ace munyi photon nan kafin ka tafi Ähmäd" jin abinda ya fad'a yasa Ahmad dakatawa yana bashi wayar alarmar yayi musu kar'ba prince Hamid yai yana mi'kawa Maryam wacce da sauri ta kar'ba ganin wayar Ahmad ce to d'auka iya su biyun zata d'auka sai taga Ahmad yasa su Baby su shigo tuni ta tsuke fuska tana sau'ke wayar kasa ta kalli prince Hamid tana cewa.
"Ya haka ba photo kace zanyi muku kai dashi ba"? Kaiya d'aga yana cewa "eh man d'auke mu sauri yake zai wuce lokaci ya cika" 'kara had'e rai tayi tana cewa "ok su fita gefe nayi muku zakufi kyau ku biyu".
"Su waye zasu fita"?.
"Su Khairat idan sun shiga zasu 6ata muku photo" ta fada kanta tsaye tana harare-harare da mamaki prince Hamid yace "akan me zasu fita taya zasu 6ata mana photo"?.
"Ta yadda ake 6atawa kalli ma basu dace ku d'auka dasu ba nidai badasu zan d'auka ba kaine ka bu'kaci ayi muku photo kaga kuwa ai banda su ko"?.
"No harda su wannan na family dukkan mu zamuyi saboda tunawa kin gane"? Jin abinda yace yasa Maryam tace "oh indai photon family ne saidai mu nemi wani yayi mana tunda nima ba bare bace bari naiwa wani magana" tana rufe baki Ahmad yace "give me my phone" ya fad'a yana mi'ka mata hannu bata bashi ba sai baya kad'an data matsa tana cewa "akan me zan baka ka bari man ga wani ya taho ya d'auke mu kodan nace haka shine zaka 'kwace gani nayi nima jininku ce akan me za'a wareni"? Jin abinda take cewa yasa Ahmad yai banza da ita ko karasa kallonta baiyi ba sai prince Hamid da yace.
"kina jiko Maryam ki fahimta ba hakan yana nufin za'a wareki bane a'a photo ne zamuyi na family 6angaren gidan mu d'aya ba dangi ba shiyasa ba'a saka dake ba ke kina 6angaren Momy ne basu abbanmu ba amma idan mun 6ata miki ranki akan hakan kiyi mana afuw.................
"Abdul-Hamid" Ahmad ya fad'a muryarsa da alamar fushi kallonsa prince Hamid yai ganin yadda ransa ya 6aci akan maganar da Maryan ta fad'a yasa ya mayar da hankalinsa kan Maryam d'in yana cewa "bani wayar lokacinsa yana neman fita" mi'ko masa tai shi kuma ya mi'kawa Ahmad kafin suka wuce saida ya rakashi har gaban matakalar jirgin ya shiga sannan ya juyo ya dawo gurin da suke tsaye sai iya Baby da Khairat ba Maryam a gurin.
"Ina Maryam ta tafi kuma"? Ya tambaya yana kallonsu Khairat ce ta bashi amsa "tana cikin mota Kuna tafiya ta koma" ok muje" ya fad'a suna wucewa tana zaune a gidan gaba tana kallon photunan da prince Hamid yai musu yanzu ita da Ahmad sai status take dasu tana turawa a group din'ta tana fad'awa 'kawayen shine mijin da zata aura tajin sanda suka shigo motar bayan tafiyar ahmad babu wanda ta d'ago ta kalla har ya tada mota suka tafi iya su uku suke magana a motar amma banda ita har dariya prince Hamid yake ganin yadda suka ware suna hira dashi amma d'azu sakamakon da Ähmäd motar ko tari babu wacce take yi sai iya Maryam.
Suna zuwa gida ko tsayawar minti d'aya Maryam bata sake yiba kai tsaye ta wuce bedroom ta d'auko jakarta tana fitowa Momy dake zaune tare dasu Khairat suna fad'a mata abinda ya faru da Ahmad yasa dole suyi masa rakiya kawai sai ganin Maryam sukai ta bud'o kofa ta fito zata tafi da mamaki duk suka bita da kallo Momy dake kallon yadda Maryam d'in take kumbure-kumbure tace.
"Maryam ya haka ina zuwa kuma"? Murya 'kar-'kar alamar tana cikin fushi tace "gida zan tafi" da mamaki Momy tace "gida dai? Haba Maryam rana tsaka kice zaki tafi gida babu shiri ba komai dama haka ake zuwa ziyarar"? Shiru Maryam tai Momy taci gaba "babu inda zakije saikin dad'a yimin sati a gidan nan koma ki aje jakar nan yanzu ki dawo nan muyi hirar tare" jin abinda Momy tace yasa Maryam kamar zata fashe da kuka tace "dan Allah Momy ki barni na tafi wallahi zan sake dawo muku yanzun uzuri ne ya taso min".
"Wanne irin uzuri kuma ko a school"? Kaita girgiza tana cewa "a'a ba'a school bane gida zanje gurin Mama" murmushi Momy tai tana kallonta kamar zata sake cewa wani abu sai kuma ta 'kyale tana cewa "ok ki gaishe min da ita nagode sosai da ziyara Allah yayi miki albarka" su Khairat ta kalla tana cewa "ku tashi ku d'an taka mata man" Momy ta rufe baki Maryam ta girgiza kai da sauri tace "a'a basai sun rakani ba suyi zamansu na tafi" ta fad'a fuuu tana nufar hanyar fita dakatar da ita Momy tai.
"Amma ai kya tsaya Khairat ta taso taiwa driver magana ya kaiki ko"? Nan kaita girgiza a karo na biyu tace "a'a Momy nagode zan fita can waje bakin titi na tari d'an napep saina sake zuwa miki" tana fad'in haka ta bud'e kofa wuff ta fice murmushi me had'e da jinjina kai Momy tai tana mi'kewa ta shiga part d'inta ta d'auko kud'i tana baiwa Khairat tace "tashi maza yanzun nan ku kai Mata tahau napep d'in ko ta'ki kar'ba karku dawo min dashi kusan yadda zakuyi ku bata" kar'bar kud'in Khairat tai suka mi'ke tare Baby suka bi bayanta tsabar saurin da take harta fice daga masarautar sai acan wajen gate d'in karshe ma farkon shigowa suka sameta hakan ma sai kira Khairat ta 'kwalla mata tana ji tai banza har saida suka dad'a sauri suka tarota kud'in Khairat ta mi'ka mata tana cewa "gashi Momy tace kihau napep ya kaiki gida" baki Maryam ta ta'be tana girgiza kai tace.
"No nagode ki maida mata kud'inta ina dashi kud'in da yake gurina ya isheni har yayi min yawa".
Kallon yadda ranta yake a 6ace Khairat Tai tana cewa "Tace karna mayar mata matsayin naki dabam nata dabam please Maryam ki kar'ba".
"Nace miki a'a ki mayar mata ina da kud'in zuwa gida ya ishe ni".
"Amma a tunani na Maryam ko duniya ce a tare dake dan Momy ta baki kud'i ki hau abun hawa bai kamata kice a'a ba ra'ayi tai ta baki aitasan kina da kud'in ta baki ki kar'ba dan Allah".
"Khairat kinsan halina fa idan na riga na furta abu na furta kenan bana canzawa nima yakamata ki fahimce ni nace miki na gode ki maida mata ko bakiji sosai bane"? Ta fad'a tana aikawa Baby harara da dogon tsaki wacce tunda suke maganar su ko tari batai ba sai yanzu Maryam take nemanta da fitina tace "ke kuma uwar zulai meye kika zuro min ido kina min kallon 'kurulla idan make me lashe-lashe ce toni nafi 'karfin ki saidai kici kanki gida da bedroom kuma gashi na bar miki ki dafa kici nima muna da arzikinsa ba fatara ce ta kawoni gidan naku ba balle kiyi min wani jakin kallon ki" jin abinda Maryam tace yasa Khairat tai mugun had'e rai tana cewa.
"Wai Maryam wanne irin abune wannan kike yi yada girman yayi yawa dan masifa bata kulaki bama saikin takale ta kunyi fad'a dad'in abun ma ita wacce kikeyi dan ita ko kallo baki isheta ba kotanan ya kamata ki sallama kiyi Dana sani nadama da saranda akan abubuwan da kike ba daidai bane" zazzafar harara Maryam ta sakar wa Khairat tana cewa "Babu ruwanki ba dake nakeyi ba gada wacce nake maganata idan ta isa yau ta tanka min kamar yadda Tai min kwanan baya wallahi saina 6allata a gurin nan dama ina wuya da ita dan haka duk abinda zamuyi naki idone Khairat karki shiga abinda ba'a saka dake ba karki d'auka" ta fada tana mayar da kallonta kan Baby tace.
"Ke kuma ina sauraron ki idan kin isa ke cikakkiyar fitsararriya ce kiyi min magana yanzu kiga aiki da cikawa" d'auke kai Baby tayi tai banza da ita kamar dai irin bada ita take ba takaici ne ya kama Maryam har batasan lokacin data ciji yatsa ba murmushi Khairat tai tana cewa ''nida nasani Baby bazata kulaki ba ko kanki zaki cinye saidai kici ke kad'ai gashi kuwa hakan ya tabbata kinga da zaki gane saiki daina wahalar da kanki a kanta dan indai ba rashin neman zaman lafiya ba banga abinda ta tare miki ba alhali kece kika zo kika sameta".
"Ai dama bazaki ga abinda tai min ba saina fad'a amma ki sani bani da lokacin ku dukka biyun baku isheni kallo ba banzaye ku jira dawowa gidan sai nayi maganinku mtswww" taja tsaki a fusace tai gaba da kallo Khairat ta bita tana cewa "Allah ya yaye miki wannan abubuwan idan masifa ce ta sameki idan kuma zaki gyara Allah ya ganar dake da wuri muje Baby" juyawa sukai suna komawa Momy tana zaune a inda suka barta basu nuna bata kar'bi kud'in ba ko kuma ga abinda tai kawai Khairat tacewa Baby kar tace Maryam ta'ki kar'bar kud'in sun dawo dashi zata 6oye sai abun ya wuce yadda koda ta fito da kud'in nan tace mata bata kar'ba ba tasan sannan abun bazai mata ciwo kamar yanxu ba shiyasa ma fuskarsu wasai suka dawo mata suna d'ora hirarsu daga inda suka tsaya.
Maryam kam me napep ta d'auka har kofar gate d'insu ta bashi kud'insa tana d'aukar kayanta ta shiga ciki Mama tana zaune a parlor sai ganinta Tai ta shigo mata kamar mafarki harda murje ido Tai ganin da gaske itance yasa zubur ta mi'ke tana tahowa gurinta da sauri tace "Maryam ya na ganki haka da rana tsaka meya faru dawowar me kikai ne kardai wani abu ne ya faru a tsakanin ku"? Zama Maryam tai tana sau'ke numfashi tace "a'a kwantar da hankalinki babu abinda ya faru kawai tahowar dad'i ne".
"To kice yau da labari kenan mu bud'e kunnen mu dakyau"? Kai Maryam ta jinjina tana cewa "akwai Mama labari d'aya kenan saidai kice akwai labarai".
"Tofa labarai humn a fad'a mana muji dan harna 'kagu sosai naji abinda yake faruwa" ta fad'a tana sake matsowa ta saito kunnenta dariya Maryam tai tana cewa "kai Mama akwai son jin labari dama ba wani abu bane ya sakani farin ciki sai photo da mukai da Ahmad d'azu" zabura Mama tai tana kallon ta tace "um um fa Maryam banda 'karya Ahmad d'in nan a yadda kike fad'a min baya ko kallonki shine zai yarda kuyi photo"? Murmushi Maryam tai tana d'auko wayarta a cikin handbag d'inta ta bud'e tana nunawa Mama wacce babu kunya ta mike tana rawa harda wa'ka a gaban maryam d'in saida ta gama ta tsaya ta kalli Maryam tana zama tace.
"Yauwa Masha Allah sai mene ya faru"?.
"Babu komai kawai sai rakiya da mukai masa zuwa airport ya koma Russia shiyasa na tattara kayana na dawo gida kinsan yanzu zan taho harna fito sosai wai sai sannan Momy ta turo Khairat wai ga kud'i nahau napep ni kuwa na'ki kar'ba nace ta mayar mata dan tasan naji haushi" harararta Mama tai tana cewa "ji banza kawai meye abun 'kin kar'ba raba arne da makami ibada ne kikasan nawa ta baki" shiru Maryam tai tana d'aga kai sama kamar me tunani tace"kuma fa da yawa kud'in nan Naga suna da tudu yakai kusan dubu...............
"Ke rufe min baki bana son kayan haushi kawai fad'a min meya faru a gidan tun daga ranar da kika je har zuwa yau yanzun nan da muke magana yaya kukai da Ahmad shin kin samu shiga ne koko a'a"?.
Kai Maryam ta girgiza tana cewa "humm wai babban aiki kenan gaskiya yanxu a gajiye nake zanje na huta idan na fito saina fad'a miki komai nidai kawai abinda zai Dade yana bani mamaki shine yarda da Ahmad yai ya tsaya mukai photo kawai hakan ne yake 'kayatar dani".
"A ina kukai photon ne a gidansu"?.
"A'a airport fa mukai masa rakiya".
"Ok komawa yai kenan shiyasa kika taho"?.
"Uhm ya tafi d'azu sai kuma ya dawo amma naga tunda nazo nace miki ya koma" gyara zama Mama tana d'aga kai alamar eh sannan ta kalli Maryam da fuskarta take fitar da annuri na annashuwar wannan maganar da suke tace "ke Maryam baki fad'a min ya kukai dashi meya faru da kikaje gidan yaya kinyi kokari ya fahimci kina sonsa ne ko a'a a sadaka kikaje yanzu kika dawo min gida a alakoro"? Kai Maryam ta girgiza tana cewa "eh to gaskiya ban sani ba koya fahimta domin shi murd'add'an mutum ne baka iya ganewa inda ya dosa zai iya idan ya fahimci ina son nasa ma ya shareni sai daga baya ya furta min nidai haka nake tunani Dan komadai mene na tabbata yasan ina sonsa tunda kunyi magana da Momy kuma ai nasan ta fad'a masa duk da har yanxu bakiji amsa ba a bakin Momyn zata fad'a miki idan ya fad'a mata itama fa tana so ya aureni dan ta fad'a min cewa na kwantar da hankalina Ahmad zai aureni shiyasa ba na sharesa nasan ko ya'ki da tasa baki shikenan an wuce gurin ko"? Ta karasa maganar tana kallon Mama wacce tunda ta fara magana take jinjina kai tana murmushi har takai aya kafin ta d'aga hannu sama tana cewa.
"Alhamdulillah Allah nagode maka ubangiji ka tabbatar min da abun nan ya Allah kasa Maryam tana rabon auren Ahmad a rayuwa wannan shine burina ubangijin rahma ka cika shi"
Karki damu Mama ki manta da batun aure kam nida Ahmad a rubuce yake saina aureshi domin bazanyi dakon sonshi a banza ba kuma ina kallo ya auri wata a gabana tabd'i wallahi hakan bazai ta'ba yuwuwa ba never in history har abada inko wata tai gigin shiga hurumin daba nata ba zataga hauka da bala'i saina kasheta".
"Daina ma 6ata bakinki da kiran mutuwa ba wannan maganar kawai dai bazamu amince ya auri wata ya barki ba wannan shine Kat idan kuma yaji a ransa shi da akwai wacce yake so ko yake son aura saiya had'aku biyu nan ma na gamsu amma ban amince da ace ya watsar dake ya auro wata tsinanniya shashashar ta zauna dashi ba ita kad'ai ba".
Mi'kewa Maryam tai tana cewa "bari na karasa ciki Mama idan na fito xanyi miki bayani dalla-dalla yadda zaki fahimce ni domin nima yanzu ba daidai nake jina ba" da kallo Mama ta bita tana murmushi tace "ok Maryam ina jiranki dan bazan iya moruwa ba sai naji yadda kukai dashi Allah yasa dai kinyi nasara" ta fad'a tana sake kallon kofar da Maryam d'in ta shiga kafin itama ta mi'ke tana shiga bedroom nan da awa d'aya ta fito koda maryam bata fito ba ita zataje har part d'in nasu ta fito da ita yau sai taji labarin nan da hankalinta ya kwanta...........✍️ Mrs Äl'ämëëñ Ähmäd çë🌺.
See you tomorrow morning at 8:56am insha Allahu.
Nagode da kulawa masoya godiya sosai sosai godiya🤝.
YMA DUTSE NEW WORLD 🌏
√√√√√√√√√√√√√√√√√√√√√√√
TYPING 📲Sat Apr5/25 02:49pm
YUSRAH MUSA ABUBAKAR ✨💯.
STORY WRITTEN ND EDITING
YUSRAH MUSA ABUBAKAR
✍️Mrs Äl'ämëëñ Ähmäd çë.
15~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Mustagfirinah.
@YUSRAHMS CE.
Page 29 & 30.
Rashin waya a hannun Ayrah ba karamar illah bace gashi babu yadda za'ai taje gidansu Aiman tai waya dashi ko a wayar 'kannansa tunda Daddy yayi mata iyaka da gidan Baby kuma ba wayace da itaba balle idan tazo school ta ara tai kira sosai tai mugun shiga damuwa wanda har damuwar tata bata 6oyuwa koda school taje bata tsayawa tai karatu sosai yanzu har saida Baby ta tambaye ta mene matsalarta ta fad'a mata ganin cewa itama bazata iya yi mata maganin matsalar ba tayi kokari ta rarrasheta sannan tace idan prince Hamid yazo d'aukarta anjima zatai masa magana ya bata aron wayarsa tunda tace ta ri'ke numbar Aiman d'in a kanta ta saka tai kiransa koma mene ta fad'a masa ya d'auka mata mataki.
Da yake yau dogon lecture ne har 'karfe biyar da rabi suna school sai wajen shida suka tashi sakamakon Baby tacewa Ayrah ta jira prince Hamid yazo ta amsar mata wayarsa tai kiran Aiman shiyasa bata tafi ba suka fito tare a tsaye jikin mota suka sameshi yana jiran fitowar Babyn karasawa sukai Ayrah na gaidashi cikin sakin fuska ya amsa mata domin yawan zuwa d'aukar Baby da yake yanzu yasa ya santa sosai kallon Baby yai wacce gabadaya hankalinta ke kan Ayrah yace.
"Baby yaufa 'kurarran lokaci ne kafin muje gida za'a kira sallah har yaushe naje nayi alwala bana so na rasa jam'i ko akwai abinda kike bu'kata ne naga fuskarki kamar da alamun damuwa"? Kai Baby ta d'aga ranta babu dad'i musamman yadda taga Ayran ta rame cikin kwanaki biyun da basu had'u ba tasan bata jin dad'i sosai a yadda take mata bayanin irin zaman da take a gidansu.................
"Baby" taji muryar prince Hamid ya kirata da sauri ta daidai nutsuwarta tana kallon sa tace "na'am Yaya Hamid kayi hakuri inata 6ata maka lokaci bada sona bane dama Ayrah zaka baiwa aron wayarka zata saka numbern yayanta Aiman ta kirashi yanzu suyi magana ta baka dan Allah" ta karasa maganar harda had'e hannuwanta shiru yai yana kallonta dahar zai tambayi ita ina tabar tata wayar sai kuma yai tunanin ko itama irin Babyn ce da Ahmad ya hanata ri'ke wayar shiyasa ya fasa fad'ar abinda yake son fad'a kawai ya fito da wayar ya mi'kawa Baby yana cewa "gashi nan idan tayi wayar ki taho min da ita ina mota" ya fad'a yana mi'ka mata kafin ya juya zuwa inda motarsa take fake numfashi me dad'i Ayrah ta sauke tana kallon Baby wacce ta mi'ka mata waya kar'ba tai cike da murna ta saka numbern nasa da yake ta ri'ke a kanta tayi sa'a kuwa tana kira ta shiga amma ba'a d'aga ba harta katse saida ta sake kira ana biyu ya d'aga tana jin ya d'aga tace.
"Hello Yaya Aiman" daga can 6angaren Aiman dake zaune da littafi yana rubutu yace "na'am Ayrah yakike"? Kamar zata fashe da kuka muryarta har rawa take tace "ina lafiya Yaya Aiman ya karatu"?.
"Alhamdulillahi Ayrah dama inata nemanki meyasa idan na kira wayarki Bata shiga kullum a rufe yau kuma naga kinyi