x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 26 - ROYALTY YAN SARAUTA

  • 75001 words
  • 78000 words
  • Out of 85109 words

Category: Love Stories

Views 1685

20 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
da suka zo da ita tana waje a inda suka barta fuskar kowaccen su da farin ciki suka shiga mota suka d'au hanya kasa nutsuwa Mama tai saboda wannan nasara da suka samu hai take suje gida Maryam ta fara wankan maganin daga yau d'in nan ita kad'ai sai murmushi take yi zuwa wani lokaci ta kalli Hajiya Habiba tana cewa "kai amma fa alhamdulillah na godewa Allah Hajiya Habiba dama haka kika san gurin masu magani ni harna tsaya wahalar da kaina a banxa ga inda zaka zo ka biya kud'i bu'katar ka ta biya lokaci guda kaima"? Ta fad'a cikin mamaki tana kallon Hajiya Habiba wacce tai murmushin itama tana cewa.
"Humm ai wannan kad'an daga aikinta nake fad'a miki ko matsayin da nake Kai yanxu da taimakonta ne sannan kishiya da Alhaji yaso yayi min nan ma ina fad'a mata ta da'kilar da maganar har gobe bai sake tasa zancen aure ba kusan shekara takwas ke bari na ta'kaice miki zance a yanzu haka wasu miliyoyin kud'i nake bu'kata daga wajensa da wajen abokan aikina amma ganin nayi bi bazam samu ba na fad'a mata da sanar matan kwana biyu jiya sun turo min kud'in shi kuma Alhaji yace idan ya fita office zaiyi min transfern nasa ne bai shigo ba maybe network ko ya manta bai turo min ba shiyasa kina karanta min matsalarki naji ya kamata kema na kawo ki gurinta ta taimaka miki naji dad'i shine gari domin nikam tayi min ba sau daya ba kuma naga sakamako me kyau kema ina tabbatar miki daya dawo ta karasa kammala abinda tace ku kawo mata shikenan an wuce gun wallahi 'yarki saita aureshi saita zama matarsa gimbiya saita auri d'an sarauta kamar yadda kike buri.

D'aga hannu sama Mama tai da sauri tana cewa "Allah yasa Habiba Allah ya tabbatar mana da wannan rana nagode nagode sosai tsaya anan na fita ni gida zan wuce Maryam kuma ta shiga gidan naki ta d'auko motarta ta koma school saikin jini" Mama ta fad'a tana bud'e murfin motar ta fita.

"Ok nima nagode sai anjima ki gaida gida Halima" Hajiya Habiba tai maganar tana yiwa me gadi horn ya bud'e mata gate suka shiga Maryam ma godiyar sosai tai mata sannan ta dau'ki motarta ta fito a waje ta samu Mama dan haka ta tsaya ta d'auketa takaita har gida sannan ta koma school a ranar duk su biyun wuni sukai da murmushi akan fuskokinsu ganin Ahmad ya shigo tarkon su...........
🤣TAB WALLH KUNA KWALE-KWALE AHMAD SAI BABY BAZAMU YARDA DA WANNAN BA FANS KU KWANTAR DA HANKALIN KU AHMAD YAFI KARFIN SU BABU YADDA ZASUYI DASHI YA ZAMA 'KASHIN CIKIN TURMI MAGANIN WADAN KARE😁.

**Ganin yadda 'kafar Nadiya ta kumbura duk da an gyara mata ga kwanaki sunja amma babu sauki yasa Hajiya Khubura ta cika da fushi tai dam Daddy daya tashi daga gurin aiki yaje gida ya d'auka za'a sallamo su akan lokaci amma sai khaleel yake fad'a masa yauma likita yace baza'ai mata sallama ba saboda kafar batai sau'ki ba gocewar'kashi nata bai daidaita ba shiyasa Daddyn yace khaleel ya tu'ka shi a mota ya kaishi ya sake ganota tare suka je asibitin mamaki ne ya kamashi ganin irin dukan da Nadiyan tasha duk tabo a jikinta domin ranar da abun ya faru da dare yazo dubata baisan haka jikinta yake ba sai yau bayan ya dubata sun fito ya samu Hajiya Khubura a inda suke zaune karasawa yai yana cewa "subahanallahi wadanne irin mutane ne sukaiwa Nadiya irin wannan dukan kamar su goma duk sun kumbura mata jiki gashi har yau bata jin dad'in jikin nata a garin yaya ina mijin nata" kamar Hajiya Khubura zata fasa kukan ba'kin ciki tace "wanne mijinta? bayan mitsiyaci yana gurin uwarsa tai mata dukan tare da 'kannansa su biyu Ashe tsinanne mutanen da suke kawo kayan aurensa duk ba 'yan uwansa bane itama munafikar matar data zo matsayin uwarsa ashe uwar 'karya ce siyanta yayi da kud'i asalin mahaifiyar sa tana Lagos karatu kawai yake anan kuma ya gama yayi Mata karyar bai gama ba ya dawo ya auri Nadiya aka samu wani d'an ala tsinan ya kirata awaya ya fad'a mata shine suka zo tasaka yai mata saki uku sannan sukai mata duka harda Abidah da taje gidan" kai Daddy ya girgiza yana cewa .

"Allah ya rufa asiri Allah ya tsare gaba kin ga irinta ko dama abinda nake fad'a miki akan a tsaya ayi bincike kikace a'a ga ranar nadama tazo tun ba'a je ko'ina ba shikenan ai nizan tafi gida Allah ya sauwake" yana rufe baki tace "ai basu ci banza ba zan nuna musu tana da gata saina d'aukar mata fansa jira nake Allah ya bata lafiya" jin abinda tace yasa Daddy yace.

"A'a karki soma cewa zaki dau'ki fansa laifin waye laifin kine dakin tsaya kunyi bincike duk da ba'a zo wannan matakin da muke kai yanxu ba kuma saida abu ya faru kizo ki d'aga hankalinki cewar bazaki yarda ba duk bai taso ba ha'kuri zakiyi".

A zabure Hajiya Khubura tace "wallahi Alhaji bazan yarda tazo har garinmu taiwa 'ya'ya na irin wannan dukan ba saina bita Lagos d'in naci kan uwarta zatasan wace ni nima ba kanwar lasa bace ta ta'bo masifa a kanta" Hajiya Khubura ta fad'a cikin takaici ganin Nadiya zaune a wuri daya har yanxu bata warke ba shine yake 'kona mata rai Abidah ce da batasha duka sosai ba itakam dama bata kwanta a gadon asibiti ba.

"A'a Khubura komai ya wuce ta riga ta kad'a d'anta sun tafi a Ina zaki ganta ko Lagos d'in zaki bita"? Ya tambaya yana kallonta yaga wacce amsa xata bashi da mamaki yaji tace "mezai hana nabita har can d'in naci uwarta ita bahar nan tazo ta dakar mun yaran nawa ba dan haka Nadiya tana warkewa zamu shirya muje ko Lagos zata hargitse saina dau'ki fansar dukan nan".

"Ban goyi bayan kije ba bana son tada husuma kin manta lokacin auren nace ki tsaya kiyi bincike ne kikece min wanne bincike zakiyi kinsan iyayensa ashe iyayen kud'i ne siyansu yayi suka zo akai auren idan kin tsaya kinyi tunani laifin kine Kuma na tabbata kika bisu Lagos da nufin d'aukar fansa bazaki ta'ba dawowa nan ba sai sun tsafe ki batar dake zasuyi nidai ba ruwana dama na fad'a miki haka batun yanzu ba dan kin 'ki jine amma yanzu Kam kin fahimta ai da kika ga uwar bari".

Shiru Hajiya Khubura tai damuwa goma da ashirin wanda take yi danya karfafa Mata gwiwa yace ba ruwansa to taya zata d'auki fansa saidai kawai ta kyalesu Allah ya saka mata Allah ya isa tsakanin ta dasu bazata ta'ba yafe musu ba tana gani Daddy da khaleel suka tafi ita kuma ta koma cikin asibiti.

Barinsu gidan ba karamin barazana bane ga Ayrah saboda khaleel ya samu lokacin dazai ri'ka fad'a mata zancen banza da duk abinda yaga dama saidai bai samu cikar burinsa ba duk yadda yaso ta bashi kanta ta'ki ko kad'an bata bashi fuska shiyasa ya samu Daddy akan yana so a saka lokacin bikinsu hakan zaifi masa alkairi idan ta dawo hannunsa amma a hakan nan yana ganinta yana jin sha'awar ta gashi taki amince masa zai iya shiga mawuyacin hali shiyasa ya nemawa kansa mafita tun wuri kafin yaiwa kansa illa Daddy ya tabbatar masa suna kammala school zai d'aura musu aure ko kad'an Ayrah bata sani ba Daddy ba kulata yake ba balle ta sani khaleel kuma ganin yanzu tana da waya yasa bai tareta da maganar tana graduate za'ai musu aure ba saboda tsoron gudun karta fad'awa Aiman ya kira Daddy ya hana a bashi.

***Fara wanka da maganin da Maryam tai humm yadda ta fara cikin nasara haka samari suka ri'ka yimata layi kullum idan ta fita mutun uku hud'u biyar shida sai sun biyota gida lamarin yai mugun damun Mama ganin yadda ake mata layi wanda akai hakan danshi bai ma dawo ba data sani ba'a fara ba saida ya dawo yanzu batasan yadda zatai ba tana ganin saidai su koma gidan me maganin ko akwai wata 'yar dabara da zatai wadannan samarin su daina biyota.

Mama tana zaune ita kad'ai a parlor tana tunani har batasan Amaan ya shigo ba duk maganar da yake saida ya ta'bota sannan ta sauke ajiyar zuciya tana kallon sa cikin basarwa dan kar yayi tunanin wani abu tace "Amaan lafiya kuwa naga kamar da akwai abinda zaka fad'a min ko wani abune ya faru"? Kaiya jinjina shima a nasa 6angaren yana sauke numfashi kafin ya d'ago ya kalli Mama data zuba masa ido yace "am Mama dama wata magana zan fad'a miki d'azu Ashraf d'an gidan abokin Abba yace min ranar yazo gidan nan gaisar dake yaga Maryam a lokacin ta shigo yana sonta dan Allah a fad'a miki idan babu kowa nidai nace masa babu duk lokacin daya samu lokaci zaizo" yana rufe baki Mama ta zabura har tana 'kwaruwa wajen cewa.

"Yana sonta kuma shi Ashraf d'in ne yace ka fad'a min haka"?.

"Eh hakan yace a fad'a muku idan kin amince zai shigo su gaisa Maryam d'in duk yadda sukai shikenan domin bada yaudara yake sonta ba aurenta zaiyi".

Kai Mama ta jinjina tana cewa "kuturun ubancan tabd'ijan amma wallahi yaro bashi da hankali uban me Maryam zatai dashi harda wani bada sa'ko a fad'a min? Ya fad'a a banza dan ko Maryam ta rasa masoyi bazata aureshi ba garama karya kuskura naga 'yan 'kafafunsa a gidan nan idan kuwa tsautsayi yasa yazo min gidan nan saina wulakanta shi dan ubansa shid'in banza uwar meya tara a duniya dazai nemi auren mace irin Maryam shashashan banza" ta karasa maganar da 'karfi har kumfan baki take da mamaki Amaan ya zuba mata ido kamar me nazari tambayar dake ransa wanne dalilin ne yasa Mama take fad'a da zage zage dan kawai ya fad'a mata Ashraf nason maryam bayan abun farin ciki ne yayi zaton zaiga ta amshi abun da armashi sai Kuma yaga ta ta'kile shi numfashi ya fitar yana sake d'agowa ya kalleta ganin shita zubawa ido itama yasa yace.

"Haba Mama da girman ki kike cewa haka irin wannan maganar ba taki bace Ashraf fa nake nufi d'an gidan abokin abbanmu Abba Ibrahim ko baki gane bane"? Wani irin kallo tai masa tana cewa "ai tunda kace Ashraf na sani basai ka fad'a min kayan takaici ba uwarsa zatai dashi zaice yana sonta ita ba sa'ar auren irinsa bace karya kuskura yazo min gidan nan idan kuwa yazo ubansa zaici".

"Kenan yayi laifi Mama dan kawai ya fad'i abinda yake ransa cewa yayifa yana sonta kawai to mene abun laifi anan"?.

"Ni a gurina yayi laifi kuma ya fad'i iska ya sota a banza wallahi dan bai isa na bashi auren Maryam ba kome zaiyi ita ba sa'ar aurensa bace tafi karfin irinsa ita saiya canza tasha anan dai bai samu kar6uwa ba".

"Ban gane ba Mama taya Maryam tafi karfin aurensa bayan itama mutum ce kamar sa babu wanda yafi wani sai wanda yafi tsoron Allah dukiya basune rayuwa ko jin dad'i ba naga kuma kamar ita kike hange"? Harararsa Mama tai tana cewa "eh Maryam mutum ce bance maka aljana ba amma tafi karfin aurensa ka gane ina nufin bazan bashi aurenta ba kuma kayi min shiru daga haka kar tsautsayi yasa naji ka furta wannan kalmar a gurin alhaji kasan idan magana taje gurin sa kozan mutu sai Maryam ta aureshi kabar zancen iya nan muyi tono mu binne komai a manta da zancen domin hakan bamai yuwuwa bane".

"Meyasa zanbar zancen Mama bayan abun alkhairi ne yake bibiyarku amma kuna korewa meyasa hakan"?.

"Meyasa zaka bar zancen kake tambaye ta Amaan? saboda ubanka zaka bar zancen ka gane kar nasake jin kayi maganar nan ina gargad'in ka idan tsautsayi yasa ka furta har Alhaji yaji wallahi saina tsine maka gara tun wuri ka kama bakinka" zaro ido waje Amaan yai da mamaki sosai akan fuskarsa yace "Mama meyai zafi tsakaninki da Ashraf haka dan kawai yace yana son Maryam sonta fa yace yana yi kuma dai naga ba wani aibu ne dashi ba kaso masoyinka fa idan ka'ki shi zakaso ma'kiyin ka".
Rai 6ace Mama tace "tashi ka bani gu Amaan duk uban da zakiyi Maryam bazata aureshi ba saika ha'kura sannan idan mugun fata ma kake mata itakam bazata auri ma'kiyin taba saidai ta auri masoyinta" mi'kewa Amaan yayi batare daya sake furta koda kalmar aba yabar parlon da harara Mama ta rakashi tana cewa "jimin sokon banza uban me Maryam zatai dashi ga Ahmad jinin sarauta irin 'kasaita zataje tayi zaman aure a gidan sarauta inda mulki da daula suka samu masauki wanda ya fake a inuwarsu maya huta balle Maryam me kankat da zata auri Ahmad gaskiya Amaan yau na yarda baka da hankali anace maka ga gabas kana ga yamma ana ga ruwa kana ga wuta shashashan banza kawai bari zaka dawo ka sameni saina gargad'inka dole saina sake kashe maka warning akan wannan maganar nasan ba hankali ne dakai ba zaka iya idan Alhajin ya dawo ka fad'a masa saidai naji kuna maganar" ta fad'a tana tashi da sauri ta le'ka harabar gida ko yana nan tai saurin fad'a masa kar taje ya tafi office d'in Abbansu yaje ya fesa mai labarin ya jefata a uku ganin babu motarsa harya fita yasa ta dawo ta zauna ita kad'ai sai fad'a take tana zage zage karshe da taga bazata iya ha'kuri ba ta kira Maryam a waya tace tazo yanxu zasuyi magana an samu akasi da akwai matsala gagaruma wacce ta sakosu gaba zaiyi wuya idan zasu iya tsalle wannan damuwar hanya d'aya zatabi dakatar da Amaan shine matakin farko da zata d'auka kafin ta kira Ashraf har gida tai masa tas ta nuna masa 6acin ranta bata goyon bayan Maryam ta aureshi ba matar irinsa bace ya cire idanunsa a kanta.

Mama tana zaune Maryam ta shigo ganin yanayinta yasa ko zama batai ba tace "Mama lafiya naga ranki a 6ace haka"? Tsaki Mama taja ta kad'a kai ta ri'ko hannun Maryam ta zaunar da ita a kusa da inda take zaune tana cewa "inafa lafiya Maryam yanzu naji wani abu daya daga min hankali Wai wani shige Ashraf d'an gidan Alhaji Ibrahim ne yake sonki ko a gidan uwarsa ya ganki oho masa to wallahi bari kiji ko tsautsayi zaisa yaxo karkije inda yake idan Kuma kinje kiyi masa mugun wulakancin da takaici zai hana yasake dawowa inda kike ki fad'a masa ba'ka'ken maganganu marasa dad'in ji ta yadda idan ya tafi bazai sake marmarin waiwayar kiba har abada" jin abinda Mama tace yasa ta yamutsa fuskca tana cewa.

"Wanne Ashraf kuma a ina ya ganni nidai a tunani na ba had'uwa muke ba balle yace nifa ko fuskarsa yanzu na gani bazan ganeshi ba saboda dad'ewa da mukai bamu had'u ba amma har yace wani yana sona a Ina ya ganni".

Cikin takaici Mama tace "koma menene nibai dameni ba sauri zamuyi mu dakatar dashi kafin alhaji yasani kinsan daya sani sai anyi abun nan Niko bana so me laifi ace Humairah yake so bake ba dan kan uwarsa wallahi bazaki aureshi ba idan bazai auri Humairah ba ya ha'kura" ta'be baki Maryam tai tana girgiza kai tace.

"Wallahi bai isa ba Humairah ma bazata aureshi ba tunda tana da saurayi me zatai dashi balle ni ina kallon Ahmad kyakkyawan gaske jarumtaccen soja me karfi da kwarjini me zanyi da Ashraf wanda baisan fita filin daga ba baiyi training jikinsa ya murd'e ba kullum yana banki sai kace d'an ministan kud'i nidai bazan auri banker ba garama ya sani ba kud'i nake nema ba sarauta nake so Naga idan zan wuce ana du'ka min ana yabona da yimin kirari ga bayi masu yimin hidima ina tafe ana take min baya wannan shine burina mezanyi da kud'i 'ya'yan banki ina dasu kuma sun wadatar ni tunda nima ba zaman banza nakeyi ba inada sana'a ta balle yace zai rud'e nida kud'i".

Murmushi Mama tai harda dagewa tana jinjina kai tace "Yauwa fa karkije gurinsa idan yazo nasan maybe tunda har ya tari Amaan da maganar ki ganshi yazo tunda ba hankali ne dashi ba ya saka mu shiga uku musamman idan akasi yasa Alhaji yana gida ya ganshi yazo d'in kuma yaji ke yake so tabd'ijan heeyyy dan'kari Allah ma ya kiyaye wannan masifa ta samemu domin masife babba ma kuwa da zarar akace yazo shikenan mun kad'e" Cizon yatsa Maryam tai tana cewa "aiko zan nuna masa rashin hankali indai tsantsan hauka ne ya tara ya samu saina tafasa masa jiki da ruwan zafi wallahi saina 'koneshi Allah ya kawoshi ina jiransa zaije yadda ake hauka ganin idonsa".

Kai Mama ta jinjina harda cije lips irin muguntar nan ta saki murmushi tana cewa kaji 'yar gari na tabbata kina yi masa haka azaba zatasa bazai sake marmarin zuwa gidan nan koda ziyara bane balle ya furta yana sonki hakan kawai zaki masa idan yazo ki tafasa ruwa me shegen zafi ki lalla6a ki watsawa shege a fuska idan fuskar ta 'kone yai tabo ya samu wacce zata aureshi a cikin nakasassu ko makauniya ko kuturwa amma dai bake ba kekam sai gidan da ake tambari da kakaki inda algaita take tashi wato gidan sarauta" mi'kewa Maryam tai tana cewa "tabbas Mama kin fad'i gaskiya kiran da kikai min kenan zan koma school maybe ma anshiga mana lecture ina nan".

"Eh kiran kenan dama abinda zan fad'a miki ne dan kar yayi mana shigar sauri baki sani ba amma tunda kin sani yanzun shikenan naji d'an dama-dama hankalin nawa bai kwanta ba tukuna dai" sunkuyawa Maryam tai tana d'aukar handbag d'inta batare data sake magana ba ta fita Mama kuma ta dau'ki wayarta ta kira Momy taji mene labari akan Ahmad yaya a ina suka tsaya shin yana Shirin dawowa kwana kusa ne su d'au shiri suma ko a'a domin gaskiya itafa ta matsu taga Maryam taje gidan nan matsayin matar Ahmad so take taji tambari da algaitu suna tashi shiyasa bata so abun ya dau'ki dogon lokaci ba'ai ba kar wani akasi ya shigo ciki a fasa".
UHMM ALGAITA KUWA ZATA
End Ads