamman Baby data tabbatar yaji maganar da takeyi kuma yasan a kansa ne gashi yayi musu gargad'in karya sake jin sunyi murna akan tafiyarsa, tsaye yayi ya zuba musu manyan idonsa wanda tsoro yasa babu wacce jikinta baya rawa a cikinsu kaiya jinjina batare dayace musu komai ba ya juya ya fita daga parlon saboda Momy bata gurin ta jima da tashi ta shiga part d'inta .

Babu wacce bata sauke numfashi ba a cikinsu ganin ya fita baice musu 'kala ba maybe zuwa zaiyi ya cire Kaya ya dawo mi'kewa baby tai tana kallon Khairat tace "please Aunty Khairat dan Allah taso mu bar part d'in nan mu tafi gurin Sultan Sharfaddeen kafin ya Ahmad ya dawo wallahi idan har ya dawo yadda ya jinjina kan nan sai mun kwana namu kan yana ciwo kinsan ba ruwansa da azumi mukeyi idan yaga damar cin ubanmu" ta karasa maganar tana mi'kewa itama Khairat d'in tashi tayi saboda tasan abinda Babyn ta fad'a gaskiya ne bazai duba azumi ne a bakinsu ba indai yaga dama saiyace zai hukunta su shiyasa ma suka nemarwa kansu mafita suna shirin fita Momy ta bud'o kofa tana cewa.

"Ina zuwa haka a cikin wannan ranar"?.

"Gurin Sultan zamuje ziyara".
"Amma duk da baku tashi zuwa ziyarar ba sai yanzu da tsakar rana haka kodai bakwa jin azumin yau d'in ne"?.

"Eh Momy badan son ransu zamuje ba akwai dalili ne".
"Wanne irin dalili"? Kamar Baby zata kuka gudun karya dawo ya samesu tace "laifi mukaiwa ya Ahmad"..

"A Ina kukai masa laifin bayan baya nan".

"Ya dawo fa yanzu ya shigo part d'in nan ko kayansa bai cire ba".

"Ok ya dawo amma har kukai masa laifi daga dawowar tasa".

"Su6utar baki nayi Momy bansan yana kan hanyar shigowa ba nace Allah yasa karya dawo sai bayan sallah ina fad'a najishi a bayana shiyasa daya jinjina kai ya fita nacewa Aunty Khairat mu tafi gurin Sultan kar da azumin nan ya bamu wahala koya saka mu watering a rana" murmushi momy tai tana fitowa ta zauna tana kallon su tace "ok sai kun dawo ku gaishe min dasu" tana rufe baki wuf sukai waje har rige rigen fita suke amma me can nesa suka hangoshi da alama shima inda suka nufa ya tafi humm ba arziki suka juya da gudu suna yin part d'in Mami ko tsayawa a parlor basuyi ba tana magana ma inaaa basu jita ba hankalinsu yayi gaba da gudu suka fad'a bedroom d'in su suna sanyawa kofar lock kowa tana fitar da numfashi kallon juna sukai suna dariya baby dake dafe da 'kirji tace.

"Kai Allah ya tsare mutum ya zama kamar wani dodo a riga gudunsa" zama Khairat tai tana cewa "toda meye idan ba dodon ba tunda tsoronsa muke yi Yaya Abdul-Hamid aiba haka muke masa ba sannan Yaya Shadad koke kinsan ba haka muke masa ba aidai shine ma za'a ce yana da zafin rai irin na ya Ahmad d'in amma ai yana sake mana muna zama muyi hira dashi harda dariya idan kinga fushinsa ko d'aure fuskarsa saikin yi masa laifi shi kuwa boss Ahmadi me zamani fa"? Dariya baby tai itama tana zama tace .

"Wa yaga Ahmadi humm idan tsokanarsa kike sonyi saidai kice Amadu inaga yafi kayan haushi akan kice masa Ahmadi ga wanda kika 6ata sunan sosai zaifi d'aukar zafi" gwalo ido Khairat tai tana cewa "ni kaza mijina zakara ban shirya cin sallah da tabo a jikina ba".

"Aina d'auka a shirye kike uhm Allah yasa dai bamuyi masa laifi ba dan nasan idan yaga ya neme mu ya rasa d'in nan ma sai yace munyi gudunsa ne nidai har asha ruwa bazan koma part d'in Momy ba saidai idan barci zamuyi bari ma kiga nad'an kwanta na matse kafin a kira sallah" ta fad'a tana hayewa gadon kallonta Khairat tai tana murmushi batace komai ba kuma ita bata kwanta ba sai tuna diramar su kawai take tana dariya gasu da tsoro ga son suyi gulmarsa.

Koda dare basu yarda sun shiga part d'in Momy akan lokaci ba saida suka tabbatar daya gama zamansa yabar part sannan suna rarra6awa suka je suka kwanta washe gari kuwa suna yin sallar asuba suka sake guduwa part d'in Mami sukai kwanciyarsu acan suka koma barci har wajen sha d'aya da rabi Khairat ce ta fara tashi tabar Baby a kwance saidai ta tasheta tace mata wanka zatai itama ta taho gurin Momyn shiyasa Khairat d'in tayo gaba tayi sa'a ita kad'ai ce kamar yadda tayi fata babu kowa zama tai tana gaida ita daidai Momy ta amsa idon Khairat ya sauka akan wani basket da aka 'kawata shi da ado cike da burgewa tace.

"Kai Momy wannan kyakkyawan basket d'in na waye gaskiya ya tafi dani wallahi ki ganshi d'an kyakkyawa" ta fad'a tana shafa jikinsa saboda yadda yake d'aukar ido yana she'ki kallon basket d'in Momy tai tana cewa "na Baby ne" baki Khairat ta bud'e tana qara kallon Momy da mamaki tace "na Baby kuma waye ya kawo mata nasan dai bata da saurayi waye to ya bata"?.

"Ahmad ne".
Da sabon Khairat ta zaro ido tana cewa "ya Ahmad kuma ya bata Ramadan basket tofa kyauta ya bata kenan ko kuma me"?.

"Eh kyauta ya bata man zai bata aro ko ajiya ne"?.
"Amma Momy ina sai budurwar ka kake baiwa ko har 'kanwa kana iya siyawa meyasa ya sai mata nasan dai wannan irin kyautar saurayi da budurwa ne amma ita kuma ya bata saidai idan da wani abu ko"?.

''Jeki tambaye shi meyasa ya bata domin nima ban sani ba shi kuwa ya sani zai baki amsa".

"A'a basai na tambaye shiba azumi akeyi karna jawa kaina sambad'a da rana tsaka na kasa kaiwa magriba kawai a barshi nasan maybe ra'ayi yayi ya bata matsayin sa na yayanta".

"To kinsan da hakan kike tambaya"?.
"To ai Momy abunne da mamaki indai matsayin 'kanwa ya bata meyasa ni bai had'o dani ba"? Murmushi Momy tai tana kallon Khairat tace "nasan dai keba 6angaren karatun jarida kike yiba amma kin iya tambayar 'ka'ka uwaka ta haifeka ina Babyn take yanzu"?.

"Tana part d'in Mami wanka na barota tana yi itama nan d'in zata taho".

"Ok tazo ta d'auke abunta" kawai shine abinda Momy tana tana mayar da hankalinta wani wurin daban shiru Khairat tai ta zubawa basket d'in ido tambayoyi ne masu yawa a ranta saidai tasan batada amsar su kuma bata da wanda zata tambaya ya bata amsa saidai Ahmad shi kuwa ko a buge take idan ta ganshi saita nutsu balle tana cikin hankalinta so take tasan meyasa Ahmad zai baiwa Baby Ramadan basket sonta yake ko kuma ra'ayinsa ne kawai yasa ya bata anya kuwa babu wani abu ta sani masoyi ne kad'ai ke haka indai ba sonta yake ba to me yake kaita girgiza a fili tace "ina sam ba haka bane wannan tunani nane kawai taya hakan xata yuwu" batasan a fili tai maganar ba saida taji Momy tace "meye ba haka bane"? Numfashi ta sauke tana saurin dawowa cikin nutsuwarta jin zatai 6arin zance tace "ba komai Momy bari naje na kira Babyn tazo ta bud'e mana muga mene a ciki".
"A'a ki 'kyaleta basai kinje ba saurin me kike zata zo ai duk abinda yake ciki zaki gani har ki gaji" Momy na rufe baki Baby ta shigo da sallama tana zama tace "wash Allah na wallahi kamar banyi wankan nan ba tsabar azabar da nake ji daga part d'in Mami kafin nazo nan har ruwan jikina ya bushe zazzafar iska ta fara buguna gaskiya da alama axumin yau da'kyar zan kaishi" dariya Khairat tai tana kallon ta tace "ai indai zakiyi wankan wuri to kuwa dole azumi ya baki wahala saka ruwa a jiki yana qara wuyan azumi idan baki sani ba".

"Humm aiko da alama yau zanci ubana dad'in abun ma ba wani abu zakai ba daga sallah sai kwanciya shiyasa nake tausayawa kitchens wallahi ga azumi ga zafin wuta ga aiki uhmm Allah sarki" ta fad'a tana girgiza kai kallonta Khairat tai tana cewa.

"Baby kalli wani basket" Khairat ta fad'a tana nuna mata kallonsa tai tana zaro ido cike da burgewa tace "wow wannan kyakkyawan basket d'in daga ina ko Yaya Shadad ne ya aiko miki shi daga can gaskiya ya had'u sosai"? Dariya Khairat tai tana cewa "A'a wacce ni me ido bad'an ciki ha'kori ba sakata wannan yafi karfina naki ne".

Sak Baby tai tana kallon Khairat tace "nawa Kuma ni waye xai bani Ramadan basket ba saurayi gareni ba tsokana ta kike ko Aunty Khairat saboda kinga babu me bani shikenan nima Allah ya kawo min habibty na kafin wata shekarar idan ya kawo min na rama nayi miki dariya tunda nima yanxu dariyar kike min" Kai Khairat ta girgiza tana cewa "ke Baby Wallahi da gaske nake naki ne haka Momy tace" da mamaki Baby ta nuna kanta tana sake kallon basket d'in tace.

"Nawa dai waye ya bani"?.

"Yaya Ahmad ne" Khairat na rufe baki Baby ta zabura idonta kamar zai fito waje tace "wanne Yaya Ahmad d'in amma dai bana gidan Nan ba"?.
"Na nan gidan man shine ya baki kuma ki tambayi Momyn kiji idan ni baki yarda dani ba ko kina ganin tsokanar ki nake yi" kallon Momy Baby tai jiki a sanyaye muryarta ma da sanyi tace "wai haka Momy dan Allah kice aunty Khairat tsokanata take" yadda tai maganar yasa Momy sakin murmushi tana d'an girgiza kai tace "ba tsokanar ki takeyi ba Baby da gaske take Ähmäd ne ya kawo min d'azu yace idan kin shigo a baki Ramadan basket d'inki ne injishi tun daga can ya taho miki dashi".

Dafe 'kirji Baby tai tana cewa "a bani kuma mene had'ina da Ramadan basket Momy inace sai idan kana da saurayi ne yake baka irin wannan ko"? Kai Momy ta d'aga tana cewa "eh haka ne".

A razane baby tace "toni kuma meyasa ya bani"? Dariya Khairat tai tana cewa "kika sani ko kema hakan take abu a duhu a 'kulle
End Ads