x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 22 - ROYALTY YAN SARAUTA

  • 63001 words
  • 66000 words
  • Out of 85109 words

Category: Love Stories

Views 1684

20 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
na rantse da Allah idan na dawo na tarar kun daketa saina 6allawa wannan yarinyar 'kafarta" ya fad'a yana nuna Abidah sannan ya juya inda Ayrah take tsaye yana kallonta yace "ko kallo Abidah tai miki wanda bai gamshe kiba idan na dawo ki fad'a min zataga yadda ake wasan tsutsa a rana ta sanni tasan halina dan ubanta ba'ai min raini" yana fad'in haka ya juya yama fice daga gidan gabadaya jin tashin motarsa yasa Abidah fashewa da kukan ba'kin ciki tana cewa.

"Umma kiji Yaya khaleel da mugunta nufinsa bazan rama ba kenan ta daki banza saboda yana sonta wallahi saina daketa saidai idan ya dawo ya kashe ni" ta fad'a tana tafiya ta gudu ta cafki Ayrah suka hau dambe da sauri Hajiya Khubura taje ta janye Abidan tana cewa "ke dan ubanki ki rufawa kanki asiri kinsan khaleel d'anye ne ba isasshen hankali ne dashi ba zai iyayin abinda yace ki kyaleta kawai akwai ranar ramawa domin bata isa ta fitar miki da jini mu barta taci bulus ba muma saimun fitar mata amma ba yau ba muje" ta karasa maganar tana janta suka bar gurin tsaki Ayrah tai tana wucewa ta shiga bedroom d'inta domin tai wanka tazo taci abinci tasa a ranta itama daga yau bazata sake yarda Abidah tai mata wani abu ta rabu da ita ba ramawa zata ri'ka yi tunda ta fahimci a baya sunyi amfani da damarta yanxu kuma kan mage ya waye itama ta fara gane abinda ya kamata tayi idan sun 6ata mata karta rabu dasu ta d'au mataki da kanta.

*•*•*
Su Nadiya amarya manya maganin karagar 'kasa yau bari mu le'ka gidanta muga meke faruwa idan ta rage mana kazar amarcin mu gwangwaje😋 tana zaune ta hakimce a parlor anci kwanka Sabit ya fito shima cikin shiri tana ganinsa kuwa ta sake d'aukar sabon salon kissa tana karairaya ta tashi tana rungume shi ta sakar masa kiss tana murmushi tace "wow kayi kyau sosai my one kaga yadda kake wani she'ki kamar gold"? Ta fad'a tana dafe kafad'unsa gira ya d'auke mata yana kallon ta shima yace "da gaske nayi kyau"? Kaita d'aga har lokacin bata daina murmushi ba saboda tana tsananin sonshi tace "da gaske nake har naji kishi ya kamani yadda kayi kyan nan karmu fito 'yan mata su kalle mun kai" ta karasa maganar a shagwa'be tana d'an jada baya harda bubbuga 'kafa jawota jikinsa yai yana cewa "karki damu ki daina damun kanki babu wacce ta isa tai miki 'kwace na domin ina tayaki kishin kaina" yana rufe baki ta saki dariyar farin ciki tana cewa "yauwa alhamdulillahi wallahi har kasa naji dad'i a raina dama nasan kana sona kana jidani shiyasa nima nake kula dakai sosai" ri'keta hannunta yai yana nufar kofar fita harabar gida yace "taho muje kar lokaci ya 'kure mana" janta yai suka fita har zai dau'ko musu motar a rumfar aje motors na gidan Nadiya tace ya barshi yau marmarin tafiyar 'kafa take so tare suka fita hannunsu ri'ke da juna suna tafe suna shan soyayya hummm suna wucewa Boukar dake ra6e ya fito yana d'aga waya da sauri ya kira Mah kamar yadda tace idan ya ganshi ko duk sanda ya samu wata 'yar alama ya kirata ya fad'a mata yana kiran nata kuwa kamar jira take ko wayar na hannunta cikin gaggawa ta d'aga tun baiyi magana ba tace.

"Hello Boukar ka ganshi ne"? Kai Boukar ya jinjina yana qara kallon hanyar da suka bi kafin yace "eh na ganshi yanzun nan Mah wallahi da gaske ne abinda ake fad'a domin tunda nazo nake bibiyarsa kamar yadda kika bu'kata kuma na gano gidan da yake zaune tare da matar tasa Sabit yayi aure yanzun nan suka wuce ta gabana amma ban yarda ya ganni ba" daga can 'bangaren matar tace "ok kasan mezai faru yanxu kaci gaba da kula min da motsinsa karka yarda yasan kana garin so nake nazo na ritsa shi da matar tasa naci ubansu tunda ya raina min hankali
jira nake Naomi ta karasa exam d'inta mu taho nan d'in tare harda Niseh yanxu inaso ka bisu ka gano ina zasuje".

"Ok Mah" ya fad'a yana katse kiran da sauri ya mayar da wayar aljihu yana bin bayansu da gudu tunda yaga ba'a mota suka fita ba yasan bazasu yi masa nisa ba zai tarosu yanzun nan.
HUMM MUJE ZUWA🤨.
✍️Mrs Äl'ämëëñ Ähmäd çë 🌺.
Tnks for ur supports 🔥 yusrah ce.

TYPING 📲 Fri April 2025 3:00PM
YUSRAH MUSA ABUBAKAR ✨💯.

👑 ROYALTY 👑

ANNURI WRITER'S ASSOCIATION 💫
Gidan kar'bar mutane hannu biyu da zaman lafiya ÀÑÑÙRÌ haske le'ka gidan kowa koda ma'kiya na kallon ka ramin kura sai'ya'yan ta.

STORY WRITTEN ND EDITING
✍️ YUSRAH MUSA ABUBAKAR
Mrs Äl'ämëëñ Ähmäd çë.

🕋🕌🕋
It's Friday don't forget to recite suratul al-khaf may Allah bless us may Allah open the door of success to us may Allah forgive us may Allah protect us and our family from all calamities Amin.

14~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Muttaqinah.

@YUSRAHMS CE
Page 27 & 28
Su Khairat basu san yau Ahmad zai koma ba harya shirya basu shigo part d'in ba suna part d'in Mami saida ya kira wayar Khairat yace yanxun nan su sameshi a gurin Momy kafin ya kirga goma karta kashe wayar zai ri'ka kirgawa suna ji hmm da gudu suka shigo kowa tana haki ganinsa cikin shiri yasa suka zaro ido waje suna kallon juna oh ashe tafiya zaiyi tome sukai masa yake nemansu ko dukan bankwana zai musu domin Kiran dayai ma sun d'auka laifi sukai masa saida suka zo suka ganshi a haka tuni kowa taji zuciyarta wasai da sauri suka karaso suna zuwa gabansa ya kallesu yana cewa "baku iya gaisuwa ba"? Tuni suka nutsu suna daidaita numfashi sukace "ina kwana''? Bai amsa ba sai kallo da yake 'kare musu daga baya yace.

"Ummul-khairi da Zuhra Allah ya kawo mu yau zan tafi zan barku sai ranku yai fari mugu zai koma inda ya fito amma ku sani na tafi ina nan haka nake kuma zaku gani ban baku ha'kuri ba idan bana nan dan Allah kar kuyi abinda nace ku 'ketare sharud'an dan saka muku Ina daidai daku" juyawa yai yana kallon Momy wacce ta girgiza tana murmushi yace "Momy ki zama witness na riga na fad'a musu komai kar tsautsayi yasa su aikata min zan hukunta su suce kuskure ne ko Abdul-Hamid ya shiga maganar please Momy dan Allah duk abinda sukai ba daidai ba idan na kiraki ki ri'ka fad'a min zan rubuta a littafi na aje sai ranar dana dawo idan laifi d'ari sukai saina hukunta su sau d'ari bazan gaji ba idan suna bukata harda 'kari zanyi musu".

Kai Momy ta d'aga tana cewa "Karka damu Ahmad insha Allahu bazasu kuskure ba zan lura dasu kasan su waye 'kannan ka akwai tarbiyya da ladabi ko baka bada sa'kon a kula dasu ba bazasu aikata maka kuskure kamar yadda ka hanesu ba" Momy tana rufe baki ya mayar da hankalinsa kansu yana jinjina kai yace "ba kunji ta shedeku ba wallahi idan naga abu sa6anin fahimta sai naci uban ku" ya fad'a fuska a d'aure ba wasa kafin ya mi'ke yana kallon Momy da itama ta mi'ke tana cewa "muje nayi maka rakiya Allah ya kiyaye hanya Allah ya dawo min dakai lafiya" da sauri Maryam da taci wanka tad'au kwalliya itama ta taso tana taku tazo har gabansa da karairaya tana sauya murya ta ma'kaleta sosai tana cewa.

"Nima fa Ahmad yau harda ni za'ai maka rakiya tunsa Allah yasa ina gidan yau sai munje har airport tare sai naga tashinka koda ace zan baro can" bai kalleta ba kuma baiyi magana ba sai hanyar fita daya nufa Momy kuma ta koma part d'inta zata d'auko hijab da kallo Maryam ta bishi tana cije lips ji take kamar ta sake kiran sunansa amma bakinta yayi nauyi kawai kwarjini taga yayi mata musamman yau data sake ganinsa cikin kakin soja sai ta sake jin wani irin bala'in sonsa da kaunarsa suna linkuwa suna shiga zuciyarta gashi jinin sarauta gashi soja ga kyau da kud'i da ilmi innalillahi wa inna ilaihi raji'un ya Allah ka duba al'amari na ka bani bawan nan naka matsayin miji a gareni" ta fad'a a ranta tana sake kallon kofar daya fita wayar Khairat ya kira yace su fito waje yana jiransu ganin sun fita yasa Maryam bin bayansu da sauri kamar zata kifa tana cewa "ji wani rainin hankali wato saboda ni banza ce ka shareni amma su saida ka fita ka kirasu a waya su bika to wallahi ko har Russia zasu rakaka nima sai naje babu wanda ya isa ya hanani" ta fad'a da gudu ta fita itama daga part d'in Mami ta ganshi ya fito tare da Mami itama tana yi masa kyakkyawar addu'a har gaban mota sukaje prince Hamid zai kaishi duk suna tsaye bayan ya shiga ya zauna kusa da prince Hamid ya kalli su Khairat da suke tsaye suna 6oyewa a bayan Momy yace ''kai me kuke jira ku shiga back seat ko baku gane bane"? Zaro ido sukai Ina yake nufin zasu rakashi har airport ko kuma ina yake cewa su shigo.............

Katse musu tunani yayi da cewa "Dan ubanku baza kuyi min rakiya ba zan tafi shine kuka zuro min ido kuna kallona wato yauma farin ciki kuke zan koma na dad'e ko"? Dariya prince Hamid yai yana cewa "kai malam ba'a son mugunta ina zasu rakaka ka 'kyale yaran nan su sha'ki iska mai kyau dan Allah".

"Wallahi bazan kyale suba sai sunje" ya fad'a yana sake kallonsu murya ba wasa yace "zaku shigo ko saina fito kanku"? Tun bai rufe baki ba suka bud'e suna shigo kowa salati take bud'ewa itama Maryam tai tana shiga ta zauna kusa da Baby harda sake turata tana matsar ta dan tai magana ita kuma ta share kamar batasan da wanzuwar Maryam d'in a gurin ba hakan kuwa yasa ciwo a ran Maryam badan da Ahmad a motar nan ba wallahi yau saita faffalwa Baby maruka da zuciyarta tai sanyi.................

Jin mota ta tsaya yasa ta d'ago daga tunanin da take tana kallon gurin a ranta tana cewa "to ina ne nan kuma dama ba airport zaije ba"? Ganin sun fito suna shiga yasa itama ta fito tana bin bayansu batasan gurin kakaninsu suka zo ba saida ta shigo ta gansu kan bala'i dama kakaninsu suna nan a raye bata sani ba anan suke a cikin masarautar kodan suna 6angaren su daban ne shiyasa basa zuwa kuma da nisa humm aiko taga gurin zuwa dole ta ri'ka kawo musu ziyara saboda su saba zata ri'ka nuna musu tana son Ahmad ko Allah zaisa ta dace tunda taga acan bata samu kar6uwa a gurin Momy ba.

Iya su kadai suke zancen su banda ita saboda batasan me zatace ba kusan awarsu guda anan sannan suka mi'ke suna yi musu sallama suka fita su Baby kam sunyi tunanin iya nan zasu rakoshi shiyasa da suka fito iya Maryam ce ta shiga motar sukam daba marmarin tafiya tare dashi suke ba babu wacce tai motsi saida suka ji yace "ba iya nan zaku tsaya ba har airport zamuje mun fito kun wani 'kame a gu d'aya kamar dogarai ku shigo man kuna 6ata min lokaci" ya fad'a harda zare musu ido ba shiri sukai kowa tai 'kasa dakai saboda tsoron karma su had'a ido yace wani abu ko yace sun masa laifi tunda sun fahimci so yake yad'an ta'ba lafiyar jikinsu Kuma badama domin babu wanda yai masa laifin dazai dake sun shiyasa yake jansu kafin aje airport d'in ko zasuyi masa laifin..........

"Baby da Khairat baku ji abinda nace bane"? Kai Baby ta girgiza tana cewa "kayi hakuri Yaya ni kaina ke ciwo" ta karasa maganar har lokacin kanta yana 'kasa taki d'agowa gudun karya gane karya take son zuwa airport din ne batai......

"Ko duk jikinki ne yake ciwo yau sai kinje airport d'in nan wallahi tunda na rantse ba kaffara shigo" wata iriyar harara Maryam ta sakarwa Baby tana gyara zama ta babbake gurin dan karsu shigo tana kallon Ahmad ta mirron mota tace "kaima Ahmad kamar dole saida su mezasu baka daka damu saitaje tunda tace kanta ke ciwo ka kyaleta man su koma tare da Khairat ni zanyi maka rakiyar har airport d'in ma dawo tare da Abdul-Hamid" bai kula maganar da Maryam ke masa ba sai kallonsu dayai yana cewa "wai uwar me kuka tsaya kallo na fito kenan"? Ya fad'a yana shirin bud'e murfin motar ya fito ganin da gaske yake yasa da sauri kowa ta bud'a ta shiga kaiya jinjina yana had'e fuska daidai prince Hamid ya tada mota ya kalleshi da murmushi yana cewa "Allah ya shirye ka kai dasu kamar wasu Tom and Jerry kaine Tom d'in su kuma Jerry's ace ba dama ku kasance guri d'aya bakinka bazai shiru ba ka d'an ri'ka d'auke kai mana".

"Wallahi basu isa ba indai suka samu damata kamar yadda suka samu taka humm wadannan yaran" ya fad'a yana nunasu ta mirror yana cigaba "da babu wanda zai fad'a musu suji kana gani fa wancan lokacin ina barin gari suka d'aura balloons harda sayo cake wai sukai valentine na tafiya ta kodan harda kai aciki laifinka ne daka hanasu baza suyi ba" Ahmad na rufe baki prince Hamid ya girgiza kai yana cewa "a'a malam kada ka la'ka min laifin daba nawa ba ni bansan party zasuyi ba wallahi har suka gama shirinsu saida na shigo gurin Momy zan gaidar da ita da la'asar sannan naga suna had'awa na tsaya na kalla kaga kuwa mene laifina a cikin nan waye me laifi d'an kallo ko me aikin"? Baki Baby ta rufe tana kallon Khairat wacce itama ta zaro ido ganin prince Hamid yana neman ya tada mutuwa daga barci yasa Ahmad ya dawo da laifin sabo yadda suke a airport d'in nan ba kusa da Momy ba ya dagargaje su son ransa, sun d'auka Ahmad zaiyi magana da prince Hamid yace haka sai kuma sukaga baice komai ba babu wacce batace alhamdulillahi a zuciyarta ba sai Maryam da take cika da batsewa ita kad'ai ganin kamar duk sun manta da ita a cikin motar d'an karamin tsaki taja wanda bai fito fili ba daidai sun shiga airport d'in prince Hamid yayi parking suna fitowa yana cewa.

"Ahmad wannan lokaci ma yaso fita fa"? Ya fad'a yana kallon agogon hannunsa tsaye Ahmad yai a gurin yana mi'kawa prince Hamid hannu sukai musabaha yace "please Abdul-Hamid dan Allah na baka amanar kula da yaran nan duk abinda sukai kuskure karka 6oye min ka kirani ka fad'a min dan Allah saboda tunda suka fara idan na tafi su had'a party bazasu daina ba sunyi d'aya kar suyi na biyu idan suka sake zasu had'u da fushina wanda sai sun gwammace dama basu zo duniya ba" ya fad'a da serious face yana kallon su ganin yadda duk suke a tsarake kamar masu shirin zubawa da gudu jinjina kai prince Hamid yai yana cewa.

"Karka damu Ahmad insha Allahu ni nayi maka alkawari bazasu sake aikata hakan ba idan baka nan" ya fad'a yana jijjiga hannunsa da yake ri'ke dana Ahmad d'in "ok thank so much zanso hakan ya faru na tafi saina dawo" ya rufe baki Maryam har 'kwaruwa tai wajen cewa "please Ahmad dan Allah ka tsaya Abdul-Hamid yayi mana photo" kamar bazai amsa mata ba sai kuma ya juyo yana kallonta kamar me nazari kashe masa ido tana matsowa inda yake cike da iyayi ta mi'kawa prince Hamid waya fuskarta fal da murmushi kamar an biya mata hajji tace "yauwa dan Allah d'auke mu Abdul-Hamid d'auke mu" ta fad'a tana sake mannuwa a jikin Ahmad d'in ganin yau ta samu damar data dad'e tana so har kwantar da kanta a jikinsa take tana qara matsarsa duk yana jinta yana shan kallonta kawai ya shareta ne shima saboda ganin tafiya zaiyi bai kamata ace sunyi rabuwar wula'kanci ba kusan photo ashirin akai musu kafin Ahmad yace ya isa haka kar'bar wayarta Maryam tai daga hannun prince Hamid tana dubawa jikinta har rawa yake tsabar yanayin data tsinci kanta na jin dad'i da shau'kin yau tayi photo tare da Ahmad ta ta'ba jikinsa humm har lokacin ji take kamar tana jikin nasa basu rabu ba.

"Kun tsaya kallo nane ku baza kuzo muyi photon ba saboda bakwa son gani na ko kun matsu na tafi ku daina ganina haka ne"? Da sauri suka girgiza kai a tare suna cewa "a'a Yaya kayi ha'kuri" dariya prince Hamid yai yana kallon su yace "wato harda had'a baki kukai a bada ha'kurin idan ma photon ne dashi bakwa so mene a ciki ana dolene".

"Ok Kaine kake zugasu kenan"?.

"Ni ba nine nake zugasu ba kar kayi wannan zargin kawai dai na fad'i hakan ne saboda Naga kana neman takura musu idan Kuma basu da ra'ayi fa saika 'kyale su".

"Wallahi sai an d'auka harda wani had'a baki suna bani ha'kuri kamar wasu 'kadangaru suna girgiza min kawuna zaku zo muyi ne ko saina.................

Tun basuji hukuncin dazai yanke musu da gudu suka karasa inda yake tsaye kallon Khairat yai yana cewa "ke tsaya anan" ya nuna mata 6angarensa na hagu sannan Baby 6angaren hannun dama ya baiwa prince Hamid wayarsa yayi musu kar'ba yai yana dubawa ganin babu me fara'a a fuskarta ya d'ago ya kallesu yana cewa "bakwa so mukai photon nan babu wacce fuskarta da murmushi kamar wanda kuka samu mummunan labari kuzo ya sake mana wani duk wacce batai murmushi ba tare zamu tafi muje can naci ubanta sannan na sakota a jirgi ta dawo gida idan na dawo kuma tai watering"😳 jin abinda yace yasa kowacce ta sake fuska a bisa dole sukai murmushin da basu shirya ba har saida suka saka prince Hamid dariyar dabai shirya ba ya kalli Ahmad yana cewa.

"Ahmad ka zama mala'ikan yaran nan tsoronka da suke ya 6aci please ka rage wasu abubuwan kodan gaba Ina fad'a maka haka kullum ka'ki wallahi abun zai dameka fa" Ahmad baiyi magana ba sai wayarsa daya kar'ba yana kallon prince Hamid yai mai magana da ido kaiya jinjina suna shirin wucewa yace "ya kamata nima
End Ads