x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 20 - ROYALTY YAN SARAUTA

  • 57001 words
  • 60000 words
  • Out of 85109 words

Category: Love Stories

Views 1686

20 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
sosai sosai godiya.

TYPING 📲 Wed apr/2025 09:44am
YUSRAH MUSA ABUBAKAR ✨✨.

👑 ROYALTY 👑

ANNURI WRITER'S ASSOCIATION 💫
Home of hospitality and harmony gidan kar'bar mutane hannu biyu da zaman lafiya ÀÑÑÙRÌ haske le'ka gidan kowa koda ma'kiya na kallon ka ramin kura sai'ya'yan ta.

S✓W✓E
©©Mrs Äl'ämëëñ Ähmäd çë mai tambarin yma dutse Jigawa state new world sabuwar duniya kuzo kuyi kallo dad'i yana Jigawa garin ilmi garin addini zaman lafiya Jigawa.

Dedicated to my daughter
FATIMA ZARAH SHAMSUDDEEN ABDUR-RAHEEM DUTSE.
*** * ***

13~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Khaidinah.

Bismilllahir Rahmanur Rahim 📿.

@YUSRAHMS CE
Page 25 & 26
Kamar yadda Mama ta fad'awa Maryam cewa zata kira Momy suyi magana washe gari ta kirata tunda Momy taga kiran Maman ta fahimci Maryam ta kirata ta fad'a mata abinda ya faru jiya da farko kamar bazata d'aga ba saboda bata son hayaniya sai kuma tayi tunani indai bata daga ba Mama zata gasgata abinda Maryam ta fad'a mata koda ace 'karya ta shirya gara ta d'aga taji meya faru lokacin har Mama ta gaji da kira kusan missed call goma ta ha'kura Momy tai kiranta dama a lokacin ta gama d'aukar fushi shawara take yankewa a ranta kawai ta d'auko mota taxo gurin Momyn suyi magana ido da ido sai tafi fahimtar ta akan a waya tana cikin wannan halin taga kiran Momy jikinta har rawa yake ta d'aga ko sallama babu tahau fad'a "yanzu aunty dan Allah haka ake rayuwa wanne irin abune wannan taya Maryam dan kawai tazo muku ziyara su Khairat zasu sakata a gaba da zagi dacin mutunci shi kuma Ähmäd da hankalinsa yad'au karan tsana ya d'ora mata haba dan Allah kina kallo haka yake faruwa itafa Maryam ba haka kawai tazo gidan nan ba tazo ne akan kisa Ahmad ya aureta wannan shine dalilin ba wani abu ba maimakon hakan sai wulakanci ne yake biyo baya daga an shirya abun alkhairi".

Mamaki ne ya kama Momy sosai oh wato Maryam zuwa tai nan d'in dan Ahmad ya ganta ya aureta bayan shi yana da wacce yake so kuma koba haka bama tasan Ahmad bazai aureta ba koda ace bashi da wacce yake son balle yana da za'bin ransa ta dad'e da fahimtar Maryam tana da halin da Ahmad baya so ita kuma tace abinda mutum ya nuna mata baya so shi zatai masa shiyasa tun farko basa shiri da Ahmad ko kad'an danya tsani raini baya zana inuwa d'aya da fitsararre mara jin magana................

Dawo da ita daga duniyar tunanin data fad'a Mama tai tana cewa "Hello Aunty Hauwa kina jina"? Kai Momy ta jinjina tana cewa "Eh ina jinki meya faru kuma bayan hakan naji wannan me dame ta fad'a miki"? Haushi ne ya sake rufe Mama a hasale tace "kuma kina jina Aunty amma kikai shiru bayan na fad'a miki dalilin zuwan Maryam d'in zaki ce meya faru wato saboda laifin Ahmad ne shiyasa bakya so na fad'a"?.

"Ok rashin kunya zaki min kenan'? Momy ta fad'a ranta a 'bace.

"Niba rashin kunya zanyi miki ba tambayar taki ce ta 6ata min rai sabida na fad'a miki ga dalili amma naji ko saurara ta bakya yi".

"Wanne dalilin ne"?.

"Nace miki Maryam tana son Ahmad ne dalilin zuwan ta gidan shine tana so ya ganta ya kamu da sonta ya aureta a qara karfin zumunci wannan shine abinda ya kawota gidan ba komai ba".

"Ita Maryam dince take son Ahmad"? Momy ta tambaya tana jiran taji amsa cikin 'kwarin gwiwa Mama tace "kwarai kuwa shine abinda yasa ta dawo nan domin suyi magana dashi idan ya amince ya aureta domin ta dad'e tana sonshi tana so yace yana sonta tunda shi ya'ki fad'a shiyasa ita tazo ta fad'a masa ta dad'e tana sonsa ba abun kunya bane dan mace tace tana son namiji yin hakan kwalliya ce" jin abinda Mama tace yasa Momy tai shiru tasan abun da kamar wuya amma saboda kar tace itace bata so ko taiwa abun fahimtar daba haka bane sai tace.

"Ok shikenan Halima karki damu indai haka ne zan samu Ahmad d'in nayi masa magana duk yadda yace zakiji na kiraki" jin abinda Momy tace yasa Mama sauke numfashi cikin jin dad'i tace "yauwa Aunty yanzu naji magana shikenan nagode saina jiki ina jiranki dan Allah karki manta"?.

"Ok bazan manta ba sai anjima" Momy ta fad'a tana cire wayar ta ajeta a gefenta kenan taji taku da sauri ta waiga ganin Ahmad a tsaye ya mugun had'e rai yasa ta d'an rufe ido ta bud'e tasan yaji komai tunda batasan lokacin tsayuwarsa a gurin ba shima a nasa 6angaren hakan take duk maganar da Mama take yaji kowacce kalma d'aya bayan d'aya kallonsa sosai Momy tai taga yakai ma'kura wajen 6acin rai murya a tausashe irin na ambato tsakanin d'a da uwa tace "Ahmad yaka tsaya anan shigo mana zonan dama magana nake so muyi dakai yanzu kuma sai gaka ka shigo karaso gurina" huci ya fitar yana cire hannunsa daga cikin aljihun wandonsa ya kalli kofar part din su Khairat yasan Maryam tana ciki ji yake kamar ya shiga yai mata d'an banzan dukan da a azaba zatasa tace ta tsane shi daga soyayyar da take masa tsabar rainin hankali shine zai sota ya zauna da ita aiko baida wacce yake so bazai amincewa Maryam ya yarda ta zama uwar 'ya'yansa ba balle yana da wacce yake jinta kamar ransa yake mafarkinta a koda yaushe wacce ya d'auketa rayuwar sace ya tabbata without her, his life will difficulty zai shiga tashin hankali wanda baya fatan zuwansa..........................

"Ahmad zonan" yaji muryar Momy ta katse masa tunani dawo da hankalinsa kanta yai yana kallonta kamar yadda itama ta 'kureshi da kallo 'karasowa yai yana zama kusa da ita muryarsa ba normal yadda ta sanshi ba yace.

"Barka da safiya Momy fatan kin tashi lafiya"?.
K'ara kallonsa tai karo na uku tana d'an girgiza kai tare da sakin murmushi tace "lafiya kalau na tashi Ahmad dama yanzu muke magana da Halima bansani ba ko tun daga farkon maganar tamu ka tara ko kuma karshe ne banace ba fatan kaji maganar da mukai da ita akan zuwan Maryam dukda nasan kai kana da wacce kake so batun yanzu ba amma sakamakon kar nace mata a'a taga kamar nice bana son abun shiyasa nace ta bari sai nayi maka magana tunda Allah yasa kaji komai yanzu me kace za'bi ya rage naka nasan daga baby baka marmarin qara wata saidai kai mijin mace hud'u ne idan kaga kanada bu'katar 'kari sai kayi magana nasan me zance mata koba yanxu ba zuwa gaba saika aureta hakan yayi maka"? Kaiya girgiza batare daya d'ago ba yace.

"Momy kece kika haifeni kinfi kowa sanin halina kinsan abinda zan aika da wanda bazan iya aikatawa ba koda ace bani da wacce nake so bazan iya auren Maryam na zauna da ita ba badan tai min wani abu ko tana da wani mugun hali ba a'a kawai nidai batai min ba matsayin mata wannan shine idan Mama ta sake kiraki ki fad'a mata sa'ko daga ni nace a'a indai danni Maryam tazo gidan nan to takoma gidansu karta 6ata lokacinta domin bazan ta'ba sauraron taba karta yaudari kanta niba wanda za'aiwa wargi bane banyi kama da masu yin wasa ba idan na fad'i magana gaskiya ne abinda yake fitowa tun daga 'kasan zuciyata na fad'a Maryam cousin d'ina ce bai kamata ace wani sa6ani ya shigo tsakanin mu wanda baza'a ji babu dad'i ba sannan ni bazanyi abinda zai takura niba ki fad'a mata haka" tunda ya fara magana Momy ke jinjina kai dama tasan amsar kenan kuma ta tabbata yanxu idan ta kira Mama ta fad'a mata bazata yarda ba gani zatai wannan maganar ba Ahmad neya fad'a ba itace ta zauna ta shirya zata so ace Ahmad d'in zaije da kansa har gida yaiwa Maman bayani da kansa yadda zatasan matakin da suke saidai idan ma zata jarraba kiran nata ta fad'a mata yadda sukai dashi koda bazata yarda ba numfashi ta fitar tana kallon sa tace.

"Na fahimta Ahmad dama nasan haka zai faru to amma saboda kar nacewa Halima kana da wacce kake so taga kamar nice bana son had'in da take bu'kata na aure tsakaninka da Maryam shiyasa na fad'a maka kaga na fita daga zarginta yanxu ina da babbar hujjar da zanyi mata bayani idan bata fahimce niba zakaje har gida kai da ita ka fad'a mata komai"?.

"Zanyi hakan Momy ina Khairat suke"?.

"Suna part d'in Maminsu yanxu basa kwana anan".

"Ok" kawai yace yana mi'kewa ya fita shiru Momy tai farko har tayi tunanin kiran Mama ta fad'a mata a take sai kuma tunani yazo mata idan ta kirata yanzun nan ta fad'a mata tofa zatace bata wani fad'awa Ahmad ba itace bata so shiyasa ta yanke hukunci da kanta tunanin hakan yasa ta mayar wayar ta ajiye ta fasa kiran nata gabadaya bari Ahmad ya sake shigowa ta fad'a masa yaje gidan Maman da kansa ya fad'a mata abinda ke ransa zaifi zaman lafiya kuma itama Momyn zata fita.

A wunin ranar su Khairat basu le'ko part d'in Momy ko sau d'aya ba koda suka dawo daga school part d'in Mami suka sake zarcewa acan sukai komai sai dare shima Mamin ce tace musu su koma part d'in Momy su kwana basu nuna mata dalilin dawowrsu nan d'in ba kawai da tace su koma can ba musu suka tashi suka tafi a bedroom suka samu Maryam tana waya sai dariya take tana doka qafa babu wanda yai magana a cikinsu da sukai mata sallama bata amsa ba sai wani irin ba'kin kallon qasan ido data aikowa Baby kamar ta tashi ta rufeta da duka ganin basu sake bi takanta ba sun kwanta yasa ta sau'ke waya tana kallon dukkan su biyun tace.

"Meye hakan wannan da'ki'kancin fa malamai ku tashi min anan" Maryam ta fad'a a masife dama a turare take dasu yaye bargo Khairat tai tana cewa "me akai miki daga shigowar mu kika fara neman mutane da fitina"?.

"Au abinda zakice kenan saboda wulakanci"?.

"Toya kike so nace idan bance miki haka ba"?.

Tsaki Maryam taja tana cewa "idan ba hauka ba taya zamu kwana mu uku akan gado d'aya kamar a garin mahaukata nifa a gidan mu ko mu biyu bama kwana ni kad'ai ce a bedroom d'ina ban saba da rayuwar 'kunci ba fatan kun gane"? jin abinda tace yasa Khairat tashi zaune tana cewa "me kike nufi"? Da qafa Maryam ta ta'bo Baby tana cewa "ga wacce nake so ta tashi tabar nan ta koma nasu part d'in ta kwana domin bata isa na kwanta tare da ita a gado d'aya ba" kai Khairat ta girgiza daidai Baby ta tashi zaune ta sauka akan gadon tana aje bargon ta kalli Maryam data had'e fuska tace.

"Dama nasan karshen zancen dan ni kikace haka sabida ni kike wannan maganar kwantar da hankalinki ni ba'a tashin hankali dani ga bedroom da gado nan ki kwanta kiyi barcinki Allah ya tashe mu lafiya" Baby ta fad'a tana shirin fita Khairat tace "Baby karki fita dawo mu kwana" kai Baby ta girgiza tana cewa "a'a Aunty Khairat karki damu kiyi kwanciyarki saida safe matsalarta nice kuma na fita Allah ya kaimu safiya muna tare ai" ganin da gaske fita zatai yasa Khairat mi'kewa tana kallon Maryam tace "yanxu tsakaninki da Allah ke a ganinki kin kyauta duk shariya da karar da Baby take nuna miki saikin kaita bango tun tana ganin girmanki kisa ta daina gani"? Ta'be baki Maryam tai tana kwanciya tace.

"Ta daina ganin girman nawa man waya damu itace take wahala bani ba kafinta ana ganin girmana sannan bayanta za'a samu masu ganin girmana Kinga ko aitayi ta banza idan tace zata kawo min raini kuma nayi mata shegen duka ba ruwana da gidansu nazo wallahi 6al6alla mata ga6o6i zanyi kuma na 6alla banza".

"A ganinki kenan amma ba haka bane idan tsautsayi yasa kika ta'ba Baby wallahi kinji rantsuwa ko saidai kibar gidan nan jikinki a kumbure domin ya Ahmad bazai 'kyale kiba" ta'be baki Maryam tai tana jan tsaki tace "waye kuma Ähmäd a ina yake aiko wallahi kodan abinda kika fad'a saina daketa saboda Naga irin mataki da kike fad'ar zai d'auka".

"Ok tunda har marmari kike ki gwada dukan nata zakiga abinda zai biyo baya Nina barki lafiya saida safe" Khairat ta fad'a tana ficewa da harara Maryam ta rakata tana cewa "ku jira shigowa gidan nan matsayin matar Ahmad d'in saina gasa muku gyad'a a hannu saikun raina kanku a hannuna takurar da yake muku yanzu nafila ce idan na shigo ruwa ma bazaku iya shaba a gidan nan kuma zaku gani" tana rufe baki Khairat ta le'ko tana cewa "bakinki ya fad'i a 'kasa aiba tafiya nayi ba dama na tsaya naji me zakice shine kike jawo mana mugun alkaba'i ko saidai ya koma kanki indai dan ki haddasa fitina kike burin shigo mana gida insha Allahu bazaki auri ya Ahmad ba har abada" tana fad'in haka ta ja kofar da karfi gamm ta rufeta har saida Maryam ta toshe kunne tana cewa "humm Khairat kenan naki wasa ne yarinya ki zuba ido a yayin dazan shigo saiki hana wallahi kodan ku biyun nan saina auri Ahmad naci uwarku son raina muje zuwa koni koku" komawa tai ta kwanta tana sake gyara kwanciyarta taci gaba da maganganu daga wannan tace wancan ita kad'ai ba kowa balle wadanda take yi dansu tace suna jinta.

Baby tana bedroom a kwance taji an turo kofa da farko tayi tunanin Mami ce saida taga Khairat ta shigo fuska babu walwala ta karaso tana zama ta kalli Baby wacce itama take kallonta da mamaki tace "Aunty Khairat ya haka meyasa kema kika fito da kin tsaya kun kwana tare"? Kai Khairat ta girgiza tana cewa "haba Baby akan me zakice min haka dawa nake kwana da badake bane to kuma dan wata tazo sai yazama dole mu raba gurin kwanciya ai indai kikaga mun daina kwana tare to ki tabbata daya daga cikin mune yai aure koni koke" numfashi Baby ta sau'ke tana cewa.

"Amma aida nine bata son kwanan ba dake ba shiyasa na taho na bata guri domin bana son yawan hayaniya".

"Akan me zan tsaya mu kwana tareda da ita nake kwana ba dake bane zuwanta kuma sai yasa na daina kwana dake"?.

"Eh za'a iyayin hakan kafin ta tafi ba'ko ra6a ne duk irin dad'ewar da zaiyi wata rana dole saiya tafi shiyasa bana so ace dan tazo zama nadan lokaci abinda bakai ya kawo ba na laifi dana ganin dama abi a tashi hankula har manya su shiga ciki dan haka kawai ki 'kyale Aunty Khairat dan Allah ki daina biye mata kuna yi na tabbata idan tai miki kikai mata shiru shikenan gobe bazata qara ba" kai Khairat ta d'aga tana kallon baby da murmushi tace "kinsan me baby? Wallahi shiyasa kike burgeni saboda sau'kin kanki babu ruwanki kayanki ma bai rufe miki ido ba balle kisa rai akan na wani na gane nima naki salon zan d'auka zanyi amfani da abinda kikace min bazan sake biye mata ba indai ba maganar arziki ko maganar zumunci zamuyi ba".

"yauwa Aunty Khairat haka nake so naji wallahi har kinsa naji dad'i a raina kinga yanxu kowa ya huta bazata taga mun takura mata ba muma bamu shiga safgarta ba".

"Eh hakan zamuyi harta gama operation d'inta ta koma babu me sake shiga safgarta indai ba maganar arziki za'ai ba".

"Operation d'in me tazo yi anan gidan kuma"? Baby ta tambaya da mamaki "hum operation take man idan ba haka ba meta zoyi ko d'agawa mutane hankali ni banga abun damuwa anan ba amma tunda haka ta za'ba shikenan dai" Khairat ta fad'a tana hawa gadon kusa da Baby ta kwanta tana jan bargo babu wanda ya sake magana har barci ya d'auke su.

Washe gari dan kar Mami taga cewa ba'a part d'in Momy suka kwana ba tayi musu fad'a tun asuba suna idar da sallah suka fita zuwa part d'in Momy sukai zamansu sukai azkar har gari yayi haske tar sannan suka tashi suka koma part d'in Mami suka gaida ita sun dad'e kafin suka dawo sashin Momy da suka shigo bata nan dinning suka wuce kowa tai serving abinda take so ko fara ci basuyi ba Maryam ta karaso gurin ti'kas-ti'kas tana shan 'kamshi tazo ta zauna tare da d'ora 'kafa d'aya kan d'aya tana kallon Baby tace.

"Ke yi serving d'ina".

Kamar bada ita take ba haka Baby ta manna mata ko d'agowa batai ba balle tasa ran zatai abinda tace din kai Maryam ta jinjina tana mayar da kallonta kan Khairat tace "ki sakata tai serving d'ina tunda ni ta raina ni ban isa da ita ba" mamaki ne ya kama Khairat har batasan lokacin da tace "lallai Maryam da wargi kike sannunki da kokari Babyn ce zatai serving d'inki ko kuma bayi masu hakkin kula da hakan kike magana"? Kafad'a Maryam ta d'aga tana cewa "wadanne irin bayi kuma bayan ga babbar baiwa a gabana da ita Babyn nake ko tafi 'karfin nasata aikin ne"? Jin abinda Maryam ta fad'a yasa Khairat tai dariya tana cewa "taya zan baki amsa amma ido ba mudu ba yasan kima ki kalli Babyn sosai idan tayi miki kama da wacce aikin serving ya dace da ita sai tayi miki" kallon tsaf Maryam taiwa Baby tana cewa "ta dace d'ari bisa d'ari domin batai min kama da kowa ba sai wula'kantacciya 'kas'kantacciya yanxu kin gane"? Ta tambaya tana qure Babyn da kallo taga yanayinta amma ga mamakinta sai taga ko karasa kallonta Baby batai ba kamar bata mayar da ita mutum ba ji tayi takaicin shariyar datai ya kamata a fusace ta janye plate d'in dake gaban Babyn tana cewa.

"Sai kiyi serving d'in wani kici amma wannan dai ya zama haramiyarki" ta fad'a tana d'aukar wani spoon d'in ta fara ci tsananin mamaki ne ya kama baby wato tsabar neman masifa bata kulatan ba amma bazata barta ba saitai abinda zata tanka mata humm yau kuwa zata gwada mata man nin hauka bazata koda nuna ta damu ba sharewa babay tai tana tashi ta dau'ki wani plate d'in tai sabon serving tana gamawa ko komawa ta zauna batai ba
End Ads