mutuwa ne kawai bazatai ba tsabar farin cikin da zata tsinci kanta a ciki......
"Maryam baki ce komai ba sai iya murmushi naga kinyi"? Kallon Mama Maryam tai tana jinjina kai tace "karki damu Mama ni nayi miki alkawarin shawo kan Ahmad cikin sassau'kan hanya a d'an karami lokacin da zanyi ina tabbatar miki bazan dawo gidan nan ba saida amincewar yana sona zai aureni na tafi Mama ki taya ni da addu'a" ta fad'a tana juyawa zata fita a parlon jawota baya Mama tai tana cewa.
"Please Maryam ki tsaya ki nutsu kiyi amfani da kyawawan kalamai ke mace ce kinsan abubuwan da zaki ri'ka yi wanda zai burgeshi ki jawo hankalin sa kanki da wuri dan Allah ba shashanci nace kije kiyi ba ki kokari kiyi abinda ya kaiki gidan kawai shine abinda ya kamata kiyi ba shirme ba''.
"Insha Allahu Mama karki damu nimafa ina zumud'in wannan al'amarin taya zanyi sake na bari har na samu damar zama dashi na kasa jan hankalinsa gareni kamar ba mace ba indai dan soyayyar Ahmad ne karki damu ki ri'ka sakawa a ranki kamar na aureshi ne anyi komai an gama jira dai ba yanzu zanje gidan ba? Humm muje zuwa shiri nagaba saina jiki a waya" murmushi Mama ta saki tana cewa "yauwa Maryam insha Allahu zaki nasara sai kin auri Ahmad domin kullum bana barcin kirki ina tsayuwa sallar dare saboda kicika burinki nima nawa ya cikana ganin na had'a jini da sarakai wata rana na bud'e ido naga jikanu na sune a fada hummm abun zaiyi matukar kyau koba fad'a ba".
"Tabbas zaiyi kyau Mama nasan addu'ar ki zatai min amfani sosai dan Allah karki daina kici gaba da yimin nasan zan samu kan Ahmad ya aure ni da sauri saboda addu'ar iyaye ga 'ya'yansu kar6a66iya ce".
"Ai kullum ba ranar banza Inayi miki fa Maryam kedai kawai idan kinje kiyi abinda ya kaiki karki tsaya wasa shine kawai abinda nake so".
"Ok shikenan Mama zanyi iya bakin kokarina naga nayi yadda kikace amma please Mama zan roke ki mezai hana ki bari zuwa gobe naje domin kinsan indai abbanmu ya dawo bai sameni ba akwai matsala baya so kayi tafiya baka fad'a masa ba na tabbata indai na tafi bai sani ba zan jawa kaina gaba bazai ta'ba barina na sake zuwa wani gurin ba sai an dau'ki lokaci ne tsawo" jin abinda Maryam tace yasa Mama tai shiru tasan hakan ne gaskiya ta fad'a abbansu mutum ne wanda baison yaronsa ya tafi guri kai tsaye batare daya fad'a masa ba hakan yana matukar jawo fushinsa shiyasa da taji Maryam d'in tace haka itama ta tuna domin zumud'i da saurin da take taga Maryam taje masarautar yasa ta manta da dokar Abban su Maryam d'in...................
"Mama bakice komai ba ko kina ganin na tafi ba matsala"? Kai Mama ta girgiza tana cewa "a'a karki tafi kawai ki bari ya dawo ki fad'a masa idan naji ya hanaki nasan abinda zan fad'a masa ya 'kyale kije kawai zance Aunty ce tace kije mata kiyi d'an kwana biyu saboda kin dad'e bakije inda take ba ko ina ganin zaifi yarda akan ki tafi batare daya sani d'in ba maybe a yau idan ya dawo nace kin tafi saiyasa kin dawo kawai mayar da kayanki Allah ya kaimu goben da sauri ba gurin zuwa gara tafiya a hankali maida mu bari ya dawo" to Maryam tace tana juyawa zata mayar da kayan Mama ta bita da kallo a ranta tana sake cewa "insha Allahu Maryam in Allah ya yarda sai kin zama matar Ahmad kwanan nan domin daya amince zai aureki abun bazai dau'ki lokaci ba dan kar wani abuma ya shigo ciki ko akasin da zaisa a fasa" sauke numfashi tai tana samun waje ta zauna tai tsamm tana tunane tunane iri-iri akan yadda zata tafiyar da komai................
HUMM MUJE ZUWA YANZU AKA FARA😁.
Washe gari tun safe bayan breakfast zuwa sha biyu Maryam ta had'a kaya bayan Mama ta sake fad'a mata kissa da kisisinar da zata ri'ka yi idan taga Ahmad yana gu da yadda zata ri'ka shishshige masa tana yimasa abubuwan jan hankalin da burga harta samu masauki a zuciyarsa kar tayi sake karta tsaya kallon shashanci tai abinda ya kaita.
*** ****
Lokaci indai an saka shi me zuwa ya wuce ne su Nadiya an zama amarya a gidan Sabit kamar yadda ake so buri ya cika biki kam anyisa kamar baza'a daina ba an kashe kud'i anyi abubuwan 'karya da son a fad'a a nuna a ranar da za'ai mata rakiya tana zaune a parlon part d'insu tare da 'kawayenta Ayrah ta shigo da sallama d'auke da babban tray a hannunta da kawo musu abinci da abun sha kamar yadda Nadiya ta umarceta tana ajewa kafin ta juya d'ebo sauran wata 'kawar Nadiya ta kalleta tana cewa.
"Tofa Nadiya wannan Kuma fa daga ina haka naga ta kawo abinci ba 'yan uwanku bane"? Yatsina fuska Nadiya tai tana had'e rai ta sakarwa Ayrah harara tana cewa "zaki bar nan ko saina tashi na fasa miki idon munafircin ubanki kika tsaya sauraro"? Da sauri Ayrah tabar gurin cikin takaici ta fice da mamaki duk 'kawayen Nadiya suka bita da kallo kafin d'aya tace.
"A'a Nadiya ya hakan meyasa kike Mata tsawa kuma"? Tun kafin Nadiya tai magana wataa ta sako baki "nidai banga abinda tai miki ba daga ta kawo abinci sai zagi ita kuma batai kala da 'yar aiki ba balle ace aiki take muku saidai idan bikinki tazo ko"? Kai Nadiya ta girgiza daidai Ayrah ta dawo ta aje musu plate da cokula wani wula'kantaccen kallo Nadiya taiwa mata tana jan tsaki tare da kau dakai kamar irin taga abun 'kyamar nan tace "na tsani wannan yarinyar na tsaneta bana son ko kad'an a dole dama nake zaune tare da ita a gidan nan yau kuma zan bar mata taje ta cinye gidan dama mayya ce taci mutum d'ari da ashirin nidai daga yau na huta da ganin mummunar fuskarta na barwa su Abidah jaraba" dariya Amrah tai tana cewa.
'House girl d'in muce man wace bayan meyi mana wanki girki wanke-wanke da share share shine matsayin ta" jin abinda Nadiya ta fad'a yasa cikin takaici Ayrah dake serving d'insu ta d'ago ta kalli Nadiya ba'kin ciki zai kasheta wato itace house girl d'in su lallai d'an adam butulu me manta kyautar jiya...............
Har had'a baki sukai suna zaro ido wajen cewa "wannan ce house girl d'in taku kai haba Nadiya fad'i gaskiya dai"?.
"Wallahi da gaske nake muku me aikin gidan nan ce komai itace keyi mana muna zaune domin aikin neya dace da ita ba komai ba'' ta karasa maganar tana mayar da kallonta kan Ayrah cikin tsawa tace "ke jaka 6ace min da gani" mi'kewa Ayrah tai kamar zata tanka mata sai kuma ta fasa tana ficewa Amrah da tafi kowa son sanin gaskiya 'kara matsowa kusa tai tana cewa "Nadiya anya abinda kika fad'a haka yake kin fad'a nedai saboda kiji dad'in bakinki"? Murmushi Nadiya tai tana jinjina kai tace "eh a barshi a dad'in bakin ne amma idan Abidah ta shigo ku tambayeta ko bana gurin zata fad'a muku komai zakusan gaskiya nima na fad'a muku yanzun dai kuci abincin nan karya huce dan bata wani iya girki jagwalgwalo take nikam sai ina jin yunwa kamar zan mutu nake cin abinda ta dafa'' ta fad'a tana d'aukar spoon Amrah data riga ta fara ci dariya tai tana cewa "gaskiya Nadiya kiji tsoron Allah ba'a haifi abokin 'karyarki ba ga girki yana tashin kamshi a baki da dad'i amma kici wani idan ba ji kikai yunwa zata kasheki ba baza kici ba"? Tsuka Nadiya tai tana mi'kewa tace "ke kika sani nabar miki aikin nayi gaba" ta fad'a tana fita ta barsu part d'in Hajiya Khubura ta tafi domin ta fad'a tana mata sunyi waya Sabit yace a bata wayar suyi magana bata samu ta kawo mata ba sai yanzu ma ta tuna.
Samhat ce zaune tana sauraron wacce ke kusa da ita tana fad'a mata abinda ya faru cewa da gaske ne Sabit yayi aure domin ita Samhat ta 'karyata cewa ba aure zaiyi ba sai yau da labari yazo mata ba iya mutum d'aya ce ta fad'a mata ba mutane da yawa sun kirata a waya sun gulmata mata saboda kowa yasan irin tsananin son da takewa Sabit humm tsabar d'imuwa damuwa tashin hankali da ba'kin ciki da Samhat ta shiga ko gane a inda take bata yi sai duhu da ta fara gani kanta yana sarawa da 'karfi ta mi'ke tana tangad'i da layi tai hanyar fita da sauri Laylah ta tareta tana ri'ko hannunta ta dawo da ita baya a hankali ta zaunar da ita tana cewa.
"Samhat kiyi hakuri dan Allah karki fita kina wannan halin ina yanxu kike tunanin zaki tafi" tun Layla bata karasa maganar da take ba Samhat ta sake mi'kewa tana cewa "wallahi bazan yarda ba saina rama saina ba'kanta masa kamar yadda ya ba'kanta min wannan ai tozarci ne tashi ki rakani gurinsa saina 'kaddamar masa da fushina" jin abinda tace yasa Laylah itama ta mi'ke tana cewa "haba Samhat kinsan me kike cewa kuwa me zakiyo a gurin sa inace yasan dake ya barki ya auri wata"?.
"Da yasan dani ma sanin ai baiyi min amfani ba nizai yaudara bayan ba fad'a mukai ba sannan tsabar cin mutumci da rainin hankali idan na tambaye shi ance an ganshi da wata budurwar sai yace a'a shi 'karya ake masa babu wacce yake so bayan ni ashe munafirta ta yake yasa duk na rabu da samarin da suke sona da gaskiya sannan zai rabu dani humm yayi da 'yar halak wallahi tallahi tunda yai min haka bazan bari yaji dad'in auren saba saina rabasu saina sanya musu fitina da ba'kin ciki" sosai Laylah ke kallonta jin abinda take cewa tace.
"Taya zakiyi hakan bayan aikin gama ya gamu kuma shiba d'an nan bane balle kice iyayensa zaki fad'awa taya zaki rama to"?.
"Ta yadda ake ramawar man zan zubar da hawaye na a banza ne wallahi tunda yasa nayi kuka shima sai yayi ai inada numbar wayar mamarsa na ta'ba amsar wayarsa batare daya sani ba nad'au numbar nata da naga yayi Saving da Mah kinsan dana kirata ta tambaye ni wace ni na fad'a mata humn ta ri'ka danna min zagi tana cewa karna kara kula d'anta ita bazata had'a jini da hausawa ba idan na sake kulashi saita hallaka ni to yanxu me kike tunani dayai min wannan butulcin kuma ya auri wata wallahi Laylah saina had'ashi da mahaifiyar shi saina fad'a mata cewa d'anta Sabit yayi aure ya auri bahaushiya ke karshen magana har address d'in inda yake saina fad'a mata tazo taci uwar duk tsinanniyar daya aura".
"Yauwa yanzu naji magana kinga ma zaki rama fansar abinda yai miki ta hanya mafi sau'ki kawai hakan zakiyi shine daidai tunda har mahaifiyarsa tace bazata had'a jini da hausawa ba kiyi amfani da wannan damar ki kirata a waya ki fad'a mata harda 'karya ki 'ka'kalo ki fad'a yadda zaki fusata ta sosai ko jirgi ne ta hawo tazo taci ubanta mune 'yan tayayyar duka muyi mata jina-jina domin da biyu xamuyi haka kawai kirata Samhat ki fad'a mata muji me zatace" Laylah na rufe baki Samhat data yarda da duk abinda Laylan ta fad'a waya ta d'auko tana danna kiran numbern mahaifiyar Sabit d'in kiran farko ba'a d'aga ba saida ta sake kira taji an d'auka ana cewa.
"Hello".
D'auke wayar daga kunnenta tai tana kallon Laylah wacce ta matso tace "ta d'aga fa me zance"? 'kasa da murya Laylah tai tana cewa "ki fad'a mata abinda yake ranki kawai wannan shine ni bansan abinda zakice mata ba ki fad'a mata duk abinda kike so" "ok shikenan bari muga" Samhat ta fad'a tana mayar da wayar kunnenta tai magana jin shiru yasa ta ciro wayar tana kalla ashe an katse kiran kaita jinjina tana sake saka kiran tare da fatan Allah yasa a d'auka tana shiga kuwa aka d'aga ana cewa.
"Hello waye ne ya dame ni da kira kuma baiyi magana ba idan baka da abin fad'a ka kashe wayarka"? Kallon juna sukai suna ta'be baki Laylah tace "hum'um wannan matar akwai bala'i keko da wanne tsautsayin ne yaja ki zaki auri d'anta"? Samhat bata saurari abinda Laylah d'in tace ba sai hankalinta data mayar kan maganar da matar take tana cewa.
"Ina yini ya gida"?.
"Lafiya lou waye yake min magana naga bakuwan number ban santa ba" ta fad'a da muryarta wacce hausa bata wadace taba da yake bayerabiya ce shiru Samhat tai har saida ta sake cewa "nace waye yake magana ko costumer ne me kake son saya"? Kai Samhat ta girgiza tana cewa "a'a ba wani abu zan saya ba nasan baki sanni ba dama na kiraki ne muyi magana akan d'anki Sabit".
"Eyy d'ana Sabit kuma meye faru ne wanene ke kike min magana wai d'ana Sabit"? Cije lips Samhat tai tana cewa "dama fad'a miki zanyi Sabit ba karatu yake ba anan da yazo ya gama school da yace zai maimata sheka guda ba gaskiya bane aure yayi" Samhat na rufe baki ta cire wayar da sauri saboda ihun da matar ta saki tana cewa.
"Aure kuma Sabit d'in ne ya aure bahausiya ya aura ko kuma waye ya aura fada min gaskiya"? Murmushi Samhat tai jin anzo daidai wajen inda take so matar ta furta wannan maganar tace "kwarai bahaushiya ya aura yau d'in nan aka d'aura auren ko tarewa batai ba shiyasa nace bari na kiraki na fad'a miki dalilin kiran kenan saboda yace bazai dawo Lagos ba sai matarsa ta haihu wai idan kikaga yazo miki da d'a bazaki hanashi zama da bahaushiya ba".
"Heyy haka Sabit yace inji ubanwa wallahi ba d'a d'aya ba ko duniya suka haifa saina raba aurensu balle kuma yau aka d'aura auren to bazan bari hakan yaja lokaci ba nagode sose da kika fada min wannan maganar yaron kirki ina godiya zanyi maganin Sabit tunda ya auri bahausen mutum hummm" tana fad'in haka Samhat taji wayarta tace d'it d'it iska Samhat ta furzar tana sau'ke wayar ta kalli Laylah tana cewa.
"Yauwa alhamdulillahi sai yanzu naji dad'i dana rama gaskiya Laylah kin iya kawo kyakkyawar shawara na tabbata tunda har mahaifiyarsa taji wannan labarin tofa 'karyar duk shegiyar daya aura ya 'kare ko tana so ko bata so zata zama bazawarar dole shi kuma taci 'kaniyarsa humm Allah yasa kafin ta rabasu saita nunawa tsinanniyar daya aura jikinta da duka" dariya Laylah tai tana kallon Samhat wacce ta karasa maganar harda d'aga hannu sama alamar Allah ya amsa mata tace "kina burge ni 'kawar shiyasa nake yinki to yanxu dai kin rama dan haka saiki saki jikinki mu sha'kata tunda kema yanzu kina da wanda yake sonki dan kin 'ki amince masa ne amma nasan zaki kar'bi gayyatarsa bayan da wannan al'amarin ya faru ko"? Shiru Samhat tai kamar me tunani tai tsam sai can ta d'aga kai tana cewa "eh yanzu kam na amince zan iya soyayya dashi idan ta kama har aurensa nayi nifa dama tunda na kira wannan mahaifiyar Sabit d'in a wancan lokacin ta zageni tas ta ri'ka aiko min da ashar tai min barazar zata kasheni idan ban rabu dashi ba tun sannan nayi tunanin rabuwa dashi sai kuma naji bazan iya ba sai gashi ya raba ala'kar mu da kansa hakan yayi min dad'i sosai ya bani citta" dariya Laylah tai tana cewa "indai ya baki citta har haka to tashi mu tafi mu d'ebi nishad'i ki manta da wannan gayen kisa a ranki kamar baki ta'ba saninsa ba" mi'kewa Samhat tai tana cewa "a shirye nake muje kawai" handbag da key Laylah ta d'auka suna fita daga bedroom d'in da suke suna tafe tana sake bata shawarwari akan yadda zata fara soyayya da wannan sabon saurayin nata.
Tunda Mah suka gama waya da Samhat ta mi'ke tana zaga parlonta ranta a 'bace ta kira numbern Sabit bai d'aga ba qara kiransa tai nan ma no answer kaita jinjina tana zama ta zubawa secreen d'in wayar nata ido iya kallon numbern Sabit da take ranta qara 'kuna yake zuciyarta tana tafasa wuce numbar tai ta kira wata dabam wacce bugu d'aya aka d'aga ana cirawa tace "hello Boukar kazo yanxu ina son ganinka" ta fad'a tana aje wayar da kamar minti sha biyar wani saurayi ya shigo yana zama yace.
"Barka da gida Mah meya faru naga kamar ranki a 6ace yake"?.
"Eh raina a 6ace yake man Boukar ni Sabit zai mayar mahaukaciya na fada masa bana so ya auri hausa women amma tsabar na zama uwar banza ashe yace min ya koma karatun shekara guda zai maimata yaje yayi aure yau d'in nan ya auri bahausiya humn kasan me nake bu'kata so nake ka shirya ka tafi can ka gane min da gaske Sabit aure yayi ko 'karya ne domin wacce ta kirani ta fada min bansanta ba kawai naga ta kirani ne".
Kaiya d'aga yana cewa "ok Mah ba matsala zanje zan gano miki komai kuma zanyi kokari naga na 6oye masa yadda bazai san ina garin ba harsai na gano miki komai saina kiraki na fad'a miki".
"Ok Boukar nagode idan ka shirya kayi min magana na baka kud'in mota kaje duk ma inda yake ka gano min walay sai naci uban Sabit zaisan yaje yayi aure batare da neman izini naba" mi'kewa Boukar yayi yana mata salama ya fita da shirin gobe da safe zaizo su karasa magana ya kar'bi kud'in mota ya taho neman Sabit d'in yabar Mah ranta a 'bace jiran dawowar su Niseh take daga school ta fad'a musu..............✍️Mrs Äl'ämëëñ Ähmäd çë.
TYPING 📲 +234 816 098 30 83
WhatsApp number chat with me at always my lover's ina maraba da kowa.
👑 ROYALTY 👑
💫 A*W*A 💫
ANNURI WRITER'S ASSOCIATION 💫
Home of hospitality and harmony gidan kar'bar mutane hannu biyu da zaman lafiya ÀÑÑÙRÌ haske le'ka gidan kowa koda ma'kiya na kallon ka ramin kura sai'ya'yan ta haka taken mu yake tafiyar babu rago babu maci amana tsantsan gaskiya muke nunawa.
STORY WRITTEN ND EDITING
✍️Yusrah Musa Abubakar YUSEEN AL-AMEEN CE maman Fatima