x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 11 - ROYALTY YAN SARAUTA

  • 30001 words
  • 33000 words
  • Out of 85109 words

Category: Love Stories

Views 1695

20 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
ba meka rageta dashi harda zaiyi abu batare da ya mayar dakai uba yayi shawara dakai ba" har lokacin idon Daddy yana kan Aiman yace "dashi nake magana kiyi shiru ke kam ina zuwa kanki" ta'be baki Hajiya Khubura tai tana juyar dakai gefe a ranta tace "ku gama ka dawo kaina d'in kome zakai wallahi sai yarinyar nan ta dawo gidan nan zan nuna maka kayi tsararo baka kaiba dani kake zancen ko Zainab bata isa ja dani ba balle wani banza kai data haifa".

"Aiman".

"Na'am Daddy".

"Nace meyasa ka d'auke Ayrah daga gidan nan tsawon lokaci ban sani ba kuma kai baka sameni ka fad'a min ba" idon Aiman na kallon carpet yace "kayi hakuri Daddy nayi hakan ne bisa dole ba'a son raina bane saboda..........

Katse masa magana Hajiya Khubura tai da cewa "bada son ranka bane to waye ya saka ka dole ko Zainab d'in ce tace kazo ka d'auke ta"? D'agowa Aiman yai ya mata wani irin kallo batare daya bata amsa ba yaci gaba "Daddy maganar gaskiya Ayrah bata sakewa a gidan nan rayuwa take kamar tana gidan yari alhali ita da gidan mahaifinta bata da damar data isa zama koda na minti biyar ne a parlor kullum tana zaune guri d'aya daga bedroom sai bedroom sannan Hajiya tana gani 'ya'yanta Abidah da Nadiya suke dukanta su zageta su sakata wanki da wanke toilet gugar kayansu abincin su komai itace take musu sannan abun ba'kin cikin itace zatai komai ta kawo musu amma lomar abinci d'aya bazasu bari tayi ba a gidan nan saidai idan nine na shigo Mata dashi wannan dalilin yasa na d'auketa ta koma can suna zaune tare da Fati da Ashfat lafiya kalau kuma ta sake dasu sosai taji dad'in haka shiyasa nace bazata sake zaman cikin gidan nan ba saidai tazo musu da yawo shima idan kana nan" yana rufe baki Hajiya Khubura tace.

"Karya kake munafiki wallahi Alhaji 'karya ya zauna ya shirya maka nice ina sane su Nadiya suke sakata wahala bayan su suke komai a gidan nan aiki kamar zai kashe su amma saboda baka tsoron Allah harda wani itace take mana komai tabd'ijan lallai ma yaron nan ba'a haifi abokin 'karya ka ba".

"Ai dama ba dake nake magana ba da mahaifi na nake idan ke kin 'karya tani shi zai gaskata ni".

"Shima bazai gaskata kan ba saboda babu gaskiya a cikin abinda ka fad'a sannan dole Ayrah ta dawo gidan ubanta harda wani ba dani kake magana ba da mahaifinka kake dad'in abun ma neman suna kake saidai kace ba dani kake magana ba da mahaifin wata ne ka gani domin a iya sani na 'ya d'aya ya haifa indai ba kalan dangi da son a sani ba ka daina kiransa da mahaifinka ka ri'ka cewa Yaya mahaifinka wannan shine

"Bazance yayan mahaifin nawa ba Kinga Hajiya babu ruwanki anan zancen mune tsakani na dashi karki sake saka mana baki Ayrah kuma tunda ba kece kika haife taba dole ki d'auke idonki daga kanta idan kin 'ki akwai ranar nadama tana nan zuwa

Ta'be baki Hajiya Khubura tai tana cewa "babu ranar da zata fito wacce a cikinta zanji nadama ta kamani rayuwa kuma yanzu na fara duniya yanzu nake jujjuya ta domin banyi komai ba ka zuba ido ka gani yanzu na fara tara tsinken dazan tsikari duniyar saina baka mamaki zaka yabawa aya za'kinta" Aiman zaiyi magana Daddy da abun ya ishe shi ya d'aga hannu yana cewa.

"Ya isa haka ba hayaniya nake nema ba na tambayi Aiman ne inda Ayrah take kuma ya fad'a an wuce gurin tunda ka za'bi ta zauna a gidan ku shikenan hakan yayi zaka iya tafiya" a zabure Hajiya Khubura tace "zai iya tafiya zuwa ina? Gaskiya Alhaji bazata yuwu ba wai so kake a zageka a gari nima a zageni ace 'yarka d'aya ka kasa ri'kewa amma gashi ka ri'ke 'ya'yan ri'ko har mutum biyu".

"Duk Wanda bai fasa cewa na kasa ri'ke 'yata na ri'ke d'an aro ba Allah ya tsine masa" Daddy ya fad'a a fusace.

Ganin ransa ya 6aci yasa Hajiya Khubura take "A'a nidai Alhaji gaskiya kace ya dawo da ita gidansu ina tuna maka ne meka rasa me babu gidanka daci da sha bai kamata ace 'yarka ta tafi wani gidan can gayyar tsiya a karasa goyata ba dacan lokacin da mahaifiyarta ta rasu basu nuna zasu d'auketa ba sai yanzu data d'ago ta mallaki hankalinta sannan tsabar munafirci da yawan gulmar son a sani zasu wani ce zasu rike ta kace baka so ya dawo maka da ita yanzun nan ka tashi kaje ka dawo da ita".

"Ai ba kece kika haife taba saiki bari wanda ya isa da ita yayi magana kuma indai umarnin kine bazan cika ba kin gane"? Kukan 'karya Hajiya Khubura ta saki tana cewa "yanzu tsakani da Allah Alhaji a gabanka yake cimin mutunci yana nuna ni uwar banza ce sai zagina yake yana mayar min da magana kana jinsa yana fad'a min abinda yaga dama? Wayyo Allah na ni Khubura shikenan yau na gamu da gamona" kai Aiman ya jinjina yana shirin magana Daddy yace "Aiman gobe idan Allah ya tashe mu cikin basu rai ina so ka dawo da Ayrah kamar yadda ka d'auketa" takaici ne ya kama Aiman musamman ganin irin kallon da Hajiya Khuburan take masa lokacin da Daddy yace haka kamar bazai tanka ba sai kuma yace.

"Daddy ka bar Ayrah ta zauna acan bata jin dad'in nan gidan ko kad'an".

"Haka tace maka bata jin dad'in zaman gidan nan ko kaine ka fad'a"?.

"Bani na fad'a Daddy idona ne suka gane min".

"A'a Aiman ka dawo da ita gobe da safe na gama magana tashi kaje" jin abinda Daddy yace yasa Aiman ya mi'ke ransa a 6ace ya fice daga parlon kamar jira Hajiya Khubura take yana fita ta sake matsawa kusa da Daddy tana kashe murya tace "nikam Alhaji ya maganar tafiyar Aiman makaranta ko ka fasa ne naji kayi shiru da zancen"? Kai Daddy ya girgiza yana cewa " a'a ba mantawa nai ba kuma ba fasawa nayi ba na gama komai lokacin tafiyar tasa ne baiyi ba saboda akwai wani mutum abokina ne da mukai magana tare dashi zasu tafi shi akwai abinda xanyi acan daya gama zai dawo Aiman kuma sai nan da shekara biyu idan ya kammala sannan zai dawo gida insha Allahu" Daddy na rufe baki Hajiya Khubura ta sauke wani daddad'an sansanyan numfashi tana sakin murmushin tsantsan farin ciki tare da jinjina a fili kuma sai tace.

"To ikon Allah, Allah yasa ayi mai amfani nima dai Khaleel ya kirani a waya yau kusan kwana biyar yana fad'a min ya kusa dawowa gida kwanan nan" "kai Daddy ya d'aga yana cewa "ok Allah ya dawo dashi lafiya".

"Amin Alhaji bari na duba su Abidah ko sun bar parlon nasan yanzu haka suna nan suna kallo ba hankali ne dasu ba idan na barsu zasu iya kaiwa asuba gara naje na korasu Ina dawowa" ta fad'a tana mi'kewa ta fita dama already tasan basa parlon kawai gulma ce take ciciyarta so take ta fad'a musu cewa Aiman zai bar gari ta huta dan bazata iya barci ba yau indai bata fad'a musu ba bedroom d'insu ta shiga suna zaune kowa da waya a hannunta tana chat tsaye Hajiya Khubura tai daga bakin kofar shiga bedroom d'in tana kallon su tace.

"Albishirin ku kuce min goro" duk aje waya sukai suna kallonta tace "kuce goro idan ba haka ba bazan fad'a ba" d'an ta'be baki Nadiya tai tana mayar da hankalinta kan wayarta tace "dama dai Umma baki niyyar fad'a ba indai sai munce miki goro ne" ta fad'a tana sake gyara kwanciyarta Abidah ce kad'ai tace "albishirin mu goro manya farare tas 'kwalla 'kwalla masu girma fad'a mana meya faru na ganki cikin farin ciki haka Umma"? Murmushi Hajiya Khubura tai tana cewa.

"Humm ba dole nayi farin ciki ba idan ta kama harda rawa zanyi yanzun nan nake magana da Alhaji sai na tambaye shi ya maganar tafiyar Aiman makaranta koya fasa yace a'a ya gama komai wai abokinsa yake jira su tafi tare fad'in haka shine ya saka ni murna annoba zai tafi ya barmu musha iska muyi abinda ranmu yake so batare da fargaba ba shiyasa daya d'auke Ayrah nasan yadda zanyi na zuga Alhaji yanxu yace lallai yana so gobe da safe ya dawo masa da ita" jin abinda ta fad'a yasa ba iya Abidah ba harda Nadiya wani tsalle sukai suna cewa "da gaske Umma"?.

"Da gaske man saiku sake shiri kafin tsinanniyar ta dawo ni na koma kar Alhaji yaga na dad'e" tana fad'in haka ta fita kai Nadiya ta jinjina tana cewa "humm idan muka samu wannan takurar yabar gidan shikenan komai zai dawo mana sabo zamuyi abinda ranmu yake so babu fargabar komai tunda shima Daddyn ba zaman gida yake ba".

"Uhm nikam bazan ce komai ba saita dawo bautar da zatai min bazai fad'u ba azaba zata sha iri iri wacce ta sani da wacce bata sani ba" Abidah ta fad'a tana d'aukar tata wayar itama taci gaba da chatting d'inta..........

Fitar Aiman gidansu ya nufa ransa a 6ace da yake ba sosai dare yayi ba yana shiga ganin babu kowa a parlor ya wuce part d'in mahaifinsa yana zaune ya shiga ganin yadda fuskarsa take yasa yace "Aiman lafiyarka kalau meya faru"? Zama zuciyarsa na 'kuna yace "Abba daga gurin Daddy nake yanzu akan na taho da Ayrah ran nan shine matarsa ta zugashi wai saita koma idan bahaka ba mutane zasu ri'ka masa kallon wanda ya kasa ri'ke 'yarsa ya ri'ke 'ya'yan ri'ko shine yace min dole saina mayar da ita gobe dan Allah Abba da safe kaje kace masa basai ta koma ba kaga ni 'kasar zan bari ga shegun yaranta bansan wanne hali zata tsinci kanta ba a gidan nan a haka ma suna ganin wulgina basu daina azabtar da ita ba balle akace sun tabbata bana gari abinda zasuyi mata bazai kyau banaso wani abu ya samu yarinyar nan" duk abinda Aiman ke mata Abba yana sauraron sa har yakai karshe kaiya jinjina yana cewa.

"Shi Yayan ne yace ka mayar da ita gidansa daga nan kar ace ya kasa ri'keta? Kenan mu kasa ri'keka mukai shiyasa muka bar masa kai tun bakasan waye kaina harka taso har zuwa yau mun ta'ba cewa wani abu kodan ba laifin sabane mace ya aura gur6atacciya saidai muyi hakuri da komai amma ina mamakin yadda gabadaya ya canza rayuwarsa kamar wanda aka asirce? Allah ya rufa asiri karka damu Aiman zanje nayi magana dashi tashi kaje duk yadda za'ai Ayrah bazata koma can ba amma idan naga ya matsa lamba sosai zata koma tunda har ya nuna 'yarsa ce babu kara shikenan jeka" mi'kewa Aiman yai yana fita amma yasa a ransa Ayrah bazata koma gidan nan ba kome Daddy zaiyi tunda ba ra'ayin kansa bane sawar Hajiya Khubura ce zai nuna mata tayi kad'an.

👑 Palace 👑
Yau su Khairat basu wuni a sashin Momy ko Mami ba tun safe suka shiga fada gurin mai martaba Sultan Sharfaddeen tun safe har la'asar suna can sun saka su a gaba sai tsokana suke wannan yace wannan wancan yace wannan har saida mai martaba Sultan ya gaji ya kallesu yana cewa "kunga idan baku daina sakani magana haka ba zan kira muku Ahmad a waya na fad'a masa nace tunda ya tafi kullum sai kunzo kun dame ni" kallon juna sukai suna murmushi Baby data dau'ki wayarsa dake aje a kusa dashi tace "wow ya Ahmad zaka kira mana nikam waye ma Ahmad ne Aunty Khairat"? D'aga kai sama Khairat tai kamar gaske tace "bari na tuna nimafa ga dukkan alamu na manta shi kamar Ahmad sunan anguwa ko Sultan"? Ta fad'a tana kallon mai martaba Sultan tare da rufe baki ta soma dariya kai Sultan Sharfaddeen ya d'aga yana cewa "eh sunan anguwa ne anan tunda kun manta Ahmad amma baku manta Shadad ba ko shima bakusan shiba".

"Eh to nidai kamar na san Shadad sunan wani lemo ne nima na ta'ba sha" Baby ta fad'a tana dariya "au da gaske sunan lemo ne"? "Kwarai sunan lemo ne yana can a wata qasa yana karatu".

"To ikon Allah dama mutum ne kenan kuma kikace lemo ne"? Murmushi Baby tai tana d'aga kai tace "eh mutum ne saurayin wata nema shiyasa da akazo kansa batai magana ba tai shiru tana kallon mu" jin abinda baby tace yasa Khairat harararta tana cewa "dani kike kuma saina fad'a masa idan mukai waya".

"Nima saina fad'awa nawa habibin idan kikasa ya dake ni shima yazo ya rama min".

"Waye habibin naki"? Sultana Addah dake gefe ta fad'a tana kallon ta taji me zatace ko su Momy sun fad'a mata Ahmad na sonta ko kuma wani daban zatace...............

Jitayi Babyn tace "habibina man wanda ban sanshi ba duk ranar da yazo saina fad'a masa nace inada yaya wanda ya dakeni ka rama min ko takawa ai nayi daidai ko"? Ta tambaya tana kallon Sultan Sharfaddeen kaiya d'aga mata yana cewa "eh kinyi daidai gara ya rama miki dama shima akwai zafin rai shikenan an had'u".

"Waye me zafin rai"?.

"Wani ne".

"Bashi da suna" baby ta fad'a tana kallon sa "eh bashi da suna Zuhuriyyah ke kad'ai kin dameni wallahi tun safe kin takura min kuzo ku koma 6angarenku man".

"Mufa mun dawo nan daga yau Allah yaja zamaninka da girma kujerarka takawa kakana Sultan Sharfaddeen" kallonta me martaba yai yana cewa "nikam Zuhuriyyah na tambaye ki man meyasa kike so kice min takawa" dariya baby tai tana kallon Khairat wacce itama ke dariyar tambayar da Sultan Sharfaddeen yai kafin ta mayar da hankalinta kansa tana cewa "ina nufin takawarka lafiya mai nasara Sultan Sharfaddeen mai martaba angon Sultan Addah Aisha masoyan asali haka nake nufi yanzu ka gane"? Kai ya jinjina yana cewa.

"Na gane dama haka kike nufi"?.

"Eh haka nake nufi kasan irinku sarakuna dole saida kirari da ace na iya da yanxu na rera maka amma yanzun ma idan kana son wa'ka nayi maka kana so"? Kaiya girgiza yana cewa "a'a bana son wa'ka wa'azi nake so idan kin iya kiyi min".

"Na iya amma ni yanzu wa'ka nake so bari na rera maka kaida amaryarka Sultana Addariyah" "Kai harda 6ata mata suna"? "Ba 6atawa nayi ba kwaskwarima nayiwa sunan Aunty Khairat tashi mu tafi an kusa kiran magriba Sultan and Sultana ku huta lafiya" mi'kewa Khairat tai tana cewa "ki daina gyara musu sunan wai Sultan and Sultana tsofi ba ruwansu da wannan Sutalewar kawai kice tsoho Sharfaddeen da tsohuwa Addah".

"To bazata ce hakan ba Sultan da Sultana zatace" Sultana Addah ta fada ganin Baby zata sake magana Sultan Sharfaddeen yace "dan Allah ku tafi mun gode da ziyara ku gaida iyayen naku" murmushi Baby tai tana cewa "to shikenan mun tafi ku huta lafiya Sultana Addah amaryar Sultan Sharfaddeen Aunty Khairat muje sai anjima" fita sukai mai martaba Sultan daya sauke numfashi yace "Allah ya shirye ku wadannan yara sam bakwa jin magana" yana rufe baki Baby ta le'ko tana cewa "ba tafiya mukai ba takawa muna tsaye dama jira muke muji me zakuce baku da wani abu da zaku bamu mun kawo muku ziyarar wuni guda mu tafi sungul kamar yadda muka zo"? "Eh babu abinda zamu baku yau sai kun sake dawo mana".

"To shikenan amma idan zamu sake dawowa ku shirya mana liyafa kaji Sultan dan Allah"? "To za'a shirya muku sai kun sake dawowa muna jiranku".

"Ko gobe ne mu dawo"?.

"Eh Allah ya kaimu sai anjima ku tafi dan Allah kun dameni" dariya baby tai tana d'ago masa hannu tace "bye" juyawa sukai ita da Khairat suna fita motar da aka kawosu tana nan saidai da yake dama cewa drivern sukai ya tafi ya dawo ya d'auke su da la'asar ya dad'e da dawowar kawai zaman jira yake ganin sun fito ya tashi ya bud'e musu suka shiga ya mayar dasu saboda tafiya ce mai nisa tsakanin fadar Sultan Sharfaddeen da su kamar ba masarauta d'aya suke ba akwai tazara gidan yana da girma sosai.

Momy tana zaune suka shiga ganinsu yasa tace "oh 'yan wuni sai yanxu kenan kuna can kuna takura musu ko"? Zama sukai baby na cewa "wallahi kamar kin sani muna can munata tsokanar su" "yayi kyau d'azu Ahmad ya kirani yana neman ku nace kuna gurin me martaba "ya Ahmad kuma yana neman mu meyasa bai kira a wayar Aunty Khairat ba"? "Ban sani ba kirashi ki tambaye shi kona kirashi na tambaya miki shi"? Zaro ido Baby tai tana cewa "ni a'a basai kin kira ba kawai dai nayi mamaki ne da kikace yana neman mu inaga yau ba fad'a zaiyi mana ba shiyasa bai kira wayar Aunty Khairat ba amma ranar ai kiranta yayi yasa ta bani wayar ya kashe min warning wallahi ranar da yana kusa nasan sai naci na jaki".

"Me kikai masa ya kira yanai miki fad'a"?.

"Uhm Momy idan ana sallah ba'a magana dama ya Ahmad a wuya yake dani yanzu kuma ki kirashi kice nace meyasa bai kira ta wayar aunty Khairat ba tab Allah ya rufa asiri ai inaga saiya dawo gida ya huce duk hushinsa a kaina".

"Ai baki fad'a min me kikai masa ya kira yana kashe miki warning d'in ba"? Kallon Khairat Baby tai tana cewa "waifa Momy tun lokacin daya bar wayarsa a parlor ana kira na d'aga nace baya nan sai wanda ya kiransa yake tambayar wacece ni nace masa kanwar me wayarce shikenan daya fito ya kamani ya ri'ka min tsawa ya dakeni da belt bayana kusan fashewa yayi duk ya zama ja ban sani ba kuma wannan komawar tasa ko magana abokin nasa yayi masa a kaina shine ya taso da maganar ya kirani yace idan ya dawo na shiga uku nikam ina cikin tashin hankali".

"Murmushi Momy tai tana kallon ta tace "babu abinda zaiyi miki idan ya dawo ki kwantar da hankalinki kafin lokacin dawowarsa yayi ya manta idan ma bai manta ba bazan bari ya ta'ba kiba" numfashi Baby sauke tana cewa "yauwa Momy nagode wallahi har naji dad'i da kikace haka" "uhm nikam dama ba ruwana dake kuka fi yi" Khairat ta fad'a tana mi'kewa ta shiga bedroom kallon Momy Baby
End Ads