x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 2 - ROYALTY YAN SARAUTA

  • 3001 words
  • 6000 words
  • Out of 85109 words

Category: Love Stories

Views 1690

20 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
taga prince Hamid tsaye a bayan ta yana kallonta kame-kame ta fara zatai magana ta kasa cewa komai sai sunkuyar dakai datai tana mammatse yatsun hannunta kuma ta kasa d'aga qafa tabar gurin gashi ta rasa dalilin ta na tsaiwar shiru tai ko zataji yace wani abu amma dai baice mata qala ba har kusan mintuna biyar haka zuwa shida can tsinkayi muryarsa a qasa yana cewa.

"Baby me yasa kika 'ki fad'a wa mum abinda ya faru tsakanin ki da Ahmed kina tsoron ta masa fad'a ne"?.

Kai ta girgiza "a'a ya Hamid idan na bari mum ta sani nice zansha wahala shiyasa bazan fad'a mata gaskiyar cewa dukana yai ba nasan yanzu zata hauro bansan me naiwa ya Ahmed ba da nayi d'an laifi koya yake babu d'aga qafa saiya hukunta ni"?.

"Babu wani Abu da kikai masa kuma ba tsanar ki yaiba da yake hukunta ki idan kinyi laifi baby baza ki fahimce shiba domin har yanzu ke yarinya ce saidai duk abinda kikasan baya so kina nisa dashi kinga shi ba mutum ne mai son wargi ba".

Kai ta d'aga tana cewa "to yaya Hamid nagode zan kiyaye".

"Ok yayi jeki".

Fita tai tana satar kallon qofar bedroom dinsa tare da addu'ar Allah yasa baiji me tace akansa ba tana tafe tana kalle-kalle kamar wacce take jin tsoro har ta shiga part din momy a palor ta samu Khairat tana karatu zama tai tana huci kamar wacce tai gudu wanda Khairat najin yadda take haki aje littafin tai tana kallon ta tace.

"Baby ya dai daga ina kike haka wannan hucin fa kod'ai yauma taku ta had'o kune dan Naga alama keda ya Ahmad yanzu kun zama tom nd jerry"?.

Sau'ke numfashi baby tai tana kallon ta tace "humm Aunty Khairat kedai kawai bari aiyau saida na shiga uku a hannunsa banyi tunanin zai barni darai ba😳 yanzu ma daga part din su nake".

"Innalillahi baby part d'insu kuma ke d'in me kika yo acan"? yadda Khairat tai mata tambayar tana zaro ido waje yasa ta sake jin jikinta yayi sanyi tace.

"Mami ce tace na kai masa abinci".

"Oh ina dukka ma'aikatan gidan da bayi masu kula da komai suke"?.

"Suna can 'bangaren su kisan dasun gama komai ba zama suke ba komawa yankinsu na bayi suke ni ta aika dan ma nayi sa'a bacci yake iya ya Hamid ne da sauri kuwa na baro part din".

Dariya Khairat tai tana cewa "oh ni kam baby kina bani nishadi🤗 in banda abin ki meye zai miki koda idon sa biyu balle yayi bacci duk abinsa ai baki masa komai ba bazai ce zai miki wani abu ba hum'um ya Ahmad me zamani kardai ki shiga harkarsa dan Naga alamarsa da take takensa wannan karon da zafinsa yazo hutu 'karfin samartaka yake ji dashi a banza zai 'ballaki ya barki da jinya.

Kai baby ta jinjina alamar rashin gaskiya tana waige-waige tace "hummn aunty Khairat shiga harkarsa ta nawa saidai na kiyaye gaba kefa laifi na masa yau d'in d'azu da yamma".

"Laifin me"?.

"Kedai bari kawai aunty Khairat idan akace miki tsautsayi baya wuce rana yau shine ya sameni waifa wayar sa ce ya bari a palor kan kujera ya shiga part d'insa ni kuma fitowa ta kenan na zauna banma lura da ya Hamid a parlon ba ana ta kiransa da kiran ya katse wani zai shigo ganin bai fito ba yasa nayi tunanin wanka yake ko bayanan ya fita ne ya manta ta shine na d'aga daga gurin aikinsa ne naji wani na cewa hello Buddy kana jina Ina kasa wayarka inata kira naji bakai pinking da wuri ba"? Jin haka da nai yasa nace "baya kusa mai wayar saidai idan ya dawo" tofa shine yake cemin wacece ke d'in"? Ban lura da ya Ahmad ya fito ba jin abinda ake tambaya ta yasa ya koma part d'insa da sauri nikam na manta wayar boss ce hannuna nake ce masa 'kanwar mai wayar ce.................................


Daga fad'in haka naji saukar belt a baya na bansan ya dawo ba ya kar'be wayar ya bugata a bango ta fashe ya rika min tsawa wai uban wa yasa na dauka masa waya har nake magana da wani banzan gardi 'kadagiri ina mace shiba maharramina ba wai dama wayarsa tayi kama da irina 'kananun yara zasu na dauka kiji fa yanzu meye abin qanqanta a jikina shekara ashirin da biyu just ya nuna ban isa ri'ke waya ba man amma sai yace min qaramar yarinya sai shegen taurin kai" ta karasa maganar tana 'kwaikwayon muryarsa.

Dariya sosai khairi keyi har da tafa hannu tana cewa "anayi muna jin dad'i ana bari muna jin haushi kai abin nan yayi gaskiya yaya yana burge ni akwai gyara mutum amma kedin da kika san halinsa me yasa zaki dauka masa waya".

"To aunty khairat nasan zai dawo a lokacin ne kinsan fa ya Ahmed shi laifi baya masa kadan kalli yadda hannu na yai jaa daya murde min saida na fad'i har kasa ina ihu dan azaba nayi mamaki da ban karye ba".

"Humm kinga da kin karye ai da maci kaza nasan haka ya Ahmed zaita sayo wa muna gwangwaje ta".

"Ni kuma a barni da wahala ba".

Dariya khairat tai tana cewa "To amma baby ya dauke wayar nashi ko har yanzu tana gurin da memory"?.

Ta'be baki baby tai "Wallh aunty khairat ban sani ba saidai kije ki duba".

Zaro ido khairat tai tana cewa "ni kaza🐔 mijina zakara rufa min asiri na jawowa kaina bala'i abun ya juyo min ya sassanbad'e ni nima balle dama wannan dawowar tashi kafin ya dakeki ni ya fara duka".

Sauke numfashi baby tai tana cewa "Aunty khairat nifa bacci nake ji tun d'azu tsoron karna kwanta naji yazo sake hukunta ni yasa na kasa sai yanzu tunda shima yayi barci".

"Ok muje sai mu karasa maganar a bedroom" mikewa sukai suna fita zuwa part d'in Mami bata nan ta ciki dan haka suma kawai bedroom duka wuce suna kwanciya dan maganar da sukace zasu qarasa ma bata samu ba bacci kawai suka shiga yi.

Washe gari lokacin suna parlor prince Hamid dake kula da Ahmed da yanayin sa ya d'an yi murmushi yana girgiza kai cikin tsokana yace.

"Ahmad please ara min wayar ka zanyi amfani da ita yanzu tawa banyi mata chaji ba tun jiya".

Da sauri Ahmed ya d'ago ya kalle shi dan yasan bom yake son had'a masa kafin ya kalli Abban su da shima ya d'ago yana kallon shi yace.

"Yayanka ba magana yake maka ba ka bashi waya kayi shiru kamar sabon kurma".

Rasa abin cewa Ahmed yai sai ido kadai daya zubawa prince Hamid wanda ya kauda kansa yana dariya kasa-kasa.

"Hummm bros Hamid is so funny.............

Jin Abba yace "Ahmed".

"Na'am Abba".

"Meke damun ka ne"?.

"Babu komai Abba".

"Babu komai kayi shiru ana maka magana"?
Hamid meke damun sa"?.

Gyara zama Hamid yai jin anzo daidai wajen da yake so azo yana kallon Ahmed dake masa magana da ido yai kamar bai ganshi ba.

Yace "Abba banace ba amma inaga shida Baby ne".

Zaro ido Ahmed yai yana kallon Hamid daya sakar masa hararar gargad'i sannan yaci gaba.

"Abba akwai abinda ke damun Ahmed saidai bansan maye ba amma shi Ahmad d'in ya sani ya'ki fad'a".

Wani kallo Abba yaiwa Ahmed yana cewa "AHMED what your problem"? Kasa cewa komai Ahmed yai sai bin kowa da kallo da yake har ya dawo kan Abban.

Mamaki ne ya kama Abba amma sai yace "shikenan ka samu nutsuwa daga baya zan tambaye ka saika tanadar min cikakkiyar amsa yanzu inada gurin da zanje ina Zuhra da Ummul-khairi suke ko a part Ashraf suka kwana naji banji motsinsu ba"?.

Kai prince Hamid ya d'aga "eh Abba suna can".

"Ok shikenan Ahmad kai kuma zan dawo gareka" yana fad'in haka ya mi'ke momy ta rufa masa baya zuwa rakiya ina motocin dukkan masarautar suke.

Ganin saura su biyu yasa Ahmad ya hade rai yana cewa.

"Meyasa zakai min haka gashi yanzu ka jefa ni cikin risky".

Ta'be masa baki prince Hamid yai yana cewa "Ba wani risky dana saka ka meyasa kaima ka kasa yiwa Abban bayani saboda ka daki 'yar lelen shi da ya sani da kaima ka samu rabon ka".

'kara hade rai Ahmed ya kuma yi "oh wanne irin rabo kenan zan samu"?..

"Kafi d'an dako sanin tasha saidai ya fika d'aukar kaya Allah yasa babyn su had'u da Abba koda a gurin Sultan Ameer ne aikaga asirin ka ya tonu abinda kake 6oyewa Abban zai gani ko bata fad'a Ahmad saina fad'a ko baka so kai mugu ne na ajin 'karshe".

Mi'kewa Ahmad yai zai fita yace "ai baka sani ba Abdul-hamid Aliyudeen Sharfaddeen isa nai muguntar ma iyawa ce idan wani ya isa shima yayi" yana fad'in haka ya fita a parlon d'aga murya prince Hamid yai yadda Ahmad d'in zai jiyoshi yana cewa.

"Zakaga mugunta iyawa ce wallhi so kake nasa a hanaka yarinyar nan in nuna maka qarshen mugu haba mutum sai zalunci da zafin rai kamar wani wuta kodan dama haka ka tashi tun kana yaro 'ya'yan bayi ma sunci duka hali ne a jikin rai tunda haka kake bazaka ta'ba canzuwa ba" shima prince Hamid d'in mi'kewa yai da lap Cort a hannunsa ya fita a parlon.

Mami tana zaune Sultan yana kusa da ita kuma dama shagwa'ba yake mata ganin Ahmad ya shigo yasa yai sauri shiga hankalin sa yana daidaita kansa yace.

"Good morning yaya"?.

Zama Ahmad yai yana kallon sa batare daya amsa ba yace "uban me kakewa shagwa'ba"?.

'Dan zaro ido Sultan yai yana soshe soshe yace "uhmm uhmm".

"Uhmmm me bana son shashanci so kake yanzun nan jikinka yai tsami Mami miyake nema bai tafi school ba sai lokaci ya fita".

Murmushi Mami tai tana cewa "waifa jiya ne ya tafi da tart makaranta yaji dad'in sa shine yace yauma saiya tafi dashi nace masa ba kamar indomie ne ko meat pie da za'ayi a rana daya baya amma ya d'age sai shagwa'ba yake zubawa harda shura qafa kodan yaga ya girma baida qani ne oho masa" Mami ta qarasa maganar tana shafa gashin kan Sultan wanda yai wuqi-wuqi yana d'an satar kallon Ahmad daya had'e rai yana cewa.

"Oh har yanzu bakai hankalin da za'a fad'a maka magana kaji ba tunda bazai yuwu a yau ba why not ka ha'kura zuwa gobe ko wani abu zai haifar ma idan baka ciba"?.

Shiru Sultan yai ya kasa cewa komai sai addu'a da yake Allah yasa kar hakan dayai ya zama laifi "get lost" yaji muryar Ahmad aiko da sauri ya mi'ke kamar zai kifa yai hanyar fita dakatar dashi Mami tai.

"Sultan dawo ka manta plantain mosa d'in naka ko ka fasa tafiya dashi"? Eh kawai Sultan yace sama sama bai tsaya ba hai yake ya fice saboda tsoron karma ya tsaya ya jawa kansa laifi tunda Ahmad yazo.

"Kaii dawo ka d'auka".

Cak ya tsaya waje daya cikin firgice ya juyo yana kallon Ahmad muryarsa ya kasa fita balle ya iya furta kalmar ya fasa tafiya dashi......................

"Me kake kallo ne dawo ka d'auka nace kada ka bari in tashi a kanka".

Jin abinda Ahmad yace yasa da sauri Sultan ya dawo yana ra'be ra'be ya matso a hankali yana kallon Ahmad dan abun na kusa dashi gani yake idan yazo d'auka zai rikeshi da 'yar sand'a ya yasa hannu ya d'auka da gudu kuwa ya juya faaaaaaaa🏃🤣 ya fice daga part d'in wanda yasa dole Mami tai dariya ai dama Ahmad d'in ne daidai dasu tunda prince Hamid bamai zafi bane Shadat ne d'an uwan Ahmad kuma baya nan sai ranar daya dawo shima haka yake da zafin rai..............................

Hankalin Ahmad ya mayar kan Mami yana cewa "barka da safiya Mami fatan kin tashi lafiya"?.

Har lokacin fuskar Mami da fara'a tace "lafiya qalau na tashi Ahmad ya kake ya gajiyar zama wuri daya dan nasan yanzu a takure kuke ku sojoji kun saba rai da rai kuna tsinka jinin jiki idan kunzo hutu kuma ba wani abu zakuyi ba duk sai kuji ku a takure".

Murmushi Ahmad yai yana kallon ta yace "ai Mami duk wanda ya saba da aikin ko zaman awa biyu yai batare da yayi wani abu dazai motsa jikinsa ba duk sai yaji babu dad'i shiyasa na dau qaramin hutu da wuri zan koma".

"To Allah ya taimaka Ahmad Allah ya fitar daku aikin nan lafiya".

"Amin Mami ina baby da khairat ko ba anan suka kwana ba"?.

"Kaita d'aga "eh anan suka kwana domin da asuba na buga musu qofa su tashi suyi sallah kuma ko sun tashin Allahu a'alam inaga barci suka koma".

"Ok"
Kawai yace yana mi'kewa yai hanyar bedroom d'in a qanqame yaji qofar sun saqace ta taciki bugawa yai da qarfi batare dayai magana ba jin shiru babu ko motsi yasa ya qara bugawa still baiyi magana ba juyi Khairat tai tana jan tsaki ta sake sabon kwanciya daidai an qara bugu mai qarfi fiya dana baya a hasale ta tashi zaune tana cewa.

"Sultan dallacan meye haka idan baka bar bakin kofar nan ba saina fasa maka baki idan ka bari na fito banza kawai".

Jin abinda tace yasa Ahmad ya jinjina kai yana cewa "Ok fito ki fasa min bakin, zaki bud'e ko saina 6alle murfin kofar na shigo naci ubanku ashe dama barci kuke baku tafi school ba yau sai jikinku ya fad'a muku".

Zaro ido waje khairat tai cike da tsoro domin yanzun kam ta fahimci waye d'ora hannu tayi aka tana cewa "nashiga uku dama ya Ahmad ne jin ya sake bugawa yana daka tsawa yasa a firgice tace "baby baby tashi yau za'ai farfesun mu yau mun kad'e har ganyen mu" ta qarasa maganar tana girgiza Baby wacce ke barcin ta hankali kwance batasan meyake faruwa ba jijjiga ta tayi da qarfi tana cewa.

"Baby ki tashi dan Allah masifa cefa ta tunkaro mu wacce bamu da maganinta sai Allah ba lallai muga gobe ba".

Bud'e ido Baby tai cikin muryar barci tace "Aunty Khairat lafiya kike tashi na"?.

"Inafa lafiya Baby ya Ahmad ne yake buga mana kofa yanzu na d'auka Sultan ne nace zan fasa masa baki yace na fito na fasa masa yana jirana".

Jin abinda Khairat tace yasa Baby tai cilli da bargon data lullu'ba gefe tana tashi zaune a rud'e zatai magana suka ji qarar 6alle kofa kafin su farga sai gani sukai murfin ya fad'o ciki, cikin 6acin rai Ahmad ya shigo zabura sukai a gigice musamman Baby da bata warke daga dukan dayai mata jiya ba tsayawa yai a bakin kofa yana kallonsu su gama iskancin rud'ewar yana daidai dasu ganin sun rikice sosai yasa ya buga musu tsawa.......

"Uban me ya hanaku zuwa school yau, raini ko"?.

Da sauri khairat ta girgiza kai tana cewa "wallahi ya Ahmad a'a ni bani da lecture da safe sai karfe uku zan tafi".

Maida da kallonsa kan baby yayi wacce ta gama haukacewa domin ita bata da hujjar kin zuwa yace "ke kuma fa uban me kika tsaya yi baki tafi ba".

Kuka kawai baby ta saki na tsantsan tsoro jikinta sai rawa yake ta kasa magana cikin tsawa yace "uban me ya hanaki zuwa school yau baby"?.

Yana rufe baki ta d'ora hannu aka a gigice tace "yaya wallahi bana jin dad'i ne da zazza'bi na kwana".

Wani kallo ya mata tare da jinjina kai yace "ku biyo ni" juyawa yai yana fita a rud'e suka mi'ke suna bin bayansa Mami dake zaune Ahmad yazo zai fita yana cewa "ki huta lafiya Mami".

"Ok Ahmad nagode sai anjima" ta karasa maganar tana binsu khairat da kallo Wanda babu me cikekken nutsuwa a cikinsu hum tasan za'ai haka dama tunda naji qarar 6alle kofa tasan basu suka tashi suka bud'e masa kofa ba karyawa yai ya shiga aiko yau sun shiga uku.

Yana tafe suna binsa a baya har part d'insa yana shiga ya wuce bedroom ya barsu a falo kowa hankalinta a tashe sun dad'e bai fito ba harsun d'auka ma koya manta dasu ne can suka sake jin qarar bud'e kofa ya fito yana gyara allura zaro ido baby tai a firgice tana fad'in innalillahi badai ita zaiwa allura ba.............

"Ke zomin nan" taji muryarsa a susuce ta fara zubar da hawaye kuma ta kasa d'aga qafarta balle taje.

"Baby kada ki bari na tashi a kanki"?.

Jiki na 6ari ta fara takows zuwa inda yake kafin ta sake ja ta tsaya tana kuka tace "dan girman Allah ya Ahmad kayi ha'kuri" tana rufe baki ya mi'ke yana tasowa inda take aguje ta juya zata fice ya dam'kota yana matseta a jikinsa da yadda ko motsi batai masa sannan ya juyata yayi mata allurar humm tsabar tsananin kuka daya ci qarfinta har shid'ewa take wulli yayi da sirinjin yana zama akan kujera ya d'ora kafa d'aya kan d'aya yana kallon ta yace.

"Can you be quiet or not"?.

"Idan baki rufa min baki ba na tashi sai jikinki ya fashe tsabar duka".

Jin abinda yace yasa dole da sauri ta had'iye kukanta tana na zuci kallon Kharat wacce ke qame guri d'aya yayi yana cewa "ba baki da lecture ba? Sai qarfe uku kince, saiki wuni zuwa Nan da qarfe ukun kina karbar hukunci kinga gaba ranar da baki da lecture bakiyi barci ba saiki dau littafi kiyi karatu fara frog jump" yana rufe baki da sauri khairat ta ri'ke kunne ta fara zaga falon wani kallo yaiwa baby yana cewa "ke me kike jira, ko allurar batai miki ba zazza'bin bai sauka ba" jin abinda yake fad'a yasa baby da sauri ta girgiza masa.

"Ok fara up and down".

Innalillahi up and down kuma nashiga uku yaya kashe ni yake son yi............

"Tunanin uban me kikeyi".

Baby batai aune ba taji saukar duka a bayanta a hargitse ta fara abinda yace mata yana zaune yana kallon su kowa kuka take tsabar wuya gashi babu damar d'an tsayawa su huta daga wannan su koma wannan iya gala'baita sunyi saida ya tabbatar yadda jikinsu zai fad'a musu sannan yace su tsaya haka tsayawa sukai da'kyar suke iya jawo numfashinsu kai ya jinjina yana cewa.

"Get to the point gobe ma ku kwanta kuyi barcin safen Ina daidai daku get of my sight" yana rufe baki har gware suke waje gudun fita kowa jan qafa take musamman baby da bata da lafiya har juwa ke dibanta suna shiga parlon Momy kuwa ta yanke jiki ta fad'i qasa bata ko motsi subahanallahi da sauri khairat ta dur'kusa tana jijjiga ta daidai Momy ta
End Ads