x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 6 - ROYALTY YAN SARAUTA

  • 15001 words
  • 18000 words
  • Out of 85109 words

Category: Love Stories

Views 1673

20 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
xai fisheka please Ahmad dan Allah ka daina baiwa yarinyar nan barazana idan kuwa ka'ki jin maganata hummm abun zaizo maka a baibai kai ko koyi bakai da Shadad kana gani yadda yake kula da Khairat saboda yana sonta koda ace ita da Baby sukai laifi saidai ya hukunta iya Babyn ita ya rabu da ita ko kuma ya hukunta su tare sannan ita Khairat d'in yazo yana lallashinta daga baya amma kai babu ruwanka wanda kake so shi yafi shan wahalarka meyasa hakan"?.

"Ni haka nawa tsarin yake aini dashi ba d'aya muke ba kowa daban shi Shadad sunansa ni kuma Ahmad sannan halin mu ba d'aya bane kowa da nasa bazan iya daina hukunta Baby idan tayi laifi a gidan nan ba saidai idan bana nan ba ina haka dan na zalunceta ko nasaka mata tsoro na a zuciyarta bane a'a ko d'aya ina so na horar da abata da kaina domin koma mene nine xan zauna da kayata tsahon lokaci tunda aurenta zanyi ya kamata kaima ka fahimce ni".

Kai prince Hamid ya jinjina yana cewa "ok shikenan Ahmad na fahimce ka amma dai dan Allah ka ri'ka rage wasu abubuwan" yana fad'in haka ya juya ya fita Ahmad kam bai fita ba saida ya gama abinda yake yi sannan ya d'auko wani abu kamar gift🎁 ya fito dashi har lokacin Baby tana nan zaune mi'ka mata yai yana cewa "kiyi amfani dashi kuma ban baki dan kiyi kwalliya dashi ba duk ranar da naga abun nan a jikin ki ko kin ajeshi hummm tashi ki tafi" kar'ba tai tayi masa godiya ta fita da mamaki a ranta har tayi hanyar part d'insu ta fasa ta shiga part d'in Momy suna zaune ita da Khairat ta shiga da sallama tana zama ta gaida Momy amsawa Momy tai tana kallon ta da murmushi kamar batasan daga inda take ba dan prince Hamid ya fad'a mata amma sai tace "Baby daga ina wannan kuma fa"? Sauke numfashi Baby tai tana waiwayen kofar shigowa ganin ba kowa tace "ya Ahmad ne ya bani yanzu".

"Ya Ahmad kuma"? Khairat ta tambaya tana zaro ido tace "tofa abun ya motsa mene a ciki bud'e mu gani" huuuuuuhh Baby tayi ajiyar zuciya tana cewa "yace bai bani dan naje na ajiye ba sannan idan nayi kwalliya dashi nasan sauran kuma idan na'ki amfani dashi hummm kawai yace min kinsan abun bazaiyi kyau ba".

"Ban gane karki yi amfani dashi ba sannan idan kika ajiye kinsan sauran ji Yaya Ahmad da saka mutum a tsaka me wuya" Khairat na rufe baki Baby tace "dan Allah Aunty Khairat kiyi shiru karya shigo ya jiki indai dan wannan abun ne bari na bud'e mu gani" ta fad'a tana cire d'an golden d'in 'kyallen da aka d'aure ta aje a gefe tana bud'ewa duk zaro ido waje sukai ganin wani d'an kyakkyawan littafi ne a ciki kallon juna sukai Khairat data d'auko littafin tana kallo tace.

"Kai amma fa gaskiya yayi kyau to amma taya zaki kwalliya da littafi da yake cewa kar kiyi ado dashi"?.

"Oho wallahi nima bansan manufarsa ba" Baby ta fad'a itama tana qarewa littafin kallo murmushi Momy tai tana cewa "da yace karkiyi kwalliya dashi yana nufin karki ajeshi akan mirror ko drawer ya zama bakya karantawa kin gane"? Kai Baby ta jinjina zatai magana Ahmad ya shiga da sauri ta kar'be littafin daga hannun Khairat wacce itama ta cillo mata duk da ya gani kawai ya sharesu ne maidawa ciki tai tana mi'kewa zatai waje Khairat ma ta mi'ke tana cewa "Baby jirani mu tafi" tun kafin Baby tace to Ahmad yace "ku dawo min nan wato saboda ga macuci ya shigo ko"? Duk tsayawa sukai baby kam da yake ta kusa kofar fita da sauri ta dawo Khairat kuwa dama iya mi'kewa tai dole suka zauna kowacce tana ankare sun kama kansu gudun yin laifi iya shida Momy suke magana har wani lokaci sannan ya kallesu ganin yadda suke a takure yace.

"Me kuke jira baku tafi ba ko gulmar zancen da muke kuke yi"? Ba suba da yaiwa tambayar hatta Momy saida ta kalleshi da mamaki tana cewa "amma kaine fa kace su dawo har zasu fita ka tsayar dasu".

"No Momy da nace su dawo ai ba'a nan nake nufin su zauna ba" ya karasa maganar yana mayar da hankalinsa kansu yace "kai daku fa nake ku barmin nan" aguje suka mi'ke har suna gware wajen fita suna ficewa a part d'in Khairat ta sauke ajiyar zuciya tana huci tace "innalillahi kai jama'a indai Yaya Ahmad yana gida bazai ta'ba bari kai 'kiba ba wai zamu fito yace mu tsaya sannan mun tsaya yace me muke jira ko gulman zancen da suke muke yi" kai Baby ta girgiza jin ana kiran sallah tace "nikam bani da bakin magana Aunty Khairat yau babu abinda naci ko breakfast banyi ba".

"Ked'in me kike har yanzu baki karya ba"?.

"Ina barci fa Sultan ya kirani wai nazo inji ya Ahmad wallahi bakiji yadda naji zuciyata tana bugawa ba saida nazo naji ba laifi nayi masa ba toilet zan wanke masa na had'a masa ruwan wanka".

"Ina masu yi masa hidima da saiya kiraki"?.

"Oho musu ni banga kowa ba dana shiga" kai Khairat ta jinjina tana cewa "nikam dama na dad'e ban shiga part d'insu ba yanzu kece a online kafin abun ya juyo kaina" ta fad'a daidai sun shiga part d'in Mami tana zaune Sultan yana kusa da ita yana aikin daya saba na shagwa'ba farko da yaji an bud'o kofa ya d'auka Ahmad ne harya nutsu ganin su Baby yasa yaci gaba dariya Khairat tai tana cewa "lallai yaron nan Sultan kana lokaci amma fa kayi a hankali dan ya Ahmad yana nan zuwa idan ya kamaka kana wannan shagwa'bar yau zakai bayani" kamar ba dashi take ba haka yaci gaba da abinda yake yi kuma abinci ake bashi a baki amma yana had'iyewa zaici gaba kai Baby ta jinjina tana cewa.

"Hummm rabu dashi Aunty Khairat maybe kaddara ce take jansa idan yana da rabon shan duka ne yaci gaba ya Ähmäd roba ne yana daidai da 'kugun kowa kaci gaba dayin shagwa'barka lokacin kane dama ka samu tunda kai ba'a fiya takura maka kamar niba" ta karasa maganar tana wucewa bedroom ta aje littafin ta shiga toilet tayi brush ta fito tana dawowa parlor ta wuce dinning zamanta keda wuya taji sallamar Ahmad ya shigo ji tayi abincin ya 'kwareta da sauri ta dau'ki ruwa tasha Khairat na can gefe nesa dasu Mami Sultan kuwa tuni ya daidai kansa ya nutsu sosai a hankali yasa hannu yana kokarin kar'bar spoon d'in dake ri'ke a hannun Mami dan kada Ahmad ya gani kallonsa Mami tai tana cewa.

"Ya haka Sultan ka bari na karasa baka man"? Kaiya girgiza yana kallon Ahmad yace "a'a Mami zan qarasa da kaina" ya fad'a yana kar'ba da sauri ya mi'ke bai karasa ci a gurin ba ya koma can saman dinning ya zauna kamar gaske ya ri'ka she'ka loma da ana bashi yana shagwa'ba kamar baby zatai dariya haka ta zuba masa ido tana kallon sa zuwa wani lokaci ta kallo parlor ganin hankalin Ahmad baya kansu zance kawai suke da Mami yasa tai qasa da murya tana cewa.

"A'a autan Mami yau kuma yada cin abinci da kanka wato ganin boss Ahmad yasa ka nutsu ko? Wallahi naso lokacin da muka shigo sannan shima ya shigo ya sameka kana shagwa'ba humm ya fasa bakin shagwa'bar sannan yau ka wuni har dare kana kar'bar service" d'agowa Sultan yayi yana kallon ta kamar bazai magana ba ya mayar da hankalinsa kan cin abincin saida ya gama ya dau'ki tissue ya goge bakinsa ya aje sannan yace "ai bazan yarda nayi abinda zai dakeni ba domin niba jaki bane kalli man Ina da hanyar kare kaina yana shiga na nutsu na tattara ya nawa yanawa na baro gurinsa hanyar lafiya a bita da shekara ban zauna bama balle yace nayi kuskuren wani abu kuma da salona kuka d'auka daga yau bazai sake kamaku da laifin wani abu ba balle ya hukunta ku" murmushi Baby tai tana girgiza kai tace "humm Sultan da alama ka manta waye ya Ahmad duk abinda muke yana hankalce damu wallahi ra'ayin kula kane baiyi ba da yaso zakaji yayi magana tun lokacin daya shigo ai ya ganka ana baka abinci a baki kuma yaga shagwa'bar da kake yi mata amma da baiyi niyyar yace maka komai ba kana gani ko inda kake bai kalla ba kawai kai dai kace kana da sa'a mukam bamu da bakin magana saidai muce alhamdulillah" qara qasa da murya Sultan yayi yana cewa "Aunty Baby na fad'a miki mafita ta yadda bazaki sake shiga tarkon Yaya Ahmad ba"? Kaita girgiza tana kallon sa tace.

"kaima ba tsira kayi daga tarkon nasa ba kayita kanka kafin kayita wani".

"Allah Aunty Baby da gaske nake".

"Da gaske kake me"?.

"Shawara zan baki akan hakan".

"A'a bana bu'katar shawara saidai basir indai akan ya Ahmad ne duk ta inda ka 6ullo zaka sameshi yana kofar shima a tsaye yana jiranka da akwai inda zai 6ullo maka dan haka kaima kaji da kanka baka da wata shawara da zaka bayar anan".

"Amma Aunty baby ai baki bari kinji me zance miki ba"?.

"Nifa basai kace komai ba Sultan na fahimta ka 'kyale ni dan Allah karka d'aga min hankali na kasa cin abinci kai ka gama ci" mi'kewa yayi yana cewa "shikenan tunda bakya son ji na fad'awa Aunty Khairat" Baby na kokarin 'kara zuba abinci a place tace "yauwa saidai itan zaku daidaita amma dai banda ni kome zanyi ya Ahmad bazai fasa d'irka taba" ta karasa maganar tana d'agowa ta kallo inda yake magana suke sosai da Mami cikin sakewa kaita jinjina tana fara cin abincinta tana kallon Sultan yadda ya zauna a kusa da Khairat ya kifa kansa qasa yana fad'a mata abubuwa ita kuma tana d'aga kai tana murmushi wani lokaci kuma tad'an zaro ido ta rufe baki cije lips Baby tai a ranta tace ''tabd'ijan da ace ya Ahmad zai ganku a haka humm yanzu jikinku zaiyi d'umi" ta'be baki tai tana mayar da hankalinta kan cin abincinta har Ahmad suka gama zance da Mami ya tashi yayi waje yana fita Sultan ya dau'ki mp zai kunna Mami tace.

"Wallahi Sultan ka kiyayi kanka ka guji had'uwarka da Ahmad akan wannan mp idan ba duka kake nema ba maybe yanzu ka ganshi ya dawo saboda akwai shi da wasan baya domin irinku marasa jin magana balle yaga duk ku ukun kuna part d'in".

Zama Sultan yayi yana kokarin kunnawa yace "ai Mami nasan bazai dawo ba ya fita kenan".

"Au haka kace saboda ya fad'a maka dazai fita cewa bazai dawo ba"? To ai shikenan nidai kasan ba tankawa zanyi ba idan ma ya kamaka kaine jikin ka zaiyi tsami".

"Ai Mami inada kafar gudu bazan zauna ya riske niba ni ba irin Aunty Baby bane dazan tsaya ina gani ya ri'ke ni ko zomo bazai fad'a min zilliya ba yasin saidai muyita zaga masarautar nan da gudu har ya gaji ya barni".

Kai Mami ta jinjina tana sakin murmushin zancen nasa tace "lallai kam amma shikenan ba matsala bansan shirinka ba nidai na fad'a maka kar tsautsayi ne yake janka a kowanne lokaci zaka iya ganinsa ya dawo kuma ba ruwana nidai na fad'a maka gara kaji dakyau kar kace baka sani ba ko kayi tunanin zan bashi hakuri ya 'kyale ka ina kallo zaiyi maka shegen duka" tana rufe baki Sultan ya d'ago zaiyi magana sai ganin Ahmad yai ya bud'o kofa kamar a mafarki yana cewa "Mami nabar key d'in motana anan"?.

Humm tabd'ijan aguje Sultan ya tashi kamar iska na cirashi sama tsabar sauri wuff ya fad'a bedroom Ahmad da baidan me yakewa gudun ba yace "shi kuma wannan fa"? Murmushi Mami tai ganin tun ba'a je ko'ina ba gashi ana shirin kama shi tace "humm Sultan nefa ai ya zama saidai addu'a" kawai haka tace saboda taga alamar kamar Ahmad d'in baiga mp dake aje a gurin ba.

"Baby kira min Sultan" Ahmad ya fad'a yana qarasa shigowa parlon to Baby tace tana mi'kewa da sauri ta shiga part d'in Mami amma babu alamar Sultan kira ta fara kwalla masa ya'ki amsawa saida tace ya Ahmad ne yace yaje aiko sai gashi ya fito daga toilet yana cewa ''yana Ina"? Juyawa baby tai tana cewa "yana parlor man nidai na fad'a maka idan kaga dama kazo ko ka'ki zuwa ba ruwana tsakanin kune Kai dashi" jin abinda tace gashi tana shirin fita yasa da sauri yabi bayanta Ahmad yana tsaye a gurin da yake Sultan ya fito yana ra6ewa duk xatonsa ko Ahmad yaga mp a zahiri kuwa babu abinda ya gani kawai dai yaga ya tashi da gudu ne tambayar da zaiyi masa kenan, karasowa yayi yana cewa.

"Gani Yaya kayi hakuri dan Allah" a tsume Ahmad yace "gudun me kake wato saboda kaga ban dad'e da fita ba na dawo kamar wanda kaga dodo shine harda d'ame kafa kana cin uban gudu ko"? Da sauri Sultan ya girgiza kai yana cewa "dan Allah kayi ha'kuri Yaya ba ganinka ne yasa na gudu ba gudawa nake" Sultan na rufe baki Mami ta fara dariya tana kallon yadda yake d'an ri'ke ciki kamar gudawar gaske yake tace.

"Tofa Sultan wannan 'karyar har Ina kai d'in ne kake gudawa ban sani ba amma yanzu dawowar Ahmad ta kamaka ko"? Da sauri ya girgiza kai yana cewa "A'a Mami dama tun jiya da dare na fara wannan abun da kika ban naci ne".

"Au 'karya zaka koya wanne abun na baka jiya wanda ya saka gudawa daga safe zuwa dare"?.

"Wannan abun fa" Sultan ya fad'a yana sake ri'ke ciki yace "kinji yanzu ma cikina yana 'kugi ga ciwo wayyo Allah na" ya karasa maganar yana dur'kusawa ya fara murd'e-murd'e kamar gaske.

"Uhmm" kawai shine abinda Mami tace dan tasan ya fad'a ne kawai neman hanyar tsira yake domin idan ya bari Ahmad ya fahimci dan shi ya gudu tofa saiya sakashi gudawar dole anan gun ko Kuma yace suje toilet d'in ya gani idan gaskiya ne ko kallonsa Ahmad bai sake yiba daya dau'ki key d'in zai fita yace "kaje gurin Abdul-Hamid ka kar'bi magani" da sauri Sultan yace "to".

"Ba fad'in to ba idan na dawo yace bakaje ka kar'ba ba wallahi ni dakai ne a gidan nan sai naci ubanka tunda kuna son sake da lafiyarku musamman Baby" yana fad'in haka ya fice 'kak'karfar ajiyar zuciya Sultan ya sauke yana kallon Mami wacce itama ta zuba masa ido da murmushi akan fuskarta zatai magana Sultan yace "ya zanyi Mami" kaita girgiza tana cewa "a'a bansan yadda zakai ba ni babu ruwana sai kaje ka kar'bo kafin yaje inda zaije kasan ya dawo ko baka so saiya saka a gaba kasha alhali ba jinyar kake ba gara ka wuce ka kar'bo sai kazo ka ajiye".

"To Mami bari na kar'bo" ya fad'a yana fita ganin Sultan ya fita Baby data mi'ke daga dinning bayan ta karasa cin abincin data zuba parlor ta dawo kusa da Mami tana zama tace "hummm yau dai bari mu d'ana zaman parlon kafin ya Ähmäd yayi yabar mana gu gaskiya wallahi Yaya Ahmad yana da matsala ba dama yabar mutum ya sha'ki iska mai kyau haba jama'a nifa na matsu naga ya koma yaushe nezai ya tafi Mami"? Kai Mami ta girgiza tana cewa "taya zan sani saidai na tambayar miki shi" zaro ido Baby tai tana kallon Sultan daya dawo ri'ke da magani dariya ta saki ba shiri tana kallon sa tace "masu gudawa sai azo asha magani ko ta sauka tunda wanda yasa ka kamu d'in ya tafi" zama Sultan yai yana sauke numfashi yace "barni Aunty Baby ai banyi tunanin zan tsira ba na d'auka zai gane 'karya nake".

"Humm ai ramin 'karyar 'kurarre ne maybe daya dawo nan zai fara shigowa ya duba jikinka saidai ka ri'ka kula da kaji dawowarsa ka shige bedroom ka kwanta".

"Ai Kuma idan na kwanta zan jawa kaina allura".

Kallonsa Mami tai tana cewa "eh ai kaima ita kake nema tunda kai "karyar jinya kayi fatan idan ya dawo kar yasa a d'aura maka ruwa ma" Mami na rufe baki Baby da Khairat suka fara dariya ganin yadda Sultan yayi da fuska Khairat tace "humm yau wani ya fad'a tarko Allah ya fitarka lafiya boss yana nan dawowa gare ka" tashi Sultan yayi yana nufar hanyar bedroom ganin zasu d'aga masa hankali yace "wannan maganganun naku ma kad'ai she'ke ni zasuyi idan naci gaba da zama anan gara na baku gu" ya fad'a yana wucewa cikin tsokana Khairat dake kallon Mami tace.

"Please Mami ki tambayawa Baby Yaya Ahmad yaushe zai tafi" Khairat na rufe baki Baby ta dafe 'kirji tana zaro ido waje tace "na shiga uku Aunty Khairat karki yala min masifa so kike yau yayi farfesu na kenan"? Dariya Khairat tai tana cewa "a'a ko d'aya ba son sani kike ba shiyasa na tuna mata ta tambaya miki ko"?.

"A'a wallahi ni bance ba kawai abar maganar tashi ma muje 6angaren Sultana Addah mu ganota" ta fad'a tana mi'kewa tace "please Aunty Khairat taso mu tafi Mami dan Allah karki fad'awa Yaya Ahmad komai" kai Mami ta d'aga mata daidai Khairat ta mi'ke suka fita.

✍️Mrs Äl'ämëëñ Ähmäd çë.

Banda kamarka ya rasulullah a duniya Banda kamar ka ya rasulullah lahira.
Ga Mai kyauta da aljannah irin rabon kud'i
Ga Mai kure Mai bu'kata yayan imam Ali
Ga Mai bayar da kyautar rai zo a hankali
Zaka fahimci ba kama Tai duniya da lahira.

Gashi da kyan siffa da haiba najidul awatiki in kaga sayyidil wara bakai ba ba'kin ciki ya najamul hudah Annabi dauke shamaki lamunce mu ganka ya mai salsabil da khausara.

TYPING 📲+234 81 60 9 8 3 0 83
Chat with me Yusrah Musa Abubakar.

👑 ROYALTY 👑


Dedicated to my daughter Fatima Zarah Elham little Zarahn Aunty.

ANNURI WRITER'S ASSOCIATION 💫
Home of hospitality and harmony gidan kar'bar mutane hannu biyu da zaman lafiya ÀÑÑÙRÌ haske le'ka gidan kowa koda ma'kiya na kallon ka ramin kura sai'ya'yan ta.


STORY YUSRAH CE
WRITTEN YUSRAH CE
EDITING YUSRAH CE
Idan mutane suna nuna naka kula
End Ads