x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 25 - KASUWANCINA

  • 72001 words
  • 75000 words
  • Out of 176000 words

Category: Romance Story +18

Views 143

30 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
ko tunda har almost 1wk bama ciki,yace an gyara komai neat amma ban san me yasa ba ban son komawa amma Kin San Hajja zata takurawa Daddy ne ta fara fushi dashi a kaina,abincin na fara bashi me shegen dadi fried rice tasha hadi da kaji sai fruits da sauran kayan ciye ciye,nace ba matsala karka damu zamu koma ko dan Daddy ba abinda zai faru,kin san ma mene? Nace sai ka fada yace Ameer shike zuga Hajja akan komai na tabbata ma yanzu shine yace sai an dawo daku gidan,nan take na kara Jin tsanar Ameer a raina,Aayan yace Ameer shi ya gaji Hajja a mugunta komai shike tsara mata da Alama ya tsaneki kamar haka nake gani,baki na tabe ta Allah ba tasa ba,ya zaiyi dani ai ni Duwawu ce dole a zauna dani,shegen dan iska,jaraba annamimi da fuska kamar yalo, dariya Aayan dinga yi yanda yaga sai zagin Ameer nakeyi ba ji ba gani yace zagin ma harda Raps Baby ba a tsayawa a huta,dariya nayi nima nace Allah dan iskan yaro sai iyayin jaraba yana gadara da takama sai kace shine Aayan,to ko shine Aayan ma ya isa ya min na kyaleshi,Dariya Aayan yake au nine ma me gadara da iyayi? Nace a'a misali nayi hhh,Allah mutuncinsa daya da yasa nake dan raga masa yanda kuke dan kama dashi kadai kuke kama a gidan nan ni ban san ma ya akayi yayi kyau ba matsiyaci,Nan take naga Aayan ya hade girar sama data kasa kamar zai dakeni,lfy? Allah Baka hakuri in dai akan na zagi dan uwanka ne,Allah dan kuna kama....Tsawa ya buga min rabon da naji irinta har na manta tun farkon haduwarmu dashi,masifa ya fara ni bama kama zaki ce yana da wani kyau baki da hankali idan sonshi kike ba sai kin fada min haka ba ya ja tsaki ya haura saman Bed abinsa.

Firgita nayi kaina ya daure daga ana labari sai fushi kuma ni mene hadina da wani Ameer kuma,mikewa nayi nace kayi hakuri ba haka nake nufi ba ni,da sauri ya Zabura ya Mike hado kayanku a kaiku can sai ki dinga ganin Ameer me kyau,Ka fahimceni bafa nufina kenan ba wlh,mene abin fushi a nan ana lbr to kayi hakuri na furta cikin sanyi na,shekeke ya kalleni yace na rantse yau sai kun koma Family House Hajja bata isa tasa na Canja muku gida ba ra'ayina ne ganin damata ne dan kawai hankalinku ya kwanta muje kawai na rigada na rantse,gani nayi ina lallabashi yana wani kara hawa nace fine mu koma mana mene to, na fice na bar masa Bedroom din naga cikin fushi yake gaba daya yau.

Su Meenat suna shigowa na sanar musu su Kansu basu ji dadi ba,nace su hada mana kaf kayanmu,Meenat tace sis dazu naga wani wlh kamar Abbanmu a mota wani me kama dashi tsaki Naja tare da cewa sai me to dan kin ganshi tunda bai neme mu ba me zamuyi masa,Sis kamar fushi kikeyi lfy? Ko fada kukayi da mijinki? Nan take na fara hawaye ina sanarwa Meenat,Meenat tayi dariya tace Sonki yakeyi kishinki ne,ke komai kiyi fushi ai ba haka akeyi ba,ki daina cewa zaki rama abu ko dole sai kin maida martani kinji mene abin Kuka ai zaku shirya ne,idona na goge muka shirya,Sai ga Aayan ya leko fuska a tamke yace let's go,muka bishi har mota da kayanmu,Driver ne yaja mu har gidan sai da ya tsaya a inda ake siyar da wayoyi ya siyo guda biyu masu kyau da shegiyar tsada ya bani daya ya bawa Meenat daya,sai Meenat ce kadai tayi masa godia ni shuru nayi masa muka je har gidan,Ameer yana so zai fita da mota kawai ya hangoni wani farin ciki ya kamashi Bai San sanda ya tsaya ba ya fake da gaisawa da Aayan,Bro ya kk? Aayan yana fushi kamar zai tsage yace am ok,ya kalleni kawai yace Sis barka da zuwa ko kulashi banyi ba Meenat ce ta amsa,sai da ya kara yi min magana sannan na amsa da kyar ina fitowa da kayanmu,yace Bari na tayaku kaiwa ciki,Aayan yace no need jeka abinka,murmushi ya saki a ransa yana ko banza zan dinga kallonta ina jin dadi na.

Hajja tana sama tana kallonmu sai murna takeyi burinta zai cika,Abbi bakin mugu yana kusa da ita yana tsara mata muggun nufi,matarsa ma haka tare da sauran kannen Abbi,Ameer kuwa ganin na dawo sai ya fasa fita kawai ya koma part dinsu.

Aayan sai fushi yakeyi nima haka aka shigar mana da kayanmu, komai Neat a gidan yasha gyara sai kamshi,muna Hutawa muka wuce bangaren Daddy har Meenat muka kwashi gaisuwa sai murna yake yana jin dadi tare da sa mana albarka,bamu zauna ba muka dawo part dinmu tare dasu muka fada kitchen kamshi ya fara tashi a bargarenmu,sai ga jaraba sun fara shigowa,Sajeeda da Haneefa sunzo harda lekowa kitchen suna tabe baki Sajeeda tace yara ana ta jagwalgwalon ne? kamshi na tashi kamar gaske a baki ba dadi bari yau zamu dan dana muji,Aayan yana jinsu basu San yazo sakkowa kasa ba,yace kafin nazo nan waje Ku tabbatar kun bace min a part Nonsense ya furta yana Jan tsaki,da sauri suka fice Sumi Sumi sai suka tafi wajen Hajja,tana ganinsu tace to fa Allah kawo mu jaraba ta dawo na shiga uku da kawo kara me tayi muku,nan suka shirya karya wai nice nasa Aayan ya zagesu kuma nace ya koresu,Hajja da kanta tace muje wajen nata na daina saurara mata.
Suka taho Aayan ne ya bude musu kofa Hajja ta fara ta kansa kamar zata cire bakinta tana zagin Aayan,Haneefa tace daga munce idan ta gama girki ta sanmana sai zagi,Hajja da karfi tace ina makirar take tana shigowa kitchen tace gidan ubanki ne ko kayan abincin uwarki ce ta zuba mana,to dole suci idan naga dama ma part dinsu zaki je ki dafa musu abinda suke so,Aayan yace wlh basu isa ba ai ba baiwarsu bace ni na biya sadaki na aureta ba wanda zai sata ko ya hanata sai ni,Hajja ta fashe da kuka Wlh sai na fadawa ubanka yiiiiiiii,muna jinsu a kitchen tace ke dan uwarki wlh sai jikokina sunyi abinda suke so baza ki raba min kan zuria ba,matsiyatan bayi a gama a zuba musu suci,Meenat tace ga danye nan shine naku shi kuka siyo da kudinku wannan kuwa mun rigada mun dafa,kuma hakki ne a kan miji ya ci da matarsa muma tunda ba mutunci baza mu basu ba basu kai matsayin da zamu dafa musu abinci suci ba,Hajja tace iyeeeeee kana ji da girma na suke fada min haka? Yace ai Hajja kin dade da zubar da girmanki shi yasa suka take amma matata me tarbiya ce,Haneefa Hajja ta kiftawa ido tare da cewa Ku zubar da abincin uban kowa ya rasa,Aayan yace wlh duk wacce ta zubar sai gaba daya kun bar gidan nan yau ba gobe ba ai ba gidan ubanku bane,akan Mufee ba abinda bazan iya ba dama darajar Daddy kuke ci gaba daya zaku bar min gida wlh kunji na rantse,haba wani dadi ya kamani a kitchen mijina ya tare min fada ya nuna yana sona a gaban kowa,Muna haka sai ga Ameer da zureriyar wayar wuta,yace ke Sajeeda dan uwarku abin naku har ya kai kuzo kuna zagin matar Aayan,a ransa kuma matarsa yake nufi tunda sona yasa baya so ko sauro ya cijeni,Sajeeda zata masa rashin kunya ya fara tafkarsu son ransa sai da ya Zane musu jiki Hajja na tsine masa tana kuka.

Gaba daya fadan ya koma kan Ameer Hajja ta sanarwa Abbi,nan fa Ameer aka hadu a kansa suka masa tatas,a ransa kuwa yace babu wanda zai taba Mufee na kyaleshi,ta nan bangaren soyayyar Ameer a gareni rahma ce sabo da shi ke Tsarawa Hajja komai baya bata me kyau a kanmu yanda zata ci mana mutunci,shi kadai ya samu Hajja ya lallasheta ta hakura yace Hajja Ku baku iya mugunta ba ai ba a nunawa mutum a fili ba a sonsa ta kasa zamu bullo musu ki daina bari ana musu a gabansu sai su dauki mataki suma fa suna zuwa gidan malamai nan Ameer yasa Hajja farin ciki ya gama tsarata tsab,yace Asiri muka yiwa Aayan yanzu abinda zasuyi a karya asirin dake jikinsa sai a dora sabon aiki,Hajja ta fara kiran malamai tana so a karya asirin dake jikin Aayan ko wanne iri ne,maganin tsari take so ayiwa Aayan sannan ta sake sabon kalar nata.
Hajja ta manta Sam anyiwa Aayan asirin da bazai Haihu ba bazai iya komai ba,Kuma tace a karya komai dake jikin sa ko zai karye din oho?

Abbi Kansu suna mamakin Ameer bai fiye shiga harkar su ta makircin da suke aikatawa ba sai jefi jefi amma kuma yanzu yafi kowa bawa Hajja shawara a kanmu,sai sukayi tunanin Ameer ya tsane mu ne da yawa shi yasa,suma murna sukayi za ayi maganinmu sunga muna nema mu canjawa Aayan zuciya kamarma ya fara sona tunda sunga yana bin umarnina sabanin wancan matan nasa na baya,amma Abbi yace shima dole ya shiga harkar nan dan ganin ya raba ni da Aayan.














AsmaBaffa
[1/17, 9:08 PM] Asmabaffa: πŸŒ–πŸŒ–πŸŒ–πŸŒ–
πŸŒ–πŸŒ–πŸŒ–πŸŒ–

KASUWANCI NA







71-75











Official








By
AsmaBaffa










Ina matukar Godiya ga masu Sharhi Allah ya bar Kauna,kuma Insha'allah daya bayan daya sai kunga sunanku a Novel din nan na Kasuwanci na,sai dai ko Halin mantuwa,ina ganin sharhin ko wacce kuma kuna cikin list dina,sai dai duk wacce taga kamar na manta da ita ta tuna min pls love u all❀❀

Sai masu Sharhi wanda zasuyi watarana ban kula ba suga banyi musu reply ba kuma nayiwa wasu to ayi min Afwa ban kula bane, wacce taji ban kyauta mata ba kar tayi shuru tazo taci kwalata sannan ta tsige min dankwali ta wankeni tasssss🀣🀣🀣na baku dama.


Ga page dinki ta gidana,Al albarka, masoyiya ta gaske me Sharhi kamar ruwa,kina birgeni KHADIJA A HAMZA



Gaisuwa ta zuwa ga babbar me kaunata HANAN ta Gp na gata nan na Cillo ta ki cafketa.😍









Abbi cikin takaici ya ja Hajja bedroom dinta yana cewa Hajja munyi sake,wlh munyi sakaki,taya zamu bari mu rasa dukiya muna ji muna gani,kin san yaron nan ya fara son yarinyar nan shike nan wlh sai abinda tace dashi talaucewa zamuyi dan naga Alama yarinyar nan bata da imani ko kadan, nan Hajja ta fada masa tsarinsu da suka shirya ita da Ameer,Nan take Abbi ya Dafe kai,yace shike nan kun kashemu iceko baku aikata ba? Ya zaki biye wani Ameer ai Rusa mana aiki ne wannan kin San mene a jikin yaron?dama da kyar muka samu wannan ya zauna a jikinsa,Hajja tace mene abin yi? Abbi da yan uwansa sukace ki bar komai a hannunmu,Ameer yazo shigowa wajen Hajja ya dau wanka so yake yazo part dinmu na ga kwalliyarsa.

Yana jin me su Hajja suke yi hankalinsa ya tashi tabbas yasan sai sunga bayan Mufee amma yace ina Sam ba a isa ba baza a Rusa masa farin ciki ba,Shiga Bedroom din yayi tare da Zama gefe yana jinsu suna ta tsare tsare dan kar su gano shi sai ya dinga kiftawa Hajja ido yana mata signa da ido,ko idan Abbi yace ga abinda za ayi sai Ameer ya makewa Hajja kafada wai kar ta yarda,Hajja kadai ke gane me yake nufi,su kuwa su Abbi basu sani ba,sai ji sukayi Hajja tace me kuka sani,me kuka iya,har nawa kuke a duniyar,ni na tsuguna na haifeku zaku zo kuce ni zaku canjawa tunani,to baku isa ba iyyeee wato Ku ga wayayu wayonku yafi nawa?Ni wato bani da tunani ban san me nake ba ko? Abbi cike da ladabi ya Dafe kai yana Oh Hajja ki saurara kiji,Ameer ya kara makale mata kafada yana mata signa,Sani Kanin Abbi yace kai dan ubanka me ya sameka ne ko kafadarka ke ciwo ko tabin hankali ka hadu dashi,Abbi yace Lfy? Yace gashi nan Ameer sai wani makale kafada yake yana wani farfari da Ido ko dan daudu ka dawo bamu sani ba,kaga dan iskan yaro to uban me kake yi, pink lips dinsa ya turo yace to ni me nayi daga abu ya cijeni sai ace bazan sosa ba,Abbi yace to zaka bar dakin nan dan uwarka,Hajja tayi gazal tace kar Ku Zagar min shi ba ruwanku yaron kirki irin Ameeru dan albarka,Abbi ya tabe baki yaci gaba Hajja ki Bari muyi tsarinmu,Hajja tace sam bazai yuwu ba ni zanyi haka kawai na zauna jiranku wankin hula ya kaimu dare komai naku na yan boko sai anyi lissafi an tace an rairaye sannan a aikata,mu kuwa sha yanzu magani yanzu,Abbi suna matukar yin biyayya ga Hajja basa tsallake maganarta haka suka kyaleta cewa tayi nata suma za suyi nasu,Ameer ya kara kallon Hajja ya makale mata kafada Hajja tace a'a ban yarda ba Ku bari idan na gama kalar nawa Bai yi aiki ba sai na baku dama kuyi naku mu gani,a haka suka tsaya amma Abbi yace karta je a karya asirin jikin Aayan pls sabo da akwai shirinsu a jikinsa,A nan kawai Hajja ta yarda cewar ta fasa karyawa kawai zasu ci gaba da nasu,a nan Ameer bai hana ba tunda ya hana abubuwa da dama kar Hajja ta ganeshi ne kawai ya hakura.

Direct part dinmu Ameer ya zarce irin dole fa naga wankansa wanda ni ban san me yake nufi ba, ya kuwa yi dace muna zaune tare da Aayan a Palo yana fushi dani tun kan maganar Ameer dan nace yana da kyau,yaki cin abinci yau fushi yakeyi,har yamma 5pm yazo ya zauna a Palo,kuma nasan yunwa yake ji sai chat yake a waya,har sabon girki na masa kala biyu yaki ci,Yanzu haka ma Kunun gyada na masa na Dade banyi masa ba sai kosai naga yana sonsa,wanka na fesa Malam kamar a London cikin Wando tight iya rabin cinya Maroon,sai rigata fara me arnen kyau gashi yasha gyara na sakeshi na danyi masa style a gaban goshi kadan,Allah tsine wanda zai ce ban hadu ba yau ko mutum dutse ne yau ya kalleni sai jini ya fara gudana a jikinsa.

Sabo da haka ma na kalli Meenat da suka dawo daga Islamiyya nace to ku zauna a Bedroom kar naga yar iskar da fito palo Dariya Sukayi Meenat tace to kin manta zamuje birthday party din kawata yau ni da Ma'eesha zamu wuce ta palon, wanne which kind party ba inda zakuje kun San dai ko Ammah na da rai bata bari muje wani party,bafa wani party bane na kirki sis,Driver baya nan kun sani schl ma yau banje ba kun sani dai wa zai kaiku,zamuje a napep,fine amma kafin Ku fita kuje Ku fadawa Aayan shine ke rike mu yanzu kamar yayanku ne ko ma uba idan ya yarda kuje idan yace no shike nan.
Meenat tace uhm lallai Sis yanzu mun koma hannun mijinki ma? To kici da kanki kiwa kanki Sutura sannan ki zauna a gidanki Meenat,duk wannan shike mana ai ko dole baza muyi gaban kanmu ba,ni macece Allah ya rufa mana asiri mun samu me Kula damu shike nan kuma komai sai muyi ba saninsa?

To fa wasu idan ana rikesu a gida ganin wanda ke rikesu ba shine ya haifesu ba,kuma suna tunanin in ya tsine musu ko ya musu baki baza ta kamasu ba,kana gani zaka ciyar da mutum,ka shayar dashi,tufatarwa ka bashi ilmi da sauran abubuwa wasu ma ko yayansu basa yiwa rikon da sukewa dan riko sabo da su kyautata sai kaga kuma wanda ake rikewa yafi ma dan gidan iko,gadara,da rashin mutunci a gida,ayi ta ganin laifin masu rikon da ka zauna a gidan zaka ga yaron Ashe kwallon shege ne,ba wanda ya isa ya fada masa yaji,abinda yaga dama shi yakeyi baka isa dashi ba,da ka takura ace ka zaluncesu,kana gani zaita abinda yaga dama karshe ma wasu kaji a gari suna zaginka suna kala ma sharri cewar baka musu kaza kaza gari ayi ta tsine ma,karshe ma wasu su dinga cewa marikan nasu iyayen banza,ko a gidan suyi ta shirya ma mugunta iri iri suna zalintarka baka sani ba,more especially ace matar me gidan ce ta dauko wani ko wata take rikewa,suna ganin kamar itace da gidan ma ko saurarar mijin nata basa yi bayan komai shike yi a gidan suna cin arziki,kawai matar zasu fadawa itace take rikesu itace yar uwarsu mijin nata ko gaisuwa sai sunga dama,itama kuma tana kallo gani take ma ita ke musu komai ba mijin ba,bayan da dama zaka ga komai shi za a fadawa yayi musu amma Bai isa dasu ba,wani ko aikene sai dai ya aiki nasa ko na waje,da yawa ana magana kan azzalumai masu rikon yara ko yayan kishiya ko na yan Uwa ba a fadar laifin yaran,duk da cewa akwai masu zalincin Amma ya kamata mata masu dauko rikon Yara ko mijin ya kawo miki a daure a nuna musu muhimmancin me rikon nasu.ba kawai ayi ta yin abinda aka dama ba ana ganin ba iyayen da suka Haifa bane me zasuyi ya bika.

Fita nayi ina sheka uban Kamshi Aayan zaune a palo yana danna waya na karasa dauke da hadadden tire jere da abinci iri iri,gaba daya bana jin dadin fushinsa yau,duk sai naji duniyar tayi min zafi,tun kafin na karaso ya zuba min ido yana kallona kamar ya hadiyeni naji dadi a raina ko bai fada ba nasan ya yaba kuma nayi kyau,kafin na gama tunanina ya juya min baya a saman 3seater tafkekiya,ni dariya ma ya bani kamar yaro na fushi,
Ranka ya dade ga abinci ka daure kaci kaji,dama ni na saba da lallashin mutum kan dole yaci abinci ji nakeyi kamar nice banci komai ba shi yasa nake nacin sai anci abinci,Muna haka muka ji bugun kofar Ameer,na manta shigar dake jikina nayi hanyar
End Ads