haka kawai mu dan Allah ka kawo remote a canja ka wani kwace basai mutum zai kalla ba, Meenat taji ana shidewa a Tv Ameer ya ba da Amanna yana kallo ta dan kallo ta dauke kai tace yan iska kawai sai taga Masoya sun koma abin tsoro dama Horror film ne sai suka koma fada da zako zako hakora,mace ta bude bakinta wommm...Sai da Meenat ta buga kara tare da fadawa jikin Ameer, Ameer yana Jinta dan munafuncin Sa sai yace ai film din nan abin tsoronsa yayi yawa yanzu zaki ga ma sun koma kamar Dujal ance har mafarkinsu akeyi, na gani a BBC wani Horror rannan ana kallo a wani gida ya fito daga TV ya shiga jikin matar kin San Aljanune, Meenat ta kara kankameshi ta boye fuskarta a jikinsa taki dagowa,Ameer yana jin dadi a ransa a fili yaci gaba da cewa ai ba a barin irinku su kalli wannan sabo da idan suka ganku sukan iya Faso TV suzo wajenku,ni tsoro nake jiye miki dan yanzu zan fita sai ke daya bari na Canja Chanel,ya canja Chanel ya fara kamar zai Mike Meenat ta rikeshi kam ta makale a jikinsa tana roko Karya tafi,yace to sai dai ki dakko Ice cream ki dinga bani a baki sai na zauna idan ba haka ba tafiya zanyi.
Da sauri Meenat ta dakko tace bari na baka idan Ma'eesha ta dawo sai ka tafi kawai,nan ta zauna damfamfam tana bawa Ameer Ice cream a baki yana sha yana latsa wayarsa ya Zama dan gata,a ransa yace wlh aure zance Aayan ya min kwana nan na huta nima.
AsmaBaffa
[2/2, 12:41 AM] Asmabaffa: 🌖🌖🌖🌖
🌖🌖🌖🌖
KASUWANCI NA
107-108
Official
By
AsmaBaffa
HOUSE OF HAUSA NOVEL,TASKAR SURAYYARHMS,TASKAR FIDDAUSI SODANGI,UWARGIDA,ASMABAFFA FANS CLUB gaba dayanku gps na gode da Sharhi da kuke yawan yi kunfi kowa shi yasa wannan page naku ne.
Tnx etc da ake yawan fada basu damu Writers ba anfi son Sharhi Readers Ku daure kuci gaba munfi jin dadin typing da posting.Gp dina naga ana sanya da Sharhi ko an fara gajiya ne da Novel din a tafi Hutu?😍😍😍 Love u all fans.
Ameer yana tunani ya zaiyi ma shima yayi auren nan ya huta,kwanciya yayi saman 3seater tare da Jan eriyar tunaninsa ya shiga nazari,Meenat na gefensa ta gama bashi Ice cream tana waya da kawarta ta schl,yawancin yan makaranta musamman yan Boarding schl idan suka hadu da kawayensu zage zage zaka ji yana tashi kawai ana shegiyar ya gari etc,yanzu Meenat ita da tayi Day schl ma wannan tsabiyar ta zauna mata Ameer na gefe ta daga waya kawarta tana dagawa Ameer yaji kawar ta duro ashar, Meenat tana dariya tace amma dai Allah ya tsine miki,Shegiya ai baki da mutunci,Kawar tace dan ubanki ke Hafsat Salisu ciki ne da ita daga biki, Meenat tace ke Dan Allah? ke Amai take yi,Meenat tace ai Hafsat Salisu matsiyaciya ce,ai Allah yayi yar iska a nan wajen,Kawar Meenat tace hmm ke dan uwarki Aisha Balarabe wai aure zatayi shegiya, Meenat tace ai tsinanniya ce Aisha ta kirki zamu je gidansu ai soon, duk wayar tasu a zage zage ta kare har suka gama wai nan hira aka Sha kuma sai gulmar frnds,Abinda yan mata keyi kenan ai bin diddigin kawaye ana munafunci wance taci gaba ko baya taci,taci gaba da karatu ko a'a,anyi mata aure dadi take Sha ko wahala,ya ta koma ya gidansu yake aikin kenan sa ido,haka ma'aikata ma burinsu suga a ina abokiyar aikinsu take kwana ya gidansu ko gidan mijinta ayi ta gulmarta,duk iyayinta Ashe kaza kaza, frnds cikin su idan ba wata a kusa sai ayi ta gulmarta kema kina tashi ayi taki gulmar aikin kenan ya kamata ayi gyara mutum yaji da kansa ma matsalarsa ta ishe shi,amma sai abinda ba ruwanka zaka damu kanka.
Ameer ya kalli Meenat yace yanzu wannan wayar taku mene sunanta mene amfaninta? Gulma ko zage zage? Shuru Meenat tayi,abinda kika koyo kenan a schl din taki zagi da gulma,ki daina ba kyau kawai kuyi ta zagin juna sannan da hirar wasu kuna zagi wannan bai kamata ba babu tarbiyya a ciki,Last warning na miki wannan idan na kara Jin wannan zage zagen am serious sai na Zaneki a gidan nan,Meenat baki bude take kallonsa da mamaki yanda ya zage yake ta mata masifa ba ji ba gani,kuma ba alamar wasa a idonsa ita dai tayi shuru.
Lokacin munzo sakkowa ni da Aayan muka ji wayar da Meenat ke yi har ta gama,haka muna tsaye Ameer ya fara mata fada,naji dadi kuma ya birgeni,yau na tabbatar Ameer yana da hankali sosai kuma yasan me yake,kuma na kara yarda da zancen Aayan cewar Ameer ya tuba ya canja halayensa sabo da ace da ne ba ruwansa.
Karasa sakkowa mukayi nace Weldon Ameer na gode haka ake so idan Zama ya hada ka tare da mutum yayi ba daidai ba ka gaya masa gaskiya na gode,Ke kuma Meenat haka Ammah ta bamu tarbiyya?Ni ban sanki da haka ba wlh,Meenat zatayi magana nace dalla rufe min baki Banza ko kunya bakya ji,Aayan yace to fadan ai ya isa haka taji ta daina ko Kanwata? Meenat tace ae.
Zama Aayan yayi tare da cewa Meenat ku shirya gobe akwai Kamun Amarya a gidan nan,Meenat tace wace Haneefa ce ko Sajeeda ko a cikin su Meenal ne? Aayan yace My wife Mufeeda,tace Kamu take so ayi mata kamar ko wacce Amarya, Meenat tace tabara ce kawai da samun waje kaine ma kake biye mata,ni kuwa nace ae anji din ina ruwanki,Meenat tace wlh ba wani Kamu da za ayi miki ya wuceki sai kallo,Ameer yace ina ruwanki? Ma'eesha ta shigo itama dariya tayi tare da cewa bata lokaci ki Bari a hada da sunan Baby idan kin haihu a kama ki,Haka duka suka ki yarda dole Mufee sai hakura nayi nace Birthday din ma na fasa shiryawa a gidan,Aayan yace to gobe Ku shirya akwai surprise a gidan nan kuma gift ne na wife dina, amma kar wacce tace zata ji tsoro,muka ce to Allah ya kaimu.
Washe gari mun gama shiri muna jiran Surprise na Aayan,Ameer ma yace baza a barshi a baya ba,5pm dai dai sai ga Aayan ya shigo tare da securities dauke da akwatuna ana shigowa dasu sunfi guda Ashirin,baki muka bude muna kallo aka gama jere su kaf suka fita, sallamar Yarima Bobo muka ji tare da Mace dattijuwa a bayansa amma ta rufe fuskarta da Mayafi sai dai da ganinta Hutu da jin dadi ya ratsata, gashi kafafunta da hannayenta da muke gani fara ce amma ba kar ba sai sheki takeyi,wani lace ne a jikinta na alfarma da gani yar gayu ce,sai kamshi takeyi, Doctor din dake Kula da Ammah kafin ta rasu muka gani, Uwata zauna ga kujera cewar Aayan,mamaki ya rufeni wai uwarsa,to wai wace ne haka,dattijuwar ce muka ji tana kuka amma kamar mun San muryarta,a hankali ta bude mayafinta tare da Cewa Mufeeda ta,zo nan Mufee ta,Meenat Ma'eesha nice fa Ammanku,Ammah ce,nan take muka kalleta sosai ba Shakka Ammah ce ta Sha Hutu,to ita bata rasu ba,nan tsoro ya kama mu na tashi da gudu ina fatalwa...fatalwa....Meenat ma suka Mike tare da rufa min baya muka fada Bedroom tare da boyewa,daga su Yarima har Ammah dariya sukeyi,Haka ma Ameer duk da bai Santa ba,Qur'ani na dauka,Meenat ta dauki carbi,Maeesha ta fara Rabbana atina muna ta yi kamar makarantar allo,tafiya muka ji za a bude kofar muka kara Volume din muryarmu ina Yaseen....Meenat na Lahaula Wala quwwata illabillah,
Aayan ne ya shigo aiko muka manne kanmu waje daya,yace baku da hankali wai Ammah taku ce bafa mutuwa tayi ba,idan fatalwa ce taya zaku ganmu da ita,dama ba mutuwa tayi ba turai muka kaita akayi mata magani,shine abinda nake ta cewa zan baki wanda yafi miki ko mene a rayuwa,ita ce gift din tawa,surprise dina kenan,Mufee tace kuji haka kawai munga gawarta kiri kiri kuce waye waye, wlh Allah bata mutu ba Ammah ce kuzo muje Yarima zai muku bayani.
Da kyar Aayan ya lallaba mu muka fito,amma sai buya mukeyi a bayansa na manne fuskata a jikinsa Meenat kuma taja rigata ta rikeni,Maeesha kuwa da tafin hannu ta rufe idonta.
Har Palo muka zauna can nesa inda ba ruwanmu da Ammah,Ammah mamaki takeyi Ashe duk son da kakewa mutum ya mutu kana ihun Kuka da ace zai dawo kowa gudunka zaiyi bazai Zauna da kai ba,Allah me iko,Muryar Yarima muka ji yace a bude taro da Addua Ameer,Ameer Ashe Malam ne yanda ya dinga zazzaga addua ba a magana.
Yarima yace Mufeeda kece Babba ya dace Ku bamu hankalinku,Alhmdllh kamar yanda kuka gani Ammah ce taku ba mutuwa tayi ba kuna mamaki sabo da kunga gawarta a kwance,to wannan ba shirin kowa bane face nawa,idan baza ki manta ba lokacin da akayi aurenki da Aayan ya tafi bai kara waiwayonki ba,ko gaisuwa bai miki ba,kuma zaki tuna da kika ce masa Ammah ta rasu ko damuwa baiyi ba,sannan nace nan gaba idan kika ji rawar dana taka a aurenki da Aayan har kyauta sai kin min,nace ae anyi haka duka.
Zakituna me Daddyn Aayan ya fada miki cewar labarinki da Aayan ya bashi shine yasa yace dole sai ya aureki ko? Nace ae haka ne.
To lokacin da Aayan ya sameni da Zancen ni na kara cewa kin dace kuwa ya aureki yace shi bai yarda da tarbiyarki ba kuma da alama kina da son kudi,baki sani ba sai da muka dinga bibiyar rayuwarki sabo da ba auren mutum haka kawai shi yasa ake so har kullum ace mutum ya Zama na gari sabo da irin wannan kuma alhmdllh bamu samu wani mummunan Hali naki ba sai wanda ba a rasa ba wanda kowanne dan Adam yana da aibu ko yaya ne bazai yuwu ace 100% kake ba,nace ae, idan munzo miki da zancen ba lallai ki yarda ba a wancen lokacin,kuma lokacin kin kawo bukatar taimako na aikin Ammah idan muka ce gashi gashi zaki ce ba dan Allah muka zo ba,kuma lokacin Aayan baya son wani aure umarni kawai yabi,shine nace mu bari sai mun kai Mahaifiyarku asibiti tunda ba ranga ranga take ba sai mu fada mata muji,bayan an kaita likitan yace Ku fita za a duba ta lokacin muna Office din a can ciki,a nan muka sameta da maganar,Tayi farin ciki kuma tayi Naam,amma tace mana ko da ta rasu ga Amanar yaranta nan Aayan ya rikesu,kuma mun karba,sai tace kina da wani Hali daya wanda bata Sonki dashi Aayan yayi kokari ya canja ki,nan tace mana ke akwai son kudi bata so abin yayi nisa ya kaiki ga halaka duk da cewa tasan talauci da nauyin dake kanki yasa wannan halin ya shige ki.
Tace amma baza ki canja ba sai in kinsan bata raye sannan Zama ki yarda ayi auren,nan ta shirya mana dabara,Ammah ce tayi magana tace kwarai Mufeeda nice na shirya musu komai sabo da ki fara koyon Darasi a duniya ki san cewa Kudi ba shine komai ba,duk abinda Allah ya tsara shi zai faru,sai karfin addua kan sawa Allah ya canja,ina Sonki fiye da komai a duniya shi yasa Nace suce miki an farkeni baza a dinke ni ba sai kin yarda anyi aure nasan wannan zai sa ki yarda ayi miki auren sabo da Yarima ya bani Labarin Aayan kaf a asibitin,kuma naji tausayinsa,na yarda yaron kirki ne zai iya rike min ke da Amana,kuma naji kina jin tsoronsa shine ya dakeki kika min karya kika ce kwalabati kika fada,shine ya daukeki ya hukunta ki kika ce min kina gidan kawarki neman taimako sabo da kar hankalina ya tashi,to Mufee kin yarda kuma kinyi abinda nake zatonki wato dangina da dangin Mahaifinki sun daura miki aure,sun sani kuma makwafta sun sani,Alhmdllh an baki sadaki kin taho da burin Ammah dinki dole ta tashi sabo da tuna ninki kudi da aikin asibiti shi zai sa na rayu ba Allah ba,ya kika ji da kika ga basuyi tasiri ba na rasu a lokacin kinga hukuncin Allah,Meenat baki manta ba nace muku naji a jikina ta hadu da Alkhairi kuma na bar muku wasiyya Ku bata ko? Meenat tace ae kuma mun fada mata ashe dama kin San komai duk abinda kika fada kuma ya faru,Murmushi Ammah tayi tace to lokacin da kuke kuka kuna suma lokacin aka canja gawata wacce a asibitin idan baku manta ba Doctor ne ya daukeni tare da canja min daki lokacin aka daukeni aka kawo wata baiwar Allah wacce tayi hatsari da dadewa an rasa danginta tana motuary aka yi mata wanka tare da hada ta za a sa Alummar musulmai su sallaceta akaita makwanci ,Dangina dana Babanku duk sun San ban mutu ba,kawai kallonku sukeyi,a boye Yarima ya sanar musu amma basu San dalili ba,shi yasa kuka ga basu wani damu ba suna ta harkarsu ko? Nace kwarai kuwa ko a jikinsu a lokacin.
Shi yasa aka hanaku Ku bude gawar lokacin da za a kaita kuna ihu da kuka lokacin ni kuwa tuni anyi min Visa ina Kukan rabuwa daku cike da tsoro kar na mutu da gaske,Aayan da Yarima ne suka kaini U.s acan aka yi min aiki da komai na warke,naso nazo na ganku Amma Aayan yace min baki shiryu ba kina nan da son kudinki na jira tukkunna.
Documents from AIHAUSANOVELS
Always visit Aihausanovels.com.ng For downloading free hausa novels
Like our Facebook page Fb.me/aihausanovels
Aayan ne ya karbe zancen da cewa shine dalilin da yasa kika ga na Dade ban zo wajenku ba kina Amarya,ina U.s sai da Ammah ta samu sauki muka dawo ni da Yarima lokacin baki ga dana zo ba bana baki ko kwandala ba ban kuma siya miki komai ba,lokacin kuma tunanin ki zaki samu kudin Kasuwanci,ni kuma na nuna na fiki wayo,na hanaki sisi,sannan dana kaiki gidana na baku abinci garau garau Ammah ce tace nayi miki haka zaki kara hankali,tun kina tunanin zan saki kudi kuji dadi sai kika ji shuru,abinda kika ce na baki shi nake baki bana kari,sai da naga kin fara gane gaskiya,sannan na fara sakar miki sai naga ma kawai ma baki San wani kudi ba,sabo da Dubu biyu a wajenki kudi ce,nayi ta miki gwaje gwaje da dama baki gane ba,yanzu Ma Ammah ce tace ta gaji tasan yarta ta fara hankali ta girma ta hakura gwara ta dawo ta ganku,kuma da baki hankali kin canja ba da baza ki ganta yanzu ba,Yarima ne karfin shirya komai kuma shi ke yawan zuwa ganin Ammah a Us,shi yasa rannan muka je tare har kika yi fushi dani dole na dawo ba shiri, gata nan Ammah taga ina sonta da yawa sai garani takeyi na Zama mijin tace,Dariya Ammah tayi tare da cewa Allah kyauta Aayan,Yarima na dariya,Ameer kuwa sai yanzu ya fahimci komai,yace Ammah sannu da zuwa ni Cousin din Aayan ne ga Meenat nan ta rainani gaba daya kullum sai ta zageni a gidan nan,Dariya akayi gaba daya amma banda ni wacce nake hawayen bakin ciki,sam ni abinda Ammah tayi naji haushi gaskiya kuma bata kyauta ba,akan wannan ta iya sawa aka shirya ta rasu jibi irin kukan da mukayi da halin da muka shiga na rashinta, yanzu baza ta iya yi min fada na Canja ba kawai sai tayi mana haka yau gashi har Meenat tayi Candy anfi 1yr, kuma tasan Aayan a lokacin ba sona yake ba dan tana tunanin na gari ne kawai sai ta yarda nayi wannan auren da wuri gashi ni har ma nafi sonsa,kuma har Aayan ya rufeni shi da Yarima, gaskiya Ammah bata kyauta mana ba ni banga amfanin hakan ba amma wata zuciyar a raina tana sanar min fa ai na shiryu kuma nayi hankali sau nawa Ammah na min fada na daina abinda nake amma naki ji,to kuma idan ma naso kudin ai duk akansu ne tunda su nakewa komai,dan su nayi,sai kuma aga laifi na ai kowa da halinsa, ya Ammah za tayi da mutanen unguwa fa wanda suka Santa lallai za a dinga fyalla gudu kuwa.
Meenat kuwa da Ma'eesha duk sun tafi sun makale a jikin Ammah suna ta murna da hira tana shafa Kansu,Ameer ma yace shima Allah sai ta sa masa albarka,haka ta shafa kansa daya tura mata,amma kuma Ammah hankalinta baya jikinta ya tashi matuka,hankalinta na kaina wacce tafi so a duniya ganin ina kuka naki kulata,kamata yayi ace ni ta fara shafawa ba wasu ba,Aayan ma hankalinsa ya koma kaina yar gwal dinsa na kuka kyautarsa bata birgeni ba kenan,Ammah ce tace Zo Mufee ta kinji? Ta Mike zata zo wajena da sauri na Mike tsaye tare bin hanyar wani Bedroom wanda nake so na dauka cewar nawa ne ni kadai a sama kusa dana Aayan da muke kwana,nan na shiga kawai nayi kwanciyata a saman Bed,da sauri Aayan ya biyo bayana amma na sawa kofar Key,ko waye gaskiya zai iya jin ba dadi idan akayi masa haka Mufee tana da gaskiya cewar Aayan a ransa.
Magiya da lallashi ba wanda bai min ba naki ki magana,Haka Ammah tazo da kanta tayi tayi naki,su Meenat ma,Yarima da Ameer duk sunyi sun hakura,Aayan yace suje kawai zan huce ne.
Suna Palo suna ta hira har Ammah ina jiyo hayaniyarsu,Suka ci suka Sha,Ammah kuwa Aayan cewa yayi ta hau sama ta zabi daki ko a bata part guda tace a'a a dakin su Meenat zasu dinga kwana suna hira da yaranta kafin ta koma gidan can tsohuwar unguwarmu.
Yarima yace Ammah Aayan ya miki magani kin warke ni kuma ai na siya miki gida hadadde ciki zaki koma,Ammah harda kuka su Meenat sai godiya suke masa,Ameer yace to ni kuma Mota zan sai mata insha'allah,Mamaki Ammah takeyi har