ganin wacce ke zaune a parlor yasa lokaci guda yaji numfashinsa na neman ficewa daga jikinsa hankali tashe ya karasa gumi na tsastsafo masa na tsantsan tashin hankali da rashin gaskiya yace "Mah kece ko ido nane yake ganin kamar ked'in ce dama kinsan gidan da nake ne sannu da zuwa" hakan ma da'kyar ya iya fad'a tsabar watsattsan kallon da yaga tana yi masa jiki a sanyaye ya karaso yana dur'kusawa a gabanta ya sunkuyar dakai domin baisan me zaiyi kota Ina zai fara ba yasan wace mahaifiyarsa mace ce mafad'aciya ganin yadda Sabit yai da kuma sunan daya kira matar yasa Nadiya ta bud'e baki tana shirin magana ba zato taga matar ta d'auke fuskar Sabit da maruka a wanda a firgice Nadiya ta ri'ke nata kuncin kamar ita aka mara idonta kuwa kamar zai fito waje ya fad'o kasa tsabar yadda ta zaro shi batare da tasan tayi hakan ba sai matar da take kallo a firgice lokaci guda tsoro ya rufeta..............
Da yatsa Mah ta nunata tana cewa "ke yar matsiyata na dawo kanki uban wa yasa ki aure min d'a kinsan yadda na tsani had'a jini da wanda ba yarena ba dama dana hana Sabit ya aurenki shine daya gama school ya dawo ya aureki yai min karyar yana Cotonou hummm yau kuwa zan nuna miki kuskuren auren da uwar miji bataso akayi saina gwada miki rashin imani a gidan nan wato Sabit harda uwar 'karya ka siya anan itace ta shige maka gaba akai auren matsayina humm ka za'bi wata tai maka uwa ta maye gurbina saboda ni bana so yanxu fad'a min a ina matar take naje naci ubanta na had'ata da hukuma su hukunta min ita irinsu ne masu bata al-umma ka sayeta da kudi tayi maka aure da yake tsinanniya ce ke kuma yanxu zakici ubanki Sabit saiya sakeki".
Tunda ta fara magana jikin Nadiya yake rawa da kakkarwar tsoro jin karshen maganar ta yasa ta d'ora hannu aka tana fashewa da kuka yanxu kam idan ta fahimta duk abinda ake wannan itace asalin mahaifiyar Sabit sunzo ne daga Lagos batasan yayi aure ba matar daya d'auka anan kud'i ya bata taje musu matsayin itace mahaifiyar sa ta shiga uku da tasan Sabit bashi da mahaifa a kusa wallahi bazata ta'ba auren saba yace mata daga Lagos d'in suka dawo nan Kuma itama wancan matar karyar datai Mata kenan tace sun dawo nan da kasuwanci ne kuka take sosai tana yarfa hannu saboda tasan yanxu ta shiga tarko da sauri ta dur'kusa a inda take tana cewa.
"Dan Allah kiyi hakuri madam wallahi bansan cewa matar daya ara anan ba mahaifiyar sabace wata mata ya nuna min itace ta wuce masa gaba akai komai ni bai fad'a min shi d'an Lagos bane yace min sun dawo nan da zama shida mahaifiyar sa ne shiyasa ma na aureshi" kamar Mah batasan komai ba ta kalli Sabit wanda ya sunkuyar dakai tana cewa "au Sabit harda uwar karya ka saya saboda kana son ka auri hausa"? ta tambaye shi tana d'aga hannunwanta duka biyun sama ta d'amesu ta zuba masa duka a baya ganin yadda Mah take dukan Sabit yasa Nadiya ta sake susucewa to d'anta ma take masa irin wannan dukan inaga ita kuma watakil kasheta zasuyi.............
Bata gama tunani ba taji Mah tace "me kuka tsaya kallo ina dukan Sabit kun zuba min ido ku daka min ita yau sai jikinsu yayi tsami sannan ya saketa dan ubanta "Mah tana rufe baki su Niseh suka rufu akan Nadiya suka fara sambad'arta Abidah shigowar ta kenan ganin yadda suke dukan Nadiyan yasa da gudu ta karaso tana fincike Naomi tace "mitsiyata kashe min 'yar uwa zakuyi ubanku ne ya jawoku gidan tsinannu asararrun karnuka" Abidah ta fad'a itama tana rufe Naomi dake tsaye da duka ganin haka yasa Mah ta taso ta shiga cikinsu Niseh suka hau musu du'ka su uku tuni suka fara ihun neman taimako Nadiya sai kiran Sabit yazo ya taimake ta take yana zaune yana kallo baida ikon koda magana ne balle ya ceceta saida sukai musu duka son ransu musamman Nadiya sunfi dukanta akan Abidah d'agowa mah tayi tana huci ta kalli Sabit tana cewa "Kai Kuma zaka saketa ne ko saina dawo kanka"? Kaiya girgiza da sauri ya kalli Nadiya wacce ke kwance a kasa tana kuka yace.
"Dan Allah Nadiya kiyi hakuri 6oye miki ainishin mahaifana danayi ba ina nufin yaudararki kona cutar dake bane son da nake miki neya jawo haka bansan waye ya fad'awa mah tazo nan ta sameni ba dan Allah ki yafe min wallahi ina sonki amma babu yadda zanyi mah bazata barmu mu zauna ba............
"Dan ubanka Sabit bayani nace ka zauna kayi mata ai tasan ba yaudararta kayi ba tunda ka aureta nace ka saketa ko saina karasa kasheta daka gane" ta fad'a tana take 'kafar Nadiya 'karar azaba ta saki wanda Sabit kuma ya saki ihu ganin tana neman karyawa Nadiyan 'kafa yace "please Mah dan Allah...........
"Sabit zanci ubaka fa ka rufe min baki nace ka saketa kai nake jira zamu tafi"? Kaiya girgiza wanda ganin abinda yai yasa Mah ta kawo masa mummunan duka da sauri ya matsa baya cikin tsawa tace "Sabit Sabit kasan ni fa kasanni fa ka guji fushina walay zan kashe kafa kasanni ka saketa nace" jikin Sabit yana rawa ya kalli Nadiya wacce ke girgiza masa kai alamar karya ce ya saketa shima kan ya girgiza mata yana cewa.
"Kiyi ha'kuri Nadiya na sake ki" yana fad'in haka Nadiya ta fasa 'kara tana d'ora hannu aka ta kuma fashewa da sabon kuka mah dake tsaye harara ta sakar mata tana cewa "ban gamsu ba Sabit ba saki d'aya nake soba saki uku zakai mata bazaka sake dawowa arewaci ba har abada muna komawa zaka tafi London kaci gaba da karatu acan idan ka dawo saika nemi yarenka ka aura kayi mata saki uku inaji babu maganar aure tsakanin ku agaba" babu yadda Sabit ya iya haka yai mata saki uku mah ta saka ya d'auko takarda da biro ya rubuta mata duk abinda yasan kayansa ne a gidan ya tattare tas ta sakashi gaba yana kallon Nadiya yana zubar da hawaye itama haka tana mi'ka masa hannu ta kasa tashi baida damar daya isa dosar inda takema balle ya ta'ba ta suka fice daga gidan ihu Nadiya taita kurmawa kamar muryarta zai fashe Abidah data mi'ke da'kyar gefen fuskarta harya fara kumbura da bakinta da'kyar taja 'kafa taje inda Nadiyan take ta d'agota tana cewa "amma dai Allah ya tsinewa wannan matar Allah yasa baza suje gida lafiya ba kiga yadda ta fasa miki goshi"? Nadiya dai batai magana ba sai kuka da take a hakan kowa tana jan'kafa suka fita waje motar Abidah tana can wajen gate d'in saboda bada ita ta shigo ba me gadi yana zaune yana kallonsu suka fita kaiya girgiza yana sakin murmushi domin jiyan nan ta fito ta tsiyata shi saboda Seemah ta kawo masa abincin Sabit bata sani ba zagi harda na 'kyama ashe itama washe gari daula zata 'kare a koma gidan innah.
Ba gida suka wuce daga Nan ba saida suka bi ta chemist akaiwa Nadiya bandage ita kuma Abidah aka bata magani saidai yadda Nadiya take jin ciwo a cikin 'kafarta tasan da matsala amma ta bari suje gida tukuna sai a kira mata likita har gida saboda wani irin zazzafan zazza'bi ne ya rufeta humm tashin hankali wanda ba'a saka masa rana Hajiya Khubura har tafisu ihu da kuka lokacin data gansu da kuma bayanin da Abidah tai mata ga takardar saki reras har uku sannan ta kad'a Sabit sun tafi yankinsu ga zazza'bi da kuka Nadiya ta dameta lokaci guda taji hawan jininta yana neman tashi da'kyar ta lalla6a bedroom d'inta tasha magani sannan ta samu damar kiran likita yazo har gida ya duba Abidah da Nadiyan saidai yace Nadiya ta samu targad'e a 'kafarta da kuma gocewar 'kashi dole saidai a kaita asibiti a gyara mata gara Abidan ita iya kumburi ne Nadiyan sukafi duka saboda gurinta suka zo, a take sukai asibiti da Nadiya akai mata gyaran dole Hajiya Khubura ta zauna acan Abidah kuma ta dawo gida tai musu abinci ta koma...............
HUMM MUJE ZUWA ✍️MRS ÄL'ÄMËËÑ ÄHMÄD ÇË.
TYPING📲Sun, Ap/6st/25 10:00am
✍️Yusrah Musa Abubakar Gimbah
👑 ROYALTY 👑
In the name of Allah the must benefits and the must merciful ALLAH THE MOST HIGH DOESN'T SLEEP ALLAH THE MOST HIGH IS PURE HE ACCEPT ONLY WHAT IS PURE.
Manzon Allah SAW
May the blessings and the peace of Allah be upon you ya rasulullah muna sonka fiye darai da iyaye da dukiya you have no limits ya Annabi💓.
💔ZUCIYAR ALIYU CE💔
NEXT BOOK D'INA KENAN ZUCIYAR ALIYU CE ITAFA YARINYAR ZUCIYAR ALIYU CE ME KUKE TUNANI FANS KU KASANCE TARE DANI AKWAI AIKI A GABA INSHA ALLAHU ZUCIYAR ALIYU CE ZAI FARA SAUKA MUKU DA IZININ ALLAH DANA KAMMALA WANNAN.
Masu bu'katar littafai na kofa a bud'e take akwai free akwai paid duka wanda mutum yake bu'kata zai samu amma fa bana tura free sai an sayi paid book d'ina ehe karma mutum yace na tura masa alakoro😂.
Free book.
Yarima abdul-maleek
D'an millionaire
Husnah ko Badiyat
Me kamar sarki book 1
Minister Ashraf book 1
Safreeyyah book 2
Paid book
Me kamar sarki book 2 #300
Minister Ashraf book 2 #300
Safreeyyah book 2 #400
Ga duk mai bu'kata zaka iya yi min magana ta WhatsApp number na +234 816 098 3083 Yusrah Musa Abubakar ina maraba da kowa.
Nifa I have no girman kai if you fushi dani to wallh you are just 6atawa kan/ki lokaci 🤣 haka nake bani da haushin kowa kuma kowa nawa ne.
Bismilllahir Rahmanur Rahim 📿
16~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Nadiminah
@YUSRAHMS CE
Page 31 & 32
Abun duniya ya damu Mama ganin idan Maryam tai kiran Ahmad a waya baya d'agawa tunda ya tafi bata ta'ba kiransa ya d'aga ba wani lokacin ma idan ta dameshi da kira kashe wayar yake ko yasata a silent sannan ta WhatsApp ma idan tai masa magana bazaiyi mata reply ba harya sauka takaici ne ya ishi Mama ganin yadda Maryam ta shiga damuwar rashin kulawar da Ahmad yake nuna mata dan haka taje har gida ta karantawa wata 'kawarta Hajiya Habiba ga abinda yake faruwa dan Allah ko tasan yadda za'ai hankalin Ahmad ya karkato kan Maryam yaji duk duniya duk cikin yan mata babu wacce tai masa sai ita a take Hajiya Habiba tace tabbas da akwai wacce zatai mata wannan aikin da zarar tayi baza'ai sati ba sai hankalinsa ya dawo kanta bazai samu nutsuwa ba sai yaji muryarta tasha kai mutane ana yi musu magani kuma suna dacewa jin wannan bayani ya faranta ran Mama ta take ta kira Maryam tana school tace ta baro makarantar tazo zasu je anguwa tana gidan 'kawarta tazo nan ta sameta, suna zaune Maryam ta shigo jikin Mama har rawa yake suka fita ta ciri kud'i suka tafi gidan Hajiya me bada maganin farin jini.
Layi kuwa suka samu sosai kamar wanda sukaje ganin likita haka mata ke tururuwa a gidan kuma zamansu ma sama da mutum goma sun sake shigowa kusan wuni sukai kafin su samu layi yazo kansu suka shiga d'akin da matar take tana zaune a cikin magunguna kanta ko d'an kwali babu tayi wani irin hargitsastsan kitso ta zane fuskarta da ba'ki sai zare ido take yi zama sukai Mama dai sai kallon ikon Allah take ganin yadda Hajiya Habiba ta ware suke zance harda dariya kodan ba abun mamaki bane tunda tace sun saba anan take kar'bawa yaranta magani kafin suyi aure da bayan sunyi auren bayanin abinda ke tafe dasu Habiba tai mata sannan ta fad'a mata maganin farin jini suke bu'kata, kallon Maryam me maganin tai tana jinjina kai tace.
"Kina sonshi sosai ba? Kuma kina so ki aureshi haka ne"? Tun kafin Maryam tai magana Mama data fita za'kewa tace "haka ne wallahi daidai ne abinda kika fad'a gaskiya ne" hannu ta d'aga tana cewa "ba dake nake ba wacce aka zo dan ita nake tambaya" shiru Mama tai tana kallon Maryam da ta'ki magana da ido ta nuna mata ta bata amsa murmushi Maryam tai tana cewa "eh haka ne abinda kika fad'a akansa gaskiya ne amma shi kwata-kwata hankalinsa baya kaina bai damu dani ba ko kiransa nayi a waya baya d'agawa idan yaga zan takura masa da kiran ma saiya karshe wayarsa wannan shine damuwa ta indai da yadda za'ai ya soni ya kaunace ni fiye da yadda yake son kansa ya susuce a kaina ya manta inda yake ya daina samun nutsuwa da zaman lafiya idan bai ganni ba ko yaji muryata" Maryam na rufe baki Mama tace.
"Farko fara a Bata maganin farin jini idan har tana da farin jini duk wannan abun bazai samu ba tayi masa kwarjini kawai dan Allah a taimaka a bamu a fad'i abun sadaka nawa ne"? Mama ta fad'a tana kokarin zuge zip d'in jakarta.
"Bana yankewa ko nawa ne kawai aje min ake ko naira biyar ce itace karamin kud'i" cewar me magani tana 'kure Maryam da kallo kamar me tunanin wani abu kaita jinjina tana d'agowa ta kalli Mama sai kuma tai murmushi tana sake mayar da hankalinta kan Maryam tace "amma fa wannan sai kunyi da gaske domin gaskiya yana da zazzafar zuciya sannan ko kad'an bata gabansa bata ransa babu ruwansa da ita har gobe haka abun amma tunda kunzo nan kusa a ranku ta faru ta 'kare bashi daja indai na fara yi muku aiki a kansa aure kam saiya aureta dolensa".
Kai Hajiya Habiba ta jinjina dakyau cikin yardar da taiwa matar tace "kwarai wannan maganar taki haka take a zaune gaskiya ne ko bayaso dole ya amsa Kira indai kika kirashi" mayar da hankalinta kan Mama tai tana cewa "kawata karki damu kinzo gurin da za'a kar'be ki hannu biyu kuma a share miki hawayen ki dan haka karki tsaya sanya ki bata abin sadaka yadda kika ji ranki yaga damar bayarwar ita ba yanke kud'i take ba amma ki sani tana yanke damuwar mutum indai anzo gurinta" jin abinda Hajiya Habiba tace yasa Mama bud'e jakar ta saka hannun ta dam'ko kud'i dubu hamsin ta aje tana cewa "biyan bu'kata yafi dogon buri indai zatai farin jini tai kwarjini bani da matsala ko nawa ne zan kashe daga kan dubu d'aya zuwa million d'ari na tabbata idan na samu ya aureta kud'in dana 6atar zasu dawo saboda ina fad'a miki ranki ya dad'e me magani yaron da nake so ta aura millionaire ne gashi Kuma jinin sarauta kyau da diri iya d'aukar wanka gashi soja 'kak'karfan gaske jarumi ma kuwa idan na tsaya kwatanta miki shi zamu iya kwana anan ban gama ba saidai na ta'kaita ta ko'ina Ähmäd yayi wallahi burina kawai naga mun samo kanshi".
Kai me magani ta jinjina tana cewa "karki damu Hajiya indai batun farin jini ne anzo daidai wajen 'yarki ta samu kisa a ranki kamar ta auri wannan saurayin wanda kike so ta aura ne wuya ta fara indai tabi yadda nace mata bisa 'ka'ida zata dace".
Cikin tsananin farin ciki Mama tai murmushi tana sau'ke daddad'an numfashi tace "yauwa nagode sosai idan zamu dawo mene abun sadakar sannan ya ake aikin"?.
"Zan fad'a muku abun sadakar da zaku zo dashi a gaba amma ba yanzu ba sai shi saurayin ya dawo da zarar kun samu labarin dawowarsa kar kuyi 'kasa a gwiwa ku dawo gareni zan karasa baku babban sirrin da zaku ri'ka yi wannan ta ri'ka wanka dashi yanxu kafin ya dawo wannan kuma ta ri'ka turare yana bin jikinta a hankali ya zagayeta kafin ya dawo ta tsumu sannan idan ya dawo zan bata sirrin wanda zata ri'ka kwalliya dashi indai har shi wannan saurayin ya d'aga ido ya kalleta wallahi tallahi kunji na rantse ko? Saiya susuce ya manta inda kansa yake akanta ya sota fiye da yadda yake son kansa kuma bazai barta ba saiya aureta me kankat kenan".
Jin wannan daddad'an bayani yasa Mama shiga yanayi har tana sauke numfashi me sanyin gaske a hankali ta dafe saitin zuciyarta tana murmushi kafin ta kalli Maryam tana jinjina kai tace "masha Allah haka nake son ji na tabbata yanzu kam dole Ahmad ya shiga tarkon mu ko baya so sannan itama Aunty Hauwan ko itace bata so indai Ahmad d'in ya gani yana so babu yadda zatai dashi dole ta barshi ya aureki" mayar da hankalinta kan me maganin tai tana cewa "yanzu dame zamu dawo idan har shi Ahmad d'in ya dawo"?.
"Idan zaku dawo ku taho min da powder wacce take shafawa a fuska da kwalli wanda zata ri'ka sakawa a cikin idonta dasu zanyi muku maganin daya kalleta zaiga fuskarta tana fitar da haske da annuri powder zata kara mata kyau a idonsa sannan daya ya had'a ido da ita wannan 'kwallin data saka zaiji duk duniya babu wanda yake so yake son aura sai ita sannan zan bata sar'ka wacce zata d'aura wuyanta ita kuma amfaninta idan har ya kalli wannan sar'kar shikenan ta mallakeshi tas ta gama samun kansa ta samu zuciyarshi idan hakan ya faru daga wannan lokacin shikenan labari zai sauya salo zakuga abun mamaki daga gareshi abinda zaiyi akanta baza'a ta'ba tunanin ba zai haukace ne a kanta ya zama mara nutsuwa bayan duk awa biyu zuwa uku idan bai ganta ba kunsan mene hikimar? Da sauri suka girgiza kai a tare Mama harda gyara zama tana sake matsowa kuda me maganin taji yaya meye hikimar cigaba da musu bayani tayi "idan ya kasance baya jin sassauci idan bai ganta ba rashin nutsuwar sa da susucewarsa zaisa mahaifansa su sakashi ya aureta kobai shirya ba kuma koda ace bashi da niyyar hakan a ransa zamu sanya masa dole yabimu yayi abinda muke so zaku iya tafiya kuje da wannan d'in tana wanka da turare kafin dawowarsa saina ganku ku kula sosai a aikin banda mantuwar sharud'a ko sa6a lamba kunji"? mi'kewa sukai Mama na cewa.
"To ranki ya dad'e mun gode sosai da taimakonki garemu sai kin ganmu" kaita d'aga bata sake magana ba har suka fita daga gidan motar