x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 10 - ROYALTY YAN SARAUTA

  • 27001 words
  • 30000 words
  • Out of 85109 words

Category: Love Stories

Views 1672

20 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
kashe wa'kar da yake jiba ya mi'ko mata yana cewa.

"Baza'a yi babu mu ba Aunty Baby ku tashi muje yau akwai buduri a gidan nan nima ina da chocolate gida guda bari in d'auko mu tafi da ita ku jirani" ya karasa maganar yana wucewa ya shiga bedroom d'insa kallonsu Mami tai tana cewa "yanzu ku da ace saikun fara ku ganshi ya dawo kamar a mafarki ya zakuyi"? Had'a ido sukai tare da jinjina kai a ransu suna hango irin hukuncin dazaiyi musu Baby tace "sai muce ba farin cikin tafiyarsa muke ba mu farin cikin yau wacce rana ma"? Ta tambaya tana kallon Khairat amsa ta bata "yau laraba".

"Yauwa Mami kinga yau laraba sai muce murna muke taya Sultan tunda kinga ranar labara da dare aka haifeshi".

"Ai kuma ba watan bane baku da yadda zaku kare kanku a gunsa" Mami ta fad'a daidai Sultan ya dawo yace "muje muyi partyn nan dan Allah ni harna fiku 'kaguwa" zasu fita Mami ta mi'ke tana cewa "bari nazo naga wanne irin shiri ku kaiwa tafiyar d'an nawa" ta fad'a ta biyo bayansu dariya sukai Khairat na cewa "gaskiya kam Mami ya kamata kizo ki gani kar ayi bake Momy kam dama tana gurin".

"Nima ina biye daku yau zanyi kallo".

Suna shiga suka ga prince Hamid a zaune ga Momy data kallesu taga harda Mami suka gayyato kawai tai dariya tana girgiza kai zama Mami tai tana kallon Momy tace "um muna can ashe suna nan suna shagali abinsu wai murnar tafiyar Ahmad suke"? Kai Momy ta d'aga tana cewa "eh haka suka ce gashi nan harda gayyatoku kuma mukam dama an dad'e da gayyarmu tun d'azu" murmushi Mami tai tana gyara zama tace "humn rabu dasu zanyi maganinsu" ta fad'a tana saita wayarta ta fara musu video duk abinda suke rufe baki Momy tai tana dariya Mami kam duk wani abu da suke tana d'auka Baby ce mai gabadatarwa kamar gaske Khairat ita da Sultan suna zaune kowa ya d'ora kafa d'aya kan d'aya idan tai magana sai su tafa mata harta gama Khairat ma ta kar'ba itama ta nuna murnarta da ranar 'yanci da suka samu sannan suka yanka cake duk abinda suke Mami tana tayi musu video Momy kuma datai sa'a Ahmad yana online tai kiransa video call duk abinda suke yana gani tsabar yadda suka bashi dariya har baisan lokacin daya saki murmushi ba gashi sun qure mp yaga harda prince Hamid dama yasan shine yake gayon bayansu kaiya jinjina yana katse kiran ya kira ta normal call yana cewa.

"Momy kice ina magana dasu" kallonsu tai da murmushi akan fuskarta tace "Khairat da Baby ku kashe mp nan Ahmad zaiyi magana daku" Momy na fad'a d'iff Sultan ya kashe mp yana zaro ido yace "wanne Yayan"?.

"Yayanku Ahmad gashi yana magana saiku karaso ku bashi amsa" ta fad'a tana mi'ka musu wayar rasa wanda zai kar'ba a cikin su akai domin sunji maganarsa da gudu sukai bedroom Sultan ma daya mi'ke da mpn sa a hannu ba arziki ya fece dariya sosai Mami tai tana cewa "ga tsoro ga rashin ji mukam munsha party sai ranar da Allah ya dawo dakai zasu sake yi mana irin wannan partyn na tayaka murnar dawowa gaskiya abun yayi dad'i sosai".

Kai Ahmad ya jinjina yana cewa "zasu ci ubansu ne idan na dawo zasu san sunyi murnar nabar gida dani suke" yana rufe baki prince Hamid yace "to sarkin mugunta ba wani ubansu da zakaci kaima kasan dole suyi farin cikin barinka gida dan haka babu abinda zakai musu garama ka sani tun wuri" jin abinda prince Hamid yace yasa Ahmad yace "ai dama nasan kaine kake goyon bayansu kuma zasu gane ruwa ba sa'an kwando bane dani suke zancen kai kuma babu ruwanka tsakani na dasu ne ka gane"?.

"Ban gane ba kasan Allah Ahmad baka isa ka yiwa yaran nan wani abu ba".

"Haka kace"?.

"Eh haka nace kuma babu yadda ka iya dani".

"Ok ni kuma zan nuna maka isar tawa a aikace Allah ya dawo dani lafiya wallahi sai naci ubansu" yana fad'in haka ya katse kiran kallon Momy prince Hamid yai yana cewa "kiji fa Momy kiji abinda yake cewa ina ruwansa dasu yaran nan dole suyi komai idan baya nan shima ya sani saidai ya'ki Allah kawai mutum ya zama barazana ko motsinsa sukaji sai kiga suna shiga taitayinsu suna nutsuwa suyi shiru ko su nemi tashi subar gurin saboda dashi koda ace suna son zaman gun humm Allah ya dawo dashi d'in lafiya zan had'ashi da Abba yayi masa magana karya ta'ba lafiyarsu dan tunda yace haka saiya yi musu wani abu da hankalinsa ya kwanta ni kuma bazan bari ba" yana fad'in haka ya fita murmushi Momy tai tana cewa.

"Zai huce kafin ya dawo yanxu ma ba fushi yayi ba kawai dai yace a basu wayar ne daga baya idan ya kira zanyi magana dashi" mi'kewa Mami tai itama tana cewa "bari na tafi Allah ya kyauta munzo munga party ai shi Sultan sarkin tsoro ya dad'e da guduwa".

"Dole ya gudu kin manta shine mai mp sarkin DJ ya zama" dariya Mami tai tana cewa "uhm sarkin DJ manya zaici ubansa ai nasan idan Ahmad ya dawo sai yayi seizing d'inta".

"Gaskiya kam tunda ya ganta kuma yaji kid'an shima Sultan d'in ba sha zaiyi ba ki huta lafiya".

"Ok sai anjima" Momy ta fad'a daidai Mami ta fita itama Momyn ta mi'ke tana kallon kayayyakin da suka gudu suka bari kamar zatai dariya sai kuma ta girgiza kai tana wucewa.

🌆Russia🌆
Ahmad yana zaune bayan sun gama waya prince Hamid ya kirashi yayi masa tas akan su Baby dama ransa a 6ace yake baya so nan da gobe a samu wanda zaiyi masa magana cike yake dam da fushi ji yake kamar yayi fuffuka ya tashi ya koma gida yaci uban yaran nan ko zai sauka daga fushin da yake dasu yana cikin wannan yanayin Samir yazo ya sameshi baisan me yake faruwa ko meke damun Ahmad d'in ba kawai yana zama ya kalleshi yana cewa.

"Yauwa Ahmad dama inata so na tambaye ka tun kwanan baya da dad'ewa lokacin danai kiranka wata budurwa ta d'aga baka nan tace min baka nan amma ita 'kanwarka ce dan Allah wacece ita ya sunanta"? Ahmad baiyi niyyar d'agowa ba saida yaji abinda yace ji yayi ransa ya sake 6aci fiye da d'azu da prince Hamid ya masa magana akansu Babyn tunda yaji yace 'kanwarsa yasan baby ce lokacin data d'aga harya fito ya sameta ya daketa da belt yanzu kuma shi Samir tambayar da yake a kanta me zaiyi mata...............

"Ahmad baka fad'a min ba 'kanwarka ce"? A takaice yace masa "eh" cigaba Samir yai da cewa "wow masha Allah fad'uwa tazo daidai da zama mene sunanta sannan zan iya ganin photonta"? Wani kallon 'kasan ido Ahmad yayi masa ji yake kamar ya rufeshi da duka akan tambayar da yake masa amma saboda baya so ya fahimci wani abu sai kawai ya danne yace.

"Sunanta Zuhra".

"Wai Zuhra nice name daga ji kyakkyawa ce sosai zan iya ganin photonta"? Kai Ahmad ya girgiza da sauri ma kuwa yana cewa "a'a" da mamaki Samir yace "meyasa bakaza nuna min ba"?.

"Saboda wani dalili".

"Kai dan Allah Ahmad ka nuna min wallahi ina jin muryarta naji na kamu da sonta dama a 'kagare nake ka dawo na tambaye ka idan har zan samu ka shige min gaba na aureta wallahi da gaske nake maka Ahmad ina son 'kanwar nan taka fatan zaka bani ita................

Kusan numfashin Ahmad ne yaso ficewa yabar jikinsa tsabar yadda kalmar ina sonta da Samir ya fad'a ta daki zuciyarsa har saida ya runtse ido saboda jin wani abu kamar mashi ya soki zuciyarsa da sauri ya dafe 'kirji bai iya d'agowa ba duk da kiran sunansa da Samir yake saida aka dad'e kafin da'kyar cikin son danne 6acin ransa ya d'ago idonsa daya sauya kala muryarsa ma a sauye ba kamar yadda Samir ya sanshi ba yace.

"Tana da miji".

Zaro ido Samir yai yana cewa "dan Allah tana da miji Ahmad is this some kind of joke dan kaga yadda zanyi ne ka zolaye ni right"? Kai Ahmad ya girgiza yana cewa "Samir idan da zanyi maka wasa tun farko dana ja maka rai daka tambaye ni sunanta ina fad'a maka gaskiyar abinda baka sani bane a kanta domin anyi mata miji tana da wanda zata aura tunda dad'ewa lokaci ne bai karaso ba" Ahmad yai maganar da serious face musamman da yaga Samir d'in yana kokarin mayar da abinda ya fad'a masa wasa zazzafan huci Samir ya fitar yana kad'a kai yace.

"Ok shikenan na fahimta amma banso wani yai min shigar sauri ba to amma Ahmad bayan ita baka da wata sister dan Allah nidai ina son nai aure a cikin 'kannanka muryar wannan ladyn taja hankalina sosai na shiga halin kamuwa da 'kaunarta please idan kana da wata 'kanwar bayan ita ina so dan Allah" a takaice Ahmad yace "Ina da ita amma itama tana da wanda zata aura".

"Haba Ahmad bama haka dakai duk ta inda na 6allo saika zille ka sanni kasan halina sannan idan yaudara ce kasan bazan yaudari 'kanwarka ba dan Allah Ahmad ka taimaka idan kana da 'kanwa ka wacce take free ko Kuma wasa kake min please na had'aka da girman Allah ka fad'a min"? Ya fad'a harda had'e hannu ran Ahmad a dagule yace.

"Bayan ita ba wata".

Kai Samir ya girgiza yana shirin sake magana ganin bazai ha'kura ba yasa Ahmad yace "Samir kai aboki nane na ha'ki'ka kasan bana 6oye maka wani abu daya danganci sirri na amma nayi mamaki dana fad'a maka gaskiya ta yau ka kasa fahimta ta why"? Ganin da Samir yayi ran Ahmad ya 6aci sosai sannan yasan abinda ya fad'a masa gaskiya ne da ace 'kanwar tasa bata da miji bazai 6oye masa ba saboda akwai sha'kuwa da yarda mai 'karfi a tsakanin su tuna hakan yasa Samir yayi murmushi yana kallon Ahmad wanda ya gama cika yace.

"Ok Ahmad kayi ha'kuri na 6ata maka rai ba a son raina bane nayi hakan ne saboda na nemawa kaina mafita".

Kai Ahmad ya girgiza yana cewa "karka damu Samir baka 6ata min rai ba kafin 'karfin komai a guri na da ace ina da 'kanwa zan baka ita kaika san da haka".

"Haka ne Ahmad ka fad'i gaskiya nagane ba damuwa Allah yasa gidajen zamansu ne".

"Amin kawai shine abinda Ahmad yace daidai an kira wayar Samir ya mi'ke yana cewa "ok bari nazo Mum tana kirana".

"Ok".

Samir na barin gurin Ahmad ya d'aga waya ransa a 6ace ya kira numbern Khairat dan yasan idan ya kira Momy maybe basa kusa da ita Khairat suna zaune a bedroom jin wayarta na ringtone yasa da sauri ta d'aukota ganin wanda yake kira yasa ta tsaya cak tare da kallon Baby tana cewa "na shiga uku Baby shikenan na kad'e yau" da alamar tambaya Baby tace "meya faru waye ya kiraki" daidai kiran ya katse wani ya shigo a susuce Khairat tace.

"Wallahi ya Ahmad ne yake kiran na" zaro ido Baby tai har ruwan data d'auka tasha ya 'kwareta ta kama tari da'kyar tace "ya Ahmad dai"? Kai Khairat ta d'aga tana cewa "ni yanzu bansan yadda zanyi ba kuma kar na'ki d'agawa na sake jawa kaina wani sabon laifin akan na d'azu".

"To ki d'aga man tunda ba'a gida yake ba da sau'ki kome zaice tsakanin mu dashi da nisa bazai dake muba saidai fad'a da baki kawai" jin abinda Baby tace yasa Khairat ta jinjina kai a karo na uku da kiran ya shigo cikin azama ta d'aga tun kafin tai magana muryar Ahmad cikin tsawa yace.

"Ummul-khairi uban me kikeyi baki daga min kira ba bayan kina gun raini ko"? Kamar yana ganinta da sauri ta girgiza kai tana cewa "dan Allah yaya kayi hakuri wayar tana bedroom tana caji ne mu kuma muna parlor saida muka shigo naga kana kirana kayi hakuri dan Allah" ta fad'a cikin son kare laifinta jin abinda da Khairat d'in tace yasa Ahmad sassauta murya yana cewa.

"Okay ina Babyn take"?.

Zaro ido baby tai tana rufe baki tare da yarfa hannu tana gwadawa Khairat tace bata gurin ita kuma bata fahimta ba saboda tsoron kar ta sake 'kular dashi tace "gata nan a kusa dani".

"Bata wayar".

Mi'ka mata Khairat tai da'kyar Baby ta kar'ba tsabar rawa da hannunta ya d'auka tana karawa a kunne tsawar da Ahmad ya daka yasa tai wulli ta wayar tana 'kan'kame jikinta kamar shine a gurin ganin da Khairat tai kiran bai katse ba yasa taje ta dau'ki wayar tana sake mi'ko mata a hankali saboda kar yaji cikin rad'a Khairat tace.

"Baby kiyi magana kema kisan 'karyar da zaki masa ki fita kamar yadda nima nayi" Kai Baby ta girgiza zatai magana Ahmad yace "Khairat kina jina"? Da sauri Khairat tace "eh Yaya ina jinka".

"Oh kina jina kuma dan ubanki nace ki baiwa Baby wayar kikai banza saboda kinsan bana ne ko"?.

"Kayi hakuri Yaya gata nan kar'bi baby" ta fad'a tana mi'ka mata kar'ba Baby tai da yake hand free ne tana jinsa sosai yace.

"Baby"

Muryarta na rawa tace "na'am" jin ta amsa a fusace Ahmad yace "Baby! Baby!! Babby!!! na rantse da Allah duk ranar dana sake aje phone d'ina kika d'auka har kika sake yin magana da wani ban saka kiba saina 6allaki yau kin 6ata min rai sau biyu kenan ke kad'ai ki jira dawowa ta saikin shiga uku a hannuna had'uwar mu bazai miki kyau ba" yana fad'in haka yaja dogon tsuka yana kashe wayar d'ora hannu Baby tai akai tana kallon Khairat tace "na shiga uku Aunty Khairat me nayiwa ya Ahmad kuma ya taso da zancen tun d'aukar wayarsa da nai lokacin da abokinsa ya kira".

Zama Khairat tai a bakin gado tana girgiza kai tace "to banace ba tunda kinga ya koma maybe abokin nasa ne daya kira kika d'aga yayi masa maganar ki kinsan dole ne zai tambayeshi wacece ta d'auka masa waya ko 'kanwarsa ce tunda yasan baida mata" jin abinda Khairat ta fad'a yasa Baby dafe kai tana cewa "innalillahi wa inna ilaihi raji'un Allah gani gareka kaine gatana ka fidda ni daga wannan damuwa data tunkaro ni".

"Insha Allahu zai manta kafin ya dawo kar kisa abun a ranki harya dameki nasan yanzu ransa a mugun 'bace yake dan haka zuwa nan da kwana biyu zan kira miki shi ki bashi ha'kuri sannan ya huce" numfashi Baby ta sauke jiki a sanyaye tace "shikenan zan gwada Allah yasa ya kar'bi ban ha'kurin nawa".

"Zai kar'ba kawai yanzu abinda zaki ki dage da addu'a kafin nan da kwana biyun wannan shine mafita" kai Baby ta d'aga tana cewa "bari na fara tun daga yanzu duk da ba'a makara wajen yin abinda ya dace bari nayo alwala" ta fad'a tana wucewa bathroom yayin da tabar Khairat itama tayi shiru ta shiga duniyar tunani............
✍️MRS ÄL'ÄMËËÑ ÄHMÄD ÇË🌹.


TYPING 📲Mon mar17/25 09:45PM
YUSRAH 🤞 MUSA 🤞 ABUBAKAR

👑 ROYALTY 👑

💫A*W*A💫
Home of hospitality and harmony gidan kar'bar mutane hannu biyu da zaman lafiya ÀÑÑÙRÌ haske le'ka gidan kowa koda ma'kiya na kallon ka ramin kura sai'ya'yan ta haka taken mu yake tafiyar mu babu rago babu maci amana tsantsan gaskiya muke nunawa.

_________________
__________________________
___________________________________
ALLAH THE MOST HIGH DOESN'T SLEEP ALLAH THE MOST HIGH IS PURE HE ACCEPT ONLY WHAT IS PURE.
Ubangiji ka sanya mana tsarkakar zuciya ya Allah kaine mai badawa ubangiji muna ro'konka lafiya a jinmu da ganinmu Allah ka bamu lafiya a duniyar mu da lahirar mu ubangiji ka kyautata makwancin mahaifan mu Amin.

YÜSRÄH MÜSÄ ÄBÜBÄKÄR
Wrïtër
1~ yarima Abdul-maleek
2~ Rayuwa biyu
3~ Safreeyyah
4~ D'an millionaire
5~ Dama kece
6~ Husnah ko Badiyat
7~ Minah-Umer
8~ Tajuddeen Aryam
9~ Me kamar sarki
10~ Minister Ashraf
11~ Yarima Aryan
And now 12~ 👑Royalty👑

Later insha Allah👇
13~ 💘Zuciyar Aliyu ce💘
Yana nan tafe insha Allahu dana gama royalty zan fara shi akan #300 shima babu tsada sai dad'i.

Littafai na basu da tsada sai dad'i da ilmantarwa da tunatarwa da kuma koyon darasi da hali masu kyau da d'abi'u na gari sannan ina saida su akan qaramin fara shi saboda masoya na duk mai bu'kata should DM me kayi min magana ta WhatsApp number na.

+234 816 098 3083
Chat with me.
Farashin book d'ina
01_Me kamar sarki #300
02_Safreeyyah #400
03~Minister Ashraf #300

Free kuma kyauta ne ga mai bu'kata shima should DM me.

01-Yarima abdul-maleek free book
02- D'an millionaire free book
03- Husnah ko Badiyat free book
04- Rayuwa biyu free book.

7~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Abidinah.

@YUSRAHMS CE
Page 13 & 14
Tunda Aiman ya tafi da Ayrah gidansu koda wasa bata sake le'ka su Hajiya Khubura ba tana gurin mahaifiyar Aiman tare da 'kannan sa har tayi 'kiba sakamakon d'an hutun data samu dama rashin kwanciyar hankali ne ya hanata sakuni duk kwanakin datai bata gidan Daddy bai ta'ba sani ba tsabar bata gabansa bai damu da ita ba har saida Hajiya Khubura ta gaji da aikin dasu Abidah suke yi saboda rashin Ayran ta samu Daddy ta fad'a masa 'karya da gaskiya sannan tace Aiman ya mayar da ita gidansu yace anan Daddyn bazai iya ri'keta ba bai damu da damuwarta ba kamar ba shine ya haifeta ba jin wannan maganar tai bala'in 6ata ran Daddy a take ya d'aga waya ya kira Aiman cewa yazo yana nemansa humm Hajiya Khubura abinda take so kenan dama ta samu Daddy ya kirashi tayi amfani da wannan damar tasa Daddy yasa Aiman ya dawo da Ayrah gidan ko yana so ko baya so, suna zaune a parlon Daddy ya shigo da sallama yana samun guri ya zauna cikin ladabi ya gaisa Daddy amsa masa yai yana kallonsa murya a nutse yace.

"Aiman meyasa ka d'auke Ayrah daga gidan nan ka mayar da ita gidanku batare daka fad'a min ba"? Jin tambayar dayai masa yasa Aiman d'agowa ya kalli Hajiya Khubura wacce ta sakar masa murmushin mugunta tana jinjina kai alamar yasan aikinta ne kafin tai masa magana da ido tana kallon Daddy wanda shi kuma Aiman d'in yake kallo tace.

"Ai dama na fad'a maka Alhaji bazai iya baka amsa ba saboda bashi da wata hujja haka kawai ya d'auke yarinyar yabar gidan da ita bayan baka gagara ri'ke iyalinka
End Ads