4~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Khaifinah.
@YUSRAHMS CE
Page 07 & 08
Ayrah tana kwance a bedroom d'inta Abidah ta shigo da ruwa a Kofi a hannunta yaye bargon data lullu'be jikinta tai tana watsa mata ruwan tace "tashi 'yar matsiyata tun d'azu muna jiran kizo ki had'a mana breakfast ashe ke barci ma kike wato gaki isasshiya 'yar gidan isiyaku ko"? Ayrah data tashi a firgice tana sharce ruwan data watsa mata a fuskarta ga sanyi muryarta na rawa tace.
"Kiyi hakuri bansan gari ya waye ba wallahi tunda nayi sallah na koma barci" wani irin ba'kin kallo Abidah tai mata tana cewa "oh baki san gari ya waye ba? To ai yanzu kin sani zaki tashi kije ki had'a mana ko saina d'auke ki da mari"? A zabure Ayrah ta mi'ke tana saukowa daga kan gadon ganin Abidan ta d'aga hannu tace "dan Allah kiyi hakuri" a tsawace Abidah tace "zaki wuce ko saina fasa miki baki" ta karasa maganar tana hankad'ota gaba suka yo waje suna fitowa parlor Hajiya Khubura dake zaune ganinsu yasa ta sakarwa Ayrah harara daidai sun karaso Ayrah ta dur'kusa tana cewa.
"Ina kwana"?.
"Ubanki keda kwanan 'yar gwana na nemi gaisuwarki ne ko shisshigin da kika saba zaki min hamsha'kiya daga barci kika tasheta Abidah ko kuma a zaune kawai take raini ne ya hana tazo tayi mana breakfast d'in"?.
"A'a a kwance na sameta sai gwarci da munshari take kamar rago Wai Kuma na tasheta harda wani batasan gari ya waye ba".
"Au batasan gari ya waye ba meyasa data fad'i haka baki buge mata baki ba ko ki sharara mata mari yadda zata wartsake da wuri ta dawo cikin hayyacinta"?.
"Humm kinsan ma wani rainin hankali Umma tana tashi sai cewa tai wai wani uwarta barci ta koma bayan datai sallah kamar batasan da aiki a gabanta ba".
Jawota Hajiya Khubura tai tana tula mata duka a baya tace "Iya barci kika koma ba mutuwa kikai ba naso duniyar kika bari zaki wuce ki had'a mana ko saina tashi a kanki kika zuro min wadannan mayun idanuwan naki masu kala dana mujiya" cikin takaici da 'kunan rai Ayrah ta mi'ke da'kyar take d'aga kafarta tsabar rashin dad'in da take ji a jikinta ta wuce kitchen harta bud'e kofa zata shiga ta tuna bata tambaye su me za'a dafa musu ba dawowa tai tana tsayawa daga nesa dasu ganin yadda duk suke binta da wani irin kallon rashin mutunci tasan ta karaso gurin su sai taci shegen duka muryarta a hankali tattare da damuwa tace.
"Me zan had'a muku"?.
A masife Nadiya ta mi'ke tana cewa "uwarki da ubanki zaki had'a mana 'yar bagidajiya kullum sai ana fad'a miki yadda zaki aiki idan kinga dama ki kawo mana d'anyan abinci ko kuma ga hanya nan ki wuce ki koma kiyi barcinki ina daidai dake a gidan nan badai gadararki Aiman ba? To wallahi koshi bai isa yai min na 'kyale shiba balle ke banza a banza da'ki'kiya ma irinki" shiru Ayrah tai kamar zata fashe da kukan ba'kin ciki ganin yadda suka saka ta a tsaka me wuya zata iya dafa abinda basa so shiyasa ta tambaye su domin mafi yawancin lokuta suna yi mata haka saita dafa musu suce bashi suke soba suyita bata wahala tana kai komo daga kitchen zuwa dinning karshe idan batai sa'a ba bayan zagi harda duka suke had'a mata..................
Aje wayar hannunta Nadiya tai tana mi'kewa tayo wajenta ganin ta tsaya bata juya ta tafi ba cikin tsawa tace "kee ubanki kike kallo? Zaki wuce kiyi abinda aka saka ki ko saina kashe ki a gun nan" ta karasa maganar tana yowa kanta da gudu Ayrah ta koma kitchen tsaki Hajiya Khubura tai tana cewa "ni wallahi na kasa gane wannan yarinya sam ace kwa'kwalwarta bata ja kullum dan masifa sai ana maimaita mata magana kamar batasan me zatai ba".
"Ai Umma idan baki gane ba nasan manufarta so take tayita ja mana lokaci har wannan mara mutuncin Yayan nata Aiman ya shigo ya samu tana yi mana aiki shine dalili saboda tasan kema ba darajaki yake ba balle mu daya tsane mu kamar gidan ubansa ne bayan shima d'an karo ne gara mu munada uwa a gidan zamu taka bazarmu muyi tun'kaho shifa gidan 'kanin ubansa ne kawai bayan haka baida wani hurumi a gidan sai nuna gadara"? Abidah ta fad'a tana hararar kofar da Ayran tabi.
Tsaki Hajiya Khubura tai tana cewa "gadararsa ta banza dad'in abun ma tunda ba gado ne dashi ba tanan nake godewa Allah da ace wannan mara kunyar yaron d'an gidan Alhaji ne toda na kad'e wallahi ni kaina bazai barni na huta ba zama saiya gagare ni a gidan nan balle ku saidai ku koma gidanmu to inda Allah ya rufa asiri shima a raka6e yake yana cin arziki shine dad'in abun".
"Humm ya kwantar da hankalinsa zai gane kurensa a gaba sharrin da zamu shirya masa saiya gwammaci dama ya mutu kafin zuwan wannan ranar ni nasan abinda zan shirya masa kawai kuyi shiru ba tun yauba na fahimci so yake yasa sai munbar gidan nan 'karfi da yaji d'an Daddy ya share shine shiyasa yanxu ita kuma take sake hura tata wutar da zatai mana sharri kinga idan ya shigo ya tarar tana aiki ai zaiyi magana hakan yasa ta'ki wucewa tai abinda muka sakata jiran shigowar sa take ni kuma saina gwada masa aikin sharri domin sai nayi sanadin barinsa gidan nan".
Duk wannan zancen da suke Nadiya tana tsaye tun lokacin data mi'ke zata bi Ayrah bata zauna ba sai yanzu ta koma ta zauna tana cewa "ai kuma tayi a banza wallahi indai ina gidan nan sai tayi aiki ba Aiman ba ko ubansa ne yazo bai isa ya hana ba idan kika ga na daina sata wahala a gidan nan d'ayan biyu ne ya faru kodai nayi aure ko kuma Umma aurenta ya mutu" tana rufe baki Hajiya Khubura ta zaro ido waje tana cewa "ke baki da hankali kike min fata aure na ya mutu kuma? Dan ubanki daina fad'a karki fad'a a bakin mala'iku yana dawowa kisa ya sakeni mu fito rana" dariya Abidah tai tana cewa "ai Nadiya muda gidan nan mutu ka raba takalmin kaza wallahi bamai fitar damu haka Umma babu inda zataje tana nan sai tayi masa takaba wa zai bar irin wannan dukiyar kina gani fa daga iya wannan yarinyar baida wani d'an to me kike zato idan akace ya mutu dukiya ta zama tamu domin wallahi ko sisi baza mu bata ba sannan saita bar gidan kota shiga duniya ko tasan inda dare yayi mata".
Kai Hajiya Khubura ta jinjina tana cewa "yauwa 'yar albarka har kinsa naji dad'i domin hakan da kika fad'a har kinsa na shiga wani yanayi kawai haskoni nake dukiyar nan ta zama tawa humm akwai wada'ka dan saina mayar mana da rayuwar mu irin ta turawa yau muna wancan 'kasar gobe muna wancan 'kasar mu zaga duniya mu bud'a idanu ba zama kuma babu wanda ya isa ya tuhume mu duk wanda yayi yunkurin tarata da maganar gadon Ayrah wannan dama sunansa gawa".
"Tabbas Umma kin fad'i gaskiya domin babu wanda zai taka mana burki duk wanda yayi yunkurin hakan kuwa zai had'u da bala'in da yafi karfin sa sai mun mayar da rayuwarsa abar tausayi''.
Humm Allah sarki duk abinda suke Ayrah tana jinsu saboda ta d'auko plask d'in shayi data dafa zata kawo musu taji abinda suke fad'a jikinta na rawa ta juya zuwa kitchen tana kuka a ranta tana tunanin ya zatai wa zata tara da wannan maganar duk da watsar da ita da mahaifinta yayi a hakan tana son abinta batasan wani abu ya sameshi taji su suna wadannan maganganun innalillahi wa inna ilaihi raji'un Allah ya fidda mahaifin ta daga wannan tarkon da suke shirya masa Allah ya toni asirin su fasa fita takai musu tea d'in tayi kawai ta juya zuwa kitchen d'in tana kuka tsabar yadda jikinta ke rawa da abinda taji suna fad'a da'kyar ta iya karasa had'a musu abubuwan breakfast d'in sannan ta d'auko ta kawo musu fuska ba walwala tai musu serving zata tafi Abidah ta dakatar da ita ta hanyar fisgota baya tana cewa.
"Ke tsaya min anan gidan ubanki zaki tafi dama mun sallame kine"? Ran Ayrah a 6ace ta d'ago tana kallon Abidah wacce ta koma tana huci ta zauna babu wanda ya kalli inda take suna ta zancen su har suka gama suka mi'ke duk sunyi banza da ita kamar sun manta da tsaiwarta a gurin parlor suka koma Hajiya Khubura dake waya bayan ta sauke ta kalli Ayrah dake tsaye kamar an dasata tana cewa.
"Ita kuma wannan tsaiwar uban me take ne acan nifa bana son ganinta a parlon nan domin ba irin gurin zamanta bane ke Abidah me zatai miki kika tsayar da ita" d'agowa Abidah tai a wula'kance tace "oh nina manta da ita ma dama takalmi zata goge min zan fita anguwa" ta karasa maganar tana kallon Ayrah tace "ke zo nan ki goge min kafin na tashi tunda naga yau da wani sabon raini kika tashi kuma zanyi maganinki" ko tari Ayrah batai ba balle ta nuna taji haushin maganar da Abidan ta fad'a ba sai qarasowar datai tana shirin dur'kusawa a tsawace Abidah tace.
"Da ubanki zaki goge min baki d'auko towel ba" ta fad'a tana kai mata duka da sauri Ayrah ta matsa baya dukan bai sameta ba daidai Aiman ya shigo baiga dukan da Abidah ta kai mata ba amma yaga sanda Ayran ta matsa baya fuska ba rahma ya karaso yana kallon Ayrah data sau'ke sansanyan numfashi cikin jin dad'in ganinsa har tana d'an sakin fuskata dan karya fahimci wani abu muryarta a daidai tace.
"Yaya ina kwana"?.
Bai amsa ba sai tambaya daya jefo mata "me kike yi anan"? D'an sauke kai tai tana cewa "babu komai".
"Babu komai kike tsaye a gabansu matsawar ne naga kinyi"?.
Nan ma kaita girgiza tana cewa "babu komai" ganin bazata bashi amsa ba kuma yasan wani abu suke mata amma ya share yana jinjina kai yace "ok muje" wucewa gaba tai yana bin bayanta suka shiga part d'inta da harara duk su ukun suka rakashi Hajiya Khubura data ja tsaki tace "anya wannan yaron kalau kuwa kullum yazo ya 'kule a bedroom d'inta yayi shiru kamar ya mutu ba iskanci suke yiba karfa nan da 'yan kwanaki muga ciki a jikinta dan ban yarda da wannan yawan shige da ficen nasa ba tabbas akwai wani abu a 'kasa".
Ta'be baki Nadiya tai tana mi'kewa zata bar gurin tace "aiko Umma da gani babu tambaya kina ganin yadda yake mata abubuwa bayan ba uwa d'aya uba d'aya suke ba kinsan bazaiyi mata a banza ba wallahi akwai morar da yake mata kuma abinda kika fad'a saiya zama gaskiya nikan nayi anguwa" tana fad'in haka ta dau'ki handbag d'inta tai waje kai Hajiya Khubura ta jinjina tana cewa "to haka ne kenan na canka daidai iskanci yake yi da ita tabd'i aiko wallahi ba'a gidan nan ba bari Alhaji ya dawo xan fad'a masa ya dakatar da Aiman ya daina shiga d'akin ta idan yaki wata rana yana gaf daya bud'e ido yaga 'yarsa da cikin shege a cikin gidansa" dariya Abidah tai tana girgiza kai tace "a'a Umma ki kyale shi kawai karki fad'a masa dan Allah ki bari ta haihu idan cikin ya tabbata muci ragon suna musha minti".
''A gidan ubanwa zaku sha mintin kuci ragon? hummm nifa bawai cikin shegen da zatai ne damuwata ba a'a tsorona kar ace 'yar gidan mijina ce labari ya karad'e ko'ina samari su'ki zuwa neman auren ku gara idan ma cikin zaiyi mata ya bari na aurar daku ko kuma ku fara samun wanda zasu aure ku bayan an gama komai saitai cikin nasan dai duk tsiya ita da mahaifinta ne zasu shiga cikin tozarci bani ba ke wannan maganar ma tasa dole naje gurin Hajiya Basirah naji yaya meke tafiya" tana rufe baki Abidah tace "indai haka ne Umma muje na rakaki ayi komai a gabana domin duk burin da kika d'auko zan taya ki cika shi" mi'kewa Hajiya Khubura tai tana cewa.
"Yauwa Abidah haka nake son ji ina so naga d'an dana haifa yana bin hanyar da nake bi bari na d'auko mayafi na mu tafi" ta fad'a tana mi'kewa ta shiga part d'inta itama Abidah mi'kewa tai tana shiga nasu part d'in ta shiryo kusan tare suka fito d'an mayafin da Hajiya Khubura tasa ko 'yar shekara sha biyar iyakaci kenan d'an karami iya kafad'arta suka fita.
Aiman kam suna parlon part d'in da Ayrah take yana lallahinta da bata hakuri cewa ta daina saka damuwa a ranta komai me wucewa ne insha Allahu wata rana gaskiya zatai halinta ta daina ganin kamar Daddy baya sonta ba laifinsa bane akwai abinda basu sani ba a duhu domin bayan rasuwar mahaifiyar ta ba haka Daddyn yake mata ba kullum yana kula da ita yana tausaya mata komai ya sayo ita komai take so zaiyi mata amma yanxu idan xaiyi shekara guda cur bai ganta ba bazai tambayi Ina take ko meya sameta ba ko kallonta baison yi idan ta gaisar dashi baya amsawa tuna hakan yasa ta fashe da kuka domin batasan me Aiman yake fad'a mata ba tsabar tunanin datai zurfi a ciki ba zato sai gani yayi tana kuka ransa ne yai mugun 'baci yasan yarinyar nan tana cikin matsananciyar damuwa wacce idan bai tsaya tsayin daka ya magance mata ita ba tabbas akwai babbar damuwa huci mai zafi ya fitar yana mi'kewa muryarsa babu yanayin dad'i yace.
"Tashi ki d'auko hijab d'inki muje gida gurin Aunty Umma" goge hawayen tai tana mi'kewa ta shiga toilet ta wanke fuskarta dan kada mahaifiyar Aiman d'in ta tambayi kukan me take amma duk da haka idonta yayi ja fitowa tai ganin baya parlon ya fita yasa ta sauya kaya ta d'auko hijab ta fito baya main parlor ma wucewa tai zuwa harabar gida acan ta ganshi tsaye karasawa tai tana cewa "ya Aiman na shirya" "ok muje" gaba ta wuce yana bin bayanta suka fita daga gidan yasa a ransa daga yau bazata sake kwana a cikin gidan nan ba gara ta koma gidansu gurin mahaifiyar sa ta zauna tare da 'kannansa hakan zaifi mata zaman lafiya amma kullum yarinya tana fama da shan wahala sai karewa take kamar kud'in guzuri ya bari Daddy ya dawo zai zo ya fad'a masa sannan zai d'ebe kayanta kaf ya mayar gidansu koda marmari Ayrah bazata sake shigowa nan ba saidai idan sabon aure Daddy yayi ko kuma hankalinsa ya karkato kanta ya bud'e baki ya nemeta da kansa idan ko ba haka ba Ayrah tayi sallama da zaman gidansa har abada saboda halin Hajiya Khubura da na 'ya'yanta suna neman hallaka masa 'ya da azabarsu batare daya sani ba..................
✍️MRS ÄL'ÄMËËÑ ÄHMÄD ÇË.
See you tomorrow morning at 10:50 insha Allah tnks for ur supports masoya nagode da kauna godiya sosai sosai godiya 🌺.
Manzon Allah saw
Ya shugaban halitta kowa yana a kwance Kaine tsayayye
Ya ashja'ul kalki Mustapha ai waninka ne tauyayye
Dakai na dogara nake tarewa kaidi na aljani harda maye
Dole su ganni tilas su barni dominka ya aba zamzamiyyah.
Saleem Musa Abubakar
Naja'at Musa Abubakar
Fatima Musa Abubakar
Aishat Musa Abubakar
Abubakar Musa Abubakar
I know everything about you is so good but one thing is wrong that you are not mind wannan haka yake ubangiji Allah ya kara had'a kanmu Allah ya bamu zuriya dayyiba Amin.
TYPING📲Sat Mar 15/25 10:50AM
YUSRAH MUSA ABUBAKAR ✨ ✨.
👑 ROYALTY 👑
In the name of Allah the must benefits and the must merciful ALLAH THE MOST HIGH DOESN'T SLEEP ALLAH THE MOST HIGH IS PURE HE ACCEPT ONLY WHAT IS PURE we love our NABI MUHAMMAD SAW no success without him he's the mirror of our life he's the light of every darkness he've no limits ya rasulullah muna sonka fiye darai da iyaye da dukiya muna sonka fiye da dukka muradi na zuciya ANNABI mu mu ganka shine buri na zuciya lamince mu ganka ya mai salsabil da khausara.
5~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Da'inah.
@YUSRAHMS CE
Page 09 & 10
Sakamakon komawa da Ahmad zaiyi kamar yadda ya saba idan zai tafi zaibi 'yan uwa yakai musu ziyara hakan yasa ana gobe zai tafi suka shirya shida prince Hamid suka tafi dangin Momy zasu gaishesu a 'ka'ida sai sunje ko'ina karshe suke zuwa gurin 'kanwar Momy saboda suna dad'ewa a gunta tana zaune tare da d'anta saurayi a parlor suna hira ta gansu sun shigo kamar a mafarki musamman Ahmad take bi da kallo domin ya dad'e baizo gida ba kusan shekara biyar shiyasa lokacin daya dawo yaga yadda Baby da Khairat sukai girma yayita mamaki wai 'yan yaran nan ne sukai wannan girman balle yanzu da itama a nata 6angaren take mamakin ganin yadda shima Ahmad d'in ya qara cika mata ido har suka zauna bata daina kallonsa ba saida suka gaida ita sannan ta amsa da murmushi akan fuskarta tace.
"Ahmad wai kaine haka kamar kana shan yis"?.
Murmushi prince Hamid yayi shima yana kallon Ahmad d'in yace "ai Mama Ahmad aikin sojan nan ya kar'beshi kalli fa yadda yake wani irin 'kyalli ga 'kiba har aje tumbi yake kamar irin manyan alhazawan nan" ya karasa maganar yana sakin dariya ganin wani kallo da Ahmad yayi masa itama mama dariyar tai tana cewa "kai Abdul-Hamid akwai ka da tsokana ina wani tumbi a jikin Ahmad kawai dai kace yayi 'kiba shine".
"Eh Mama ai hakan nake nufi kalli fa wuyansa kamar goyayyan bujimi😁".
"To ko goyayyan bujimin ne"? Ahmad ya tambaya yana had'e rai kad'a kai prince Hamid yayi yana cewa "oho waya sani ko goyayyan bujimin ne amma da alama shi d'in ne tunda harka tambaya Mama ya kike ya gida kwana da yawa nima bana samun lokaci nazo kullum muna hospital".
"Ina lafiya kalau Abdul-Hamid ya wajen Aunty take fatan itama tana lafiya"?.
"Lafiyarta kalau tace ma a gaisheki" ya fad'a yana mayar da hankalinsa kan Amaan yace "kai kuma yau kaine abokin taya zancen kenan ina sauran yaran suke Maryam da