irin wulakancin da Ammah bata gani ba a hannun Abba,idan suna fada har Kuka mukeyi,amma duk lokacin bamu da wayo bamu San akan me suke fadan ba,muna dai ji yana cewa idan ya gaji korarta zaiyi,tun abin baya damun mu har muke damuwa muna bashi hakuri,bamu San dalili ba dai sabo da Ammah bata bari mu San halin da suke ciki,sai dai muga tana kuka watarana Abbah yace zai fita wata state dake Kudu Abia state neman Kudi tun da Allah yasa ya tafi bamu kara Jin labarin Inda yake ba ko a waya.
Mun shiga damuwa me tsanani,Amma taje har garinsu wajen danginsa tare da mu amma sukace suma basu da labarinsa,haka abokanansa na business da sauransu duk an nemesu shuru suma basu sani ba,munyi kuka munyi bakin ciki har aka kwashe shekara guda lokacin na gama primary,anyi cigiyar Abbah har gidan Radio amma ba labari haka Ammah ta fara Sana'ar kosan siyarwa da Awara tare da sauran kanana nan sana'a gida dasu take mana komai na rayuwa,har na shiga Jss1 na gama na shiga jss 2,Katsam lalura ta samu Ammah haka kawai bata iya motsa kafafunta daga Hips zuwa toes,munci kuka gashi nice Babba ga karancin Shekaru haka makwafta suka taimaka mana muka kai Ammah asibiti mafi sauki,da yan kudin da Ammah ke Tarawa muka sai mata magunguna sannan suka ce dole akwai wani aiki da za ayi mata nan gaba,tun da muka dawo Ammah ta dan samu sauki ni kuma dama duk sana'oin nata na iya su sai naci gaba da yi na daina zuwa schl nake biyawa su Ma'eesha suna zuwa,ni ke kula da Ammah da gidan baki daya,akan sana'ar ma sai na kara wasu da yawa ina yi iri iri komai siyarwa nakeyi ba sauki,har Allah yasa Meenat na Ss1 Maeeshah na jss2 ga Islamiyya suna zuwa ni kuwa komai ya tsaya min sai neman kudin jaraba kamar zanyi sata.
har yau munyi munyi da Ammah ta fada mana fadan dake tsakaninta da Abba kafin ya bace amma taki fada mana sabo da haka muka kyaleta sannan muka kara tsanar Abba da ya gudu ya barmu,dan ni ko zancen wani Abba bana yi sam bama na so a ambaci Sunansa shi yasa a makaranta ma Sunana Mufeeda Adam Fatima sabo da sunan Ammah Fatima kawai nace ai bazan sa Kakanmu ba Ammah ta zan sa,haka Meenat Adam Fatima tare da Maeeshah Adam Fatima haka duk muke Amfani dashi da ace da halima sai dai nasa Mufeeda Fatima Adam to kawai dan da uba ake ado shi yasa ba kyau dole nake Sa Adam.
Za muji nan gaba Ina Abbah ya boye oho,ko da gaske ya bata,ko yana raye,ko yan Mafiya ne,mene ya hadasu da Ammah suke fada,wacce lalurace a jikin Ammah haka? Oho dai.
Ci gaban labari
bayan kwanaki kadan na yanke hukuncin zan fara zuwa gidan yan siyasa tare da yan kasuwa da sauran masu kudi na fara neman taimako ko Allah zai sa a samu me Imani ya tallafa a biyawa Ammah kudin magani,bayan na gama kosan siyarwata tare da gyaran gidan haka nayi girkin rana na kwashe a cooler sannan na fara daka lallen da nake siyarwa ina daurawa a leda ina saidawa ashirin,lallen ma ban barshi ba sai dana yi masa Algus na hada da gayyen bishiyar sabara na daka ya kara yawa na daura na ajiye,idan mutum ya siya lalle sai yaga lallen yaki yi masa ja yadda yake so to anyi masa Algus da wasu gayyen,wanka nayi na shirya cikin skert dina dan gwanjo tare da T-shirt dita nayi kyau nasa Hijab dina me hannu sunsha wanki da guga,ban shafa ko Powder ba na yiwa Ammah Sallama nace na tafi kasuwa siyo kaya,tayi mun a dawo lfy,ban zarce ko ina ba sai gidan Chairman din local government dinmu,ban san gidan ba da tambaya aka nuna min ni da me Napep,bayan na sauka mutane damkam a kofar gidan har da yan Sanda masu gadi gida me kyan gaske,maza yan siyasa sai kallo na suke domin sunga baiwar kyau wajena,da gani kuma sun San ba yar siyasa bace ni kamilalliyace ni yar mutunci,salamu alaikum nayi musu sallama tare da gaishesu sannan nace Dan Allah yau Hon yana nan? Suka ce ae kinyi sa'a yana gida muma shi muke jira,amma tunda ke macece bari mu rokar miki masu gadi ki shiga kice wajen matar Hon kika zo,ai kuwa haka akayi nan take yan Sanda sunga kyau suka ce na shiga,
nayi godiya na fada gidan cikin nutsuwa,wata yar aiki ce ta nuna min kofar shiga ciki,nace tayi min jagora zuwa wajen Hajiya,har nan ta kaini sannan ta shiga tare da sanarwa Matar Hon,cikin Sa'a aka ce na shiga har ciki yar aiki tayi min iso,matar Hon yarinya baza ta wuce 24yrs da ganin irin kyau da Allah ya min yasa ta tsaneni kar na kwace mata miji,nan take naga ta canja fuska ta Mike tare da miko min Dubu biyu tace na tafi an sallameni,babu bakin magana jiki ba kwari na karba na dau hanyar fitowa kenan kicif sai ga Hon ya sakko daga sama da katon cikinsa yana shafa tumbinsa,ya kalleni nan take ya lashe bakinsa tare da yi min signa da Ido kamar kwarto,ni dai na fice da sauri daga palon.
Matar Hon tana Alhaji ga abincinka amma tuni yace Hajiya na fita Office ana jirana ya fito da sauri yazo kusa dani a bakin gate,da sauri na durkusa na gaisar dashi sannan na fada masa abinda ya kawoni nan take yace ai karamar matsalace wannan ya bani card dinsa yace na samesa a guess house dinsa,na tsorata amma dai na karba nace sai nazo na fito daga gidan na tafi gida ina murna ta.
Ban fadawa Ammah inda naje ba nasan fada zata min kawai nayi shuru,washe gari kuwa dama yace 5pm zanje gidan da yace,ba tsoro na shirya na tafi ba wahala na gane gidan na fita daga Napep,Naga gida rafkeke na kwankwasa sai ko ga me gadi ya bude yana ganin budurwa yasan irin matan da Hon ke Tarawa kullum ne da fara'a ya tarbeni yace shiga yana ciki,nan ya min iso har cikin palon Hon,sai lokacin tsoro ya kamani,lokacin na hango Hon daga shi sai Singlet da gajeren wando yana latsa waya,da fara'a yana washe baki yace zauna mana kyakyawa me kyan sura,Nace ba sai na zauna ba idan zaka taimakeni to ka bani dan Allah,dariya yayi yace zo mana ke ya kike abu kamar bagidajiya ina ganinki wayayya zo muji dadi mana sannan na baki kudin a wuce wajen kawai,tsorata na karayi na fara ja da baya nace ni ance ba kyau namiji ya rike ma mace hannu nidai zan gudu,Hon yayi dariyar Kuruciyata yana lallabani yana hure min kunne amma naki matsawa ko kusa dashi,tasowa naga yayi ya taho jikina ya fara shafa min fuska yana kokarin cire min Hijab,yana sakin wani Gurnani ai da gudu na ja baya a rude na bude kofar na fice da gudin tsiya ko me gadi gani yayi kamar walkiya na bude kofa na fice wufff.
Ina Haki na fito da matsiyacin gudu na cukwikwiye Hijab dina na tattara skert dina ba takalmi a kafata tuni na watsar dasu,Na samu gefen titi kawai na Mike na dinga tsinka uban gudu ka rantse yan Mafiya ko Zaki ne suke Bina,ga unguwar shuru irin ta masu kudi ba kowa ba a ganin ko mota a titin,can naji karar mota ta bayana tunanina Hon ne haba ai sai na kara karfin gudu na yi nake kamar numfashina zai fita,a hankali motar take tafiya a saitina sai lokaci ina gudu na dan kalli glass din window din an sauke glass din ana ta min magana ta ciki gudu nake iya karfina da karfi nace wlh bazan tsaya ba Hon tsinanne dan Iska ina ta zagin me motar ji nake Hon ne ashe Aayan ne yake ta Bina da motar yana sheka dariya yanda yaga ina uban gudu kamar na tashin kiyama,tsabar mugunta sai yaki yin magana kawai yake ta Bina da mota duk inda nasha kwana sai yasha da motar yana ta dariya har sai da karfina ya kare tas na fara kokarin tsayawa Ashe ban sani ba idan gudu ya cika yawa yakai wani limit mutum kasa tsayawa yake da kansa sai an rikeshi kawai zai ta gudu ne,ina so na tsaya ina kokarin tirjewa amma ina gudu kawai nake falfalawa na fashe da kuka kuma ina ta gudu na kamar masifa har dai da kyar na samu na rike wata bishiya sannan na zube a kasa wajen ina maida numfashi,Dai dai lokacin Saurayi Aayan yana ta dariya harda kwalla sannan ya take birki a inda nake Kuuuuu yana ta dariya yana rike ciki,sai da na Huta sosai da sosai sannan na tashi tsaye ina karkade jikina,sai lokacin na hangoshi cikin motarsa Ashe shine ba Hon ba,kawai nima abin ya bani dariya kamar sabuwar Kamu na dinga sheka dariya harda kwalla,a ransa yace lallai yarinyar nan da alama mahaukaciya ce ko Aljanu gareta,na kalleshi saitin window na daure fuska sannan na maka masa harara,ai ko ya fito a fusace na firgita ba damar guduwa dan na gaji ina ji ina gani ya fito ya zabga min Mari sannan ya jefar dani a kasa keee ya daka min tsawa ba a min ko kallon Banza mind ur fucking Business,bana jin turanci tunanina yasan Business dina dana keyi a gida kawai sai nace dama ai ni Kasuwanci na nakeyi ina ruwanka dani haka kawai sai ka dinga cin zalina dan kaga bamu da kudi,ai kudin naku bana tsoron Allah bane tunda ba a taimako sai yawo a mota ana zalinci,tsaki yaja me karfi cikin takama ya koma labebiyar motarsa fuuuuuuu ya figi abarsa.
Ni kuwa na turo baki tare da cewa Allah ya isa wlh duk ranar daya mareni again Allah sai na rama za a gani ai,nan na gama Kuri na sannan na tafi gida abina.
Washe gari ban tsorata ba na kara shiri na tafi gidan Vice Chairman neman taimako amma haka na yini ban samu ganinsa ba sai yaronsa,Nace dan Allah wajen Vice nazo idan baza ka damu ba ka min hanya na ganshi,cikin daure fuska kamar zai bigeni ya hayayyako min da masifa ke malama an fada miki ya tafi Umrah bazai dawo yanzu ba,irinku dama yan mata makaryata da Iyayenku sabo da son abin duniya sai ku fara karya kuna zuwa Maula daga nan a lalata Ku yan iskan yara,har nawa kike amma har kinsan yawon Maula,nan dai yaron Vice ya min tatas na baro kofar gidan da takaici.
Ban dai kara hakura ba washe gari haka na kara shiryawa na nufi gidan wani Commissioner na Ilmi,a bakin gate kofar gidan na yini ina jira ko za bani dama na shiga ciki amma masu gadin ko kallona ba wanda yayi,har zan tafi sai ga wani ya taho da Jibgegiyar mota kida na tashi Malam nan take mukayi Ido hudu da wani Saurayi black Handsome dan gayu,sai kallona yake,ina tsaye aka bude masa gate,sai wani kallo yake Bina dashi kamar tsohon maye,nan take naga ya sauke glass yana murmushi tare da yafito ni da hannu wai naje,da sauri na karasa,sai kallo yake kare min tun daga sama har kasa yace yan mata wa kike nema?nace wajen Babanka nazo Commissioner na Ilmi da alama kai dansa ne ko?murmushi ya kara saki yana min kallon irin na yan duniya,yace ae dansa ne ni ya akayi?Nan na sanar masa taimakon da nake nema akan rashin lafiyar Ammah yace wannan ai karamar matsala ce Beauty,kawo na sa miki Number ta,nace ni bani da waya mu talakawa ne,baki ya tabe tare da dauke kai yana cewa ai kuna da amfani ta wani fannin,ban gane me yake nufi ba kawai naga ya miko min wata waya sabuwa dal a kwalinta amma karama ce Nokia me kyan gaske,yace kinci sa'a Baby na siyo wa yaron Mama waya karbi ki rike wannan ga sim card sabo bari na sa miki zamu dinga magana ta waya kafin Abba ya dawo sai a kaita asibiti.
Documents from AIHAUSANOVELS
Always visit Aihausanovels.com.ng For downloading free hausa novels
Like our Facebook page Fb.me/aihausanovels
Tunanina da gaske ne ba tunanin komai nace nidai ka bar wayarka amma ka bani Number dinka zan nemeka kaji,yace karbi karki damu kyauta na baki yan mata kamarki ba waya ai abin kunya ne,cike da tsoro dai na karba hannu na rawa garin zai miko min sai da ya shafi hannuna yana sani harda lumshe ido,da sauri na dauke hannuna ina godiya,da kansa ya hada min wayar da komai ya sa min Number dinsa ciki ya dauki number ta sannan ya miko min Dubu biyu wai na hau Napep,naki karba kawai sai ya zubar min da kudin a kasa yana shu'umin murmushi ya figi motarsa ya shimfida cikin wannan gida na alfarma,na dade a tsaye ina tunani kawai dai nace Allah gani gareka na kwashi kudin nayi gaba abina.
Danaje gida Ammah dan kar ta hanani amfani da wayar sai nayi karya nace Ammah yau dai na karbi kudin adashina na gidan Haule kinga na siyo waya sabo da baza a ace a gidan nan bamu da waya ko daya ba,nan suka dinga murna da tsalle,Ammah harda sa albarka tana murna dama yaran Zamani badai zuba karya a kifar da iyaye a corner can.
Next day ban hakura ba dai sabo da ina tsoro kar fa nazo ba a samu tallafi wajen Dan Commissioner ba kawai na shirya na Tafi gidan Dan Majalisa na tarayya da suke Zama Abuja,ni dai nasan ba lallai na sameshi da family dinsa ba domin wasu ma ba a Sanin inda gidansu yake buya suke su canja unguwa ko state dan kar a je musu Maula,ni kuwa tsabar jaraba sai da na kwakwulo gidan da tambaya tun daga unguwarmu nake bin gidajen manya ko wani ya sani,idan ance me zaki yi sai nace sako wasu zasu kai gidan da haka aka gwada min gidansa amma fa basu cika Zama a kano ba kawai dai zanje na gani ko me gadi na samu contact Dinsa ya min hanya, haka na fada Napep sai gidan Dan Majalisar tarayya Abuja,gidan kansa abin kallo ne sabo da ya hadu karshe.
Securities ko ina a gidan harda mutane a kofar gidan Yan maula,haka na kutsa kai cikinsu tare da tambaya ko me gidan yana nan suka ce ai rabon da yazo kano ma yau Shekara biyu kenan.
Baki na bude tare da mamaki wani ciki yace sai dansa Yarima Bobo da ake aikowa da sakon yan siyasa ana kawo musu,yanzu ma shi muke jira ya fito kin San shi a kwai gadara da wulakanci sai yaga dama yake fitowa ya bamu sakon Hon Rep,
Nan take nace aiko sai na jira dan nasa dan Ubansa ko shi waye,ina nan tsaye na gaji da jira har 2pm a wajen nayi Sallah saman dankwalina wata me tallan Fura tana zaune a kusa nace ta dama min ta Hamsim,haka ta dama furar tasha Nono me kyau da sugar, nace juye min ita a leda ki kulle,haka ta bani katon Dauri a farar leda na Fura da nono na bata ,sannan na siyi yogourt yar hamsim a leda tayi kankara,ina fara sha sai ga wani dan sanda yace Yarima yace Ku shigo ya ganku zai wuce Flight dinsa ya kusa tashi,da sauri mazan suka fada gidan yuuuuu,ni kadai ce mace haka na danna kai ciki ina Shan furata a leda yanda nake zuka kamar jariri ya kama Nonon uwarsa haka na lumshe ido ina tsotsa Malam ba ruwana.
Muna shiga ciki nan na hangame baki wajen kallon irin haduwa na gidan ba a magana,Saurayin muka hango chocolate dashi ya hadu sosai ga kyau ga iya wanka abin kallo yana kamshi yasha light blue shadda yana sheki ga motoci a gidan birjik,muka karasa gabansa yana zaune a wata farar kujera yana faman yanga da gadara,ido muka hada dashi yasha mamaki ganin harda yarinya haka,dan a wajensa bana Sahun yan mata
Ya fara sauraron wasu kawai muka ga Securities sun wani gigice sun nutsu waje daya tare da bude gate jikinsu na rawa,sai ga wasu motoci dalla dalla sun shugo gidan sun kai biyar kamar nasan motocin,ashe kuwa shine domin Saurayi Aayan ne me tashen kyau da Naira.
Gani mukayi Yarima ya fadada fara'arsa tare da mikewa ya tarbi Aayan da alama abokaine harda wani tafawa suna dariya,Yarima Bobo yace amma kai dan Iska ne Aayan tun safe kace zaka zo kasan yau zan koma Uk amma ka bata min time yanzu na daga flight dina sai 12am na dare,Murmushi Aayan ya saki cike da izza ya dage masa gira daya kana yace to ya akayi ne man sauri ka gama da mutanen nan naku kasan ban son jira,Yarima yace ai kai dan Iska ne ga sit can,kusa da mu ya zauna can nesa a wata kujera ta yan gayu,Juice aka kawo masa yana korawa,a raina nace Allah sarki talakawa mu ko ruwa babu me bamu.
Yarima yana ta ganin mutane yana sallamarsu da kudi,sai yace pls Ku mazane kuyi hakuri na sallami yarinyar can tunda macece,a raina nace Ashe yana da kirki,nan yace ke zo naji na sallameki sai lokacin Aayan ya kalli inda nake muka hada Ido,da mamaki ya kalleni lallai yarinyar nan wato har maula take zuwa gidan masu kudi sabo da son kudi,ko dai bata da iyaye ne oho,yana gani na karaso gaban Yarima ba tsoro na durkusa gaban Yarima tare da cewa ina yini?yace lfy tashi tsaye ki fadi abinda ya kawoki sauri nake ina da bako,ina durkushe a gabansa kaina a kasa kuma ina ta zukar Fura ta kamar yarinyar yaye,idan nayi magana daya biyu na zuki furata,babu wanda baiyi dariyar abinda nake ba kowa yana ganin