x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 7 - KASUWANCINA

  • 18001 words
  • 21000 words
  • Out of 176000 words

Category: Romance Story +18

Views 139

30 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
ai yarinya ce,shi kuwa Gogan Aayan a zuciyarsa yake Dariyar kwadayi na,kuma sabo da kuruciya a gaban kowa ina mace ko dai bani da hankali ne. na karanta masa ciwon Mahaifiya ta,yaji tausayina kuma lallai yaga mu abin taimako ne,sai yace jirani a gefe bari na sallami sauran,

nan na Mike na koma gefe,Aayan ko kallona bai kara yi ba har Yarima ya gama da mutanen kaf suka tafi ya rage daga ni sai Aayan sai Yarima,yace zo ke,da sauri na karasa gabansu su biyu,yace ina babanki ko ya rasu? Bana so na fada a gaban Aayan wanda ke latsa waya,sai nace Sirri ne sai dai idan zamu koma gefe na fada ma,murmushi ya saki yace to ya Mike ya taso na kara kasa da murya da rada nace bacewa yayi ba a San inda yake ba,kawai ko guduwa yayi wa ya sani,dariya Yarima yayi yace to shike nan ki kawo takaddun asibitin naki mu gani,nace to ai naji ance zaka yi tafiya,no ki jira zamu fita da frnd dina sai mu saukeki ki dauko takardun,a tsorace nace tab wancan masifaffen ne zai yarda,kin sanshi ne?ya tambaya,nace ae na sanshi kullum sai ya mareni idan ya ganni,murmushi yayi yace to ki jira ai motata zaki shiga,murmushin da nayi shi ya tafi da Imaninsa ya tsaya yana kallona,sai can ya dawo hayyacinsa yace ina zuwa ya koma wajen Aayan dake ta faman cika yana batsewa,Yace kai Yarima kasan fa ban son jira wlh zan tafi ka tsaya kuyi hirar,ba class ba komai,Sorry let's go,Aayan da mamaki yaga na shiga Motar Yarima shima cike da takaici ya shiga nasa motar suka ja muka bar gidan cikin zugar motocinsu,sai da aka zo kusa da gidanmu suka tsaya,Yarima yace yarinya yisauri ki dakko mana na gani,ina fita na kwashe da gudu na karasa gida na fada daki na ebo kamar kiftawar Ido na fito da wani gudun kowa ya ganni sai ya tsorata ko wani abu ne ya biyoni,da gudu ina Haki na kawo masa takaddu ya sauke glass kasa ya karba ya gani tabbas da gaske nan ya miko min card dinsa yace ga Number ta na Nigeria dana waje ki kirani kiji,da sauri na daga kai sama,ya zaro Dubu goma ya bani yace gashi ki siyawa marar lfy ko ruwane,godiya nayi na karba, Yarima yace ki daina gudu kinji yarinya ba kyau mace tana gudu,da ladabi nace to na daina ai tsoro naji kar Ku tafi sannan na juya na dau hanyar shiga gidanmu,sai da naje bakin kofar gidanmu zan shiga na juyo baya sai naga Motar Yarima sunyi gaba sai Na Aayan yana kallon inda zan shiga kamar Munafuki muna hada Ido suka figi motarsu fiii suka kara gaba abinsu nima na shige gida.
Still ban gamsu da taimakon Yarima ba sabo da yan siyasa basu da tabbas ayi maka karya ka dauka gaske ne kayi ta jira ana ja ma rai,don haka kwana nayi ina tunanin cewar wanne gida kuma zanje nan take na tuno da wani dan kasuwa Hamshakin me kudi a GRA unguwar su Aayan,har matsuwa nayi gari ya waye na tafi,ga kuma gidan wata Mata nan ma Naji ance tana taimakon Talakawa.
Sannan Zan biya sakateriya ta unguwarmu wajen Kansila Adamu me tallafi ko Allah zai sa ya shigar da sunana cikin masu karbar tallafin Manoma na Gomnati.
Kuma duk a gobe zanje wani Training shima ko zan samu a dauki sunana cikin masu koyon sana'a idan ka gama a baka jari.gaskiya gobe ina da tsare tsare da yawa,don haka kosai ma kadan na soya na barwa su Meenat komai tare da shiryawa yau ba Hijab nasa ba mayafi na yafa nayi kyau yau doguwar rigar material nasa red and green mayafinta green da takalmin robata baki,Ammah nayiwa Sallama ta zuba min addua sannan na fita da addua a bakina.








AsmaBaffa
[1/3, 9:47 AM] Asmabaffa: 🌖🌖🌖🌖
🌖🌖🌖🌖

KASUWANCI NA






16-20





Official





By
AsmaBaffa







JIDDER ZARIA ina godiya kema ga page dinki.

Masu Sharhi kuna kasheni da dadi Allah dai ya saka.







Napep kawai na shiga 8am dai dai ina kofar gidan dan kasuwar nan me kudi dake Unguwar Su Aayan,abin takaici ba irin buga kofar da banyi ba amma ba wanda ya bude min hasalima me gadin ne yazo yace ai sun Dade da tafiya Kasar waje basa rayuwa a nan sai jefi jefi,haka na juya da Niyyar tafiya katsam sai ga yan matan gidan su Aayan su uku sun fito a cikin mota da Alama schl ko wani waje zasu je sunsha wanka da kyau,suna Shan kida,da sauri suka fito daga motar suka zo ba bata lokaci suka fara dukana,ina ihu nima ina ramawa Amma sunfi Karfina,nan take daya ta cire takalminta me tsini ta kwala min a kaina a akasi nan take na zube a Sume wajen na fitar da jini,ba Imani suka koma cikin mota suna murna sun rama abinda nayi musu suka shige mota,ina yashe a kasa ban san inda kaina yake ba,sai 10am Aayan ya fito yau a mota daya zai fita shi ke Driving ma,kawai ya hangoni a kofar gidansu cikin mawuyacin Hali,mamaki ya lullubeshi me ya kawo ni nan da sassafe ko dai Aljana ce ni,a tsorace ya tsaya tare da bude motar ya fito da ruwan roba ya watsa min,nan take na ja numfashi na Mike zaune a firgice ina Dafe goshina wajen da jini ya fita,mikewa tsaye nayi ina Jiri kamar zan fadi na dauki gyalena da kudin Napep dina,na fara tafiya ina Kuka gwanin tausayi,amma marar Imanin ko a jikinsa sai ma tsawa daya buga min yace me ya kawoki nan again da safe,ko kulashi banyi ba naci gaba da kuka na ina tafiya,shuru yayi tare da cewa Yau sai naga inda zata kara zuwa,ya shiga mota.

Yana gani na shiga Napep yana Bina a boye ban sani ba,tuna ninsa gida zanje amma ina sai yaga me Napep ya Parker a gate din wani makeken gida,na biya Napep ya tafi na shiga kwankwasa gida,Aayan dai yana mota yana Shan kallon ikon Allah mutum jini na zuba a jikinsa amma bata lafiyarsa yake ba ta neman Kudi yake.
Security ne yazo yana turanci where are u From? To ni dai Na gane me yake nufi amma bazan iya juya yaren ba sai nace na kakalo karya nace ni yar gudun Hijirace daga wajen Nijar nake,wajen Hajiya nazo a tallafa min Mahaifiyata bata da lfy,lokacin da nace haka Ashe Aayan yana bayana yaji komai harda yiwa Gate man signa yayi shuru,ni kuma ban san yana wajen ba sai nayi karya a akasi,abinda nacewa Frnd dinsa Yarima Bobo daban abinda na fada anan daban,sabo da bana so nayi ta tona sirrin gidanmu shi yasa ni a ganina idan nace yar gudun hijirace mahaifiyata ba lfy Zanfi samun tallafi kuma Ashe Munafuki yazo jin gulma.

Tuni gate man yaja tsaki tare da banke kofa ya rufe,ina juyowa muka hada Ido da Aayan yana mun mugun kallon tsana alamar yaji komai,karya ba kyau yan Uwa mu guji karya kanayi watarana sai asiri ya tonu duk da akwai dalilina na karyar amma ya dace kayi gaskiya a komai idan za a baka a baka don Allah. bai ce komai ba yana gani goshi na yana jini amma yayi tafiyarsa ya shiga mota,nima na siyi pure water na wanke Raunin tare da fuskata sannan na sa gefen gyalena na danne gaban goshin nawa Ina duba agogon robar dake hannuna,
lokacin Training yayi nan na nufi sakateriya inda za ayi,mun taru da uban yawa amma sai me hanya da gata shi ake dauka mu da bamu da hanya sai muka koma yan kallo muna zare Ido,

Ina duba lokaci na shiga wani part can cikin sakateriya nan na fara neman Kansila Adamu me tallafi aiko yana nan na sameshi a Office dinsu na kansiloli,masu son mata suna lashe baki ana kallona wanda kuma basu damu ba kallo ma ban ishesu ba haka na karasa wajen Adamu Kansila wanda yana daga cikin masu son mata,Adamu ko kudin Hotel zaka biya masa shi da mace to ba abinda bazai yi maka ba,kullum rayuwarsa a hotel take da mata,aikinsa kenan a kai mata hotel,ko so kake ka yaudari Adamu Kansila to ka biya masa Hotel ya kai mace ciki.

Ni dai ban sani ba muna ta hira da Adamu ana kallona a karuwarsa har muka jero tare da ketowa ta cikin mutanen dake sakateriyar har bakin titi ya rakoni yana cewa ki kwantar da hankalinki ai tallafi kamar kin samu ki kyale wannan na sana'ar aikin banza ne zan sa ki a me tsoka,ina murna still hannuna yana kan goshina na danne ciwon,Adamu yace me ya sameki nace bigewa nayi wajen shiga mota,yace sannu muje na kaiki Chemist ayi miki dressing,muka jera tare da Adamu Kansila muna hira yana ta murna ya samu Damar hure min kunne,yana wani taku da iyayi shi a dole Kansila me kudi,haka muke tafiya muna ta murmushi kamar saurayi da budurwa ga Adamu akwai wankan shadda gashi matashi dan kyakyawa dashi ba laifi dai,sai kallonmu akeyi,abinda ban sani ba Aayan yana can side din da mota yana tafiya a hankali yana kallon komai nawa da nakeyi don yace sai ya kure karyata bai yarda dani ba.

Yana kallo Adamu ya kaini chemist akayi min Dressing muka fito tare Adamu na kokarin rike min hannu na matsa gefe da sauri shi kuma yana borin kunya,amma duk da haka Adamu yace yaushe zamu hadu,nace ban gane ba,yace akwai maganganu da nake so muyi amma a Hotel zamu fi samun sirri ko? Nan take nace ban gane ba,yace au da nufin ki a banza zan saki a tallafin?ai ban gishiri na baka Manda,nan take bakin ciki ya mamayeni wato duniya baza a taimakeka don Allah ba,yan Iska sunyi yawa kowa sai ya nemi lalata ma rayuwa,ban san sanda naji haushin bata lokacina danayi a wajensa ba na fara masifa shi kanshi Adamu bai San bani da mutunci bani da kunya ba sai yau da nayi masa tatas daga karshe nace Algungumi a haka kamar mutum Ashe mata kake yiwa ciki to baka isa ba in dai hannu ne bazan bari ka taba ba bare kayi min ciki,ni tunanina ai kawai hannu ake rikewa ana yiwa mace ciki,nan na kara boye hannayena cikin mayafi tare da gallawa Adamu Kansila harara nayi gaba abina ina tafiyata a hankali,duk abinda nakeyi Aayan na kallona ban sani ba.Napep na shiga na koma gida nace na fawwalawa Allah na daina fita neman taimakon kowa Allah ya kawo min hhh naji wuya.

Kasuwancina na rike bilhakki da gaskiya domin yanzu har funkaso da miya nakeyi da yamma,shima na kan danyi masa Algus yanda za aci riba me yawa nifa komai nawa sai anyi cuwa cuwa.
Ammah kwana biyu da alama ciwonta kara karfi yakeyi sai addua muyi kuka mu gaji ina ta kiran wayar Yarima bata shiga idan kuma ta shiga ba a dagawa.
Haka na kira dan gidan Commissioner da gudu ya dauka sabo da yayi saving number,dama kwadayinsa ya tashi yana ta neman Number ta amma bata shiga har yana masifa cewar yayi asarar kudinsa ya bani waya Bai Mori kudinsa ba,shima muna fara waya naji yana kawo min maganar iskanci,Hello Baby ya kike?nace lfy idan na kawo maganar maganin Ammah sai naji yace za ayi yan mata karki damu sai ya dauko maganar iskanci me kikeyi yanzu?wanne kaya ne a jikinki? Ai da zan aureki kullum sai na miki sucking sau biyar,ni ba wani ganewa nakeyi ba da na gaji na gano lallai dan iska ne kawai sai na kashe wayar tare da cire layinsa na ballashi sannan na siyi sabo na sa a wayar da ya bani nace naci banza yaro nasa mata kudi naci gaba da neman Yarima Bobo.hh

Ina ta nema amma ba a dagawa sai na tuna abokinsa Aayan ne nan take na shirya da yamma wurin 5 lis na rubuta yar takarda na tafi har gidan su Aayan nasan ba lallai a barni na shiga ba kawai na mikawa wani security nace ya bawa Aayan,yace ai yana gida ma jira ya kai masa abinda yace sai na fada miki,nan ya tafi ciki ni kuma ina daga wajen gate ina faman jira cike da tsoro kar yan matan nan su dakeni ko Aayan ya wulakantani.
15mnt sai gashi ya dawo yace wai ki shiga yan mata,yace ayi miki iso,a tsorace na bi bayan Mutumin mukayi tafiya me uban Nisan gaske kamar zamuje wata unguwar yan aiki kawai muke wucewa har muka isa wani part wanda ban san dashi a cikin gidan ba ya kai karshe wajen tsaruwa har Palo aka shigar dani sanyi da kamshi ya daki hancina har wani bacci nake ji.
Daga shi sai dogon wando ya fito jikinsa ba riga wow...wow Innalillahi ko wace sai taso ta kwanta a kirjin Aayan sabo da tsananin kyansa wayyo,nidai nayi kasa da kai ina jin kunya,cike da Izza ga masifa yace karki kara zuwa gidan nan da zummar kina nemana wajensa kika je can da matsalarku,ni da kika ganni dana taimaka miki gwara na zubar da kudin,kuma sai na baki punishment na aiko min da takarda da kikayi wai na fadawa Yarima Number kaza ta kirasa ya kiraki back ni zaki aika? Look at u Nonsense yaja tsaki a gabana ya zura farar riga ko kunya babu yace follow me,haka na bishi kamar Rakuma,abin haushin duk kusan mutanen gidan kowa ya fito a wannan lokaci duk part in muka zo sai mun iske mutane mata da maza dattijai duk yan uwan Aayan,kowa baki bude yake kallonmu yana gaba ina baya,shi kuwa Gogan ko kallonsu baiyi ba bare su sa ran yasan da zamansu kayi masa magana bashi da mutunci dole sukayi shuru sai kallo da mamaki kucaka kusa da Aayan kuma a part dinsa to karuwa ce? Nan take yan matan da suka dakeni suka ce Mommy wlh akan wannan yarinyar ya dakemu rannan kamar zai kashe mu karuwarsa ce,Abbi dake fitowa shima yace haka zancenku yake yaran nan.
Hajja kakarsu Tsohuwa me ji da kai da kudi tuni labari ya kai kunnenta cewar maganar Abbi gaskiyace cewar Aayan mata yake bi na banza don haka ya Zama dole a dauki mataki a kansa tsatsaura,ranta ya baci amma tace zata yi maganinsa.

Ni dai a tsorace nake har muka karasa wajen mota yace get in the car,ba shiri na fada ciki sabo da na matsu na bar gidan a tsorace nake,Driver ne yaja ina baya,Aayan yana wata motar daban wannan gidan nasa muka shiga,da sauri ya fito nima na fito ina murna Allah yasa ya bani irin abincin ranar nan,ban San me yasa Bana Jin tsoron komai idan ina tare da wannan masifaffen Aayan ba.

A baya na bishi har ciki yace Oya fara gyara gidan nan,da sauri na fara aikin sai da na gyara komai yana sheki duk da cewar dama ba wani dirty kawai mugunta ce,sai da na gama ya sani kneel down hands up na Sha wahala sannan ko ruwa bai bani ba ina kallo yana ta cin abun dadi da lemo haka yace na tashi na bar masa gida,ba shiri na Mike da sauri domin magrib ta kusa ina tsoron Ammah,har zan fita sai na dawo gabansa yana daukan wani abu kamar hanta yana ci yana kora lemo na faki idonsa na dauke ledar zan kwashe da gudu ya sa min kafa nayi muguwar faduwa a kasa,a fusace yayi kaina nasan duka zanci kawai na fara kuka amma ko tausayi yana huci zai mareni sai kuma ya fasa hannuna yaja tare da jefani waje ya banke kofarsa,sai da na ci kuka na sannan na Mike tare da karkabe jiki na,zan fita kenan wani cikin yan aiki yace kiyi hakuri kinji ki daina shiga sabgar Oga wlh baya kaunar mata ki kiyaye ba abinda bazai miki ba kuma bazai taba nadama ba,ke naga yana daga miki kafa ma wlh da wasu ne ko hanyar da yabi basu isa sun bi ta ba,amma ke har yana kyaleki ki shiga gidansa har ya saki aiki,a raina nace ni ina ruwana da zai taimakawa Ammah ai da na yarda ko kullum yankar naman jikina zaiyi ba matsala,haka na fita na bar gidan na koma gida, my
Ammah sai fada take min ta gaji da yawon da nake ranar ta sa min doka tace bazan kara fita ba sai bayan sati biyu ko me za a siyo Meenat ta karba taje ta siyo.

Tun daga Ranar ban kara fita ba ko kofar gida Ammah ta hana,ina zaune da wayata ina game Ma'eesha na kallo Meenat ta tafi cefane kawai sai ga kiran Yarima,jiki na rawa na daga muka gaisa yace gobe na kai Ammah Hospital din an gama biyan komai da komai,sabo da murna ban san sanda Hawaye suka kwararo min ba,na dinga godiya ina masa addua yace ba komai ko mene ake ciki na kirashi a waya,nan take na sanarwa dasu Ammah kowa murna haka ma Meenat da ta dawo harda Rawa,ranar har Nafeela mukayi na godiya ga Allah.
Washe gari da wuri muka shirya tare da daukan Ammah a napep muka tafi asibitin Murtala.
Ba bata lokaci akace Doctor mu yake jira an biya komai da komai yau za ayi wa Ammah gashin kashi tare da sauran aikin da za ayi mata,muna ta addua aka shiga da ita.
Abin da ya bamu mamaki shine abinci lafiyayye na resturant take away tare da ruwan roba carton biyu,tare da lemuka iriri sai fruits da kayan hada tea duk aka dinga shigowa dasu wai inji Boss dinMufeeda,ni kuma tunanina ya bani dama Yarima ne,kuma ina tunanin so na
End Ads