Maryam tai wuf ta janye plate d'in ta turo mata ainishin nata na farko tana cewa "ga jagwalgwalon kinan saiki cinye dama nayi hakan ne dan kiyi serving d'in nawa ko bakya so" murmushi Baby tai kawai tana qara d'auke kai daga saitinta wanda Khairat da tafi babyn jin d'acin abinda Maryam d'in tai mata tace.
"Wai dan Allah Maryam me kikeyi haka ne meyasa bakya neman zaman lafiya duk kawar dakai da baby take miki saikin shiga safgarta gaskiya bakya kyautawa wannan abunfa da kike ya Ahmad yana sane bashi kike ci akwai ranar da zaki kwashi adahin ki a gurinsa" baki Maryam ta ta'be tana hura hanci a gadarance tace "a gurin wa zan kwashi adahin? Humm indai a gurin Ahmad ne saidai na kwashi nishad'i kin gane dama ni ina son bashi I love credit wallahi ba abinda ya isa yai min domin ni baku bace bazai takani na 'kyale shiba".
Kai Khairat ta jinjina tana cewa "Ok haka kikace ko shikenan zakiga you love credit Allah ya taimaka kici gaba dayi wata rana zaki dana sani dama duk yadda akai da jaki sai yaci kara lokacin dazai taka kin ya gurjeki muna kallo" wata uwar harara Maryam ta sakar mata tana jan tsaki tace "ya taka wa? Ai na rantse da Allah Ahmad bai isa na tsaya ya dakeni ba ko 'kasa ce abinci na ni nafi karfin wulakancin sa".
"Shiba wulakanta ki yake ba kawai yana nuna miki hanyar shiriya ne wacce zakibi amma tunda kince haka ba damuwa nidai ina qara tuna miki kibi a sannu wata rana zaki dana sani".
"Wallahi ba ranar da zata fito ta fad'i wacce zanyi nadama a cikinta abinda nake aikatawa shine daidai saina hanaku jin dad'i harsai kun sallama min" ta fad'a tana sake aikawa da Baby harara wacce batasan tanayi ba ita kam hankalinta na wani gurin dabam daidai Ahmad ya shigo ya nufi inda Momy take xaune acan parlor wani irin kallo Maryam ta bishi dashi a ranta tana fad'in "wayyo Allah na dan Allah kalleka Ahmad kalli 'kirar jikinka me d'aukar hankali tana son she'ke ni inaso naga jikinka a bayyane zanso naganka batare da rigaba tabbas ina 'kwadayi idanuwana suyi tozali da kyakkyawan jikin nan naka indai baka amincewa soyayya ta ka aureni ba huuuuh ta fitar da huci tana sake d'agowa ta zuba masa ido yadda yake magana ma kad'ai abin kallo ne komai nasa cikin aji da tsari yake yinsa" numfashi ta fitar tana cije lips ta jinjina kai tana sakin murmushi lokaci guda ta shiga wani yanayi duk abinda take Khairat na kallonta kamar zatai dariya sai kuma ta maze itama tana kallo inda Ahmad d'in yake zaune a ranta tace "humm lallai wato Maryam son Ahmad take ko mene nayin wannan abubuwan aiko indai tsautsayi yasa ta kamu da ciwon sonsa ta had'a kanta da wahala ta d'auko damin daba saukewa jin 'kak'karfar ajiyar zuciyar da Maryam ta sauke yasa Khairat dariyar da take 6oyewa ta fito fili rufe baki tai ganin irin kallon da Maryam d'in take aiko mata dashi tace.
"Tofa Maryam anya da gaske ne"? A kaikaice Maryam tace "da gaske ne me"? Murmushi Khairat tai tana cewa "da gaske ne kina son Ahmad"? Jin tambayar datai mata yasa ta had'e rai tana cewa "meyasa kika tambaya bayan kin sani"? Gira Khairat ta d'age tana kallon ta tace "mena sani ni bansan komai ba shiyasa na tambaya saiki fad'a min idan 'kaunarsa kike".
"Eh 'kaunarsa nake sonsa nake yanzu kin sani"?.
"Uhm na sani yanzu amma aurensa zaki kome"?.
"Toda me kike tunani zanyi soyayya kad'ai dashi ne aurensa man zanyi zuba ido ki gani" zaro ido waje Khairat tai tana rufe baki da sauri ta danne dariyar data taso mata da'kyar tana d'an tari tace "masha Allah ashe kwanan nan zamu sha biki kenan ko"?.
"Yes fad'i ki 'kara babu fashi aure kamar na aureshi ne kuma zaki zama sheda ranar dana aureshi zan tuna miki da wannan maganar".
Kai Khairat ta kad'a tana cewa "ok Allah ya kaimu lokacin mukam yan shan biki ne da zuwa wajen dinner su gwangwaje".
Cikin nishad'in maganar da suke Maryam ta rausaya kai tana cewa "tabbas zaku sha idan ma isgilanci kike min insha Allahu Ahmad shine mijina shi zan aura saiya ranki"?.
Dariya Khairat tai tana cewa "ni raina babu komai fes yake sai alkhairi kinsan bazan yi miki ba'kin ciki dan kince ke ya Ähmäd zai aura ba ko?.
"To Khairat idan zaki min ba'kin cikin ma kezaki d'orawa kanki wahala a banza nikam na riga na tsallake rijiya da baya domin ya riga yasan da maganar ma kuma bai nuna bai amince ba saiki fara shiri tun yanzu saboda kar lokaci ya 'kure miki tunda neman d'orawa kanki wahala kike yi".
Ta'be baki Khairat tai tana girgiza kai tace "meye abun d'orawa kai wahala kawai dan kin aureshi idanma baki aureshi ba ina zai auri wata nidai kinsan 'kanwarsa ce ba aure ne a tsakanin muba balle kice zanyi kishi dake saboda kince kina sonsa idan haka kike nufi"?.
"Oh aina d'auka kina 'kanwar tasa ma zaki kishin dani ne kodan idan ke baki ba wannan ballagazar zatai tunda ita akwai auren tsakanin su cousin d'insa ce" ta fad'a tana aikawa da Baby muguwar harara cike da tsananin kishinta da taji ya kamata lokaci guda had'e da tsanar Babyn kai Khairat ta girgiza tana cewa "A'a ita kam babu aure a tsakanin su domin baby ba ya Ahmad zata aura ba kuma shima ba ita zai aura ba karma ki sake wannan maganar ba ruwan Baby da Ahmad kawai ala'ka ce ta jini amma ba soyayya ba" jin abinda Khairat tace yasa Maryam sauke sansanyan numfashi cikin jin dad'i har tana kallon Babyn da murmushi akan fuskarta muryarta normal kamar yadda zatai magana da Mamanta tace "humm Allah ya taimake ki baby kike sunan naki ko beblo kin hutar da kanki gara kar zuciyarki ta kamu da sonsa ki d'auke hankalinki karma ki fara tunanin hakan idan auren kike so ga Abdul-Hamid nan kunfi dacewa dashi sosai fiye da Ahmad kije ki kalli kanki a mirror Abdul-Hamid shine tsaranki shine zai iya d'aukar nonsense d'inki ba Ahmad ba domin shi d'an gayu ne me aji da 'kasaita nice na dace dashi da tsarin rayuwarsa nice zan tarairaye shi na soshi na nuna masa 'kauna kamar zan mayar dashi ciki amma bake me siffar gidadawa ba" Maryam na rufe baki Baby ta mi'ke tana barin dinning d'in batare data koda kalli inda Maryam d'in take ba balle ta nuna abinda take fad'a ya dameta ko tsayawa batai ta ta fice daga part d'in gabadaya ta tafi part d'in Mami.
Tana fita cikin matsuwa Maryam ta kalli Khairat tana cewa "ke Khairat ina jinki bani labari da gaske ne Ahmad baida budurwa baida wacce yake so ko kin fad'a ne dan kiga yadda zanyi"?.
"A'a bana fad'a ne dan dad'in baki ba da gaske nake miki ya Ahmad baida budurwa ko kusa bai fara soyayya ba maybe Sai gaba" farin ciki ne ya rufe Maryam ta sake 'kar da murya tana cewa "to amma baku ta'ba ganin ya nuna alamar yana da itan ba"?.
D'an tsaki Khairat taja saboda maganganun sun fara isarta tace "ke nifa ban sani ba inace gashi can a gurin Momy suna magana mezai hana kije ki tambaye shi kyazo ki takura min ni nasan yana da budurwa ko baida ita ne".
"Humm Khairat kenan kinada abun mamaki kamar kin manta waye Ahmad ke ganinki yanxu kina da tabbacin idan na tambaye shi zai bani amsa jin kansa yayi yawa kamar na wancan yarinyar"?.
Tabe baki Khairat tai tana kallo wajen inda yake tace "A'a ban sani ba ki gwada sa'arki maybe ya tsaya ya saurareki abun dace ne auren mace da ciki kinsan zan iya cewa bazai saurare kiba kije ya saurareki kizo kina yimin kallon ma'karyaciya amma gashi can kije ki gwada" tana fad'in haka ta mi'ke itama tana fita daga part d'in shiru Maryam tai tana kallon Ahmad da hankalinsa yake kan abinda Momy take fad'a masa a ranta tace "haba Ahmad! Haba my husband🤔 taya kake tunanin zan barka kalli kyau iya kyau ta ko'ina ka cika namiji kwarjini jarumtaka humm wash Allah ubangiji kana gani na ka cika min burina akan Ahmad ya Allah ka sanya akwai hukuncin aure tsakanin mu Allah yasa bani da wani mijin bayan kai dakai nake so nayi rayuwa kaine komai nawa ina sonka" ta fad'a tana bud'e idonta dake rufe kamar ance Ahmad ya d'ago aiko karaf suka had'a ido dashi murmushi ta sakar masa tana d'aga masa hannu alamar barka kaiya d'auke daga saitin ta yana mi'kewa yaiwa Momy sallama ya fita da kallo Maryam ta bishi harya fita kamar zatai ihu tsabar ba'kin cikin wannan halin ko'in kular da yake nuna mata ji tayi hawaye yana taruwa a idonta da sauri ta kifa kanta a table d'in dinning d'in saboda kar Momy ta gani itama Momyn bata kula da ita ba hankalinta bai kawo kan dinning d'inba shiyasa bata ganta ba gashi lokacin breakfast d'inta bai karaso ba balle idan tayo wajen gurin ta ganta haka ta 'karaci zubar da hawayenta ta ha'kura tana mi'kewa ta shiga bedroom.
••°°••°°••Yau tunda Ayrah tai sallar asuba bata sake komawa barci ba tana garden tana wankewa Abidah da Hajiya Khubura kayansu a ranar wuni tai tana wankin ko karyawa batai ba har karfe hud'u da rabi da yake ranar period takeyi ba sallah zatai ba shiyasa ma tunda ta fito garden d'in bata sake komawa ciki ba saida ta gama ta tattara komai ta d'ebe wadanda suka bushe ta shiga dasu ganin babu nefa sun d'auke kawai ta aje da nufin koda dare suka kawo saita goge musu duk zirga-zirgar da Ayrah take Abidah tana kallonta har saida ta gama komai ta fito daga part d'in su Abidan tana kokarin shiga nata tai wanka Abidah ta daka mata tsawa tana cewa.
"Ke dabba kinfi karfin kizo kice min kin gama kenan saboda da gaki isasshiya ko"? Juyowa Ayrah tai ranta a 'bace tace "a tunani na keba makauniya bace ai kina ganin abinda nake yi ba'aiwa me ido gafara idan baki gode min abinda nai miki ba bazaki tsine min ba" gwalo ido Abidah tai tana cewa "uban waye zai gode mikin amma badai niba Allah ya sauwake nace miki koda sannu ne balle godiya ked'in banza wai ma tsaya nayi miki tambaya da yaushe raini ya shiga tsakanin mu har haka Ina magana kina kallona kina mayar min da martani"?.
"Tambaye nidai na fad'a miki abinda yasa nake kallonki ina fad'a miki magana isa nayi".
"Au isa kikai? Humm kan masifa da bala'i ni kike fad'awa haka tabd'ijan aiko wallahi yau sai naci uwar uwarki saikin gane ruwa ba sa'an kwando bane" ta'be baki Ayrah tai tana wucewa batare data sake bi takan taba tsalle Abidah tai tana cewa "ke dan uwarki dan ubanki dawo min nan ban gama dake ba" ta fad'a tana jawota baya da karfin gaske a fusace Ayrah ta juyo tana fisgewa tace "karki sake zagin mahaifana" jin abinda tace yasa Abidah zaro ido waje cike da tsananin mamaki ta bud'e baki da hanci tana kallon ta tace.
"Me naji kince maimaita kalmar da kika fad'a dan inaga kunne nane baiji sosai ba"? A masife Ayrah tace "nace karki kuskura ki sake zagin mahaifana kin gane"? wani irin kallon baki da hankali Abidah tai mata tana cewa "au karna sake zagin mahaifanki humm lallai idan na sake zagin sufa me zaki iyayi zaki dake nine"? Kai Ayrah ta jinjina tana cewa "kwarai zan miki abinda baki ta'ba tunani ba idan kin isa ki maimaita wallahi yau ko Umma zata kashe ni a gidan nan saina fasa miki baki"
"Ni zaki fasawa baki"? Abidah ta fad'a tana nuna kanta taga kodai mafarki take cikin 'kwarin gwiwa Ayrah tace "kwarai ma kuwa shashasha haka nace ko kina ganin nayi 'karya ne bazan iya ba"? Cikin 'karaji Abidah tace "eh 'karya kike wallahi 'karya ne abinda kika fad'a amma tunda kince zaki iya bismilllah zoki fasa min bakin d'in nagani" gyara tsaiwa Ayrah tai tana cewa "ok yau kuwa zan gwada miki wace Ayrah a gidan nan idan kin isa kije ki saita min bakin naki a jikin bango ki gani idan ban gurje shiba" kallon tsaf Abidah tai mata tana cizon yatsa ji take inama Nadiya tana nan yau su taru su karya Ayrah ku faffasa mata jiki.................
"Ko baki shirya ba na tafi harkar gabana nace kije ki saita min bakin naki a jikin bango ki gani idan ban gurjeshi yai jini ba" maganar Ayrah ta dawo da ita daga maganar zucin da take wani mugun kallo Abidah tai mata har zuciya ta debeta ta sha'ki wuyan Ayrah ta rufeta da duka sai kuma tace bari dai ta taje jikin bangon taga gudun ruwan Ayran da gaske zata iya abinda ta fad'a ko korarin banza ne 'kwafa Abidah taja tana wucewa taje jikin bango tana cewa "zoki gurje min d'in" ta fad'a a fusace tana kallon Ayrah wacce ta karaso itama tana kallonta fuska a tamke tace "ki saita min bakin naki a jikin bangon nace yanzun nan kiga aiki da cikawa yau zan nuna miki kalata duk zaman da muke daku na zuba muku ido ne yau zan fara gwada miki Nima ba kanwar lasa bace bani da dad'i fad'awa a rijiyar fetur d'in da take cida wuta yafi sau'ki akan shiga gonata".
Murmushi Abidah tai tana jinjina kai tare da fashewa da dariya tana nuna Ayrah tace "kalleta da Allah sakaryar kawai wato kenan yanzu zaki iya abinda kika fad'a idan na saita miki bakin nawa"?.
"Ai magana da cacar baki bazata wadace muba kawai ki saita min bakin kiga yadda zanyi idan zan iya idan ma bazan iya ba zaki gani".
Juyawa Abidah tai tana cewa "ok gashi zoki gurje" ta fad'a tana juya fuskarta ta saita mata bakin a jikin bango kamar yadda tace zuciyar Ayrah ta riga ta hangulo da abinda Abidan take mata tana ganin ta samu dama tasa hannu ta dam'ki wuyan Abidan wacce ta d'auka fad'a kawai Ayran take bazata iya mata komai ba saida taji ta danna kan nata a jikin bangon ta fara gogawa da 'karfi Abidah ta d'auka Ayrah bazata iya bafa humm saida taji azaba zata kasheta batasan lokacin data fara ihu ba tana kiran Hajiya Khubura khaleel dake zaune dariya yake harda ri'ke ciki yana hautsinawa akan kujera ganin Hajiya Khubura ta fito da gudu yasa ya mi'ke shima da gudu ya karasa inda suke saboda yasan idan ya bari Hajiya Khubura saita daki Ayrah yana zuwa ya janta yana 6oyeta a bayansa kamar ba shine ya gama dariya yanzu ba ya hade ransa ganin yadda Hajiya Khubura ta susuce ta karad'e gurin da salati ganin yadda bakin Abidah ya fashe yana fitar da jini ta kalli Ayrah dake bayan khaleel tana cewa.
"Mitsiyaciya bankad'addiya kashe min 'yar zakiyi kiga yadda kika fasa mata baki har wannan jinin yake ambaliya haka kamar an yanka rago wallahi yau saikin shiga uku a gidan nan" ta fad'a tana juyawa kan Abidah dake kukan azaba da rad'ad'in da bakinta yake mata tana cewa "kema ubanki kika tsaya kallo har wannan figaggiyar ta iya danne miki kai a jikin bango tana gurzawa kamar tana gurza kayan wanki kina tsaye so'ko'ko ya 'kawar bora harta fitar miki da irin wannan jinin tabd'ijan aiko yau idan baki mata dukan mutuwa ba sai naci ubanki a gidan nan" jin abinda Hajiya Khubura ta fad'a yasa khaleel yace.
"Wallahi Umma bata isa ta daketa ba meyasa tace taxo ta gurje Mata bakin ita kuwa ta nuna mata isar tata a fili yanzu da taci ubanta gaba zatai shakkarta dama kullum suna takura Mata suna matsa mata daga yau ta fara ramawa dan ubanta itama Nadiyan naso ace harda ita akaiwa haka shegun yara yan iska" nunashi Hajiya Khubura keyi da yatsa ranta a 'bace tace.
"Khaleel karka sake zagar min yara na akan wannan 'yar ala tsinan dama Kaine me zuga ta kenan saboda Nadiya tayi aure wato ta rama akan Abidah kenan"?.
"Ni bance ta rama akan Abidah ba kawai dai ina fad'a muku gaskiyar magana ne kun dad'e kuna cutar mata yanxu kuma lokaci yazo da zata rama wani abin sai gaba ma idan na aureta ta zama matata wallahi ta daina komai kuma ba 'yar aiki zan nemo ba kura ce za'a ramawa aniyarta Abidan ce zata ri'ka mata komai kama daga girki wanki wanke-wanke da share-share harda wanki toilet wallahi duk saita yi mata idan ta nuna taurin kai ko bana nan tace bazatai ba nazo har gabanki nayi mata shegen duka kuma dole taje tai aikin".
Khaleel na rufe baki Hajiya Khubura tai masa wani irin kallon ka fara hauka ne tana cewa "au kaine me goyon bayanta shine kana gani tai mata haka dan asara bakai komai ba karshe yanzu ka 6oyeta a bayanka kana fad'ar wani idan ka aureta Abidah ce baiwar wannan yarinyar hum'um wallahi bata isa ba sai naci uwarta yau saina sumar da ita sannan wahala tasa ta farfad'o".
"Kinsan Allah Umma bazaku daketa ba saboda banga abinda tai muku ba idan kuma ramawar kike so Abidan tayi to kibarsu ki koma gefe ki zauna ki zuba musu ido aga wanda zaiji jiki a cikinsu" ya fad'a yana dariya saboda yasan Ayrah tafi 'karfin Abidah kawai dai tana ha'kuri ne da danne komai saboda tsoron abinda Hajiya Khuburan zatai mata murmushi yai yana sake kallon Hajiya Khubura data cika tai fam yace "a fara bismilllah ga fili my Baby fito ku had'a damtse kar kiji tsoron kowa ina so ki nunawa Umma da wannan 'yar iskar yarinyar keba abar rainawa bace Umma kun shirya my wife a shirye take jin abinda yake cewa yasa a masife Hajiya Khubura tace bazan zuba musu idon ba da kaina zanci uwarta ba Abidan data rainawa hankalin ce zata rama ba balle ta mayar da ita kamar wata sa'ar ta".
"Umma kar kiyi haka dahuwar hankali ayita da ruwa Abidah bata da gaskiya anan bai kamata kice danta tsokani Ayrah ta daketa saikin rama mata ba zan fita amma wallahi